Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 11 / 27

ya bata hijab din Ayya ta dauko ko dan idan an yi baki, wani irin kulawa Ayya take baiwa Agaishat (Bak'a), kudi ta kashe na mamaki wajen siyen mayuka masu gyara fata ba canza kalar fata ba, sannan ta shiga kasuwa da kanta tare da Agaishat tana nununa mata abubuwa nasu na tubawa na gyaran jiki ta kwaso itacen magarya ta kwaso kayan gyaran jiki suka dawo gida, wata irin shakuwa ce ta shiga tsakannin Ayya da Agaishat, domin Ayya wayayiyar mace ce ta yo anfani da irin yanda ta waye ta ja Agaishat a jiki tun tana tsoro tana baya baya har ya zamana sun shaku tana dora kanta saman cinyar Ayya ta yi baci ba tare da wani dar ba. Yauma sun tashi da niyar yin gyaran jikin ne, Ayya ta dadaure mata gashinta da abin nan na saloon wanda idan an wanke kai ake sakawa a dadaure gashi da shi dan ya nanade ya bushe, ta kwaba abin gyaran jikin nan ta samu ta shafa mata ta yi mata hayakin mai mugun zafi wanda fuska kawai ake fitarwa, tana gamawa ta sakata ta yi wanka ta shafa mata na madarar nan suka zauna a fali sunna kallo aman ta hanata magana dan kar na fuskar ya saka fuskar ta yakune........ Mai gadi ne ya fara shigowa da jaka, Wardugu na biye da shi sai Mu.azam wa.inda shigowarsu ne ya ankarar da Ayya ta warci hijab din Agaishat ta ...... 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2️⃣2️⃣ Da sauri Ayya ta samu ta rufa mata hijab din inda Bak'a ta yi mutuwar zaune a ranta tana ayana Ayya wayo daman sai da na fada maki Ayya ........... Karasowa suka yi, Mu.azan na kallon inda aka rufe da hijab yana son sannin ko waye, Wardugu kuwa kallo daya ya yiwa wajen ya kawar da kai a ransa fadi yake" me Ayya ke son yiwa fatar nan da ta rine? Da murna Ayya take kwalawa mai aikinta kira da ta zo ta dauke akwatin Mu.azam sannan ta kawo masa tarba, Ayya ta tarbo shi tana murna ta kamo shi ta zaunar da shi sai murmushi take tana kallonsa ta ce" yarona, yaushe gamo? Mu.azam dake jin wata nutsuwa na saukar masa ya dube duba irin na mahaifiya, a hankali ya duka kasa ya ce" Ayyana ina yini Ayya ta kuma kamo shi ta tayar da shi tana kallonsa, yannayinta ya fara canzawa ta kai hannunta wajen wuyansa ta ce" me ke damunka? Ya haka ka rame har haka? Ko dai ka je ka sakawa kanka ayuka ba hutu ne?? Dariya ya saki yana kallon Ayya , kafin yake maida dubansa wajen Wardugu ya ce" freind Ayyana har yanzu akoy yannayin nan? Wardugu ya yi dan murmushi yana kallon su, Ayya ta yatsina fuska ta ce" ba wani nan, yanzu tashi ka je ka yi wanka ka fito zan fara yi maka dura ne tunda abin haka ne! Yana dariya ya mike ya kalli Wardugu ya ce" mu je ko? Wardugu ya gala masa harara ya ce" a matsayin matarka ko dan jagorarka? Mu.azam ya yi murmusho yana ji a cikin ransa ya yi missing din abokinsa da mahaifiyar abokin nasa, Juyawa ya yi ya nufi dakin da ake sauke shi wanda yake a matsayin nasa, Ayya ce ta dubi wardugu, da idannuwanta ta yi masa nuni da ya tashi mana shima baya gannin mutun? Wardugu ya daga kafadu ya ki tashin yama mayar da dubansa wajen tv inda ya dauki commande ya canza tasha ya kai Canal plus sport ya shiga kallon ball. Ji take ta fara gumi , ga kuma ta kage a yannayin zaman nata, ba.a jima ba Mu.azam ya dawo daga wankan da ya tafi ya zu suka kara kasancewa mutun biyu maza kennan, Ayya ta tashi da yannayin jin haushi ta dunguri kan Wardugu ta ce" ta yi maka kyau! Wajen Agaishat ta karaso ta kamata ta mike kafarta ta yi mata tsami sosai, ta samu ta saka mata hijab din ta ce" je ki yi wanka Agaishat ki sauko mu ci abinci . Da toh ta amsa ta bi ta bayan kujerun ba tare da ta gaisar da su Wardugu ba, Mu.azam da ayar tambaya ya kallo Ayya, bai yi nauyin baki ba ya ce" Ayya ina kika samo wannan? Ayya ta karasa kusa da su sosai ta zuba jus ta mika masa shima kamar yanda ta mikawa Wardugu ta ce" Me ke damunka tukunnan yarona?? Mu.azam ya shiga dan sosa bayan keyarsa, ya kallo wajen Wardugu, ya kuma kalli Ayya. Haka kawai wardugu ya ji gabansa ya fadi, shima kure shi da kallon yake kafin ya ajiye yar wayar dake hannun nasa ya zuba masa ido, Murmushin dai ya kara yi masu, ya ce" na yi rashin lafia ne Ayya, kuma yanzu alhamdulilah na samu sauki, Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" na tsorata da yannayinka, ka wani rame, ba komai haka ne idan jiki ya tabu sai a hankali aman yanzu ka zo kennan sai na ga yarona ya koma yanda yake da koma ya fi haka kafin ka bar gidannan, Wardugu dake kallonsa ya shafa kansa shima kwata kwata bai yarda da maganar Mu.azam ba! Kai haba a irin yanda suka san juna Mu.azam ba zai layance masa ba Mikewa ya yi ya nufi kofa da wayarsa a hannu inda suka bi shi da kallo, Mu.azam ya ce" Ayya ya tafi fa kennan?? Ayya ta daga kafadunta ta dan yatsina fuska ta ce " ya gaishe su! Mu.azam ya yi dariya yana kallonta, a ransa kuwa dadi yake ji yannayin, kai yana jin dadin zama da su, Wardugu rikitace, mahaifiyarsa ta iya zama da shi, ta kai ta kawo ne idan tama da bukatar ganninsa a wayarsa ya yi mata activen localization, du inda yake idan ta shiga nema za.a nuna mata kawai sai dai ya ganta kuma sam baya gigin kashewa doka ce! Suna tsaka da tataunawa mai aikin Ayya ta shinfida ledar cin abinci ta kawo abincin ta ajiye, ta kawo kayan zubawa da na sha, ta kawo su jus na gida da Ayya ke yin abinta da kanta ta saka a frij du ta ajiye, Ayya ta umarci Mu.azam da ya sauko bara ta dubo yarta..... Wardugu ya dawo, bayansa *ALHINAYET* kawarsa ce ke biye da shi, Salama ta yi ta shigo dakin inda Ayya ta tsaya ta saki baki tana kallon Wardugu da Alhinayet din, Alhinayett na zuwa ta shiga gaisar da Ayya cikin yannayin ladabi da mutunta mutun, Ayya ta dan kebe baki, ta amsata ta juya dan dubo Bak'a Mu.azam dake zaune ta juyo ta dafe habarta ta ce" su likitoci ne a garin namu??? Mu.azam ya sakar mata murmushi ya ce" lauya, lauya, lauya mai kunce mai laifi , zamani lauya iko, lauya mai saka kato ya duka, Kai ta dafe ta ce" wace ni, rufani ka sayani, ai ba dan an san ni aminiyar *Aboki* bace da an fige ni a Niger! Mu.azam ya ce" kai ai rigimama ta san waye *Oga* Wardugu ya girgiza kai yana zama ya ce" *ALHIN* ki zauna mu hau wannan abubuwan kafin ku ci gaba da kirar da kuka koya! Alhinayettt ta je kusa da Wardugu ta zauna tana fadin" General ka duba lamarin nan je ten conjure................(plz) Wardugu ya kaleta zai yi magana sai ga Ayya ta dawo da Agaishat, Doguwar riga simple irin ta zaman gida ce Ayya ta bata, bayan ta saka ayya ta bata Dan kwalin rigar nufin ta yane kanta sai dai suka hau rigima kan aa dan Allah ta bata hijab, Gannin sai su bata lokaci ne ya saka Ayyar bata hijab ta zumbula suka sauko, Sai a lokacin Agaishat ta duka ta ce" ina yinin ku, Alhinayettt da Mu.azam ne suka amsa inda Wardugu ya kebe bakinsa bai wani amsa ba aman yana yi mata kallon tsaf, a ransa yake ayyana black, but ko a baki *BUZU MAI KYAU NE* πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ€ͺ😜😜😜😜😜😜😜😜😜πŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ na fada a zo a dake ni🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐 May be 23......zuwa dare in sha allah, idan comment ya birge niπŸ˜„πŸ˜πŸ˜†πŸ˜…πŸ˜‚πŸ€£ 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2️⃣3️⃣ Waje Ayya ta samu ta zauna , nan Agaishat ta je kusa da ita sosai itama ta zauna ya kasance an saka baban plateau din a tsakiya, Ayya ce ta bude inda abincin yake, tuwon tsaki ne da miyar kubewa wace aka yita da naman shanu ta sha dadawa da kayan miya πŸ˜‹..ga kuma man shanu na kirki a gefe, Sai su fruits da aka hi masu yanka mai kyau aka sasaka cikin plat plat, sai jus da ruwa, A hankali Ayya ta dauko abincin, Agaishat ta dauko abin zubawa, Cikin wannan banban plateau din Ayya ta zuba abincin ta daidaita miyar, ka.ida ne in dai ka zo gidan Ayya daidai cin abinci bata raba assiete, sai dai a hadu a ci a abu guda ....... Bayan ta zuba ta kare Agaishat ta kawo abin wanoe hannu da kuma cokula a wata yar roba, Gaba dayansu cokulan suka dauka banda Agaishat da Ayya , hannayensu suka wanke .... Ayya ce ta fara saka hannunta, sai Wardugu, sai Mu.azam, sai Alhinayettt, sannan Agaishat dake karamar cikinsu, hakane gidan Ayya baba ke fara saka hannu cikin kwanon cin abinci sannan yaro ke rike kwanon dan kar ya ringa yawo, ba.a magana idan ana cin abinci, ba.a dane danen waya, ba.a wani kale kale sai an gama, sannan bata yarda ana tsaka da cin abinci ana shan ruwa ko jus, sai an gama ake sha, sannan ana cin abinci daidai ne ba.a matsawa ciki a yi mugun koshi, lamarin gidan Ayya sai yayanta (🀣), Abincin nan ake ci cikin nutsuwa, Alhinayettt ta kure Agaishat da kallo, sam batai mata kama da tubawa ba, sannan ba bahausa bace ko daya duda hijabin dake kanta gaban goshinta lufluf yake kwonce da gashi, girartama wani irin gazar gazar da ita, du bakinta lebenta haske ne da shi tas tas, ga girar ido ga manyan idannu, wannan cikin biyu daya ce ko bakar balaraba ko bakar buzuwa! Alhinayettt dai ba wani yawan zuwa gidan Ayya ba take ba, sukan hadunsu ne da wardugu a wani wajen, yanzuma zuwa ta yi da rigimarsu ta kansu wace ta zo su yi kan irin yanda ake cece ku ce a gari na matarsama idan ta cika dare kwanan cel take bare wani banza! Alhinayettt kwata kwata ta manta zancen ba.a magana idan ana cin abinci gidan Ayya dan haka ta kali Agaishat da kyau, haka kawai ta yi niyar yi mata magana da buzanci dan ta gaskata zatonta, *ABZIN?* , ta fada tana kallon agaishat, Agaishat da ta hadiye abinci ta kaleta itama, itama ta so ta ayanna hakan cewa wannan buzuwa ce, gannin yannayinta sai dai bata fadi ba dan ba wajen fadin bane, Ai kuwa Agaishat ta washe baki itama da yaren buzancin ta maida mata cewa" eh , ke fa?? Alhinayettt zata maida mata maganar Wardugu ya tsimki hannunta na dama dake kusa da shi, sannan ya zabgawa Agaishat wata muguwar harara wace ta sakata sada kanta hannunta na rawa rawa, Ayya yatsina fuska ta yi bata yi magana ba, Sai da aka gama mai aiki ta shiga kwashewa, Agaishat na tayata kaiwa komai wajensa ta dawo ta zauna kasa kusa da kafar Ayya, Wardugu ne ke kallon wayar Alhinayet tana nuna masa hotunnan birthday dinta da ta yi baya nan yana dan murmushi kasa kasa ya ce" Alhinayettt , ina tunanin kin girma ashe dai na daina tunanin nan? Alhinayettt ta yi dariya ta dora hannunta saman nasa ta ce" na baka ka sha? (Irin su taba zata bashi wani labarin) Ai kuwa Wardugu ya dan cafke hannunta yana sauraronta, inda ya bata hankalinsa suna ta hirar su, Ayya ce ta dan ja tsaki, ta girgiza kai tana kallon Mu.azam ta ce" kana ji? Zamani ya zo mana da abubuwan mamaki, sai ka ga mace na tafawa da namiji, tana raba jikinta da nasa wai a zuwan mutunci kawarsa, ! Mu.azam ya zaro ido yana kallon Ayya, a fili kuwa ya furta" Lah, yana dafe bakinsa, Wardugu da ya gama jin komai ya saki murmushi yana kallon Ayya, ya ce" Ayya, qna abota mace da namiji, abota sak ba wani soyaya ba kuwa, Ayya ta juyo bangaren su a takaice , daman jira take wani abin ya hada su ta ce" wardugu ba abota ba dai yayan awaki! Nace yayan awaki, Ke yanzu Alhinayettt kike ko wa? Aman ke marainiya ce ko? Ina nufin mahaifiyarki ta rasu? Alhinayettt dake kallon Ayya a dan tsorace ta ce" Aa Ayya, Ayya ta dafe habarta ta ce" Toh abin mamaki, aman ita baku rainata kamar yanda kuka rainani ba ko? Ina nufin Wardugu baya zuwa gidan ku a matsayin aboki sai saurayi? A tare suka kalli juna Alhinayettt da Wardugu, suka maida dubansu wajen Ayya, Ayya ta ce" to in ba haka ba, ya za.a yi ni ina mahaifiyarki , kato ya ringa zuwa wajenki a matsayin aboki kuma na zuba ido yarinya kin kai kin kawo min a gida? Wardugu ya shiga gyada kai yana kallon mahaifiyarsa, ta jima tana son aikata wannan aika aikar wa zumuncinsa da Alhinayettt, yau dai ta yi hankalinta sai ya kwonta kuma ko? Ayya kamar zugata ake sai magangannunta take son ranta karshe ta ce" to ni ba tsohuwar banza bace, in sonta kake ka fito a mutun ka fada ku daina boyewa Allah kadai ya san tsakanin ku! Dan haka tun wuri a fasa daukana a wata marar ilimi ana ce min wai kawa! Aa abokiyar tagwaitakarka ce Wardugu! Wardugu kallon Ayya kawai yake, inda Alhinayettt ta dan sada kanta kasa, a ranta ayannawa take ita bata ga laifin zumunci da suke da Wardugu ba, walahi da soyaya suke da ba haka ba, kwata kwata ba wani zance wai shi soyaya tsakaninsu, haka kawai Allah ya hada jininsu suke mutunci, Wardugu bashi da shamaki a gidan su, hakama saurayinta wanda zasu yi aure suna mutunci da Wardugu, aman haka ne itama kakarta ta sakawa zumuncinsu ido har sun mayar da ita tamkar mahaukaciya domin idan sun ga zata fice sai su shiga magana kasa kasa da yaren french ai kuwa ta kama zage zage tana fadin ita za.a munafinta? Toh gashi itama maman Wardugu kallon masu soyaya take masu bayan ita koda bindiga ba zata iya soyaya da wardugu ba domin ta san waye shi, Wardugu dan yana son ki ba zai hana ya yi maki dukan mutuwa ba, dan yana son ki baki fi hukunci a wajensa a gaban koma waye ba, hum soyayama da wardugu ai tashin hankali ce, ita mai ya kaita? Ta fi son namiji marar rigima mai bata damar ta yi rayuwarta cikin aminci........ Wardugu dake kallon Ayya tar, ya maida dubansa wajen Mu.azam ya ga sai gumtse dariya yake, Kansa ya girgiza ya maido dubansa wajen Ayya, da hannunsa na dama ya daga ya sara mata, sannan ya yi mata nuni da ta ci wasanfa , ta more abinta, Hannunsa na hagu ya mikawa Alhinayettt ta mike itama ya ja hannunta tana waiwaye tana so ta yi hira da agaishat aman ya jata kiiii sukai waje Kusan motarta suka tsaya, Alhinayettt bata bi ta kan fadan Ayya ba, bata nuna damuwarta ko a fuska ba, ta ce" Wardugu, rigingimunka sun isheni haka, ya isheka malan! Wardugu ya shiga gyada kai yana kallonta bai bata amsa ba, Ta ci gaba da maga domin ta san ba amsar zai bata ba, ta ce" ta ya zaka saka Walyn kwana a cel? Wardugu ina jin zafi idan na ji ana fadin baka da sasauci, baka wasa, baka sulhu, Wardugu matarka ce fa? Ya kake so mutane su fasaraka?? Wardugu ya tsura mata ido kawai, Ta ci gaba murya a sanyaye" ka daina Wardugu, ina so idan na zo waje na tarda ana fadin alkhairi a kanka, ina so idan ana maganarka ta kasance ana yabonka Wardugu, ka ringa sasauci freind, Wardugu ya yi mata dan murmushi ya miko hannunsa ya dungure mata kanta bai ce mata komai ba, Alhinayettt ta ce" Wardugu ina kula samu buzuwa?? Wardugu ya yatsina fuska ya ce" hum, Ayya ce ta daukota wai ta yi y'a, Alhinayettt ta ce" yarinyar ce ta birge ni, irin yanda tana buzuwa , bakar buzuwa aman bata bata bakinta ta hanyar shafe shafe ba, ina son mutun haka walahi..... Wardugu ya daga kafada ya ce" daga kauye, can cikin kauyen kauye fa ta fito, inama ta ga man bale ta shafa? Allah dai ya sa idan ta dan waye ta zama dan kauye ya fi na birni shegantaka.... Alhinayettt ta ce " sai dai idan ba tare da Ayya take ba, Ayya ce zata wani bari haka ya faru? Yarinyar ce innocente, dan Allah ka hada ni da ita mu zama kawaye, Wardugu ya waro ido, a fili ya furta" kawaye? Ki kirani aboki kuma ki yi kawance da wannan? Aa! Alhinayettt ta yi murmushi tana kai masa dan dukan wasa ta ce" ina son ta zama kanwata ne Wardugu, ina son na kara nuna mata shafe shafe karma ta saka kanta, sannan na kara wayar da ita...... Kafadunsa ya daga irin ita ta gano, kafin yake bude mata motar ya yi mata nuno da ta shiga Dariya ta yi ta shiga , ta kunna wato dai ta ishe shi da magana ko? Hannu ta daga masa, ya yi mata nuni da sai ya zo , ta tayar da dankareriyar motarta ta kama hanyar makarantar kannenta dan ta dauko su ta mayar da su gida Komawa Wardugu ya yi, yana shiga ya tarar da su sai labari suke suna dariya abinsu, Mu.azam kuwa ya kasance du motsi sai ya kali Agaishat dake zaune tana kallon Tv kuri, ita har yanzu

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 11

WAReaders TGUpdates