Allah na kallon ku! Ko hakin ciyar da ku da na yi zai bi ku, Ya kara tofar da yawu yana duban Mariama dake bin sa da wani mugun kalli itama da sansanninta a bakinta kamar na sauran yan uwanta da Anna, ya ce" ke kuwa ke ce gagarara ko? Mai tarda ni wajen majalisa ki tirke ni gaban abokaina, ke mai karfi wace ta fi kowa iya rashin kunya, a gaban yan uba kika yi ikirarin zaki ga ubanda zai maki aure ko? Ba laifi, ba laifi Mariama, in sun zo sai mu basu gidan su saya su tafi mu kuwa mu koma zaman titi , Mariama ta yatsina bakinta ta kawar da kanta, Babar rigarsa ya kabe ya ce" kudinku yanzu na fara ci, ni da ku ba shari.a domin ni na haife ku! Dole na yi maku aure na mori kudin ku! , Ke kuwa, ya nuna Anna da take jan dan karamin carbinta tana shamaninta ya ce" kin ji kunya, anai maki kallon saliha sai gashi kun hada baki da tsohon can kun tura yarinya nema; ana zaton wuta a makera su Annar yara sun kunata a masaka. Yana gama fada ya fice a gidan yana ta tofe tofensa, Mariama ta dantsa yatsarta a bakinta tana yiwa yayarsu kallo mai kama da harara, domin ita ta yi masu kashedin kar ta kuma gannin wani ya biye masa, dan ta lura hakan na masa dadi Gaishat ta yi murmushi tana dubansu ta ce" baku lura ya fara yin sanyi ba? Mariama dake hararar Amaryar Ba ta ce" sanyi? A wannan tsohin najad..... Bige bakinta da Anna ta yi ya saka ta kasa karasawa tana turo baki, Da yannayin bacin rai ta ce" in kina irin magangannun nan hankalina tashi yake, mahaifin ki ne fa, ko me ta zama adu.a ce tsakanin ki da shi, ya zaki ringa halaya irin na wace bata da tarbiya? Bana so Mariama , Aman Anna, kina ganni abinda yake yi fa, ke tsoronsa kike , to ni bana tsoron sa, Kuma bakya tsoron Allah? Gaishat ta fada tana dubanta, hakin dake tsakanin ki da shi na matsayinsa na uba Allah ba zai bar maki ba, ki bi shi, ki yi masa biyaya, ki bar shi idan shi gobensa bata dame shi ba kai nasa, Shiru ta yi tana duban fatimata dake dan zane a kasa ta ce" wacen matar ciki ne da ita fa? Kuma kum san ba cikin Ba bane, Anna ta kwalalo ido tana dubansu, a dan harzuke ta ce" na ga mai isata yau da yaren nan, kun yi da shi ne? Bama wannan ba sa.anku ne? Du wace ta kuma gigin muguwar magana a kan mahaifin ku a gabana zamu bata da ita! Ba ruwana ban koya maku ba, baku ga ina yi ba, kuma idan na ji tsoronsa ai ba laifi ba, shugana ne, wanda aljannata ke karkashin kafafuwansa, a haka ma ya muka kare da shi bare na yi masa gatsali? Ku daina bana so! Ta karasa tana dan dafe kanta domin har ya sara mata maganar nan da ta yi, Da dadaya suke bata hakuri suna masu lura da yannayinta............. Daga inda yake ringeshe yake biya bagara a fili hannunsa a kan zuciyarsa, Sai da ya kai karshe ya samu ya dan daga ya jingina yana duban hanya dan ya san yanzu Mariama ta zo, Yana jin dadin lamarin mariama sai dai ita ba.a hira da ita, kimkim take masa har yanzu haushinsa take ji, bata san irin yanda shima hankalinsa ke kan Agaishat ba, adu.arsa a gareta ne, da fatan saduwar fuskokinsu kafin ya koma ga mahalicinsa, Jama.a Wardugu na neman karin aureπ€£, du mai son karya kafa ta shigo layiπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ................... dan Allah aunty Alhinayett kar ki tura masa wannan page din wollah lalla batai kwari ba kar ya karya min kafar nimaπππ π«π«π« *BAK'A CE*π«π«π« Na *SAJIDA* *Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
* ____________________________________ *πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π» ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 3οΈβ£7οΈβ£ Yana nan zaunen kuwa sai gata ta shigo da salamarta ciki ciki, Ajiye masa robar abincin ta yi bayan ta dan jefa masa wani kallo , Wajen ruwa ta je ta dibo masa ta zo ta tsuguna ya wanke hannunsa ta kuma cikowa ta ajiye , Dakin ta tatare kamar kulun shi kuwa yana cin abincin yana duban yannayinta, Mariama akoy shiru shiru sai dai yannayinta na yau kamar ranta a bace ne, A hankali ya ce" me ke damun Mariama? Tana gurza goron hannunta ta dan dago ta dube shi, ta ci gaba da gurzar abinta, Can ta ce" idan ta zo hankalinta a tashe, ranta a bace, idan ta fada maka ka taba yi mata maganin damuwarta ne sofo? Baba tsofo da ya gane Agaishat take nufi sai ya girgiza kansa a hankali , kafin ya ce" ban taba magance mata damuwarta ba Mariama, sai dai nakan saurare ta, na ji damuwarta, na yi mata nasiha a musulunce da girma, nakan ji ciwon damuwarta a raina na nuna mata ba dadi, aman kuma sai na nuna mata girman hakuri, Shiru ta yi tana jinsa, can ta ce" wai dan na kire shi da mumunan sunna Anna ta dake min baki bayan bata taba koda shakunana ba, kana da labarin irin manya manyan munana halayansa, aman sai ta wani tare mashi? Baba tsoho dai kallonta yake , har ta dasa aya tana hucin bacin rai, a nitse ya ce" su iyaye, sune masu madaukakiyar daraja in kika cire Allah da mazon sa a wajen dan adam, su iyaye Allah ya ce a bi su a yi masu biyaya banda hanyar sabonsa, Shi abinda yake ba sobon Allahn bane yake?, ta fada tana duban Baba tsofo, Baba ya gyada kansa yana dubanta ya ce" ya taba daukan y'a ya bayar ba.a daura aure ba? Mariama ta girgiza kai, Ya ci gaba da fadin" yana yin aurwn yayansa dan dukiya, adini bai jaramta hakan ba sai dai ta yannayin da yake yi ne, Yana yi ne tamkar yana siyar da yayan, Wa ke tafe da duniya da abinda ke cikinta Mariama? Ya kuma watso mata tambaya, Mariama ta ce" Allah, Shin baki da labarin ya fi gannin abinda kike aikatawa? Ya fi ki jin abinda ke wakana a tare da ke? Na sani , ta fada tana kawar da kanta, Baba tsofo ya ce" shi zai kare ku! Yana fadin hakan ya yi shiru tamkar ba shi ba, Da mamaki take dubansa, bata san lokacin da ta dawo facing dinsa ba ta riko hannunsa tana dubansa ta ce" shikenan? Hukuncinsa kennan? Baba ya yi mata murmushi ya ce " ke kika halice shi da zaki hukunta shi? A hankali ta sada kanta, muryarta ne ya yi rauni ta ce" ya cika cin zalinmu, bai san darajar matarsa ba wace take mahaifiya a wajen mu, mu yayansa yakan dauke mu ne ya yi kudin mu, yanzu ya tare da matar da wani ke ziyara a kan idannuwansa, shin yaya ake so dole dole sai na daraja wannan mutun? Baba tsofo yana dubanta ya sada kansa shima, ya dago ya ce" muna tursasa ki yi masa biyaya ne dan goben ki, kar ki ga duban laifukan da kike hange nasa, idan kika taka hakinsa a kanki na matsayinsa uba a gare ki, Allah ba zai bar ki ba, ki yi masa biyaya, sai ki ga Allah ya jibanci lamuran ki Mariama, A hankali ta cika hannun Baba tsofo ta juya ta hado goronsa ta kule sauran ta kula a harshen zannin ta, Miko masa ta yi wanda ta gurzan ta duka gabansa tana dubansa ta ce"ya aka yi mutun mai mutunci irinka ya rayu shi kadai? Ni tunda aka haife ni kai kadai nake gani sai almajiranka wa.inda da sun fara tasawa suke tafiarsu birni neman kudi, ya aka yi baka da mata da yara? Dubanta yake da mamakin ashe dai ta iya magana, sai dai tambaya ne da Mariama tamkar me, komai so take ta gane ya aka yi ? Ta ina aka bi aka yi? Wa ya yi? Su waye shaida? π
, Iyayena yaki ya tafi da su, Na tashi ni daya sai Allahna, Na yi aure sau biyu a rayuwana, sai dai rashin haihuwa ya saka matan na guduna, Me ke birge ka a rayuwar wannan daji kai daya kwal da ranka? Tsareta ya yi da ido kafin ya ce" nan ne muhalin da Allah ya ara min, Kalonsa take da wani yannayi na tsoro, a hankali ta mike tana dan duban yannayin dakin baba tsofo, Fitowa ta yi ta hangi anguwar ba wani mutun mai gitawa bukar baba tsofo a tsakiyar rana take sannan nesa da jama.a, A hankali ta waiwaya bayanta ta tsurawa kofar bukar ido, a ranta ta ayanna " *Wannan mutun ne ko aljan?* (π₯ΊπΆπ»ββοΈπ³π³π³π³πΆπ»ββοΈπΆπ»ββοΈπΆπ»ββοΈπΆπ»ββοΈπΆπ»ββοΈ) Rakiyar Aghali aeroport tamkar za.a raka shi tafiar da ba zai dawo ba, Idan ma ya yi salama da iyayensa kuma yin salama suke , Har aka fara harama kiraye kirayen suna wanda hakan ya saka shi komawa wajen mahaifiyarsa ya dan duka kansa ya ce" Allah ya ja zamanin sarauniyar garin Agadez, sai Allah ya dawo da ni. Dago da habarsa ta yi tana dubansa ta ce" Allah ya kai ka lafia yarimana, ka gaisar min da aminiyata domin ban lamunci ka sauka hotel ba bayan gata a gari, Murmushi ya yi mata yana daga mata kansa , kafin ya juya wajen matarsa ya sakarwa yarinyarsa kiss a goshi da kunci, itama matar ya yi mata kiss a goshinta a hankali ya ce" *Tarhanine* (masoyiya) Dago da kanta ta yi ta dube shi, da dara daran idannuwanta ta yi masa salama kafin take juyawa ta nufi dankareroyar rangrover din su Sauka lafia Yarima Aghali . Yai tunda ta farka a barci ta ahige bayi ta yo wankanta ta fito ta kimtsa jikinta domin ta farka da al.adarta wace ta zo mata tsakiyar dare, Bayan ta gama ta kuma rufa ta turara turaren wutar da ya zame mata jiki karfi da yaji Ayya ta koyar da ita saka turaran wuta a jikinta da kowani lokaci, barema idan ta fito a wanka sai ta turaru kafin ta bushe, Sai da ta gama turaruwa ta dawo ta ciro doguwar rigar atampa , jar atampa ce mai adon baki baki a jikinta, An yi mata dinkin mai turmi , saman ya dan rike daidai kirjinta ya yi mata das sai ya bude kasan , , A hankali ta zauna saman yar kujerar gaban madubin ta caje gashinta wanda Ayya tace yau za.a kitsa shi, domin ana kitsawa yana warwarewa ne Ayya kuwa tace sai an yi kitso mace ce dole ta yi kitso, A ranta ta ayanna , ina yake? Ya ya kwana? Har yanzu yana kan bakansa? (Domin rabonta da Mu.azam tun guduwar da ta yi jiya,) yanzu har karfe goma ya gita na safe, tana jin lokacin da Ayya ta shigo take fadin zasu je su dauko Aghali dan aminiyarta , sannan ta ji lokacin da mai aiki ta shigo tana fadin Wardugu ya zo Ayya bata nan, aman ina ita barci ya ci kargfinta domin idan tana al.ada takan yi wani barci mai nauyi ne, A hankali ta saki murmushi ta kuma furta "Mu.azam nawa , Ji ta yi an turo kofarta dan haka ta mike tana duban kofar, Shigowa ya yi da salama a bakinsa, da sauri ta kai dubanta saman bed dinta, Allah ya so ta abin shinfidar ya rufe pant dinta da ta ciro ta zabi wanda zai riketa da kyau ta saka, bata rigaya ta mayar da sauran ba, A hankali ta mayar da dubanta wajensa, kafin murya a sanyaye ta ce" i....i.ina kwana , Yauma bai amsata ba, sai kallo da yake binta da shi na mamakin yaushe ta iya saka kaya haka? Yana gannin yan aikin gidansa har kulun su shigarsu tamkar an tsamo su daga rafi, domin Walyn nata daukan yan aiki yan birni sai yan kauye, baya taba gannin sun waye su kulun tamkar mahaukata, shi ya sa koda wasa ya hana su taba wani abin a bangarensa, hakan ya sa ta samo masa namiji mai aikace aikacen bangarensa wanda ta yi ta rantsuwar ba dan daudu bane, shi kuwa dan daudu ne idan ya shigo gidan ne yake namiji! A hankali ta karasa ta dauki dan kwalin atampar ta daure gashin kanta da kyar , wanda yake lumbuk gaban goshinta, ta koma gaban madubin ta zauna abinta ta shiga daure gashin kanta, Wani irin mamaki ne zai kashe wardugu dake tsaye yana biye da ita da kallo, kai! Ya fada a ransa, ya shigo ne dan ya tambayeta kys din dakin Ayya dan ya san ita zata barwa, sai dai mamakinsa, ya hadu da macen da bata nuna tsoronsa, kakahin ta birge shi, shishigi a gare shi ba, ita bata nuna tana tsoronsa ba , ita bata nuna bata tsoronsa ba, ita dai ta gaishe shi, gaisuwar da ya tsana wai wani *Ina kwana*, sai kace wani sa.anta! Yana nan tsaye har ta gama daurin dan kwalin da ya boye baki daya gashin kanta, ta dauki turaren ruwa ta kuma fesawa a jikinta mai sanyin kanshi wanda Ayya ta sayi kwali guda irinsa sunnansa princesse , Kwali ta dadage ta saka sannan ta shafa dan man lebe kadan, , Mikewa ta yi ta juyo facing dinsa tana dubansa yana dubanta, a hankali ta shiga takawa tana nufo shi, wanda du takunta daya sai ya ji gabansa ya dadage ya fadi , da sauri ya kawar da dubansa a kanta daidai nan ya jiyo muryar Ayya, Tamkar an hankada shi haka ya fito daga dakinta wanda har ya waiwaya da sauri yana duban kofar, hankali ya furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, abinda Wardugu ya furta kennan kafin yake tura dakin Mu.azam dake kasa kadan da dakunnan su Ayya ya shige ya rufo ya nufi gaban madubi da sauri, Duban kansa ya tsaya yi, kaki ne a jikinsa, sosai yannayinsa na ban tsoro ya bayana a jikinsa, sai dai kaki din wandon ne kawai sai bakar rigar da ya saka, a fili ya furta" ko dai makauniya ce? π³π³π³π³π³π³ Ba laifi yau kun yi comment, dan haka ga kariππππππ π«π«π« *BAK'A CE*π«π«π« Na *SAJIDA* *Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
* ____________________________________ *πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π» ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 3οΈβ£8οΈβ£ Murmushi ya yi bayan ya tabatarwa kansa da yarinyar ba makauniya bace tana gani sosai, To aman ayar tambayar shi ne me ya sa bata tsoronsa? Ko ta tsaya ta shagalta a kallon sa kamar yanda du yawancin mata da mata ke yi? Bale ita da ga irin wajen da ta fito wato kauye zai kasance shi ya zama abin kallo a wajenta, sai dai abin mamaki tamkar ba.a yi halitarsa a gabanta ba, Kansa ya girgiza a fili ya furta" Ayya kwashe kwashe, idan kuma aljana kika kwaso mana ba sai ki huta baπ₯΄. Sai da ya gama abubuwansa sannan ya juya ya fice ya tafi falo domin yana jin hayaniyar samarin biyu da muryar Annarsa. Agaishat tsam ta yi bayan fitarsa ta sauke ajiyar zuciya, murmushi ya kubuce mata a fili ta furta" idan Mu.azam nawa zai aure ni, cikin abokan ango da zasu zo daukana a rakumi (πππ ke malama a birni kikeπ), harda wannan mai kama da mutanen cikin alon nuno mutane (tv), Dariya ta yi tana dafe goshinta ta ce" kai aman katoto ne, kuma wai dan Ayya neπ€¦ββ, ko ta yaya ta goya shi? Kys din Ayya ta dauko ta juyo zata fita, ta ja ta tsaya ta dubi wajen da Wardugu ya tsaya ya zuba mata ido, nuna wajen ta yi da hannunta ta ce" kai katoto, ka daina irin kallon nan, baba sofo yace ba kyau irin kallon nan da kake! Yatsina fuskarta ta yi , ambaton sunnan baba sofo da ta yi ya sace mata lakar jiki, a hankali ta shiga takawa da zancen zucin ko ya yake? Ya Annarta? Ya yan uwanta? Ko da wasa bata tuna yannayin mahaifinta, sai ta tuna da baba tsofo sau dari bata kawo sunnan Ba a layin zuciyarta ba, tsananin tsoronsa da ya dasa mata ya saka har a zuciyarta idan ta yi kamar ta tuna shi sai ta gargadi kanta cewar ki kula Agaishat kiyayarsa gare ki madaukakiya ce. Agaishat na saukowa, kanshin turaranta ya fara karasowa, kafin a hankali ta idasa fitowa fallon, Da murmushi Ayya ke kallon ta, domin ta ji dadin irin yanda yar tata ta koyi saka kaya da wuri haka, Mu.azam da ya dago daga hirar da yake yiwa Wardugu ya zuba mata mayatatun idannuwansa , zuciyarsa na luguden kida yana dubanta da wani yannayi mai nuni da " kin azabtar da ni, Wardugu dake gefensa yana sauraron sa, jin ya yi shiru ya saka shi duba wajen nasa, nan ya bi abinda ya tsurawa ido, ya kai dubansa wajen Aghali da yana tsakar waya da mamansa yana shaida mata ya sauka lafia, aman ya tsaya mamakin wai yarinyar da Ayya ta dauko ce haka? Da sauri Wardugu ya mayar da dubansa wajen Mu.azam, shima zuba masa idon ya yi yanai masa kallo mai cike da ma.anoni, Salama ta yi , kafin ta zarce wajen Ayya , inda a takaice ta ce" ina kwana.......... (wannan na cikin abubuwan da Ayya ta koya mata, cewar ta ringa kiyaye sakin baki, kai ko gaisar da bako zatai ta takaita , in dai ta yi salama cikakiya halas!) Tana zuwa ta zauna inda Ayya ta nuna mata, Hannunta Ayya ta kama tana duba faratunnanta , domin ta umarce ta da sakawa yatsutsanta jan lale, Ta kuwa saka , ya kama yai mata das a hannun , Ayya ta saki hannun ta lakaci kuncinta, kafin ta yi kiran Hanne, kan ta kawowa yarinyarta abin kari, Kai Wardugu ya girgiza, ya mike yana daukan wayarsa ya kai dubansa wajen samarin dan ya ankarar da su , da haushi haushi ya ce" ni zan tafi, Da sauri Aghali
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN