Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 7 / 27

tas, Ayya ce ma baka domin Ayya baka ce mahaifin wardugu ne farin batube shima tas tas tas , sai sojan dake saye da kayan sojoji komai harda bindigarsa da katon takalmin nan nasu da komai sai muzurai yake Sarki ne ya amsa gaisuwarsu kafin yake kai dubansa bukar Sofo, Bukar kanta ta tsufa du ta zuzube sai abinda ba za.a rasa ba, ga dati sosai a dan nesa da wajen domin an yi rasuwa baka bata samu zuwa ta share masa ta gyara masa ba, Ruwa kawai take zuwa ta dauko masa ta koma Nuna masu wajen ya yi bayan ya samu ya shiga ya tarar yana zaune saman buzunsa da carbinsa yana ja ya kurawa waje guda ido yana ta istighfari(Allah ka bamu nitsatsen tsufa in muna da rai wanda zai kara kusanta mu da kai ya Allah) Gaishe shi ya yi ya juya inda sofo ke bin kofar da kallon mamaki, me ya kawo Sarki har wajena? Kuma hayaniyar me nake ji haka? Ku shigo; Sarki ya fada yana dubansu wardugu ya ce" anya kuwa? Me zai hana ya fito??? Ayya ta kallo shi ta ce" Wardug..... Da sauri ya yi gaba ya fara nufar yar bukar sofon a ransa yana ayyana ai idan Ayya ta nadaka toh fa tana yi da kai Shishiga sukai banda sojan nan, Walyn na saka kanta ta yi baya tana kakarin amai da coshe hanci, a fili ta furta" kai ina , ba zan iya ba! Ayya ta karasa a hankali kusan tsofon dake zaune ya zuba masu ido gaba dayansu yana mai binsu da kallo, ko gezau bai yi ba daga zaman da yake sannan yana jan carbinsa cikin nutsuwa A hankali ya amsa salamar Ayya da ta nufo shi cikin nutsuwa ta tsugunna dan nesa da shi aman suna facing din juna A hankali ta ce" lokaci mai tafiyar da abubuwa, lokaci mai bayanna abubuwa, lokaci mai rarabe abubuwa, Baba tsufa ya zo haka? Allah ya sa mu cika da kyau da imani Murmushi ya yi na gano wacece ita, tabas ya ganeta, idan ba zai manta ba shekaru sun kai talatin da suka shude ya sha kai mata magannin athsma na yaronta da bai fi shekara hudu a lokacin ba tana karbar masa aman ya ki karbar komai da sharadin sai yaro ya samu lafia Murya na rawa baba tsoho ya ce" y'ata ke ce a garin timiya? Ya jikin yaronki? Na koma ban same ku ba sai na yi adu.ar Allah ya sa ya warke Ayya da murna ta janyo hannun Wardugu dake tsaye kikam ta ce" baba ai gashi, kana ganni soja ne, cikin ikon Allah magannin nan mun ji dadinsa, nima a raina kake, na nemeka Allah bai yi ba, kwanan nan na yawaita mafarkinka, a sifarka ta da hakan ya daga hankalina na saka aka nemo min inda kake, shi ne na zo na yi godiya sannan na yi salama kamar yanda na dauki alkawari, Baba na murmushi yana kallon wardugu wanda shima zuwa lokacin ya risina, yana kallon tsohon yana kidaya shekarunsa a ransa, ya yi imanin a kadan ya linkasa uku da rabi, Baba ya maido kallonsa wajenta, kafin yake bin dakin da yake zaune da kallo, ya yi murmushi bai ce komai ba Ayya ta ce" Baba ka yi magana mana, Baba ya dago yana dubanta ya ce" kaya y'ata, ki dubi dakin da nake ciki a zaune a yanzu, me ya rage min? Me zan yi da arziki? Kyakyawan karshe kawai nake nema, shekaruna dari da ashirin da uku a duniya a hasashe mai yiwuwa na fi, Kallonsa kawai suke suna masu adu.a a ransu, adu.a suke da Allah ya datar da su da irin tsufan nan, wanda zaka yi ram da kai da carbinka, Jikin ayya ya yi sanyi sosai , a hankali ta zauna a kasar dake dakin tana kallonsa, murya a sanyaye ta ce" haka ne baba, Allah ya sa mu cika da imani...... Aman na so na yi maka wani abin da zai faranta maka, da zaka aminta ma da mun tafi da kai mun kula da kai Baba tsofo da kansa ke kasa cikin rawaninsa ya dago yana kare masu kallo, ya yi imanin wannan matar da muguwa ce da bata bi bayan alkawarin da ta yiwa talaka futuk kamarsa domin ta san bai isa ja da ita ba domin zamani ya zama mai abu shi ne sarki, shi ya isa shi ke da magana ya dora doka, aman du ta manta ta tako ta ci gari da gari, ta ratso sahara du dan ta yi masa godiya sannan ta cika alkawarin da ta dauka,? Sannan ya san ba yar yankan kai bace domin ba da kansu suke nema ba kawo masu ake har gida, shi kam ji yayi gaba daya ya samu nutsuwa a zuciyarsa da shawarar sa, Murya a sanyaye ya ce" tabas ina da bukata mau girma baiwar Allah, sai dai ban san ta inda zan fara ba, banma san ko za.a dace ba, Hankalinta ta maida kansa ta ce" Mecece ita?????????????........ 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣5⃣ Baba cikin yannayin damuwa ya ce" me zai hana na baki auren y'a? A nitse ayya ta ce" Auren Ya baba? Baba tsoho ya ce" eh, domin shi kawai zan nema a bada yarinyar dindindin , Aman baba wace yarinya ce wannan?? Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce" yarinya ce mai tarbiya mai ladabi da biyaya, yarinya ce mai nutsuwa, bata da kwaramniya, inda aka ajiyeta ta zauna kennan sai an ce ta tashi, yarinyar nan ina jinta a raina tamkar yar da na haifa, a kulun damuwana na mutu na barta a wannan hali, tana cikin halin matsi dan kawai Allah ya yita *BAK'A* sai dai ni murnar hakan nake domin fatarta ya sa har ta kai warhaka sai dai har yanzu bata samu mijin da zai aureta ba a kauye ta girma sosai shekarunta goma sha takwas a duniya , Jim Ayya ta yi tana kallonsa, kafin take cewa " me dinka ce Baba? Baba tsofo ya kalli Sarki dake kallonsa shima cike da rausayawa, da wani ne duda tsufanda in dai yana iya magana yana gane wasu abubuwan da gudu zai karbe makuden kudin da aka baza masa, sai dai shi bawan Allah ta yarinyar fake tare da shi tun tana yar shekara shida a duniya yake, irin tunanin da iyaye zasu kwana su tashi da shi na gannin yayansu sun samu mijin aure mai nagarta wanda zai kula da yayansu, toh haka baba tsofo yake kasancewa, du motsinsa itace a ransa, tambayar kansa yake ina? Ta yaya? Wanene wanda zai rike masa Agaishat mudin ranta cikin mutuntawa da kauna? Ya hanga ya hango bai samu ba, har almajirinsa ya tuntuba aman ya watsa masa kasa a ido, hakan ya saka shi dukufa wajen kai kukansa wajen Allah, yana rokonsa da ya bili masa da hanya ta inda baya zato baya tsamani, ya bilo masa da hanyar da zata zamo alkhairi gareta,,,, Sarki ya ce" kanwar matana ce, Sunnanta *AGAISHAT* Kana nufin farar buzuwa? Ayya ta tambaya Sarki ya ce" buzuwar ce tabas, sai dai ita wannan Bak'ar buzuwa ce, Ayya ta kai dubanta wajen Baba Tsofo da ya yi kododo yana kallonsu, kallonta ta maida wajen Wardugu dake tsaye ya tsareta da ido yana jiran jin me zata ce,? Ya san halin mamansa, ya san Ayya da daukarwa kai, ! Murya a sanyaye ta ce" Warduggggggggg.......... Fuskarsa a hade ya ce" Lalalalala, Daga haka ya tamke fuska yana kallon su Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon kasa ta afka tunani (Tabas a al.adar Tubawa ba.a yiwa namiji auren dole, bake Wardugu, sannan idan namiji ya yi aure sai matarsa ta yi haihuwa kamar uku zuwa hudu kafin ya yi mata kishiya idan kuwa bata haihun ba sai ta dauki shekaru kafin ya yi mata kishiya, wannan haka ne ba ja, haka al.adar garin yake, ) Ayya ta kuma kallon su, ya zata yi? A hankali ta ce" baba, wannan yaron shi daya Allah ya bani a duniya, Sannan bai jima da yin aure ba, Ban ki ba, ina so idan da hali a bani yarinyar a matsayin yar rikona, yar amanata, in sha Allah zata ci abinda na ci ta kwonta a makwoncin da na kwonta ko wani iri ne, kafata kafarta Har Allah ya bata miji, zan yi dukan abinda ake yiwa ko wace y'a na kaita gidan miji sannan zan bi dukan lamuranta a gidan miji mudin raina Baba tsoho ya jima yana nazarin maganarta, baya shakun za.a bada AGaishat in dai sarki ya yi magana, damuwar shi ne: Agaishat zata so bin bakin fuska duda irin matsin da take ciki? Gida fa gida ne, sannan mahaifiyarta zata yarda da radin kanta a rabata da yarinyarta budurwa ba da wani dalilin aure ba ko dangi na jini haka kawai a tafi da ita tare da mutanen da bata sani ba? Ko wannan karon ma isar za.a nuna mata a kuma kwace mata *Y'A*? Duda haka baba ya kai dubansa wajen sarki, Irin kallon da baba ke yi masa sai da ya saka ya ji kunya, ya ce" abinda za.a yi, zamu kama baba a je da shi da ku baki daya ga mahaifiyar yarinya da mahaifinta, du yanda hali ya kama zuwa ya fi aike Sun lamunce da hakan inda Wardugu ya kama baba a hankali ya mikar da shi sarki ya kama masa suka fito yana dan dingisa kafarsa har suka karasa wajen motar inda sojan nan ya bude wardugu ya daga baba a hankali ya saka shi gidan gaba sarki ya shiga suka shishige gaba dayansu Walyn da binsa da kallon meye kuma haka? Shima kallon Ayya dai yake, Basu zame ko.ina ba sai kofar gidan Algabiitt ...................... ................. Anna, ki yi hakuri haka kin ji? Ki daina damuwarnan kin ji Anna? Agaishat ta fada tana miko mata gurasa ta kasa da aka kawo sadaka gidan mutuwar Anna ta lumshe idannuwanta bata karba ba ta bude tana kara bin yayan nata da kallo, Mutuwar nan da aka yi bai saka Algabiitt ya yi sanyi a lamuransa ba, ya sako Agaishat gaba dole sai ta yi shafe shafe itama ya samo mata miji kamar yan uwanta tamkar damuwarsa ta yi auren ne, Yarinyar bata isa ta wulga ba sai ya dura mata zagi Ya hana a yi zaman makoki sai yayanta dake zagaye da ita Amarya kuwa idan yau wannan ya zo ta ce dan uwanta ne , gobe sai wancen ya zo ta ce kaninta ne, ta mayar da gidan filin kawo kwartayenta ba tare da wani dar ba domin mai gidan ya bata lamuni.... Anna murya a shake ta ce" bana so ya kashe mini wani cikin ku, Mariama ta juyo fuska du ta yi mata ja abin kuka ta ce" to ki biyo mu mu bar masa gidan mana, dan mi ba zaki bi mu mu yi tafiarmu ba? Kin san abinda ke daure mu a nan ke ce, Hankalinta tashe ta ce" a duk lokacin da kuka ambata mini abubuwan nan biyu asalina da barin Algabiit bara ku ji na fada maku yau abinda nake ji! Ji nake tamkar lumfashina zai tsaya idan na ji an ce na bar inda Algabiit yake in dai ba da yawunsa ba, ji nake zan fada halaka, ji nake duniyara shi ne, ji nake in ba inda yake ba ba ni! Wani duhu ke rufe mini ido kaina ya dauki nauyi idan na takura sai na tuno wacece ni? Nakan fada damuwa mai tsanani juwa ta ringa dibana du idan aka yi maganar dangina, kun ji damuwata Suke suke kallonta, Agaishat (Bak'a) kanta na saman cinyar Gaishat, Mariama na zaune gefensu, Fatimata na jingine da garu tana facing dinsu, Jiki a sanyaye Fatimata ta ce" me ke damunki haka Anna? Wannan ba soyaya bace, Mariama ta kallota ta ce" wace soyaya? Ai koda an yita a baya a yanzu Ya kasheta da kansa, Me ke damun Annarmu? GAISHAT ta buda baki zatai magana sai ga Algabiit bugum ya fado dakin yana dan dudukewa dan tsayi Direct ya zarce gurin Anna bakinsa na rawa ya ce" sai dai su tafi da ke da tsinaniyar yar ki! Ba wanda zai kama ni, ba abinda na yi! Da sauri ta mike tana dafe kirjinta, tsinaniyar yarki ke mata yawo a kwakwaluwa, wacece kuma? Me aka yi? Su wa zasu tafi da su? Bata kai ga tambaya ba ya duko ya dago Bak'a da gashinta ya mikar da ita, Yawun bakinsa ya tatara mai cike da warin Sansani ya tofa mata a fuska ya ce" ga dan iskan tsohon da kike wuni wajensa tare da sojoji, to ki sani sai dai su kama uwarki Janyeta Anna ta yi da karfi sannan ta yo fallon nasu da sauri dan jin lafia? Gaba daya yayan nata suka biyota inda Algabitt ya labe yana leke yana kuma sauraron abinda ake fadi Da kallo Anna ke bin su, sukai mata salama suka shiga gaisar da ita da yaren buzanci, Ayya ta kalli wardugu dake karewa kowa na wajen kallo, ta ce" ban san bama da wani yare zamu tatauna da ita da alama buzanci kawai take ji Anna dake tsaye ta ji komai abinda aka fada da yaren da ba zata ce ga sunansa ba, kuma ba yaren da suka yi da likitan nan a asibiti bane............................................ 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣6⃣ Bata kai ga magana ba dogarai ke sanar da shigowar sarki falon sirikan nasa , daman da baba tsoho ma shi ke fasara tsakaninsu domin ba komai yake ganewa ba shi kuwa sarki ya zauna da tubawa Tunda ya shigo Anna ta sada kanta dan kunyar siriki, shima du a wani takure yake inda Gaishat ke binsa da kallo tana tambayar kanta me ya kawo shi ko bakinsa ne? Gyaran murya ya yi ya ce" Anna, ina fatan kin san baba tsoho, wanda Agaishat ke zuwa wajensa babanta kennan Daga inda yake ya daga murya da irin abin haushi haushi ya ce" ya zata manta kwartanta uban yarta? Ai ni dama na san dubunki sai ta cika munafuka, yau dai ga zance zai bude Da wani irin yannayi Wardugu ya kai dubansa daga inda ake maganar, wa ke magana ta rashin da.a haka? Shine abinda yake tambayar kansa din wardugu na jin yaren buzanci kai bama buzanci kadai ba wardugu irin mutanen nan ne masu kwakwaluwar kwashe yaren da ba nasu ba, yana jin yaruruka da dama, hakan ya bashi damar jin abinda ake fada harma wanda Algabiit ke aikowa daga daka Sarki ya girgiza kansa kawai, ya san wanene Algabiit farin sani, kuma fa ya san harma gudumuwarsa wajen Algabiit ya tsula tsiya a garin aman ba komai zai dauki mataki ne tun kafin ya saka a tarwatsa su baki daya Anna da ta kasa hada ido da shi ta gyada kanta, ya zata kasa gane mutun mai daraja a idannuwanta? Wannan mutumin ko dan tsufansa a girmama shi aman Algabiit ke aiko masa da zagi haka? Ta yi imanin ba ita ba ko Algabiit din baba tsoho ya haife shi Bak'a kuwa tunda ta kyala ido ta ga baba tsoho ta samu ta rakube jikinsa tana dan jefo masa tambayoyi a hankali da alamun tsegumi Hannunsa ya saka ya dungure mata kanta yana murmushi, a ransa ya ayyana idan kika tafi,....nishadina, murmushina, zai tafi da ke Sarki ya ci gaba da fadin" wadinnan mutanen da kike ganni, wannan baiwar Allahm mahaifiyar wannan bawan Allahn ce, sannan ta taso tun daga garin da kuka kai Fatimata rashin lafia ta zo Agadez daga nan sun dauki hanya sun zo garin nan dan neman baba sofo da ya baiwa dan nata maganin huka tun yana yaro bisa alkawarin idan an samu lafia sai ta bashi abinda ya samu Toh Sai aka tashe su Allah bai yi sun kara haduwa ba, tun daga lokacin take nemansa domin mutun ce mai son cika alkawari abin na tsaye a ranta sai yau Allah ya yi Dan numfasawa ya yi, ya ci gaba" kin ga, ba a niger ba, ko a kasar waje masu fada a ji ne, Sun zowa Baba sofo da alkhairi na mamaki sai dai abin mamaki baba ya ce sam shi yanzu ba ta abin duniya yake ba, ya yafe sai dai damuwarsa *AGAISHAT CE* Anna ta dago da sauri ta ce " AGAISHAT? Sarki ya ce" kwarai kuwa, Baba ya nemi alfarmar......................................................gaba daya sarki ya kwashe yanda suka yi baba da su Wardugu ya fadawa Anna dake zaune kanta na kallon kasa sauran yayanta na zagaye da ita Bak'a kuwa na jikin Baba sofo Da sauri Bak'a ta dago ta kai dubanta wajen Anna da Sarki, ta maida dubanta wajen baba Sofo, Baba Tsoho ya yi gyaran murya ya ce" shakuwa, da tunani ya hana ni sakun nutsuwa Annar Agaishat, na sani bani da ikon zartar da hukunci kanta domin ban haifeta ba sannan ni ba wani shakikikin dan uwa ba A duniya adu.ata biyu ce, Allah ya sa in gama da duniya lafia Aljanna ta zamo makomata , fatan Allah ya nuna min ta zama mutun mai cikaken inci, ta samu nutsuwar zuciya , ta samu zama itama mutun, Anna Agaishat ta yaya hakan zai faru? A timiya mu duka bamu fi kirgo da yatsu ba, nan da kike ganina har limamin garinnnan na nemi alfarmar ya aure man ita mana aman ya nuna aa ba zai iya ba Almajirina ma ya kiye min, Gashi yau da gobe sai Allah, Agaishat girma take, mu kuwa gajiyawa muke kara yi, Idan ta fito daga nan ina ta fada? Me ta ci? Ya ta yi ta samu Allah ne masanin gaibu, ni kam a matsayina da wanda take zuwa wajensa sannan ta

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 7

WAReaders TGUpdates