Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 9 / 27

ba Wardugu ya samu dan bakinki da farin mahaifinsa sai ya samu kalar fatar nan ta yan ethiopia baki ga yanda fatarsu take ba? To aman wannan yarinyar kina ganni da akace wanka ta saka kuka aman kika biye mata wai kika rakata ta yi baci a haka? Anya kuwa zaki iya wani gyarata? Ayya ta ce " ki saka ido kawai..... Sojan nan tafiya dai yake aman ba karamin gajiya ke tatare da shi ba, sai ya ga Wardugu daga kafa kawai yake yana jefawa yana kara kutsawa cikin duhun garin suna ta sauki su karasa hotel din Ba su su karasa ba sai kusan sha biyu na dare, Suna karasawa Wardugu ya saka kai kai tsaye ya nufi shiga wajen da idan ka shigo harbi ne zai salamo maka .................... Kadan ne ku yi maneji😍😍😍😍 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣8️⃣ *Godiya ta tabata ga Allah sarkin sarauta ubangijin talikai, godiya mai dumbin yawa gareku da adu.a Allah ya saka da alkhairi ya biya ....* *Khadijat tawa ta grup BAK'A CE* wannan page din naki ne Ja sojan ya yi ya tsaya bai san lokacin da ya ce " Oga, zone interdite ce fa Wardugu ya juyo yana kallonsa, ya yi murmushi ya ce " tsoro kake ka mutu sergent? Kansa ya dan shafa yana kallo Wardugu, wardugu ya kara cewa" mutuwa fa ko kana kan gadonka sai ta daukeka sergent ba gwara mu tunkareta ba? Kara kwalalo idannuwansa ya yi yana kallon wardugu Wardugu ya matso ya dafa kafadarsa ya yi murmushi ya ce" mu je ...... Haka suka kutsa gaban Sergen din nan tamkar ya bale ya fado dan tsoro, Sai dai ga mamakinsa sai ya ga sun kama wata yar raga a nan Wardugu ya bude ya shige Shima shiga ya yi yana ta waige waige yana biye da wardugu nan ya hango ashe har sun shiga balbalin hotel din sun fice hatsarin Wara wawar ajiyar zuciya ya sauke yana biye da wardugu Wardugu ya rage sauri ya dan rage sautin muryarsa ya ce" nima bana so na yi mutuwar bindiga fa Sergen, ina so na mutu cikin nutsuwa kai da zabi gareni in mutu ina sallah kuma ranar juma.a, Aman kawai yau ranar asabar gatsai gatsai sai mu tarbi mutuwa? Da juma.a ne ma, Ya dan yi murmushi ya yi gaba ya barshi nan tsaye yana murmushin shima, kai ogansa idan ya yi wani abin tamkar ba shi ba, wai shifa a nan wasa ya yi masa da rai🤔 Tun fa wuri ta farka daga bacin da ya saceta, sai dai ta ki motsawa tun a jiya da aka sauketa saman gado ta yi baci ta kasa ta sauko kasa ta kwonta saman farin tls din ta rufa da mayafinta na turkudi tana kallon yanda pankar sama ke juyawa har baci ya dauke, a yanzuma ta farka tun da wuri tana son tashi sai dai tsoro take hakan ya sa ta yi kuri da abin mamaki a fuskarta tana kallon pankar nan, mamaki take menene? Ya aka yi bai daina gudu haka ba? A gaban idannuwanta aka kunna , tunda ya dauki gudu bata ga ya tsaya ba, ita tsoroma take ya yo kasa kasa ya kasheta Ayya ce ta bude dakin ta shigo da salama a bakinta Firgigit Bak'a ta tashi ta zauna jikinta jikin garu tana bin Ayya da kallo Ayya ta yi tsam itama tana karantarta, a kasa ta kwana du sanyin nan na kasa, sannan da alama bata yi sallah ba Dukawa ta yi kusa da ita tana kallon yanda take jan mayafinta tana lulubawa a jikinta, Murya a sake ta ce" kin yi sallah? Da ido kawai Agaishat ke bin Ayya domin bata san me take fada da yaren tubanci ba Ayya ta yi dabara ta kamo hannun Agaishat ta mikar da ita ta jata suka nufi bayi Suna shiga Ayya ta dauki butar karfen dake wajen ta kunna ruwa mai dumi dumi ta cika mata ta nuna mata wajen da zata iya dukawa domin ta san ba wani gane lamarin wc zarai ba tukunnan dai, ta yi mata nuni da ta yi dagara ta yi alwallah ta yi sallah , ta yi mata nuni da har rana ta fito Da kai Agaishat ta amsata tana kallo sai da ta fita ta duka ta yi fitsari nan inda aka nuna mata ta wanke jikinta ta mike ta yi alwallah tana jin dadin yanda ruwan keda dumidumi Tana gamawa ta fito ta ga salaya aman ba kowa a wajen dan haka ta hau ta tayar da sallah ta yi abinta cikin nutsuwa kamar yanda Baba tsofo ya koya mata Tana gamawa ta zauna ta hade kanta da gwuiwarta tana zubar da hawaye, tunani take ya Anna ta tashi? Ya yan uwanta? Ya baba sofo? Wa zai kai masa ruwa? Wa zai gurza masa goro? . ..... Buda kofar aka yi aka kuma shigowa , Wannan karon matar sarki ce da wata baiwa buzuwa da kuma Ayya Ayya ta kali matar sarkin ta ce" so nake a fada mata ina so ta yi wanka ta shirya mu tafi garinmu domin Wardugu yace jirgin karfe daya zamu bi Matar sarki ta yi murmushi har yanzu tana mamakin daukarwa kai irin na aminiyarta, ita da ko hausar juna basu iya ba Ta kali baiwar nan cikin isa da dakewa ta fada mata abinda zata fadawa Agaishat wace tunda matar sarkin ta fara fadi take kallonta daga zaunen da take tana fahimtar yarenta Kafin ma baiwar ta fadi Agaishat ta kallo Ayya, a hargitse ta ce" ina zamu tafi kuma? Kar ki kaini wani wajen kin ji? Ki barni a nan ma Tana fada ne tana dan nufo su Ayya dake tsaye Baiwar ta yi saurin tareta , da yaren buzanci ta ce" ki tsaya nan, kin san ina ne kike a nan? Kina garin agadez, a garin agadezma kina masautar agadez, a masarautar agadez ma gaki gaban matar sarki uwar gida sarautar mata, Ki koma baya ki cika umarninta Rakubewa Agaishat ta yi tana kallonsu, ta shiga ukunta, ya zata yi? Matar sarki kuma? Ko sarkin garinsu talaka bai isa ya yiwa matarsa ko yayansa wargi ba bale na garin Agadez Kanta a sade ta ce" zan yi wankan Ayya dake tsaye ta karaso kisanta tana kamo kafadunta ta kallo aminiyarta ta ce" me ta ce mata? Sai nake gannin kamar ta tsorata? Kar ta tsorata min yarinya fa kar ta rikitata Anna dariya ma kawai yannayin Bak'a ke bata, ta fadawa Ayya abinda aka yi Ayya ta dafe kanta ta zabgawa matar nan harara ta ce" ku tafi abinku tunda dai ba zaku tausasa ba, idan ita sarauniyarta ce ke ni ai aminiyata ce, bana son irin yanda kike nunawa kan yarinyar nan, kina manta mutun ce itama ? Anna ta yatsina fuskarta ta ce" kin ga bara na je na ga in an kawo kayan da kika ce kina so, gaskiya ki yi hakuri ba zan iya wannan faman ba Ayya na kallo Anna ta juya baiwarta ta bi bayanta suka tafi Zaunar da Bak'a ta yi gefen gado wace ta takure waje guda, ta juya ta fauko wayarta ta zauna ta danna kira Ana dagawa ta ce" kana ina? Amsawa ya yi da" gani gefen aghali muna ratauna wata magana To ka bari ka zo yanzu yanzu nan bangaren da aka saukeni ina ciki ina jiranka Da toh ya amsa ya mike yana cewa Aghali ina zuwa 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣9️⃣ Shiga ya yi ya zarce dakin Ayya ya tarar bata nan sai ya fito ya shiga dayan dakin, daman falo ne mai daki biyu, Yana shiga ya tarar da ita tsaye , Bak'a kuwa zaune inda ta ajiyeta Karasawa ya yi yana tambayar lafia? Ta amsa shi cikin kulawa ta tambayeshi kwannan iyalinshi Ya yi murmushi dan ya san Walyn bata zo nan ba kennan wajen matar sarki ta je? Ayya ta ce" Wardugu, zo ka yi mana fasara da y'ata ka ji? Ina son yi mata magana yanda zata fahimta aman ban lamunce maka ka rikita min ita ba ka ji? Da mamaki yake kallonta, daman shine dalilin kiran nasa? Kai? Yanzu Ayya ya zata yi idan baya nan toh? Kai kawai ya dan girgiza ya karasa inda Agaishat ta kara rakubewa jikinta ya fara rawa ta nuna alamar tsoronsa take ji Ayya ta ce" Wardugu ka yi wani abin mana, ka ga tsoronka take ji, bana so dan Allah Wardugu ya sauke ajiyar zuciya ya kali Ayya ya kara kallonta, uwa uwa hummm Karasawa ya yi ya dan rage tsayinsa yana kallon yarinyar, kokari ya yi ya saisaita maganarsa ya ce" me ke damun ki? Kallonsa take ita kuwa, irin kallon nan na kana jiran gannin me za.ai maka Wardugu ya dan rontse idannuwansa ya bude ya ce" kin ga, mu fa ba mayu bame, ba mugaye bane kamar yanda kike tunani, mamanki tace mu zo da ke, idan kika kwontar da hankalinki kika nutsu sai ina kai ki kina gaishe da mamanki, kinga dai yanda kuka yi da ita ko so kike a mayar da ke ne?? Tsam ta yi tana kallonsa bata bashi amsa ba Ayya ta matso ta ce" me kake ce mata? Wardugu ya kali Ayya ya ce" ba komai Ayya ta ce" to ka ce mata ta tashi ta shiga ta yi wanka , ko na yi mata da kaina ma Ido Warsugu ya zaro, sai kuma ya basar, ya kaleta sosai ya ce" kin ce Sofo na koya maki karatu ko? Kai Agaishat ta shiga daga mai Ya ce" yawa, kuma sofo ya fada maki tsafta na cikin adini? Sai mai tsafta zai shiga aljannah fa Agaishat ta kara gyada masa kai, Ya fara jin haushin gyadegyadan kan nan, aman Ayya na wajen ta kasa ta tsare, ya tausasa murya ya ce" toh ki tashi ki shiga bayi, Ayya ta nuna maki kayan wanka ki yi wanka sosai kin ji? Kai ta kuma gyada masa ta mike tana kallon Ayya, tunda ta ji yace za yana kaita wajen Annarta zata gwada yi masu biyaya ...... Ayya da jin dadi ta rakata bayin ta kuna mata ruwa masu dumi sosai ta bata sabulu da soso sababi, ta bude bruch da maclean ta mika mata ta yi mata nuni da yanda zata yi , Har ta juya ta dawo tana nunawa ta ce" ki cuta jikinki lungu lungu sannan ki wanke tafin kafafuwanki kin ji Kai Agaishat ke gyadawa har Ayya ta gama ta fice A hankali ta tube kayan jikinta, ta yi tsaye gaban ruwan tana kallon yanda yake zuba Da tsoro tsoro ta tara hannunta ta janye, ta kuma tara ta janye hardai ta yarda da ruwa ne ke zubowa kuma ba zai konata ba A hankaki ta shiga tana bismillah a ranta ta yi tsaye ruwan ya shiga kwararun mata a jikinta tun daga kanta dake da kitso kwaya daya tal har jikinta Sai da ya gama dukanta ta dauki sabulun ta shiga gogawa a jikin soson tana jin yanda kamshinsa ke tashi tana jin dadin kamshin A hankali ta shiga cuda fuskarta da soson nan ta cudeta da kyau ta darwaye kafin ta shiga wanke wuyanta sosai da bayan kunnayenta da cikin kunnen ta gangaro hamatarta kamar yanda Ayya ta nuna mata ta daga ta kama dirza ta yi kasa ta wanke jikinta sosai ta bi ruwan nan ya shiga darwaye mata kumfar da har ta zama baka dan tsabar datin dake jikinta, tana kallo ruwan na bin yar magudadar ruwa yana tafiya Ta koma ta darwaye soson ta kara yin yanda ta yi , ta shiga saba sabulun a tufkeken gashinta na buzuwar usul ruwan nan na dareaye mata, Abinka da tufkeken gashi wani wajen ya wanku sama sama aman cikin kam da datinsa daskare, haka Agaishat ta yi ta wanka tana sakewa tana jin kanta wani sakayau tana kara balbaluwa a cikin ruwan nan tana jin dadinsa abinka da ba sabanba ta wanke tafin kafafuwanta da abinda Ayya ta nuna mata nanma ta ga dati sai fita yake , har yatsarta ta saka ta debo datin tana kallo da gaske dati ne ta wanke da sabulu tana daga kanta sama ruwan na shiga idannuwanta yana kara ratsa gashinta da jelar ta sako tana yawo du idan ta juya kan Fitowa ta yi ta dauki kayanta wa.inda sai a lokacin ta ji suna wani irin bugawa da ta rabu da datin jikinta, har ta shiga tunanin ko ta wanke? Sai wani abin yace mata idan kika wanke ki saka me kuma? Mayar da kayan ta yi ta fito ba tare da ta kashe panpan ba domin bata iya ba Ayya dake zaune tana jiranta domin Wardugu ya tafi abinsa , ta mike tana fadin" eyah Agaishat ki cire kayan nan mana Agaishat ta yi kasakai tana kallonta Ayya ta dafe kai ta ce" wani yare kika iya Agaishat kin iya frencais? Angalais? Ko hausa? Agaishat dake kallon Ayya ta ce" Ayya, hausa kadan kadan Ayya cikin itama dan yaren hausar nata ta ce" ouf , mun samu na gaisuwa, ki fida kayan nan ki canza wasu kin ji Agaishat ta gyada kanta tana kallon wa.inda Ayya ta nuna mata, sannan ta juyo dan gannin a gaban Ayyan zata saka sai ta ga Ayya ta nufi kofa abinta Ajiyar zuciya ta sauke ta tube kayan ta dauko wa.inda aka ajiye mata Tsayawa ta yi tana kallon doguwar rigar abaya baka wace bata san ina ne gabanta ko bayanta ba sai dogon wando wanda ta daga tana ta jujuyawa irin na maza ta ayanna a ranta sai dai ba irin na mazan garinmu ba domin wandunnansu tamkar buhu........ Da daurin kirjinta tana tsayen nan Ayya ta dawo ta ga bata saka kayan ba Nufota ta yi ta ce" aa ya baki saka ba? Agaishat ta mika mata ta ce" Anna ban iya ba Ayya ta yi murmushi ta shiga nuna mata ta juya ta saka wandon da kyar domin ya yiwa jikinta kadan duda fadinsa da yanda kuma yake jayuwa, Ta dora rigar ta kule yar igiyar dake ciki Ayya ta juyo tana kallonta, ba laifi kayan sun amsheta sai dai sam wankan nan bai yiwa ayya ba , gani take bata wanku ba da saura duda yanda du wani jirwayi na turkudi da fari fat din nan ya fita Mai ta miko mata ta shafa , ta miko mata turare ta tayata shafawa Agaishat bata san tana sakin murmushi ba sai da ta waiga wajen madubi A hankali ta taka ta karasa, hannunta ta mika ta taba madubin tana kallon kanta, a hankali ta juyo wajen Ayya ta ce" na gode Anna Ayya ta karaso da dan kalabin rigar ta kama kanta da bai karasa bushewa ba ta saka mata ribom ta daure mata sannan ta nada mata dan kwalin ya zagaye fuskarta Kwali ta dauko ta nuna mata da ta shafa , Agaishat ta ce bata iya ba , hakan ya sa Ayya ta saka mata idonta ya fara ruwa ruwa abin rashin sabo Ayya tace ta jure karta murje ta kuwa juren Abin maskara ta dauka ta fitar da shi ta saka wani mouchoir (kyale) ta goge bakin jikin tas tas, ta dauki jagira mai ruwan baka ta gogoga a jikin abin ta samu ta caje girar bak'a, girar ta kwonta tsaf a inda ya kamata ba kamar da farko yanda take wawatse ba Ayya ta juyata wajen madubin ta ce" Agaishat, Tsafta, kwaliya, ya zama wajibi ga macen da ta san ciwon kanta, ki rike wanka , ki kasance mai tsafta kin ji?? Kai Agaishat ta daga tana kallon kanta da mamaki, tamkar ba ita ba, ta sawaya hancinta ya wani tafi zuwat, wai a nan Ayya bata gamsu da wankan ba jira take dai su karasa Niamey ta dauki lamarin a hannunta.......... Karfe sha biyu da minti arbadin suka fito daga masarauta suka nufi aeroport, ita dai Ayya bata san yanda wardugu ya yi ya samawa Agaishat waje ba bata tambaye shi ba Sauran minti biyar suka karasa, suna zaune Ayya na kallonsa yanda ransa ke bace, bata ga Walyn ba bata tambayi inda take ba domin ba wani shiga lamarin juna suke ba, bata san zuwanta ba sai da ta ganta daga ina kwana wani abin bai kara shiga tsakaninsu ba sannan dan yanzu bata ganta ba itama ba zata wani tambayi inda take ba , Allah ya basu zaman lafia ita da mijinta ba abinda ya shafeta da zamansu haka kuma ba zata shiga dan wani gyara ba! Ba.a jima ba suka mike domin an fara kiraye kirayen sunnaye, Ita dai agaishat tunda aka haliceta bata taba gannin jirgin bama bale wai har ta shigeshi Ta dai bi bayan Ayya da ta kama hannunta ta shiga nuna mata yanda zata taka matatakalar ta hau suka hau tare tana kara rike Ayya da kyau dan kar ta fadi har suka shiga Kallon tsarin cikin jirgin take a ranta ta ayanna ba irin na mota ba , Nan Ayya ta tsaya sai da Wardugu ya shige kusan madubin domin sam ya hannata zama a nan in dai tafiar jirgi zata yi, ita dai sai dai ta yi murmushi kawai irin yanda yaron nata ke sonta ke kokarin kareta har mamakinsa take , Yana shiga sai ta saka Agaishat ta shige tsakiya , shi kam bai yi magana ba domin ransa a kololuwar bace yake, wai Walyn ta bi jirgin damagaran gobe ta bi na niamey ta karasa, shi zata nunawa zuciya ko? Han...... Ayya ma ta zauna ta ja ceinture ta sakawa Agaishat sannan itama ta saka bayan ta kashe babar wayarta ta android Ba.a jima ba aka shiga fadin a daura ceinture a kashe waya da yarurukanmu na niger da kuma french

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 9

WAReaders TGUpdates