iska ya zo kusan babansa ya ce" aban Wardugu ka sake ta, ka rufa mani asiri ka saketa , kar ka yarda wani abin ya shiga tsakaninka da ita, Aba, wannan bata da tarbiya, bata da haramun! Abanna ya zaka kawo macen da ta gama talatarmin da kanta a irin yannayin da ta fado duniya ni danka a matsayin matarka? Haba Abana, me mukai maka da zafi haka? Marahut ya dube shi ya ce" ita ba mutun bace? Kun haihu da ita ne? Na yi niya ina sonta na aureta da kudinka ne? Ka bini a sannu Wardugu, ni na haifeka kar uwarka ta zigaka ka kauce hanya! A lokacin ni tuni na fara gannin jiri, ni Marahut? Na sha dukan kirji nace ni mijina dan goyo ne, ba zai wulakanta ni ba, sai gashi haka ta faru, ni ba aurensa ya dame ni ba, tau da gobe ai sai Allah Allah wacece ni da zan ce ba za.ai min kishiya ba? Damuwana irin auren da ya yi, ya yi shi dan ya nuna min iyakata? Dan ya wulakanta ni? Ko wani abin ke tsakaninsa da yaronsa mai zafi haka? A lokacin Wardugu ya fara wani irin numfashi, idannuwansa suka shiga canza launi zuwa ja, suka cicika da kwallah, ina gannin hakan na tisa shi gaba da kyar na samu muka shiga motarsa na ja muka nufi gidansa, Muna zuwa muka tarar da Wakyn ta zo nemansa, a nan ya sauke haushin kanta domin sai da ya bala mata hannu du ya kusan canza mata halita baiwar Allah da kyar aka kwaceta, Kin ji marabina da gidan Marahut domin akai ruwa aka yi iska Wardugu ya hau, ya gindaya rantse rantse, ya juye, nima fushi, mamaki, tsoron lamarin maza ya saka na yi watsi da shi na rungumi yarona wanda na san a duniyarnan ni ce duniyarsa ,..... Ayya ta karasa tana dan shafa kan Agaishat, Agaishat ta dago fuska shabe shabe da hawaye,, tana duban Ayya , ta sani bata da damar da zata iya tofa wani abin a wannan lamari domij ta yi imanin ba komai Ayya ta fada mata ba, tabas ta boye wani abin ko dan karancin shekarunta, Sai dai wannan lamari ya tuna mata mahaifiyarta, Anna baiwar Allah, yoh ita haka rayuwarta ta kare fa, kuma bata da wani mai dauketa ya matsata daga wajen da ake cuzguna mata, ita bata san bama marainiya ce ko yar dangi, bata san daga ina ta fito ba, ba abinda ta sani, A hankali ta mayar da kanta saman cinyar Ayya , daidai lokacin da Wardugu ya shigo dakin da salama, Daga inda take kwoncen nan take kare masa kallo, tabas wardugu ko bashi da ko sisi sai mace ta yi haukansa, ko bashi da hali zai mitsa zuciyar mata, dan farin batube mai zamani, Idannuwanta ta lumshe a hankali wani hawayen ya kuma zubowa daga gurbin su ta mike a hankali bayan ta share hawayen ta kai dubanta wajensa , kanshin turarensa ya cika mata hanci, A hankali ta ce" ina yini, Gaisuwar da tunda suka daukota daga timiya shi dai bai taba jin ra yi masa ita ba, tsumamun idannuwansa ya zuba mata ba tare da ya amsata ba, yana kallonta har ta fice a dakin dan basu waje su tatauna ta nufi wajen Mu.azam dan gannin ko ya ci abinci? Ayya ce ta lakato shi tana yi masa murmushi tana saisaita kanta ta ce" dan gidan Ayya, sannu da dawowa, Wardugu ya juyo da sauri yana dubanta, ya yi murmushi ya ce" Ayyana, ina yini? 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 3️⃣4️⃣ Amsawa ta yi tana dubansa da madaukakiyar kulawa kafin take mikewa ta kama hannunsa, Shima biye yake da ita suka fito daga dakin Agaishat suka nufi dakinta, Walyn ce zaune a saloon mai suna Tawaye saloon, fitacen saloon ne na manya wanda sai ka isa kake saka kafarka, Akifunta ake gyara mata bayan an yanyanke su an wanke su sosai aka dauko na kanti zako zako din nan aka shiga dora mata, Kawarta dake gefenta tana karanta magazine, itama ana gyara atach din da za.a yanyara mata kitso ........ Wata mata da ta tsare Walyn da kallo tunda ta shigo ce ta yatsina fuska, a ranta ta yi murmushi tana ayyana ba laifi , matar tasa bata da laifi, Kadan ta dan muzguta ta dubi cousint dinta dan daudu wanda suka zo gyaran gashin tare da shi ta ce" ina son aikin General a rayuwana, ina son yanda yake cin uwar kananun yan iska! Kallota ya , ya wani yi far da idannuwansa, ya yatsina fuska tamkar mace ya ce" ke kawa, ya iya tata rashin mutunci ne fa, mutumen nan kin san da matar tsohonsa ce ya rufe? Uhum ke ni ko a lahira bama fatan mu hade da General Wardugu domin bashi da mutunci, ya iya aiki da doka, ke matarsa fa ta yarda ta kai dare a waje sai ta kwana a cel! Daman inda take so a tabo mata kennan dan haka ta maida hankalinta sosai ta kali dan daudun nan ta ce" kawaliya matar naci ta taba daraja ne? Walyn dake kalonsu tana kada kafarta, ta kai dubanta wajen mai saloon din, ta maida wajen kawarta da ta yi kasake itama tana jiran gannin me zata yi? sai sauran matan dake wajen da yan tsirakun ya daudun dake wajen suna suba nasu sha.anin..... Walyn ta saki murmushi mai ciwo, ta daga idannuwanta cike da isa da takama ta ce" Wardugu kennan, mijin mace daya, jarimina mai ban tsoro, Warduguna zazafa ne, kawata kin san Wardugu baya bin kadangarun bariki? Ke na yi imanin da Wardugu na bin mata zai je ya zabo zuga zuga ne, wa.inda idan ya zaga zai dire chek ba wai ya dane karamar yar bariki ya kasa iyanta harda kason shekara sanadiyar rabuwa da mace ba! Dan daudun nan ne ya sheke da dariya yana duban matar da suka zo tare, wace ta ji abin tamkar saukar guduma domin mijinta ne ya jewa wata yar bariki ya ki biya sannan ya yi mata duka hakan ya sa harda su kaso, wani tukukin bakin ciki ne ya taso mata, bata tsamaci jin haka ba , abin ya dake ta, Kallonta ta yi da yannayin bacin rai ta ce" ke Walyn kike ko wa? Kin san ko wacece ni? Walyn ta fizge hannunta daga hannun mai saka mata farcen ta ce" ke ce katuwar yar barki marar aji! Sai me kuma? Mikewa ta yi itama ta ce" ke din ba yar barikin bace? Ke naki a boye kike yi ko ji kike ba.a sani ba? Meye bambancinki da yar bariki? Ke kawai bakya yi dan kudi ne aman menene bakya yin? Ko dan kina rufe takunki ne baki san wa.inda kuke labewar da falasawa ba? Ki jika ki ajiye Wardugu General ya fi karfin zama da mace daya wace na sani ne bakima goge a kai shi wata duniyar ba! Zaki ga aikin gogagiyar yar bariki domin Wardugu katuwar kadara ne wanda malakarsa sai tsayaye ba isa ce zata kai ki ba mu je zuwa!...... Walyn ta yi murmushin rainin hankali kafin take bufe jakarta, Yan jika goma goma ta fitar dami guda ta bale yar takardar dake zagaye da su wace itama sai kyali take, ta dauki bakin gilas dinta ta jefa katuwar wayarta a jaka ta juyo sosai wajen matar da sauran mutanen saloon din ta daga kudin nan ta sake su a iska wanda hakan ya saka du suka shiga wawusoso harda mai saloon din da yarenta kiwa na nema har wasu suka shiga dambacewa , aman banda wace ake kira da kankana! Walyn ta bi kawayen da kankana ta zo da su da ido ta ga suma sai wawa suke harda yan daudun, Yatsina fuskarta ta yi ta ce" abokin mai kanwa ba ya rasa burbudi, Wardugu ya daure min a niger tunda ya sakar min yayan banki, na kwana lafia koda Wardugu ya shiga tsakiyar yan bariki ba zata motsa ba domin kyankyaminku yake! Ta kara taku har gabanta ta zaro idannuwanta ta ce" ki sauke girman kai ki duka ki kwashi kudi.....su kike kwadayi! Iska ta ja ta kaiwa Walyn duka warda itama ta damketa suka shiga dukan junnansu, Sai da suka lilisa junnan su sannan mutanen wajen suka shiga tsakanin su kowace na haki, Walyn ce ta warce jakarta ta yi gaba inda kawar tata ta biyota da gudu tana kiran ta tsayata, aman ina cikinta take ji yana wani irin hautsina mata, bata san me ke damunta haka ba yanzu, ya kasance tana yawan jin abubuwa a tatare da ita, Wardugu ya jima wajen Ayya, inda suka tatauna sosai sannan ta saka shi a gaba kan sai ya ci abinci, Agaishat na fitowa ta nemi Mu.azam, sai dai bata ganshi ba hakan ya saka ta fice ta nufi wajen runfar Ayya mai wani ni.imtacen sanyi tana neman Mu.azam, Nan kuwa ta same shi, ya kurawa waje daya ido, ya zurfafa sosai a tunani wanda yannayin fuskarsa ta nuna ba tunanin dadi yake yi ba, A hankali ta karasa ta kuma maimaita salamar da ta yi ta yi masa tun daga dan nesa da shi, A dan tsorace ya kalota kafin yake daidaita yannayin fuskar sa ya amsata yana mai kokarin gyara mata kujerar dake kusa da shi, A hankali ta ja ta zauna tana dubansa, yannayinta ya nuna itama ta shiga damuwar da yake ciki, A hankali ta ce" me ke damunka ya Mu.azam? Daman ita yake kallo, dan haka ya bi bakinta da kallo yanda ta fadi maganar a hankali sannan a cicire domin dai tana faman koyon yarensa ne, A nitse ta janye idannuwanta daga cikin nasa, domin kallo nr yake mata tamkar zai fada idannuwan nata take ji, A hankali ya ce" Agaishat, Ta dago tana dubansa, inda a take ta ji gabanta ya fadi da yannayinsa, Mu.azam ya ce" kin san soyaya? Agaishat ta zaro idannuwanta tana dubansa, tama rasa me zata ce da shi, Mu.azam ya ce" kin taba yin saurayi wanda kika ji kina so? Agaishat ta saki murmushi mai kama da na sakalci, domin ita abin har ga Allah dariya ma ya bata, A hankali ta maimaita kalmomin" *So, Soyaya, Saurayi?* Mu.azam ya dan kankance idannuwansa ya ce" yeah, Agaishat ta dube shi, duba na ido da ido kafin take fadin" *Ban san shi ba*! Da mamaki yake kallon ta, bata san shi ba tace fa? Aman daga ina Agaishat ta fito haka? Ko dai masu son nata ne basu yi mata ba? Yin wannan tunanin ya saka gabansa ya fadi, a ransa ya ayanna ya salam, kar dai a je nima ban yi mata ba,? Muryarsa sanyaye ya ce" du a maneman soyayar ki ba wanda kika taba jin kina so? Agaishat dake dubansa itama, bata dago ina ya nufa ba, domin dai ita ba.a taba kamanta za.a ce ana sonta ba, dan haka ta bashi hankalin ta sosai ta ce" ba wanda ya taba fada min ya ake so din ne, Dariya ya shiga yi kasa kasa yanai mata wani duba kafin yake fadin" ba fa zolayana nace ki yi ba Madame, Bata san kalmar madame ba, aman ta gane yana nufin wasa take yi masa, dan haka ta ce" ban taba yin saurayi ba, ko an zo zaben yan mata a gidan mu ba.a taba zabena ba, Ba yace dan na cika baki da muni, ni ba alkhairi bace dan baki ba alkhairi bane, hakan ya sa ba mai zabena bare a biya sadakina, har kanwata an zaba sai dai kafin auren ta rasu ita, Dubanta yake har ta gama yi masa bayani da kwatance da komai dan ya gane da kyau, ajiyar zuciya ya sauke a ransa ya ayanna na godewa Allah ai da basu zabe kin ba da sun saka ni a ukunna, A fili kuwa ya ce" wa ya fada maki baki ba alkhairi bane? Agaishat ta ce" da alkhairin ne, da mahaifina bai kyamace ni ba da alkhairin ne da nima ana yi min dinkuna irin na yan uwana, da alkhairin ne da jama.ar gari sun mutunta ni a matsayina da dan adam mai daraja a cikin halitun Allah, da alkhairin ne da na yi saurayi koda mahaukaci ne a *Gida*, Katseta ya yi da fadin" aman sai na ga kina da ilimin adini sosai, ya aka yi kika kasa imani da haka? *Agaishat , malamata, wa ya halici fari da baki,?* Agaishat dake dubansa ta sada kanta a hankali, kafin ta ce" Allah ne, Shin da ya halici baki ya kawo wata ayya a alkur.ani mai girma, a hadissai ko wani litafin na adinin fake nunin bakar fatar nan da ya halita ya haliceta ne dan wani laifi? Ko mai wani laifi? A hankali ta kuma fadin" aa, ban karanci haka ba, Mu.azam dake dubanta ya ce" Bilal, bawan Allah, wacece kalar fatarsa? Ya darajarsa take? Dago da idannuwanta ta yi ta ce" baba tsofo ya ce shi ne ya fara kiran sallah , ya ce mutun ne mai daraja, makusancin fiyayen halita, Mu.azam ya gyada mata kai kafin yake ciro wayarsa ya samo hoton ka.aba ya ce" zo ki ga ka.aba a hoto Agaishat, zo ki gani... A hankali ta matsa tana kallo, kalar bakin ya tafi da imaninta, abin ya yi mata kyau a ido, a hankali ta kai yatsarta ta dan shafa hoton, A hankali ya ce" ba wani bawan da ya fi daraja, ya fi kusanci fa ubangijinsa sai mai yi masa biyaya, mai tsoron shi, mai kiyaye dokokinsa, a cikin nan kin ji an ce *Farar fata ta fi bak'a?* Agaishat da take jin wani yamyamyam a jikinta na dadi ta girgiza kanta, Mu.azam ya ce" makafi ne ko kwakwaluwar su bata ja? Ya aka yi basu yiwa abin kaunata wawa ba? Da sauri ta kallo shi, Kansa ya dan sada ya ce" kina da tsararen kyau, fitinanan kyau, baki da tsayi Agaishat...baki da kiba har can, yannayin jikin ki ya tafi da yannayin tsayin ki, Bakin ki ba mai tabo bane bare shaida, gaba daya ya tafi iri daya ne baki mai haske mai nutsuwa, agaishat, fuskar ki yar doguwa ce mai dauke da dara daran idannuwan da a kowani yannayi kike su kadai sun ishi mutun, Agaishat Allah ya tsara ki da hanci mai tsayi mai yan kofofi wanda ya yi das da dan madaidaicin bakin ki, Rashin hayanniyar ki ya hadu ya kara kawata halitar ki, ke da ba dan kar na kauce hanya ba da na fada maki sauran tsaruwar ki, Dan dakatawa ya yi gannin yanda ta zuba masa ido, sai a lokacin ya tuna ya saki baki sai zuba yake mata, Dan kimtsa kansa ya yi a hankali ya ce" Agaishat arrrakam (Agaishat ina son ki), Wata irin faduwa gabanta ya yi, da wani irin firgici ta akle shi, tsoro, mamaki, surprise, murna suka hade suka saka jikinta ya dan fara rawa, So na? Ji ta yi wani nauyinsa ya diri mata,da sauri ta sada kanta kasa, kafin take mikewa da wani irin sauri ta jua inda Mu.azam ya mike yana kiran sunnanta daidai Wardugu ya yi kokarin kawar da kansa dan kar su ganshi bayan ya jima wajen, Ganninsa ta yi yana ta faman taba labulen ayya wanda ke gyare tsaf a wajen aman kamar wanda yake gyara shi, Kanta ta shiga sosawa kafin take dan rabar gefensa ta shige ta taka matatakalar da gudu gudu ta nufi dakin ta, Da ido ya bita, da wani irin kallo, a hankali ya lumshe idannuwansa ya juya ya fice a dakin ya nufi wajen mu.azam da ya koma ya zauna ya dan dafe kansa da hannunsa cike da tsoron kar a je ta ki karbar sa, Gaban wardugu ya ji na wani irin gudu wanda har ya ji wata yar zufa ta karyo masa, A dan hanzarce ya karasa wajen amininsa yana mai cike da zulumin yannayinsa, a nitse ya kai hannunsa ya ce" Mu.azam? Agaishat na shiga dakinta ta karasa da sauri wajen madubi, lufayar jikinta ta warware ta tsurawa kanta ido, du abinda ya fada take son gani sai dai ita bata wani gannin kyanta, , ..... A hankali ta kai zaune ta cuje abinda ta daure gashinta da shi wanda hakan ya baiwa gashin damar zubowa baki dayansa ya yi lumbuk a jikinta, hannayenta ta cusa ta fashe da wani kuka mai zafi, a hankali, muryarta na rawa ta ce" Anna, ina kike? Anna wai yana so na? Ashe nima mutun ce Anna? Anna wai ina da kyau, wai nima mai daraja ce, Anna nima na yi saurayi...........tana kukan kuma ta shiga dariya a hankali ta furta" Mu.azam, nawa😌😌😌😌😊😊😊😊😊😊😊 I.m sowi fans , jiki da jinni ne 🤦♀ 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 3️⃣5️⃣ A hankali Wardugu ya kai hannunsa ya taba Mu.azam, murya a sanyaye ya ce" Mu.azam? Da sauri ya dago da kansa daga yannayin da ya afka, ya kali Wardugu da kyau kafin yake sakar masa murmushi, Wardugu ya ce" me me ke damun ka? Mu.azam dake dubansa ya dan sada kai, ya kuma dagowa yana dubansa ya ce" jinta nake a raina har jikina Wardugu, sai dai ban san ba ko zata aminta ta aure ni a dan kankanin lokaci kafin mai yiwuwa ta yiwu da ni? Wardugu ya ji gabansa ya fadi, Allah yana ganni idan da abinda ke tayar masa da hankali a yanzu bai fi rashin lafiar Mu.Azam ba, lamarin na girgiza shi in ya tuna, yakan tsinci kansa ba karfi bare laka a jikinsa idan ya tuna, ....... Duk da ya fahimci wa yake nufi aman sai ya kashe ido guda yana kallon Mu.azam ya ce" kai, soyaya ka afka daga zuwa garin mu? Fada mini wacece mai sa.ar samun abokina ? Mu.azam
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN