ba idannuwana sun nuna mini abubuwan da suka faru na ga komai na gane komai Magana ya yi masu wace ban san me yake nufi ba suka gama kasuwancinsu ya cashi kudinsa sosai kafin suke tafiya Sai da ya gama shaye shayensa ya taso kusa da ni sosai da muryar mashayi ya ce" ke fa sai na yi maki filafila dan kuwa an caje ni kudi kafin a bani ke kuma dan iskanci aka kawo ki daga ke sai wannan bakin kayan Tashi ki tube Da mamaki nake kallon shi, in tube, wai ina ne nan? Me hakan ke nufi? Matan nan su waye? In tube haka kai tsaye ai ko matarka ce ni koda mun saba da sannin juna fitsara ne gatsal ka kale ni ka ce mini tube Mikewa na yi da yarena na rufe ido na shiga zazaga fitsara ina son sannin inda ya nufa Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya kafin take kara sakin wani kukan mai karfi ta ce" Anna matan nan da suka fita bayan ya amshi kudaden karuwanci da zasu fita su kwana da karti ashe gaba dayan su suna zaune a matsayin matansa mace har bakwai ni ta takwas cikinsu ba daya ta yarwa sannan ba daya da ta san hanyar gidansu A wannan ranar da katsa ya dake ni kafin yake zuwarmini da wata irin sufa yayi anfani da ni ba imani yana gamawa ya wawatsa kafafuwana ya goge gaba daya najasar nan ya shafe a fuskarsa harda jini jinin nan ya side hannayen nasa ya fice Anna a wannan ranar.kafin gari ya waye sau tara yana zuwar mini Mariama ce ta dauko kwan fitilar sosai ta haska wajen kafafuwan Fatimata, ruwa ne ke yawo wanda ya saka Mariama cewa" Anna ruwan nan kuma na menene? Fatimata ta ce" fitsarina ne ba ruwa ba, haka fitsari ke zubar mini bama na sannin yana binna Anna ta fashe da wani irin kuka kafin ta ture kan Fatimata ta mike ta yi dakin yaren da sauri hannayenta duka biyu saman kanta, *YoYo, YoYon fitsari Fatimata ke yi*! A wannan rana yanda suka ga rana haka suka ga dare inda suka cure gaba dayansu waje guda ba mai yiwa yar uwarta magana sai dai suna bin juna da ido , nan Mariama ta mike ta dauko wata leda baka baba ta shinfida ta dauko zani ta shinfida ta kallo yan uwanta ta ce" ke fatimata taso ki kwonta saman nan, ke Agaishat(Bak'a) tafi wajen Anna, kuma ku taso mu kwonta dare na tafiya kar safiya ta yi mana a nan A hankali ta samu ta lalaba ta hau, suma du suka samu waje suka kwonkwonta ba dan zasu samu yin bacin ba, sun dai yi zuru ne domin Fatimata bata gama basu labarin irin ukubar da ta sha ba aka ga fitsari na binta hakan kuwa ya tayarwa da Annar hankali bata ma tsaya ta ji sauran zancen ba Anna ce duke kanta kasa ta kai sujada tana ta sheka kuka ta ce" ALLAH ka san wacece ni, kai ka halice ni, ya Allah ina cikin jarabawarka tun daga yannayin aurena har zuwa yau, na rasa me ke daure da ni da wannan mutumin ainahi Allahna idan ba a cikin sallah ba bana iya tuna wacece ni, menene tarihina, ina da yan uwa ko haka nake ni daya? Bana son a yi min maganar ko wa ya kawo min zancen zan nuna bacin raina ne, Allah yayana, ka bayannar sauran, wa.inda basu da lafia ya Allah ka basu lafia, wa.inda yake niyar aurarwa dan samun abin duniya Idan da alkhairi a cikin auren ka tabatarda, idan kuwa ba alkhairi bane Allah kai ka yi shi ka hana, ka hana ya Allah Allah sannan ka yaye min duhun dake cinkushe min ganina Ta jima tana kai kukanta wajen Allah kafin take mikewa ta yi tahiya ta salamce ta dora adu.a tana ta yawaita istigfari domin ba abinda ke saurin yaye kunci irinta Da safe tana tashi ta dauki sansani (tabar buzaye) a cikin nata ta matsa a bakinta ta yane jikinta ta buga safiya ta fice a gidan Zugum suke ba mai yiwa dan uwansa magana har wajen karfe tara Anna bata dawo ba, Aba daman tun cikin daren nan ya fice basu san ina ya kwana ba sannan bai dawo ba, sun zubawa sarautar Allah ido ne kawai A hankali Bak'a ta kali gorin tsofo, ta mayar ta kule a harshen zaninta a ranta take ayanna bawan Allah ko a wani hali yake? Ko an dauko masa ruwa? Tabas yana cikin damuwar rashin ganninta yau har za.a kwana biyu, sai dai ba zata iya fita ta bar gidansu a wannan halin ba, a hankali ta rike goron ta ce" sofo ina nan lafiata klau, ka ga na saya maka goro ma kar ka damu ina nan tafe wajenka ..........inna Anna ta tafi????? Gyara kimtsi, mai zamani dan sarki jikan sarki, Buzu jinnin sarauta, yaro mai zamani, taka lafia bijimin sarki, taka lafiya gagara gasa, kai ne na uku baban Rabatima, ka shigo a hankali yarima, taka sanu sanu sarkina , Kirarin da jakadiya ke yi masa kennan tunda ya tunkaro dakin mahaifiyarsa, dan dakatawa ya yi har ta yi gyaran murya kafin yake saka kai da salama a bakinsa Dago kanta ta yi tana murmushi ta amsa shi, a hankali ya karasa yana wata irin tafiya idan ya daga kafa daya kafin ya daga dayar sai ya jima Dukawa ya yi har kasa kansa kasa ya ce" ta gode Anna, ta gode Amy (Wato mahaifiyar Wardugu aminiyar matar sarki....da Amy suke kiranta bisa umarnin mahaifiyarsu,) Murmushi take sakar masa kafin ta ce" oh son tashi mana, amynka ce fa ko dan ka daina zuwa wajena ne? Yana murmushi ya mike ya zauna saman kushin dake wajen cikin nustuwa suka shiga gaisawa da harsen freinsh domin ita ce kawai yaren da zasu yi su jima suna hira cikib gane abinda suke fadawa juna Dan jim ya biyo baya kafin yake cewa " Amy ya labarin Oga ne? Na yi na yi ya siyar min da wata mota aman da yake yan rigimar a kansa cewa yayi aa motar ba ta yara bace, ki ji fa Amy Dariya suka saka gaba dayansu, Ayya ta ce" Wardugu, Wardugu baya jin magana Aghali, sai hakuri da murdaden halayen Wardugu Mahaifiyar Aghali matar sarki ta ce" Kawata, wai ina labarin aban Wardugu ne? Ni kam ina mamakin lamarinku, kawai daga wannan dan laifin? Ayya ta dago tana kallonta, a ranta ta ayanna ban ga laifinki ba, ku baku dauki haka a matsayin laifi ba, A fili kuwa ta ce" manta Murmushi Mahaifiyar Aghali ta yi, Ayya akoy mulki wannan da gidan sarauta take da an ji jiki domin mace ce mai mulki da isa, ga jan aji, da yake an dauko hirar da bata so daga haka ta katse hirar ta mike tana yi masu salama dan tana son shiga ciki ta kirayi number Wardugu rabonta da shi tunfa suka karaso jiya ba shi ba labarinsa ...........rashin Comment ne kawai zai saka ni daukan matakin siyar da novel din nan ko na tsayar da shi, 😊 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 9⃣ Ayya na zuwa dakin da aka sauketa zauna ta jinginar da bayanta jikin kujera ta daga kanta sama, Ta jima tana tunani, kafin take sauke ajiyar Zuciya a fili ta ce " *MARAHUT*, ina ka shiga? Ka san komai ka tarwatsa rayuwarmu, Marahut ina tausaya maka sai dai mutuncina darajata ba zan yarda ka zubda mini ba! Ka zabi wancen rayuwar ko? Ba komai ka je sannu duniya zata koya maka hankali, Ranta ne ta ji yana suya, yama aka yi ta tabo mata wannan mikin, ta sani da gangan ta tuno mata da maganar domin ta fi kowa sannin abinda ya faru, ita kadai sai Wardugu suka san takamaimai abinda ya faru aman zatana tuno mata da shi , ita so take sai ta yi hakuri bata san ta rufe babinsa ba kuma ko da jaraba sai ya saketa dan bata fatan idan ta mutu ya kasance shine alwalin gawarta (Toh fa😳 tubawa akoy zuciya) Aghali, dan me ba zaka kara aure ba? Matanka biyu yarka daya mace sai matan daki , ko a cikinsu har yanzu ba wace ta samu ciki bayan ina kula da irin zubin da ake maka ana canzawa du wace ta kwana biyu, ko dai baka zuwa inda suken da gaske? Domin na ji kishin kishin cewar wannan matar taka ta shanye min kai, Mahaifiyar magajin sarki ce ke fada kan ya ki karo aure bayan tana son ya tara yaya Murmushi ya yi ya ce " zan kara aure, ki kwontar da hankalinki, Ajiyar zuciya ta sauke kafin take miko masa yar akwati tana murmushi ta ce" ka ga Amynka ta kawowa wannan mumunar ( wato yarsa jikarta) Hannu ya saka ya bude ya gani, sarka ne da yan kunaye na zinari masu kyau sosai kirar yara, murmushi ya yi ya ce" zata je ta gaisheta sannan ta yi godiya........ wannan kennan Sai da ta bude lulubarta suka ga mace ce bayan ta fada masu ita mahaifiyar Gaishat ce , suka je suka shaidawa sarki ya bada izinin a shigar da ita bangaren Gaishat din yana mamakin zuwanta da fadawa zuciyarsa ba lafia ba domin shekara kusan takwas da aurensu bata taba takowa ko aiko da kannen Gaishat din ba duda tana yarta ta fari, itama bata wani zuwa gidan du ta takura rayuwarta da tsoronsa ta mayar da kanta ta daki duda kuwa irin yanda yake daukaka martabarta fiye da iyayen yayansa Tana shiga dakin ta nemi waje nan kasa ta zauna ta sada kanta , da kujeru da komai aman ta fi fanewa zama a kasan nan Da sauri ta fito jin sakon Sarki wai mamanta ce ta zo Tana fitowa ta karaso da gudu ta riko hannayenta a rikice ta ce" Anna lafia? Anna wa ya mutu? Anna na shiga uku me yake damunki? Anna me ke faruwa? Me aka maki Anna? Anna..... Shiiiiit anna ta fada tana dora yatsarta saman leben Gaishat, itama tana kare mata kallo, yarinyar bata wani karu ba a jikinta na da, sai dan girma daga fuska da ta kara, duda jikinta bai nuna alamar wahala ba aman tana da rama, kanta daure , Kunyar Gaishat din ta ji ta kamata, dole ta rikice domin bata taba zuwa alkhairi ko tashin hankali ba, itace ma ke yin kokari idan ta san Abansu baya gari ta leko a tsaitsaye ta koma shima ba wani zantawa suke sai dai su bi junna da ita Tunani ta afka shin fada mata zata yi ko kawai ta yi shiru ta juya A hankali Gaishat ta dago habar mamanta, dara daran idannuwanta na gado ta saka cikin nata ta ce" Anna, me ke damunki? Ki fada mani kin ji? In sha Allah ko bani da maganin damuwarki zan taya ki da adu.a Anna ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Gaishat, Algabitt ne....ya samarwa su Mariama mazajen aure wa.inda bama a niger din suke ba, kin san bani da labari tghmass ita a niger din ma aka bayar da ita, jiya Fatimata ta dawo, mariama fatimata ta kamu da cutar rashin rike fitsari , kin san ba maganinsa a kauye sai asibiti, baki ga fatimata ba, ta dawo wata iri, Ga irin tsanar Agaishat (BAK'A) , ya sako yarinyar a gaba tamkar ya kasheta dan ya san gardawan da yake zuwa da su dan zaben mata ba zasu zabeta ba, shi ya sa nake kara barinta da datinta, mai yiwuwa ita ta tsira daga muguwar rayuwar da yake saka mini yaya Shiru ta yi kanta sade tana gursheken kuka daga ita har Gaishat din, Ajiyar zuciya Gaishat ta sauke ta ce" Anna zan zo gidan kin ji? Sai mu samo abinda ya samu mu samu shiga asibitin Ido Anna ta zaro ta ce" ta yaya zaki fita Gaishat? Gaishat ta yi murmushi ta ce" Anna, ki daina damuwa da damuwata, ni na dorawa kaina, tabas Aba ya yi auren dole da mutumin da bana so, mai mulkin garina aman shi mutumen jira yake in nuna bukatata a wani abin jiki na rawa yake yi min ko menene , bana tunanin fita zata zama damuwa tsakanina da shi Anna ta sauke ajiyar zuciya, ta dago habar Gaishat ta ce" me ya sa toh ba zaki kyautata masa ki kontar da hankalinki ba? Shekarunnan ba fa kwanaki bane, ya ci ace kin zubar da komai kun fuskanci juna, ke Allah ya taimake ki kina cikin konciyar hankali kar ki bijirewa Allah mana Gaishat ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Anna na kara nade jikinta da fuskarta wato dai tafia zata yi, ita ba zata ki su dawama a nan suna hira da mahaifiyarta ba Tana ji tana gani Anna ta yi mata salama ta fice a gidan tana fatan kar ta hadu da wani a kusan gidan yarta ta fari , haka kawai take jin kunyar haka ....... Da dare, bayan ya gama salama da kowa ya nufo dakin mai motsa zuciyarsa, ya sani ne ta san sarai itace da shi aman taga damar ya tarar da ta rufe kofarta Ga mamakinsa yana taba kofar ya tarar da ita a bude, Turawa ya yi a hankali ya shiga da salama a bakinsa Kanta ta dago duda tana jin kunya , ta yi kokari ta amsa salamarsa cikin nutsuwa tana dubansa Da sauri ya karasa inda take zaune, da alama har wanka ta yi, na menene? Taba jikinta ya fara yi hankalinsa a dan tashe ya ce" GAISHAT baki da lafia ne? Me ke damun ki? Dan bakinta ta turo, kafin take dauke hannun nasa ta kara turo bakin, murya a matukar kasalance ta ce" me ya sa ka zabi aurena ta hanyar baiwa Abanna damar ya ci gaba da tafka tsiya a cikin garinka? Dakatawa ya yi, ya yi tsai yana kallonta, a hankali ya rungumeta a jikinsa ya ce" ba dai za.a yafe min ba du irin hakurin da nake bayarwa? Ki gane dan adam nake mai cike da izgili da sabo a doron kasa, Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" ina so ka bar ni na je gida Da sauri ya zabura ya cikata yana kallonta, muryarsa na rawa rawa ya ce" zaki tafi ki barni kennan? Yau kin fitar abinda ke cikinki shine zaki yi nesa da ni? Me yasa ba zaki yi mini adalci ba? Ina sane da du ranar da zan zo gare ki sai kin sha madaciya dan kar ki haihu da ni, na so daukan mataki a kanki aman bana iyawa Gaishat, ki yi mini adalci mana Dora dan yatsarta ta yi saman lebensa jajaji abinka da jan buzu ruwan sarauta ko na kauye dawisu ne, ta ce" zama da kai yanzu na fara, ina son zuwa gidanmu ne dan kanwata ba lafia, muna son kaita asibiti, ka bani dama da ikon da zan yi bajinta a lamarin Ajiyar zuciya ya sauke, ya rungumeta sosai har kamar ta yi ihun zafi, ya mikar da ita yana kallonta ya shiga warware lafayar da ta yane jikinta yanai mata kallon maita, haka ya idasa shigar da ita uwar dakanta cike da zumudi, wa ya isa in ba ita ba? Ita kadai yake tardowa har dakinta, hajia Gaishat mai sarkin garin *TIMIYA* Kamar yanda ya yi alkawari haka ya bayar da rakumi har goma, ya bata kudi masu yawa ya lamunce mata zuwa gari dan kai kanwarta asibiti inda gari ya dauka ana ta lale lale gimbiya ta karbi soyayar sarkinsu, abinka da kauye har yar salah aka yi ta murnar hakan ................... 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣1⃣ ........Niamey....... Gidan Wardugu Kawata, dan Allah wai da gadke kike? Gaki ga yan kaso wa.inda suka aikata mugun laifi? Gaskiya oga ya san kan mugunta Walyn ta ja tsaki ta ce" ke, a dakin nan a nan suke fitsari, mata sai kawai ki ga an dage buje an tsirara fitsari a tsaye, basa kunya basa kyankyamin wajen , kai gaskiya Wardugu ni da shi akoy tashin hankali, ba ni ya wulakanta ba, walahi sai na rama! Me zaki yi masa? Wardugu ne fa? Kin manta waye shi? Ko mu da muke gari bama rayuwa da shi mun san waye shi, koda kina kema jinnin tubawa ba lale ki iya da rigimarsa ba, ya hada abubuwa da yawa ne, kin ga shine da daya kwalin kwal a wajen iyayensa, shine Wardugu mai sunnan rikitatu a cikin ku, shi ne Batube, kuma shi ne Soja! Wardugu kakarfa, tsayaye, isashe, hamshakin...... Ke meye haka? Walyn ta fada tana kallon kawar tata, Ta ce" ya zaki tsaya kina koda min miji sai kace wata mai son min miji? Toh bara ki ji mu a yarenmu ba.a yiwa mace kishiya sai ta cika wa.adin yin hakan, duka duka shekarana biyu da aure da mijina, ko na kai shekarun da yana iya kara wata Wardugu haramiyar wata mace ce a nan duniya, ban ki ba lahira idan ya dace da aljanna! Murmushi ta yi tana kallonta ta ce" dadina da ke saurin hawa , toh yi hakuri ni ban kai abin can ba .......... Bakinta ta tabe ta ci gaba da shafa cream dinta kan kurajen cizon sauron da suka yi mata cin balaki a cikin cel din nan, rabonta da ta saka kafarta kofa tunda abin nan ya faru, gashi ta rasa Wardugu a waya kwata kwata, ! Dogo ne fari kar, datijo ne christa sunansa Docter Lucien, kwararen likitan mata kennan wanda ya karanci abin kuma ya lakanta, Allah ya taimaki su Anna sun samu gannin Docter Lucien a dasha kuma tausayin irin ciwon da ya gani bayan ya sha fada ya karbe su ya shirya shiga tiyata da ita
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN