Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 26 / 27

zai tashi, Ayya na roke ki, ki saki ranki, ki yiwa dukan lamarinnan kyakyawan gani, ki bashi matarsa su tafi, Galala take dubansa har ya karasa maganar ya mike ya nufi fita, Kuma juyowa ya yi ya ce" Walyn ce ta ba lafia, zan je clinik Damuwarta ta nuna da yi masa adu.a, taso ma binsa aman ya nuna ta yi zamanta dan yayi imanin in dai Walyn na cikin hayacinta sai ta batawa mahaifiyarsa duda tana boyewa shi ai ba makaho bane, Yana fitowa ya tsurawa kofar Agaishat ido, wani abin na tunzura shi ya je wani na hana shi, A hankali ya taka ya je kofar dakin ya tsaya, Hannunsa ya dora saman abin budewar ya lumshe ido, Da sauri ya saki ya juya sai dai me Alhinayett ce tsaye, bai san lokacin da ta hayo ba, bai san ko tun fitowarsa take wajen ba, idannuwansa sun rufe, Hade fuska ya yi tam irin karma ta ga fuska ta kawo masa raini, Rabata ya yi ya fice ya sauka kasa inda ta bi shi da wani irin kallo, Hannayenta biyu ta dora saman kanta, ta shiga girgiza kai da yaren buzanci ta ce" na shiga uku Nauyin baki ya saka aminina tafka barna, Wardugu me ka aikata haka? Tura kofar Agaishat ta yi ta shiga da salama, Agaishat dake kwonce saman bed ta mirgino tana amsawa da murmushi shinfide a fuskarta tana duban Alhinayett, A nitse Alhinayett ta karasa kusa da Agaishat inda ta mike zaune tana duban yannayinta, Hannayenta Alhinayett ta kamo tana dubanta cikin yaren buzanci ta ce" Tarhanine (masoyiya), ina son mu yi magana da ke. Agaishat ta bata hankalinta sosai , Alhinayett ta ce" ban taba aure ba, aman a islamiya an fada mana irin girma da darajar aure da kuma girman ikon miji a kan mata, Sunna ce ta ma.aiki, daga lokacin da aka daura aurenki maganar mijinku ta fi iko kanki fiye da ta iyayenki, kin ga kuwa banban nauyi ne da bawa zai kasa rintsawa idan ya tuna, A yanzu ba maganar kina sonsa ko bakya sonsa, ba maganar ke wata ce ko wani ya tsaya maki, in dai mace na tsoron haduwarta da ubangiji to ya zama dole ta gane itace karama mijinta ne baba, ta yi masa biyaya. Agaishat, ki yiwa Mu.azam biyaya, kin samu tarbiya domin zaman da nayi da ke na dan lokaci jifa jifa ban ga rawar kai , tsayaya a tare da ke ba, zan so mijin aurenki ya yabe ki, ki ci gaba da girmama Ayya domin uwace a gare ki, ki nuna mata hankalinki ya kwonta da auren ko natama zai kwonta, kar ki tsananta bincike Agaishat, ke dai ki yi ta rokon Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi, Tunda ta fara Agaishat kallonta take, ita sai yanzuma tsoro ya shigeta, aure, aure, bautar Allah, sunnar ma.aiki, da tana tunanin ta yi nisa da iyayenta a hankali hankalinta ya kwonta da su Ayay harma ta samu gurbi mai girma ta basu a zuciyarta, aman yanzu gashi an mata aure? Kuma bama a kasar zasu zauna da mijin ba domin Mu.azam na shirye shiryen su daga da Agaishat ne? Hannayen Alhinayett ta damke tana dubanta ta ce" *ina jin tsoro, bana son barin su*, A hankali ta dora kanta saman cinyar Alhinayett inda ita kuwa take dan bubuga bayanta alamar rarashi Yana zuwa kai tsaye office din likitan ya je, wanda ya tataba za.a mika takardun matarsa can ne dan hatsari ne Gaisawa suka yi inda likitan ya nuna masa wajen zama, Labarin lokaci da yannayin da aka kawota ya bashi, inda ya ce" tanada shigar yaron ciki ne kuma ta karya da cokacola mai karfi bata ci komai bayan hakan ba, Shi ya hadasa mata ciwon ciki mai tsanani ko nace mara hakan ya saka gudan jinin ya shiga barazanar zubewa, tana cikin wannan halin ta samu hatsarin domin ciwon ya girmami nutsuwarta, A hankali ya dago da idannuwansa ya sauke kan doctern, idannuwansa ya lumshe yana jin wani irin dadi na ratsa shi, ciki, a daidai lokacin da ya rasa wani abin ya samu wani, Murya a kausashe ya ce" *Cikina, ba abinda ya samu cikina?* To faπŸ˜”πŸ˜”πŸ˜”, na zama raguwa, tun safe nake tsakurar rubutun nanπŸ˜”πŸ˜”πŸ˜”πŸ˜”πŸ˜”πŸ˜’πŸ˜’πŸ˜’πŸ˜’πŸ˜’πŸ˜’πŸ˜’ 🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* 4️⃣8️⃣ Da sauri docter ya bai Wardugu amsa gamsashiya tare da nuna masa echo din cikin, cewar bai yi kwari ba ya so zubewa aman Allah ya tsayar da shi, dan haka a kiyaye du wani abinda zai zo mata da garaje har ya zauna ya yi kwari, Kansa kawai yake gyadawa kafin ya mike ya nufi number dakin da aka fada masa take Yana zuwa ya kwonkwasa , bai tsaya an bashi izinin shiga ba ya tura ya shiga, Walyn ce zaune tana rusawa mahaifiyarta kuka inda uwar ke fadan da bai fahinci na meye ba, Gannin mai shigowar ya saka gaba dayansu sukai kit suka daina maganar inda Wardugu ya nuna tamkar bai ga abinda suke ba, A hankali ya karasa wajen kujerar dake dan nesa da su inda mahaifiyar Walyn ta saki hannunta ta mike daga kujerar dake kusa da walyn din tana mai son ta bar dakin A nitse ya gaisar da ita inda ta amsa kafin take barin dakin tana jin wani irin haushin Walyn, ta sha jus din nan ne dan cikin ya zube, da ba.a yi gagawar kawota asibiti ba da tabas sai mai afkuwa ta afku, bata san wa zata fadawa dan ya tsoratar da Walyn ba domin ba wanda take tsoro! Bayan fitar mahaifiyarta a hankali ta kwonta saman bed din tana kallon sama, Wardugu dake yi mata kallon kasa kasa ha jima a haka kafin yake tasowa ya dawo kujerar dake kusa da ita ya ja ya zauna, Rigar jikinta ta atampa wace akai mata dinkin zamani ya dora hannunsa wajen mararta ya samu ya dage rigar a hankali, Lalausan hannunsa ya dora saman mararta, a hankali ya shafa ya jara shafawa, ba zai gane komai ba shi dai yanda cikinta yake ne bai wani canza ba, tana da dan teba kadan, ko dan an ce cikin bai girma bane? Kalonsa ya maida wajen fuskarta a hankali tamkar bai so magana ba ya ce" ina son cikina Walyn, kema kina so? Wani katutun abu ya tsaya mata a makogwaro, ina ita fa ba zata iya wannan lamarin ba, ka haifi dan uban ya dawo sonsa fiye da kai, ba zata iya barin wannan cikin ba duda kuwa azabar da ta sha, Gannin tana ta yamutsa fuska ne ya saka shi kara kusanta kansa da ita ya ce"wani waje na maki ciwo ne? Da haushi haushi ta dube shi ta ce" tun cikin bai zama gudan jini ba, ba.a kai ga halitarsa ba, har ka fara manta abinda ya dace ka fara damuwa da shi? Har ka fara manta nice damuwarka ta farko domin nice zahiri? A hankali ya janye hannunsa daga wuyanta yana dubanta da wani irin yannayi, tafia ya yi ya dawo basu wani hadu ba, tun maganar da ta yaba masa a agadez basu wani hadu ba, shima ya shareta ya shiga harkokin gabansa, yanzu sun hadun zata wani saka shi gaba da hayaniya kamar yaronta, du irin murnar karuwar da ya samu da dokin da ya afka sai ya ji lokaci guda ya dishe, dubanta ya yi irin na tsai din nan, Hannunsa ya saka a aljihun doguwar jalabiyarsa ya ciro cart dinsa ta bank, Ajiye mata ya yi nan ya juya ba tare da yace da ita ufan ba, Tana kallonsa har ya fita a dakin, Ba.a jima ba mahaifiyarta ta shigo dakin tana dubanta , Wani uban tsaki ta ja ta ce" kin masa haukan ne? Walyn ta dafe kanta ta dauki cart din ta mikawa uwar ta ce" Ma, ga abinda kike nema! Plz kama ki barni na ja numfashi mai dadi! Yannayin maganar walyn, da irin furucinta bai taba zuciyar mahaifiyarta ba, hasalima dokin karbar tikitin bankin Wardugu ya sakata sakin murmushi ta karba ta fita da hanzari bayan ta shaidawa yar zata turo a tayata komawa gida ta karbi code number dinsa. Bayan ya karaso gida dakinsa ya shige, Yana shiga ya cire rigar da ya kusan wuni da ita ya kaita wajen injin wankinsa ya ajiye ba tare da ya wanke ba dan hankalinsa ba nan yake ba Dawowa ya yi ya shige bayi ya yi wanka ya dauro alwallah, Sallah ya yi a nitse, bayan ya salamce ya mika hannu ya dauko wayarsa android ya kuna, Yana kunnawa data na hawa domin baya kasheta kwata kwata, Ba.a jima ba messages suka shiga shigowa na mutane daban daban, tun daga abokan aiki, manyan mutanen da yake hulda da su, da yawa kan harkar mota ne da yake siyarwa, wasun kan kamen da ya yi ne watani da suka shude, wasun baima bude ba dan bakin number ne, Yana bin messages din yana karantawa sai dai baya bada amsa, Nan ya fita ya shiga Facebook, roger banasaran da suke harkar motoci da shi ya masa sababin zubi, zubi na sababin motaci na manyan mutane, Yana dubawa ya ga number yarinyarnan dai sai kara turo masa gayata take , a whatsupp ma sai message take turo masa tana karawa, Fita ya yo ya koma whatsupp ya shiga message dinta, Duka kalamaine na rarashi, da magiyar ya kulata, da yannayin kaskantar da kai, wai ita BASMA yar gidan minister, Hotunanta da take ta turo masa ya bude, A hankali ya tsurawa hotunan ido yana kallo, Kansa ya girgiza ya fita ba tare da ya bata amsa ba, Mesage ta turo kamar haka" du bakin da zai furta kalmar so ba makiyi bane, sannan adini bai haramta mace ta nuna tana son namiji ba, kuma ni ban roki wayar gari da kaunarka ba, kar ka ja zuciyata a kasa dan Allah ya baka dama, Mesage din yake bi yana karawa, bai iya bata wata doguwar amsa ba sai mikewa ya yi da wayar a hannunsa ya haye saman bed dinsa ya kwonta ya jawo pilow ya dora kansa, a ransa ya ayyana" haka fa suke idan suna so, da dama ta same su sai su fara gwada halaya na rashin tarbiya da hadama, Yana kokarin neman baci wayarsa ta shiga ruri, Kansa ya shafa yana jan tsaki, Kin kula wayar ya yi sai da ya ga mai kiran ya fishi naci ya dauko wayar ya daga yana fadin" ai aikin nan sai kai daman! Mu.azam ya yi murmushi, ya ce" me tace da kai Wardugu, Wardugu ya yatsina fuska ya ce" wace fa? Mu.azam dake zaune yana hangen shige da ficen Agaishat kicin tana girki ya ce" wardugu mana, bakuwata man Wardugu ya bude idannuwansa ya ce" meye tsakaninka da ita bayan amintaka? Mu.azam ya yi tsam gabansa na dan faduwa, a hankali yake goge zufar da yake ya ce" amintaka ce mafi kusanci, Budurwarka ce? Wardugu ya kaste shi, Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya, ya kasa magana hakan ya tabatarwa da Wardugu zarginsa Ransa ne ya ji ya mugun baci, hannunsa ya jimke ya kaiwa garu duka ya kausasa murya ya ce" dan me ka shigi yarinyar mutane bayan ka san amana ce? Mu.azam ya mike zumbur dan yannayin muryar Wardugu ya shaida masa ransa ya baci, A nitse ya ce" ka kwontar da hankalinka Wardugu, bamu yi soyaya da ita ba, itace ke so na, bamu tana soyaya da ita ba, ban zowa Agaishat dan na cuceta ba, kuma ba zan taba gigin cutar nata ba, Wardugu dake tsaye shima ya dafe gaban goshinsa, baya jin zai baiwa Mu.azam amsa a wannan maganar, Mu.azam ya ce" Wardugu, dan *ina sonta* na aureta, Wardugu ya matse karfen jikin bed dinsa yana rintse ido, kansa yake ji na mugun sara masa, hakama juwa na dibansa, Mu.azam ya kara sasauta murya ya ce" ina son mu tafi , na san ka san komai game da abinda yarinyar nan ta zo da shi, Wardugu koda ban auri Khadija ba tana da darajar da ba zan misalta maka ba a raina, tamkar yar uwata na fauketa kamar yanda na dauke ka, zan bita a min aikin nan, idan Allah ya yi na rayu zan tashi na rayu da *Matata*, idan ban rayu ba na san zaka kula da *Iyalina*, gobe ake bani passport din Agaishat, Khadija bata zo ba sai da ta shirya domin komawata da shigana block duka ta irga min kwana tara ya yi saura, Wardugu ka...... Wardugu ya katse shi da wani irin yannayi ya ce" *Zaka rayu in sha Allah*! Ku ci gaba da shirin tafia, in sha Allah ina nan za.a shiga aikinka, zaka rayu Mu.azam...... πŸ˜” *β˜€IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌀* ____________________________________________ *Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🀝🏻😘 🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* 4️⃣9️⃣ Bai jira amsar Mu.azam ba, Wardugu ya silale yana dafe kansa, a fili ya furta" *ban shirya ba, ba zan iya dauka ba, bani da karfin kokowa da hakan, sannan haramun ne a gareni, ya Allah baka dorawa rai abinda ba zata iya dauka ba, Allah ka cire min wannan gingirmin mikin , domin ni dai ban saba ba*!!!!! Timiya Duniya sabuwa ce ta budewa Ba, wannan karon da sabon salo domin kuwa tafe yake da isa da takama da nuna kansa a matsayin uban *BAk'a*, Anna dubansa kawai take idan yana abubuwansa, bata taba buda bakinta tace da shi uffan ba, a cikin kudin ya basu million guda wada Mariama ta karbe , ya canza masu katifa ya kawo masu buhun dawa guda ya yar masu sannan ya shiga fakar takun Anna yana so ta koma turaka Kamar yau, zaune suke su hudu domin Gaishata ta zo masu , labari suke duka yawan zancen a je a dawo ne a tile kan maganar Agaishat, Anna ta sauke ajiyar zuciya tana dubansu ta ce" mahakurci mawadaci, du wanda ya ce zai yi hakuri Allah ba zai bashi kunya ba, sannu sannu kuma bata hana zuwa, sai dai a jima ba.a je ba, Gaishata ta yi murmushin itama da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe ta ce" ni abinda ke bani mamaki Ba, wai shine har yake yi mana kallon mutunci? Mariama ta tabe bakinta ta ce" na dan lokaci ne, idan kudin hannunsa ya kare zai dawo kamar da, Anna ta ce" ki daina mumunan zato Mariama Mariama ta yi mata wani malalacin murmushi dan kar ta yi fada, Suna tsaka da zancen sai gashi ya shigo yana jan arzizimin wando bakinnan kuwa jajajir sansani su ta bata shi, Bai yiwa yaren magana ba sai Anna ya kalla ya yi kiranta ya shige dakin Da kallo suke binta dan gannin zuwa zata yi kuwa? Gani sukai ta mike ta nufi dakin ba tare da ta yiwa kowa cikinsu magana ba Tana shiga ya damko hannunta yana washe baki ya ce" Ke bakya marmarina? Kin jima baki neme ni ba, kin ga baki fice haihuwa ba, ki zo mu kara samun wata Bak'ar, ina son samun yarinya a gidannan, Sakai kawai ta yi tana dubansa, kanta ta girgiza ta janye hannunta ta juya da niyar barin masa dakin Ba da yannayin fushi ya ce" in kika yarda kika fita a dakin nan , sai na nuna maki na fi yan yamai *Niamey* iya rashin kunya! Wani irin birki ta ja ta juyo da madaukakin tashin hankali da kuma tsoron da ya bayana karara a fuskarta, Bakinta ta buda zatai magana sai dai ina jini ne ta shiga bin hancinta, juwa ta kwasheta ta zube nan tana fida wani irin numfashi Karar faduwarta ya saka Mariama mikewa domin da marfin kwano a hannunta marfin ne ya kai kasa ya bada kara wanda sam Mariama bata yarda da shi ba dan haka da hanzari ta fada dakin tana mai kiran sunnan Anna, Tana shiga daidai Ba ya kai kasa zai kamata jikinsa sai rawa yake, Da mugun gudu da taratsi ta ce" kar ka tabata, kar ka taba mini uwata! Bai sanma tana yi ba, shima fama yake ya ga ta mike, yau dai haukansa ya kaishi taka dokar da aka dodora masa na ya kiyaye kama mata sunnan garin haihuwarta, ya kiyaye du abinda zai alakantata da garin makarin duhun kan Anna shine Ba ya kusantata da asalinta, ya kama sunnan garin haihuwar Anna garin neman jarabarsa, Ihun da Mariama ke yi masa ne ya saka yan uwanta shigowa suma a guje sunna nufar inda Ba da mariama ke turayar juna kan sai sun taba Anna Gaishata ce ta dora hannayenta saman kanta da karfi ta ce" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Ba Mariama ku dagata ku dagata na ce! Tsai Ba ya yi , jikinsa na rawa ya nufo Gaishata tamkar zai maketa ya raba ta gefenta ya fice a gidan yana dumumuwa shi kadai , Da kyar suka iya cicibata domin Gaishata ba wani kokari zata iya yi ba sai su biyun ne suka iya kamata suka dora saman tabarmar kaban dakin Hurhutu suke mata suna shafa mata ruwa aman ko motsi, sai numfashinta dake fita a hankali iamar a cicire ta samkame ita ba gawa ba ita ba rayaya ba, Gaishata ce ta ciciba ta mike tana jin yanda mararta ke wani irin juya mata ta nufi kofa tana takawa da kyar tana saurin da zata iya ta nufi fada Tunda ta karaso dogaran sarki ke mata sannu inda aka sakar mata hanya ta shige fadar suna mamakin ganninta domin sarki ya hanata zuwa fada kar a kake masa ita, Kanta tsaye ta nufe shi inda ya mike da sauri daga kujerar mulkinsa dogarai suka shiga baza manyan rigunansu suna kare su, yan zama fada suka fara darewa da sauri sauri Tana isa jikinsa ta zube wanda sukai taga taga dalilin kibar da ta kara ga kuma tsohon ciki, A hankali ya samu ya daidaitata a jikinsa ya dora hannunsa inda ta dora nata wato saman cikinta da take ji baki daya yana wani irin yamutsa mata bayanta na sarawa, Me ke damunki Gaishana, Ya fada yana mai

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 26

WAReaders TGUpdates