Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 2 / 27

siyarwa SOFO goro na dala biyar, ta saka dala goma asusun da take tarawa dan ta bawa Ba ko ya daina tsanarta, Gomar kuwa itama ta ci wani abin *AGAISHAT* ta ji sunnanta a sama sama yana yawo, sunnanta na gaskiya aka kiraya, Da dan sauri ta dago sukai ido hudu da Fannata, Fannata ce ta kirayi sunnanta na ainahi ba bak'a ba............. 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4⃣ A hankali ta kai idannuwanta kan Fannata dake kara matsowa kusa da ita A hankali fannata ta saka hannunta ta dago na Agaishat, kallon hannun take tana jujuyawa, fannata ta fahimci bayan bakinta na halitarta da Allah ya yi, akoy tarin dati ga kuma karin bakin turkudi, Da sauri Ta janye hannunta tana kokarin mikewa daga cin abincin cike da tsoron menene kuma Fannata ke taba mata hannu? Fannata ta ce" kin ga, ba abinda zan maki Kallonta take da mamaki domin da hausa radau Fannata ta yi magana bayan Agaishat kadan kadan take jin hausar itama baba Tsoho ke dan koya mata dan abinda ya iya, yakan ce ba.a san gobe me zatai ba Goshinta ta dafe ta kalli wajen iya ta ga sai faman gyara Sansanninta take(tabar buzaye), tana dan kukulewa da zare tana ajiyewa gefe tana yin kulin kadago kadago (dala biyar biyar ) Kurumci Fannata ta shiga yiwa Agaishat, Ta yi mata nuni da hannayenta da fuskarta gaba daya, Ta yi saurin taba ruwa ta nuna mata alamar bata wanka ne? Agaishat ta shiga faman saka tsohon takalminta na soso tana faman guduwa domin ta saka a kasan zuciyarta wannan abin zai kare ne a wulakanci da tozarci *WaRDUGU* Ta fada tana mai daga murya kamar zata kaiwa gabjejen mutumin dake tsaye a gabanta duka, Ta kuma cewa" WaRDUGU Odon jidu anna indahan yuna yugusnan gwa ( tun kana yaro yake fama da kai) Kansa ya dafe, ya kai dubansa kan agogon hannunsa, kallota ya yi ya yatsina fuska, can ya ce "Ayya (wato mama), Ayya inda medi mundu tam (wato mama ke rigimarki ta yi maki yawa) Hannunta ta dora a goshinta ta shiga kai kawo, kai take tana kawowa, can ta dauki wani ihu ihu tamkar tana buda, ta je ta dawo ta je ta dawo, ta kallo shi cikin yaren hausarta da bata fita da kyau ta ce" shikennan rayuwar bariki (gayu) ta lalata min kai, shikennan na zama uwar da ina fadi ba.a saurarena, ko nima zaka kula zazafar gabar da ni ne kamar yanda ka kula da Abbanka (mahaifi)? Hannayensa ya jimke ya daki garu da su, kafin yake juyowa wajen mahaifiyarsa, Taku ya yi zuwa gabanta kafin yake sada kansa, shima cikin yaren hausar sai dai tashi ta fi dan goguwa ya ce" Ayya ba dai saboda wajen wannan bugudin (tsofo) ne kike daga hankalinki harda hada kanki kike min da wannan Bugudin (wato mahaifinsa)? Kanta ta kawar ta ki bashi amsa hakan ya sa ya mike ya fito daga falon Yana fitowa ya nufi wani dankareran mashin *ROUTIER* jibga jigban nan masu shegen tsada domin daga million daya abinda ya kai har million shida ne, kuma mashin ne ba mota ba...gudunsu ma daban yake da kananun mashin Bakin gilas dinsa ya fitar ya saka ya tayar da mashin din ya yi masa wani irin ja wanda kana ganni tamkar dambe ake da mai jan da mashin din domin mugun karfi ne da shi ga kyau Hangame gate mai gadi yayi don kar ya jawa kansa bali wajen Wardugu Yana fitowa daga anguwa *Plateau* a birnin Niamey ya nufi *Francophoni* inda gidansa yake Yana karasawa shima tuni an hangame kofar ya shige da gudun tsiya ya silala wani waje da nan ne ma.ajiyar abinda ya shafi mashin da motoci Dira yayi ya juya da sauri sauri ya shiga hawa matatakalar bangarensa domin bangare daban daban ne da matarsa mai sunna *GALayn* Wata yar karamar carte ce ya dora mai dauke da hotonsa ya dora daidai wani detecteur ya bada dan kara titeeee kofar ta bude Caicaicaicaicaicaicai wash, gidan tubawa kamshi, wayo gidan batube ni.ima, bale mai auren gimbiya hajiar hajia, sarkin tsafta, sarkin ado, kwaliya ba dai a nuna mata ba, ta kasance cikin kamshi wanda indai kai ka ce zaka kwaikwaya sai dai ka tashi da mura (gaisuwa yar baba) Sanyi mai hade da kamshi ne ya buso shi, sanyi mai sanyaya zuciya Terrace din dakin fara kal kal kal haka take daukan ido ta sha guga, Tafka tafkan salon ( kujeru) ne irin na zamani masu kalar fari kal kal sai dan coussin kananuwa sosai su kuwa masu kalar baki kamar yanda mauquette (capet) Rido (wato labulaye) yen dakin suma kalar fari ne, sai dai farin ba kar ba kamar yanda kujerun suke , shi ya fi ruwa da kalar peinture (colern) dakin, shima an saka abinnan na daure labule baki wanda kana ganninsa ka san ba karamin kudi bane dakin ba wani tarkace aman komai ka kai dubanka ka san karshe ne sannan ya bada kala ta mamaki, Nan ya yada zango, ya daga kansa sama , Iska ya furzar yana jin yanda takalmin matarsa ke tahowa kwaskwaskwaskwas Kamshin da take fitarwa shima na daban ne, ta shafa turaruka har ta gaji, Tunda ta fito take kallon yannayin fuskarsa, a cikin ranta ta ayanna" wani masifafe kuma ya hargitsa min yannayin miji? Bata yi kasa da gwuiwa ba ta karaso kusa da shi ta daga damatsunnan hannayensa ta shiga masaging a hankali tana kara kallon yannayinsa Murya can kasa ya ce" *ADIBIRA* (Matata) Tsai ta yi tana kallonsa kafin ta ce" qu'est-ce qui ne va pas mon Bb? (Me ke faruwa Baby?) Kansa ya kawar gefe kafin ya janye hannunta a hankali ya mike ya nufi uwar dakansa Bakinta ta tabe, Galayn akoy saurin fushi, mace ce iya mace aman bata tunnanin zata tsaya tana wani bibiyar namiji ko waye shi balatanna wardugu? Wardugu zuma ne ga zaki ga halbi, wardugu ko a cikin tubawa tsoronsa ake, mutumin da idan ransa ya baci idan bai samu ya damki mutun ba yake suma? Mutumin da ya wawuri ogansa ya daga sama ya nana da kasa ogan nasa bama na niger ba domin a niger ba marichal, bako ne da kowa ke tsoro yana shayi, gardama kadan ta hada su General Wardugu ya daga shi ya nana shi kasa a gaban yaransa da kuma yaran general, wannan abin ya jaza masa da mukaminsa da komai shugaban kasa ya tsaya kai da fata aka tura shi daji can wajen mali sai da ya yi wata hudu ya sauko, aman maimakun abin ya yi sauki sai kara gaba da yayi, mutumin dake gaba tukura da mahaifinsa , fada yayi gwa da gwa cewa abansa ya kiyayi hanyarsa kan laifin da ya boyewa kansa sai shi sai mahaifiyarsa suka sani, ita a wa zata tsaya ta bi bayan wardugu da idan ransa a bace ka bashi hakuri yake hucewa kanka? Du irin yanda yake ikirarin shi yanzu ba ruwansa da fada da mutun na gugar jiki karya ne ! Ka yarda ka yi gigin kai masa wargin baya ce masa komai ya ciro daya daga cikin wukaken dake jikinsa ya burma maka idan ya so a kashe shi, Wardugu nada zuciya ta ainahin tubawa.... Mu je zuwa labarin *BAK'A CE* 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 5⃣ Mikewa Galyn ta yi ta fice itama ta bi ta babar kofar danma ya san ta yi tafiyarta ta je ta kara bada turaren ruwa a jikinta ta fito ta je wajen da kys din motoci suke ta dauki guda ba tare da ta tsaya zabe ba domin kuwa kaf ciki manya ne Tana fitowa ta shige motar ta tayar ta fice abinta wajen auren kanwar kawarta tana mai duba carte dinta ta bank dan ta tsaya ta ciro yayan banki na kari a wajen wasa.... Wannan kennan Ya yi kai kawo ya fi a kirga, ya dafe kansa yana tunanin irin nacin mamansa kan abu, ita yanzu dan wani tsoho can daban zata dame shi kan sai ya kaita, shi ya san wani bai isa ya bashi lafiya ba aman har fadi take shi ya taimake shi yana yaro, an dai dudura masa itatuwa haka kawai za.a kashe masa kwayoyin jiki Tsaki ya ja mai karfi, ya mike ya shiga cire kayan jikinsa masu nauyi ya rage masa culotte kawai Da dan gudugudu yake kara taka matatakalar benen bangarensa har ya karasa bangaren da piscine dinsa take Ba tare da wani tsaye tsaye ba ya fada cikin ruwan nan ya shiga iyo tamkar wani kifi yana kai yana kawowa ba wani alamun gajiyawa a tatare da shi Ba ita ta kai gidansu ba sai can dare har wajen karfe tara abinka da jeji shiru garin sai kukan tsuntsaye sai jefi jefin samari da yan mata ana tadi domin sukan kai har goma suna tadinsu A hankali ta shige gidan nasu ta samu ta leka kanta Fitilar kwai a kunne, sai dai tana jiyo minsharin Abansu dan haka a hankali ta kutsa ta nufi dakinsu yan matan gidan Mahaifiyarta ta gani zaune saman abin sallah, da alama ita take jira duba da irin yanda ta tsareta da ido Jiki a sanyaye ta karasa kusa da ita kanta duke ta ce" ANNA Bata amsata ba sai kureta da ta yi da kallo, Ta jima duken nan, aman bata mike ba domin ta san wani abu guda da mahaifiyarta keda na buzaye tamkar wata yar gidan sarauta koda yake du buzuwa ko buzu haka ne dadaya ne basu da shi wanda mutane ke jifansu da sun cika *Ashak* , Can kamar ba zatai magana ba ta ce" kin ga, ko wani hali zaki shiga, ko wace rayuwa zaki fuskanta *AGAISHAT*, ki guji sabawa mahalicin ki, ki rike mutuncin ki , ki ci gaba da hakuri watarana sai labari Kanta take gyadawa, kuma wani dadi ta ji har cikin ranta, ko ba komai ta san a duniya bayan baba Sofo Annartama bata kyamatarta, tana kawar da kai a lamuranta ne dan gudun fitina, irin yanda Abanta ke binta da shari kwararo kwararo ya sa mutanen garima haka, ba mai kulata da daraja, ko magana za.ai mata ba.a mata ita a mutunce, ya kasance ko gaishe da mutun ta yo sai ya yi mata yatsina domin Abanta bai barta haka ba har shari ya yiwa annarta kan cewa ko dai wajen baba Sofo take zagayawa gannin irin yanda ya damu da ita ? Wannan wutar kafin ta mutu sai da aka sha tashin hankali, baba tsoho ya yi kuka sosai aman bai daina kula Bak'a ba domin tana da mutunci yarinyar, shi Allah bai azurtashi da yin auren bama domin bashi da lafia ko ya yi ba anfani hakan ya sa yake jin yarinyar tamkar yar da ya haifa, itama tana mutunta shi tamkar mahaifinta Mamanta na gama fadar haka ta yi shiru kanta itana a saden tamkar tana gaban sarakuwarta A hankali ta mike ta nufi dakin su Tana zuwa ta tarar du sun yi baci abinsu dan haka ta dauro alwallah ta shige ciki ta tayar da sallah ta shiga ramuwar wa.inda batai ba , tana so du rintsi ta ringa samun gurin sallah sai dai tana tsoron mutane da kwagirar su, yanzu za.a wulakantata dan haka take bari idan ta zi gida sai ta yi wanda bata samu ta yi ba Tun karfe takwas na safe Aba ya fice bayan ya canza rawaninsa daga baki zuwa maroon turkudi sabo fil, ya sayi tufafi ya sayi rawanininka harda waya, ya fito sabo kudi sun fado shikennan a haka zai fada su tamkar wuta shima ya dankaro aure daga an cinye kudin shikennan ta gudu abinta Bai jima sosai a wajen ba ya dawo, Daidai lokacin Anna na fitar da dawar masararsa a ruwa wace ra jika dan tana son yin garin tuwo Bai yi mata magana ba ya zarce dakinta dake baban daki idan ka cire nasa a gidan, daman dakuna uku ne, da nasa da na Anna da na yan matan gidan Bai yi wata wata ba ya shiga kwasar kayanta yana kaiwa dakin yan matan yana jibgewa gefe guda, Ba wanda ya tanka shi ko ya yi mamakin lamarinsa domin sun san halinsa, haka yake du idan zai yi aure dakin mahaifiyar su yake fitar da ita ya hadeta da su ya kawo amarya, bama zai barta a dakinta ba sai dai ya hade su ya kawo amarya su sha shagalinsu ba wanda ya isa ya yi magana yanzu zai cici masa uwa ko waye Ko kallo bai isheta ba, don ta daukarwa kanta alkawarin in dai ba mutunci ne lamarinsa toh ba zatana kai kanta yana wulakantata ba gaban yayanta. Sai da ya gama fitar da komai kafin yake fita ya shigo da magini Sosai aka gyara dakin ya yi tas da shi Tare suka fita , sun jima sosai kAfin yake dawowa Wannan karon kuwa masu shigo da kaya ne Mariama dake wanke fuskarta bayan ta shafa kurkum ta yi tsai tana bin kayan da kallo, A gaskiya siyayar idan ka yita a kauyen ka isa ne, tun daga gado har kayan abinci na gayu ya kwaso abinsa sai dai abin haushin babu rabonsu a ciki na amarya ne, domin idan ka auri jar buzuwa ko duniya zaka kai gidansu nasu ne ba za.ai mata komai ba sai dai a kawo maka ita daga ita sai butarta (a kauye fa kar a ce inji sajida🤣) Sai da suka gama kawo kayan tsaf Mariama ta je faban mahaifinta ta tsaya masa kerere a gabansa, somin kuwa in dai haihuwar rashin mutunci ne ya haifa Mariama ta isa ta iya tsayaya tamkar mahaifinta Ido tar cikin nasa da yaran buzanci ta ce" Aba ya haka? Na ga ka fara kwaso kaya alamun aure zaka yi? Ya baka fitar da mu ba? Baka ba anna kudin siyayar kayanmu ba? Kun san wasu iyayen sun fi son yaya masu tsayayar nan, domin Aba yana dan shayin lamarin yar tasa domin a yanda yake gani tama fi shi rashin mutunci dan haka ya dan gyara rawaninsa irin zai yi magana ya ce" wani siyaya kuma? A sanina cikakiyar buzuwa ba.a yi mata kayan daki? Ta yatsina bakinta ta ce" sai kuma cikakiyar buzuwa ana yi mata sutura Karya ne Mariama, ya fada yana matsowa kamar zai doke ta, ya ce" ku ne yayan zamani kuke zuwar mana da abubuwan da suke neman fin karfin tunanin mu, ko uwarki haka aka bani ita, haka ake kai ku daga ku sai turkudin amarci da buta, kudin auren ku kuwa mu iyayen ku ke siyan maku kadara mu ajiye maku a nan wanda idan kun waiwaya zaku ji dadin su Wani malalacin murmushi ta saki tana kallonsa Ya ci gaba da fadin" ke da kin ga minister ne ya turo a nemi aurenki, ya saya maki komai, sannan ke da auren wata shida ne zaki yi ki kwashe komai ki dawo mini mu more da kudi? Tar ta kara saka idannuwanta cikin nasa kafib take juyowa ta ga mahaifiyarta ta fara daka dawar da ta wanke ta baza a rana ta sha iska tana so ta mayar da ita gari kennan , ta kuma kai dubanta wajen yayarta *BAK'A* dake ta dirzar wankin yan matan gidan harda na su kanenta ita dai burinta idan sun tashi su bata konce, ta kuma kallon mahaifinta dake kokarin shi dole sai ya yi mata wayo, wai wani harda cewa wai ya siyar masu kadara, shi? Kudin aurwnsu bai taba wata a hannunsa ba komin yawansu zai kashe su ne ya dawo talakansa marar mutunci, yan yatsunta biyu ta hade ta yi tap tap da su suka bada dan sauti kafin ta ce" ka kirga kudi, ina so ka bawa Anna kudi har million shida a cikin kudin da ka karba na auren mu domin na sani cinikinmu kake tamkar abin siyarwa baka amsan kasa da goma, ka bamu shida mu je birni tare da Anna mu siyo kaya mu dawo idan baka yi haka ba zan shiga duniya na saka ka a matsala kai da wanda ya kawo kudin aurena, ka san ni horonka ce Yana tsaye bami bude har ta fice a gidan, kallonsa ya dawo wajen Anna, da sauri ya karaso ya ce" kina jinta kika yi tamkar baki gani bayan kin san tana jin nauyin zuciyarki? Ko ke kika kitsa mata a taru a cuce ni? Har million shida? Ai kudin sun kusa karewa idan na baku haka! Bata bashi amsa ba ta ci gaba da dakanta , nan ya juya wajen Agaishat ya ga shi take kallo Ke dan ubanki daina kallona da wasu tula tulan idannuwanki masu kama da na mayu, shegiya da aka kwaso cikin ki a waje aka yayaba min, dan bakin jini ko almajiri na yiwa tayi guduwa yake, zan zo in kwakwale miki idannuwan nan in baki a hannayen ki ki je ki kaiwa tsohon dan iskan nan da kike zuwa kina wuni wajen shi wama ya san ko me yake maki a bukar nan Da sauri Annan ta juyo wajen shi, ta kai dubanta wajen Agaishat da ta sada kanta jikinta na bari, tausayin yarinyar ya kara dirar mata, nan ta kara gane shi ya sa idan ta fice take cika dare dan kar ta hadu da mutumin dake mahaifinta aman ya zamo makiyinta , ta rasa da wata kalma zata kirayi mutumin dake miji a gareta, ta san ya yi karatu, sai dai son kudinsa ya fi imaninsa yawa A hankali ta ce" ki je kawai zan idasa maki aikin Da sauri ta ajiye wankin ta warware mayafinta na bakin turkudi butubutu da shi ta yane jikinta gaba daya ta fice har tana hardewa tana waiwayen gidan nasa Bakin wata bishiyar mangwaro ta zauna ta

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 2

WAReaders TGUpdates