da inglish duka , bayan an gama jirgin ya fara tafiya wace suuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu ne saman doguwar hanyarsa har ya zo wajen hatsarin wato tashi da saukar jirgi ba, Cikin adu.a a bakin Ayya Nan fa ake yinta domin abin tashin jirgin nan, kun san ko wanda ya saba sai ya ji cikinsa ya yi kasa bale wanda shigarsa ce ta fari kuma sha.af Ayya ta sha.afa da fada mata abinda kan iya zuwa sannan tace da ita tashi zasu yi sama, ita kuwa a kauye baba sofo ya taba gaya mata akoy harda wani abin mai tashi sama a birni sunnansa jirgi , Ai gaba daya ta shiga jijiga ta damki cinyar wardugu dake gefenta na dama ta damko ta ayya ta bude baki ta........ 🤣🤣🤣🤣 ku taro su kauyawa a birni🤣😂😂😂😂😂 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2️⃣0️⃣ Ido Wardugu ya zaro, ya kai kallonsa kan hannunta wanda ke dauke da dogayen akaifu domin ba wani cire su take son yi ba sai baba sofo ya sakata gaba take yanke akaifunta sai tace nai ai susa take da su, Wardugu bai gama tantance meye haka ba ya ji wani irin ihun da ya yi barazanar tarwatsa masa dodon kunne, A tare suka juyo wajenta shi da Ayya ...... Ayya cikin yannayin tashin hankali da yaren tubanci ta ce " Wardugu Wardugu tsoro ne take ji na manta ban fada mata ba, kuma ban riketa ba , mai yiwuwa bata taba ganninsa bama bale ta shiga; Bak'a da jikinta ke bari gaba daya ta kwalallo idannuwanta, daurin dan kwalin nata ya kunce , hawaye tuni sun kama zarya, ihu kawai take tana ambatan innalilahi wa.ina ilaihi raj.une! Mutanen dake kusa da su harma wa.inda ke dan nesa da su ne hankalinsu ya fara tashi du aka fara jiyowa wajen su Ayyar da ayyar tambaya da alamun tsoron a fuskokin su.... Daga can kofar masu kula da passenger wata mata mai kulawa da bukatun passenger ta fito da sauri da dan sket dinta, ta sha kwaliya, tana dan sauri tana fadin kowa ya zauna kowa ya kwontar da hankalinsa ba komai bane , sannan tana nufo wajen su wardugu; Hannunsa ya daga na dama ya shafa sumarsa, a kasan zuciyarsa ayannawa yake wannan wani irin tashin hankali ne? Shi Wardugu da girmansa da irin yanda duniya ta san shi, shine za.a yiwa taro da yar kauyen nan! Merde! merde! merde! Juyowa ya yi wajenta, hannunsa na hagu dake kusa da ita ya saka ya janyota jikinsa, ya sakata a jikinsa da hannun nasa ya karkata fuskarta gefen hannunsa na dama , ya saka hannun nasa na damar ya yiwa bakin nata mai ihu wata damka ...ai kuwa shiru kake ji ba ihu ba di kira da salamcewa sai dan mutsu mutsu wanda shima da ya kara riketa sai laf tamkar ta lafe ne a jikinsa. (WARDUGU kan keta) Tambaya matar nan take lafia ? Me ke faruwa?? Wardugu gannin bakuwa ce yar amerika, sai ya ciro carte dinsa da hannun hagu dinsa ya nuna mata mai shaidar ko shi waye, sannan da lebensa ya yi mata nuni da mahaukaciya ce kar ta wani damu........🤔 Ai kuwa ta shiga bada hakuri da iya yi, ta juya ta koma. Ayya sai faman ya cika yarinya take aman ya tsareta da ido ya ki yin maganama; Nauyin da ya ji ta yi ne ya saka shi sasauta rikon, ba.a wani dauki lokaci ba Agaishat ta yi baci sai kace wata baby, bacin tsoro da tashin hankali, bacin wahala, gashi daman daren jiya ba wani bacin kirki ta yi ba dan tsoro da zulumi, sai ajiyar zuciya take saukewa du ta goge hawayenta a jikin rigar wardugu. A hankali wardugu yake kokarin kwontar da ita jikin kujerarta, Ayya ta zabga masa harara ta jinginar da Agaishat a jikinta tana kara tabata dan tabatarwa in ba suma ta yi ba. Murmushi Wardugu ya yiwa mahaifiyarsa na alamun bada hakuri kafin ya jingina yana duba agogon hannunsa domin tafiar idan Allah ya yarda ba wata mai tsayi bace a jirgi tsakannin Agadez da Niamey. Allah ya sauke su lafia, Wardugu da kansa ya tuka motar da ya je da ita ya ajiye aeroport , Bai zame ko.ina ba sai gidan Ayya. Suna zuwa Ayya ta yi hamdallah ta kamo Hannun Bak'a wace ke kallo da baki da hanci da ido gaba daya Fitar da ita ta yi ta ce" mu tafi yar gidan Ayyarta A hankali ta fito itama kamar yanda Ayya ta koya mata ta bi bayan Ayya tana waiwayen Wardugu da ya fitar da kafarsa guda waje yana ta faman yamutsa gashin kansa, wayarsa ya ciro yar karama ya dannawa abokinsa kira wato docter DOCTER MU.AZAM Yana dagawa ya ce" Ranka ya dade oga *Wardugu Marahut* Wardugu ya ja tsaki ya ce" Mu.azam ni za ka yiwa rashin mutunci? Yaushe ka fara karya? Mu.azam ya yi shiru, ......tamkarma ya kashe kiran. Wardugu ya duba ya ga kiran na tafia, ya kara karawa a kunnensa ya ce" kai! Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya ya ce" abokina, ka yi hakuri ka ji? Jikina ne ya tashi aman yau nake fita asibiti in sha Allah da na huta sai na kamo hanya. Wardugu da ya gama jin abinda ya fada, cikin mutuwar jikin da bai san ko na meye ba ya ce" me ke damun ka ne harda kwonciya hopital? (HOSPITAL) Mu.azam dake kallon karin ruwan da aka saka masa ya lumshe idannuwansa, jiki a mace ya ce" idan Allah ya kawo ni zan fada maka koma menene, Wardugu ya sauke ajiyar zuciya, bai bashi amsa ba ya katse kiran ya rufo motar ya tayar dan ya samu ya karasa gidansa ya huta .......................... TIMIYA Rana ce, karfe biyu na rana ne, aman da dan lulumi kamar yanda garin ya saba, A kasan innuwa suke zaune su uku suna yamutsa garin kwakwi da mai da yaji da manda (gishiri), Fatimata ce mai kwadawar, Ayya na yiwa maryama susa a kanta Mariama ce ta dago ta ce" Fatimata kar ki hade yajin nan duka ki ware min a robar nan kuma kar ki zuba mai iya shi din sai mandan ya isa kin ji? Fatimata ta amsata da kai, Ayya dake mata susa kuwa a ranta take tambayar kanta Mariama ko ta daina cin yaji ne? Kai ina Mariama da yaji ai akoy amana. Fatimata na gama warewa, Maryama ta mike ta dauki dankwalinta ta daura, ta dauki robar ta nufi wajen tulun Anna kwaya biyu dake cike da ruwa ta dauki guda ta dora saman kanta ta kama hanyar fita, Kallonta suke da mamaki, Fatimata ta ce" Mariama ina zaki tafi kuma? Ki bari mu ci mana. Mariama ta juyo ta ce" ki ware min nawa, zan je wajen Sofon nan na Agaishat na dubo shi ne, Murmushin da Anna ta jima bata yi ba ta saki, sanyi ta ji a ranta daman tana ta tunaninsa halin da yake ciki mutumen kirki Mariama oga kennan, Mariama ba daukan raina, Bata zame ko.ina ba sai majalisar mahaifinta, Tana zuwa ta mika masa hannu ba alamar wasa ta ce" kudi nake so Aba, Bakinsa ya yatsina, Mariama fa ta fara isarsa da wannan ya bata ya batan, tunda ya karbi kudin aurenta take tatikarsa, idan ya nuna ba zai bada ba kuwa a ji su, Rai bace ya saka hannunsa a aljihun rigarsa ya ciro dala dari ya mika mata a ransa yana adu.ar Allah ya sa ta karba kar ta ce ta yi mata kadan! Karba ta yi ta maida tulunta da robar saman kanta ta juya ta nufi gidan mai goro.... Nan ta sayi goro har na dala Ashirin, ta sayi man zafi na ciwon jiki ta sayi yar tsintsiya, dauka ta yi ta nufi runfar baba Sofo. Tana zuwa ta yi salama har sau biyu kafin take jiyo muryarsa can kasa yana amsawa; Shiga ta yi tana wara idannuwanta dan ganni da kyau domin ta biyo rana idannuwan nata duhu suke ganni. Yana kwonce fuskarsa na dubinta, ya takure ya kara yamutsewa da cazbaharsa yana ja kuwa, Bata yi masa magana ba ta karasa inda ta ga tulun ta jawo ta fitar da shi ta wanke shi tas ta juye ruwan nan na cikin tulun Anna, Ledojin da suka shihigo da kararuwa ta tatare ta fitar kafin take juyowa ta shiga share bukar inda baba sofo ya samu ya zauna yana binta da kallo da mamaki a kasan zuciyarsa; wannan ai yayar Agaishat ce, mai fadan nan, ikon Allah kawai yake fadi a kasan zuciyarsa. Tana gamawa ta dauko robar abincin ta debo ruwa ta dawo ta darwaye hannunta ta zauna, ruwan nan ta kara yayafawa garin dan ya kara yin laushi sosai, tana yi bata ko kallonsa dan ta yi imanin ya tsareta da ido ne,............ Sai da ta kai bakinta ta ji idan mutun yace tsotsama zai yi tsaf zai tsotse abinsa ta dago da dubanta a hankali ta kai wajen baba Sofon dake kallonta ta ce""" 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2️⃣1⃣ Ta ce" ga abinci, ina magurjinka? Hannunsa dake dan rawa ya saka ya fitar da magurjin ya mika mata yana kallonta dai, Mikewa ta yi ta wanko magurjin da goron, sannan ta dauko wata yar roba mai marfi da ta amso wajen mai siyar da goro ta kara darwayeta itama, ta dawo ta zauna ta saka yar farar leda a kasan abin gurzawar ta shiga gurza goron nan manya har uku; Robar ya saka hannunsa ya janyo, bismillah ya yi har zai fara ci maganar Bak'a ta dawo masa inda take cewa < ka ringa wanke hannunka Sofo, ka ga jiki na iya daukan dati mai yawa banda ciki ka ji sofona? > Dubansa ya kai wajen Mariama, a hankali ya ce" Mariama? Dagowa ta yi tana dubansa bata amsa ba, Baba tsoho ya ce" ina kwana, Mariama ta kifta idannuwanta ba wani dar ta ce" Lafia, still tana kallonsa Murmushi ya yi ya yi mata nuni da kofin ruwan dake hannunta sannan ya nuna mata hannayensa. Tasowa ta yi ta karasa, dukawa ta yi ta kamo hannun nasa ta wanke masa da kanta sannan ta kuma ciko kofin ta ajiye masa ta koma ta ci gaba da gurza goron ba tare da ta furta masa kalma daya ba. A hankali baba ya fara cin garin nan, yana ci yana dan kallon yannayin Mariama, Mariama ikon Allah, Mariama mai albarka, A hankali ya ce" nima ina jin rashinta sosai, Mariama ta dago kanta ta zuba masa ido, murya a cinkushe ta ce" dan me ka rabata da danginta? Sai da baba Tsoho ya hadiye wanda yake dan tsotsa a hankali ya dan kurbi ruwa ya ce" dan ta rayu cikin nutsuwa, ta samu inci kafin ta yi kaura zuwa lahira Mariama ta ce" a wajen danginta, a kusa da mahaifiyarta ta fi samun inci Sofo! Idannuwansa ya dan lumshe kafin yake budewa ya ce" ta yaya? Ta hanyar ta kare rayuwarta a bakin titi? Ita ko arzikin mazan zamanin ta kasa samu idan sun shigo gari da gari dan jar fatar yayanmu ne da gashi da kyau! Ba ruwansu da tarbiya, usuli , da halaya! Burinsu shine au samu iri mai kyau ....bayan su kansu idan suka kalli kansu a madubi zasu gane cewa a da ba haka Allah ya halice su ba, kwonci tashi kuma fatarsu sai ta dawo irin tawa idan Allah ya nufa masu tsayin rai ne, Su da ka hadata da su din kana da tabacin a inda zasu kaita ba.a kyamar bakar fata? Mariama ta maido masa da amsa du a hargitse da yannayin bacin rai tamkar a lokacin ne za.a tafi da Bak'a, Baba tsofo ya ce" birni da kike ji ana fadi, wata duniya ce a cikib duniyarmu mai cike da abubuwan al.ajabi, A birni mutane basu da lokacin dan kina da fata baka ko dan kina da muni ya kasance du idan kin zo waje za.ana kwagirar ki ko a hantare ki! Sannan birnu cike take da mutanen da kwakwaluwarki ba zata iya hasaso maki ba, idan wani ya tsana wani zai so.......Mariama, ku yi hakuri. Kanta ta mayar ta ci gaba da aikinta, tana gamawa ta ware masa wanda zai ci a lokacin sannan ta zuba masa sauran ta kai kusa da dardumarsa ta ajiye masa ta ajiye tsintsiyar a gefe, ta fitar da sauran canjin kudin ta ajiye saman dardumar ta dauki robar Anna da tulunta ta juya, Har ta fita ta dawo ta duka kusa da shi kanta a kasa da yaren buzancinta ta ce" ta kasance abokiyar fadana, wace idan na tashi itace kanwata ita nake cin zali, takan kwaso kayana ta wanke min, idan dare ya yi can tsakiyar dare in na je juyawa sai in jita nanake da jikina, sai in rungumeta sosai a jikina ita da marigayiya, sai gashi lokaci guda a cikin kwana goma na rasa su! su duka biyu, ita wace ta rasu ina binta da adu.a baba wace kuwa take raye inai mata adu.a sannan zan yi iya yina dan gannin na kyautatawa wa.inda take so take kyautatawa, haushinku nake ji ku duka har Annar! Tana gama fada ta mike ta yi gaba abinta . Baba sofo ya yi murmushi har cikin ransa ya ji dadin haka, ashe dai Mariama na tare da ikon allah, Mariama kennan Allah ya sa ranar da zaki hadu da yar uwarki ki bini da adu.a koda na mutu. NIAMEY Doguwar riga fara kar ce a jikinta mai siririn hannu aman tsayinta har kasa, irin mai laushin nan ce bata da kwaliya ko das ta tafi ne ta bi tsarin halitar jikinta, Kamshi take bazawa du inda ta gota sai fai fuskarta ta cabe da hawaye tana biye da shi, Murya a raunane ta ce" WARDUGU, nice ya dace na yi fushi irin yanda ka wulakantani, ka banzatar da ni a cikin duhu a garin da ba nawa ba , a garin da na je dominka, ka fice ka barni, sannan da safe da ka dawo ko ka kali motar da ka bar ni a ciki, ka yi tafiarka wajen mamanka ni kuwa ko oho! Shine dan na tafi zaka dauki zafi da ni haka? Wardugu da ya gama saka mabalin rigarsa ya juyo ya kare mata kallo, a ransa ya ayyana '''''rainin hankali kennan, ta dawo daga tafiarta wace ta isa da kanta , shine aka sha karamar riga aka sha wankan turare aka zo ni ga maye ga mai jira aka kawo min na karbe ko? Murmushi ya sakar mata kafin yake binta da wani mugun kallo irin na rainin nan, ya dauki yar karamar wayarsa ya bar ta chating din nan ya dauki ky din mota domin garin da hadari hadari baya son ruwa ya foke shi yau, ya fice ba tare da ya furta mata ci kanki ba; Da kallo ta bi shi kafin take zama bakin bed din tana shafe idannuwanta, bakinta ta zumburo a fili ta furta" zaka sauko ne, haka kawai ka wani hada ni shakar numfashin wannan uwar taka harda wata karin malatin? Naki din wardugu! Na ki na shirya da mamanka duda baka tambaye ni ba na san hakan kake so sai dai ni a gaskiya ba zan iya jure mulkinta ba sai kaceatar wani sarki dan tana uwar General! ........hum Wardugu bai zame ko.ina ba sai aeroport, yana zuwa ya ajiye motarsa ya shige ta wajen sojojin dake tsaron kofar bayan sun sara masa ya shige ciki ya haye wajen tarban baki Bai kai ga karasawa ba ya ji muryarsa ya ce" mek (men), Juyowa ya yi, arba ya yi da amininsa, abokinsa, Mu.azam zaune saman kujera, gilas a idannuwansa ya saka costume kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai sheki take.....sai dai abinda bai masa ba irin yanda ya rame Yana kallonsa har ya karaso inda Mu.azam ya mike tsaye yana murmushi ya bude hannayensa irin ya zo ya rungume shi , Ido Wardugu ya zaro ya nuno shi da yatsa ya ce" kai ko? Mu.azam ya saki dariya yana kara kure Wardugu da kallon yaushe rabo ya mika masa hannu ya ce" Asalamu alaika amini Wardugu ya karbi musabaharsa yana mai furta" amen wa.alaika salam amini, Murmushi suka yi kafin suke gaisuwar larabawa, Wardugu ya yatsina fuska ya ce" kai dai ka cika naci, gaisuwar nan ta wani runguma ba wani sonta nake ba aman sai ka wani damki mutun kato da kai! Mu.azam ya bushe da dariya yana biye da shi inda soja guda ya karbi jakar Mu.azam dake hannun wardugu ya shiga ja har wajen mota ya bude ya saka masu ya juya bakin aikinsa, Wardugu ke jan motar yana dan kallon Mu.azam jifa jifa, a kasan zuciyarsa yana tare da damuwa na abubuwan da ya gani a tatare da Mu.azam wannan zuwan, ya rage magana, ya rage fara.a, ga dan cazbi a hannunsa yana dan dadanawa, ga rama da ya tafka ta mamaki sai dai fatarsa ta gyaru ta yi fresh aman ba alamun yana jin dadin rayuwa..... Haka har suka karasa gidan Ayya wada rabonsa da gidan kwana hudu kennan tunda ya kawo su bai samu aiki ya barshi ya zo ba , aman ita Ayyar ta ue har wajen aikin ta amshi carte dinsa ta banki wai zasu je shopping ita da sabuwar yarta, ya yi murmushi da ya tuna irin kudin da suka kaso, Ayyarsa uwarsa Ayya manya....... Zaune Ayya take saman kujera tana kallon yanda Agaishat ke dan turo baki tana kallon Ayyar da yannayin abin tausayi, Daga ita dai gajeran wando da yar rigar da Ayya ta yi mata jan ido kafin ta yarda ta zauna da su dan ta shafa mata gomage a jikinta da fuskarta tamkar amarya, gefe hijab dinta ne baki dan kar kalar abin madarar
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN