Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 22 / 27

ita, wani baya jure gannin mace a cikin yannayi na abin tausayi...zaki ga ya fada tarkon kaunarta, wani farar mace ce zabinsa, wani kuwa *bak'a*, ke wani duka biyun yana so....tambayar a nan shi ne *Sai ka karanci mutun kake gane waye shi harma ka tabo wajen da ba zai jure ba, da kansa zai nuna shi sai kai*, Walyn kallonta kawai take, Aisata ta ci gaba" mijin ki dan ra.ayi ne, gwarzona ya bani wahalar da wani namijin bai bani ba , kyauna, zubina, yannayin rayuwana na saka shi fadin"Aisata ke matar kilacewa ce, ki yi zamanki a gida zan zo na dauke ki na mayar da ke matata. kafin na samu kansa na jigata.da kuka da komai ya furtan kalmar so, domin na kai karar tsohon saurayina wajensa inda na biya mutumin ya yi min dukan tsiya, ke dai na takaita maki sai da na zama tamkar kaska, du inda wardugu yake ina nan, da naci da taimakon aminiyarsa ya furtan kalmar so... Sai dai abin haushi du irin yanda muke soyaya da shi idan na nuna koda shan minti ne a dan zaga sai ya fatatake ni, A ranar da na tube zindir a gabansa sosai na kusa cin masa wani tsinanan abokinsa ya shigo dakin domin ke shaidan ba abinda baya hasawa , kwana dakin wardugu na kusan cinma burina nan na fahinci irin zaman da ake tsakanin matar Marahut da shi, Ayya ta kasance mace mai tsafta, ta iya girki, tana yiwa mijinta biyaya ....sai dai na sha na fito tsakiyar dare falon su na kunnuwana su tsinkayo min rigimar ba zata bashi ba, ta gaji da ayyuka ya bari sai da safe! Wani wal wal wal ta yi da idannuwanta ta ce" *Walyn ba.a matsa lamarin nan, idan aka tashi a yi kawai!*, A lokacin da na gama gane Ayya ba zata aminta na auri farin cikina ba, na dauki damarar itama sai na cusa mata bakin ciki , kuma ko da kwaya sai na kwonta da d'anta! Walyn ta ce" shi Marahut din asiri ki kai masa ko? Aisata ta ce" na fada maki ban san wannan ba! Walyn ta rafka tagumi ta ce" fada mani yanda kika tarwatsa su , mai yiwuwa na yarda da labarin wai Wardugu ba asiri ki kai masa ba. Aisata ta buda bakinta zata fada mata kennan aka zo aka ce ya isa haka sun jima suna hira domin dai Aisata harkar kwaya ya kaita kaso, ido a kanta yake dan kar a kawo mata har gidan kaso... Haka Walyn na ji na gani ta fito ta kama hanyar gidanta ba tare da ta samu komai ba! Alhinayet ce zaune tare da saurayinta, malamin university ne, saurayi ne domin bai taba aure ba, bazabarme ne baki dogo , hira suke cikin nishadi nan yake shaida mata yana son turowa, Alhinayet ta fada masa zata fadawa abanta tukunnan , abinda ya ce in sha Allah. Haka suka gama hirar su ya mike ya yi mata salama ya shige motarsa ya tafi, Mikewa ta yi ta je cikin gidansu , Shiryawa ta yi ta saka dogon hijab dinta blue, ta dauki bakar leda ta je wajen mamansu , wato matar mahaifin su ta shaida mata zata je ta kaiwa Agaishat hijaban Adu.a ta yi mata kafin take fita ta shiga motarta ta tayar ta nufi gidan Ayya............. Aghali ya zo garin Niamey ne dan duba gininsu da ake yi a unguwar citรฉ laraba, Ya gama abinda ya kawo shi aman ya ki tafia bisa bukatarsa na Wardugu ya siyar masa da mota , sun tsayar zai shigo ranar lahadi wato gobe baya aiki sai su fita su je ya gani...... Soyaya suke a nitse, a hankali yake koya mata mecece soyayar ma wace a kulun sai sun gama bitar zai jefo mata tambayar" Agaishana, shin kina jin du abubuwan da na zana maki a kaina? Dariya take yi a fili sai tace" ni yaya Mu.azam gudun fankan dakin Hane mai aiki kawai ke saka zuciyata gudu, ka ci gaba da koya mani na san zata yi gudun wata rana idan na ganka Yakan tsareta da ido ne kawai , bai san me zai da ita ba, soyaya ai shigar farat daya take yi, shi da yake so ya kai kudirinsa wajen Ayya kan a aura masa ita da wuri? Kai ba zai wani jira har ta kamu da sonsa ba, zata so shi a zaman da zasu yi, shi kam yana kwadayin zama da ita a rayuwa.... Docter Mariam ce tsaye tare da shugabansu ta asibiti, kanta duke kuka ne take har jikinta na bari ta ce" nima marainiya ce docter, a lokacin da na zo wajen nan shi ya tarbe ni, ya ciyar da ni da aljihunsa, kafin na tsaya da kafafuwana shi ne komaina, tun a lokacin nake mugun son sa, ba zan yafewa kaina idan ban je na dawo da shi ba, ki taimaka mani ki sama mani takardar nan na roke ki, Cike da tausayi take dubanta, su musulmai haka suke ko kuwa wasu da wasu ne? Tana jinjina girman son da Mariama ke yiwa docter mu.azam, in sha Allah zata sama mata takardar su biyu wace zata bata damar zuwa ta zo da shi su shiga aiki, koda bai tashi ba , ba zata tsangwami kanta ba, A hankali ta dafa kanta ta ce" kar ki damu Docter, ki je zan neme ki, zan nema maki takardar Da murnarta ta yi godiya ta fito ta shiga office dinta, hotonsu ta kaiwa duba kafin a fili ta ce" wai baka son farar mace ko? Dole ka so ni docter, ni ina son ka๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ Wayo hanuna๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜•๐Ÿ˜• ๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ *BAK'A CE*๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ Na *SAJIDA* *ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ____________________________________ *๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4๏ธโƒฃ1๏ธโƒฃ Ayya ki duba lamarina na roke ki, Mu.azan ya fada kansa a kasa, kunya ta hana shi dago da kansa ya dubi Ayya domin ya fadi abu mafi nauyi a bakinsa Da mamaki take kallonsa, so? Aure? Yana son Auren Agaishat? Aman yaushe suka yi wata soyaya da fahimta har za.a kai ga aure? A nitse ta ce" Mu.azam, aman me ya sa kake sauri haka? Mu.azam dake kallin kasa ya ce" Ayya , ina so ne a yi mu juya tare da ita. Aman ai ka san sha.anin aure na bukatar nutsuwa ko? Sannan yarinyar nan amana na daukota daga garin su, eh lale mahaifiyarta ta bani damar ko aure ya tashi na yi mata aman da ransu da lafiarsu ba zan yanke hukunci irin na aure ba tare da yawun iyayen yarinyar ba ko? .... Ayya ta fada jikinta sanyaye tana dubansa Mu.azam ya gyada kansa, hankalinsa ya dan fara tashi ya ce" Ayya, ki tura ni wajen dagin nata, na je na nemi a bani aurenta, bana son jan abin ne Ayya ta kuma kale shi da mamaki, bai taba naci kan abu irin wannan ba, jikinta ta ji ya kara yin sanyi, aman Agaishat dinta dukanta ma nawa take da har za.a yi gagawa a lamarinta haka? Sai dai kuma bata tunanin Mu.azam zai wulakanta mata yarinya, duda haka tana son bin hanyar da kakarta ta bi da ita, zasu kai kulansu wajen Allah, a hankali ta ce" yarona, na ji, kuma zan fi kowa farin cikin sannin tana hannu mai kyau, kar ka damu zan san abin yi nan kusa in sha Allah, in dai Agaishat matarka ce zaka aureta kisa ba da jimawa ba. Cike da murna ya yi mata godiya ya mike ya nufi dakinsa dan yin wanka, Tsaye take a tsakiyar gidan tana kallon manyan tantabarun gidan dake kiwo nan balbalin gidan , tana yi tana duba kofa domin ranar juma.a da alhinayet ta zo tace zata dawo ranar lahadi su je gidan kitso Ayya sai fadan kitso take, Kallonta yake daga inda yake tsaye, inda ya shiga takowa a hankali har ya karaso inda take tsaye, ma.ana suka jera, A hankali ta dago da kanta daga kallon tantabarar ta kai dubanta wajensa , nan da nan ta matsa gaba sannan ta sada kanta kasa cikin yanayi na bawa wanda ke kusa girma. Aghali ya ce" a garinku ke yar gidan waye? Agaishat ta dube shi, ta kuma sada kanta, sarkinta ne, ita talakarsa ce, sarkinta ma talakansa ne, dan haka cikin yannayi na girmamawa ta ce" sunnan mahaifina *Ba*, Ba , ai sunnan du uba ne a garin buzaye! Aghali ya fada yana kara tsareta da ido, Agaishat ta ce" ka yi hakuri, Aghali ya ce" baki min laifi ba, Soyaya kike da shi? Kina tunanin zai mutunta ki zai so ki da zuciya daya? Kallonta ta dago wannan karon ta sauke kan nasa,, Bata kai ga bashi amsa ba Wardugu ya shigo da wata galeliyar mota fara kar, kusa da shi Alhinayet ce da ya dauko zai ajiye su wajen kitso wai๐Ÿคฆโ€โ™€, Birki ya ja irin na ka taka baka shiryan nan ba, da bakin gilas dinsa ya dan kale su kafin yake taka motar ya karasa wajen da ya dace a ajiye motar. Yana tsayawa ya kai dubansa wajensu, gani ya yi aghali na magana, yar gidan Ayya kuwa na kallon kasa, kansa ya girgiza kafin ya maida dubansa wajen Alhinayett ya ce" Alhi, Aba ya saka na yi bincike a kansa, yace bai yarda da adinninsa ba , hakan ne kuwa ba musulmi bane yace shi musulmi ne dan ya saje da jama.ar garin nan, Alhinayett ta ce" General ya kuke so na yi ne? Ina zan shiga na samo wanda ya yi 100/100? Wannan na uku kennan yana zuwa da niyar aure abin na watsewa tun kafin a je ko.ina, Wardugu bana son auren Lieutenan na fada maka bana son auren soja. Wardugu ya yi musrmushi yana dubanta ya ce" kuma ki ce ke aminiyata ce, a gabana kina fadin bakya son auren mai sana.ata, me zamu yi maki ne? Me muke yi? Alhinayet ta girgiza kanta ta ce" Wardugu, bana iya zama da namiji mai mugun karfi, ba zan iya rigimar sojoji ba, ba zan iya firirita irin ta matan sojoji ba, ka san ko ni wacece ban iya fada ba, ban iya ihu ba Wardugu ina son namiji mai sanyin hali ne, Wardugu ya ce" ba daga nan take ba, sai ki ga kin auri wanda ba sojan ba kuma ya kasance irin wanda bakya so din, kin gane Alhi ke dai ki yi adu.a , aman na san kina son lieutenant sosai, ke ra.ayinki na ba zaki auri soja ba dan bakya son mai fada, wannan ai shirme ne, ni na fi son ki auri wanda yake na san shi , du ranar da ya taka min ke na nuna masa bashi da wayo! Murmushi ta yi ta kai hannunta suka cafke ta ce" Wardugu, aa fa, ba zaka dakar min miji ba wollah.... Ido ya zaro ya ce" kai, har kin fi son shi da ni? Bakinta ta yatsina tana hararsa da wasa ta ce" oyah bude na gaishe da Ayya mu tafi kar yama ta yi sosai , Idannuwansa ya kai wajen su, nan ya ga Aghali baya wajen aman ita tana tsaye, Cikin hijaban da Alhinayet ta kawo mata ne ta saka milk mai haske, hijabin har kasa yake mai hannaye sannan tamkar zubin riga aka yi masa ya dinku ya yi kyau sosai, ta saka takalminta mai dan tsini kadan da igiyoyinsa ta daure abinta das da ita, Ajiyar zuciya ya sauke ya kai dubansa wajen Alhinayett da ya ga ta tsare shi da ido, sarai ta ga me yake kallo duda ya saka bakin gilas ya tamke kar a gane me yake ciki, Kuma kallon wajen ta yi ta ga Agaishat ta juya wajen kofar falon ayya tana murmushi, Wajen ta mayar da dubanta sai ta ga Mu.azam ne ya fito cikin shigarsa ta shada ya yi shar da shi , daga inda yake tsayen sai turo mata irin abin nan na soyaya yake sai yace Muah, Ita kuwa sai ta rufe ido tana dariya, Tsaki wardugu ya ja ya ce" ji wani shirme kuma? Alhinayett da lumshe idannuwanta, ta ce" na me? Ba wani shirme walahi sai soyaya, Dubanta ya yi kafin ya yi murmushi ya girgiza kansa, motar ya bude ya fita inda itama ta fito, Tafiya ya fara da sauri sauri kamar yanda yake yi kulun, dakatawa ya yi ya dubota ya ce" kuma na saka ya tura magabatansa wajen Aba , Ido ta zaro ta ce" Wardugu, Wardugu, Ina tuni ya yi tafiarsa, Murmushi ta yi itama a fili ta ce" Wardugu zai min auren dole da soja......... Yana zuwa suka gaisa da Mu.azam ya tsare shi da ido ya ce" haka ka koma kan mace? Ka saka yarinya gaba kana abu irin na yara? Mu.azam ya daga girarsa ya ce" kai raba ni amini, soyaya ce, Kai ya dafe yana mai jin matsanancin faduwar gaba, juyawa ya yi ya shige ya barshi nan kar ya hadasa masa hawan jini, Ayya bata falo dan haka ya haye sama dakinta dan ya san Aghali wanka ya shiga ..... Yana zuwa ya gaisheta kamar yanda ya saba sannan ya zauna daf da ita yana dan mamatsa mata kafarta, Ayya ta ce" Mu.azam ya zo min da maganar yana son auren Agaishat, Wardugu dake rike da kafar Ayya yana matsawa sai tsayawa ya yi tsam da matsawar yana duban kasa, Baka ji bane? Ayya ta fada, A hankali ya dago dubansa ya sauke kanta, idannuwansa ya lumshe dan ji yake har kansa ya fara sara masa sanadiyar faduwar gaban da yake ji, me ke damuna? Ya tambayi kansa, me ya sa da an kirayi sunnan yarinyar nan ko na ganta sai na ji faduwar gaba? Kansa kawai ya gyadawa Ayya, Bakinta ta yatsina ta janye kafarta da haushi haushi ta ce" Wardugu bafa na son rainin hankali, ya zan fada maka magana ka wani gyada min kai sai kace inai maka wasiya? Wardugu ya hadiye yawun bakinsa da kyar ya ce" Ayya, wai ya aka yi bakya yiwa sunana kara irin na d'An farin nan? Sai kawai in ji kin kama sunana kai tsaye wai Wardugu, Ido ta zaro tana dubansa yanda ya yi maganar walahi sai ta ji wata kunyarsa ta kamata, ai kuwa ta juya ta dauki filo ta juyo dan buga masa sai gani ta yi ya fice da gudu a dakin, Murmushi ta yi ta ce" ja.iri, ja.iri, ja.iri, ! Zan yi magana da yarinyata , in dai tana son sa, zan baiwa Aghali sako ya je da kansa wajen Mahaifanta idan sun amince ya kai kudin aurenta a daura kawai, Allah ya sa Alhairi ne...... To fa๐Ÿฅด๐Ÿฅด๐Ÿฅด๐Ÿฅด ๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž ๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ *BAK'A CE*๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ Na *SAJIDA* *ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ____________________________________ *๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4๏ธโƒฃ2๏ธโƒฃ Alhamdulilah Alla kulli halin... A wannan rana bayan Wardugu ya ajiye su agaishat saloon dan yin kitso suka zarce park dinsa tare da samarin, inda Aghali ya zabi daleliyar mota irin ta ratsa rairai mai shegen tsada, Bayan sun gama magana da yaron Wardugu, Mu.azam ya tsaya gurin wata mota mai ruwan ash , karama mai kyan gaske, kallonta yake yana murmushi, Wardugu ya gama da Aghali yace" ku mu je .... Mu.azam ya ce" wardugu, wannan motar nake so, Aghali ya ce" me zaka yi da motar nan kai kuwa? Ta mata ne fa, Mu.azan zai bashi amsa ya ji lumlumlum lema a hancinsa, Da sauri ya juya yana mai ciri hankicin a aljihunsa ya goge jinnin da ya zubo masa ta hanci, a hankali ya karasa motar Wardugu ya bude baya ya shiga ya jinginar da kansa jikin kujera, Ajiyar zuciya yake saukewa yana kara goge jinnin inda wata number ta fara shigowa saman screen dinsa, number saudiya ce, A kasan zuciyarsa ya ji nutsuwa da number dan haka ya daga ya yi shiru ba tare da ya yi magana ba, Ajiyar zuciya ta sauke kafin take share dan guntun hawayenta, so take ta yi magana tana tsoron kar ya ji muryarta ya kashe , ta godewa Allah da da ransa, ta godewa Allah da ya daga wayarta duda bai san ko wacece ba, A hankali ta ce" ina son ka Mu.azam Sai da ya ji wata kasala, a hankali ya dubi screen din, ya mayar kunnensa, ji ya yi wata nutsuwa na kara ratsa shi, a nitse ya ce" docterna, me kika je yi saudiya a tsakiyar shekara? Idannuwanta ta lumshe ta ce" na zo rokar Allah ya baka lafia, ya nuna min jininka a duniya, Murmushi ya yi ya girgiza kai, ya ce" kin ga jini ke zuba a hancina, bayan ina son na yi aure, har na saka a tambaya min auren yar, ina son yarinyar a raina ina son na aureta koda shi kadai zan yi a duniya, Wani irin faduwar gaba ta ji, jikinta ya dauki rawa, a hankali hawaye ya shiga zarya a idannuwanta, a hankali ta ce" zaka aureta, kar ka damu, zaka rayu Mu.azam, Shima idannuwansa nasa ya lumshe yana mai jinta gaba daya jikinsa, yana son yarinyar nan fa tamkar ransa, sai dai ba zai yarda haka ta faru da ita ba, ba zai yarda yana ji yana gani ya tsareta haka ba, ya sani ne idan ya nuna mata eh yana so zata sakawa ranta da zata jima da shi bayan yana ji a jikinsa an kusa zare sauran numfashin da ya ragewa gangar jikinsa, A hankali ya datse kiran inda ya shiga shafa kansa yana mai jin jikinsa ya dauki zafi,, a hankali ya furta Agaishat ki aminta da ni na dan lokaci, ina son ki kema (๐Ÿ™„) Wardugu da kansa ya fitarwa da Aghali motar nan dan baya so a komawa su yi mota daya, yana gama fitar masa da komai ya bashi hannu ya ce" aboki, ka gama da Muhsin ni sauri nake, Amanda aghali ya yi inda ya raka Wardugu da kallo yana ayyana a ransa ko

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 22

WAReaders TGUpdates