Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 24 / 27

yake, du yanda wardugu ya kai ga zafin rai yana raga mata, yana matukar kawar da kai a shirmenta, tunda ya zo niger bai ga inda Walyn ta taka kafarta gidan mahaifiyar mijinta dan ta gaisheta, bayan kulun sai ta fice yawo kwararo kwararo,, ga abubuwa na rashin da.a da take shukawa suna zuwa kunnuwansa , sai ta tafkawa talaka rashin mutunci ta yi ikirarin me ka isa ka yi bayan ikon a hanuna yake a matsayina na matar General Wardugu, Karfi da yaji ta saka wasu talakawan na shayin tunkarar iko koda da gaskiyarsu , suna tsoron gawo ya juye da mujiya! Sam halayar Walyn suna bukatar gyara, Bai iya cewa Wardugu komai ba, domin du tsakaninsu basa irin maganar nan, sam Wardugu baya bada fuskar a yi maganar iyalinsa da kowa, idan abu ya ishe shi yakan ja dogon numfashi ya ce" Mata kennan, kwakwaluwarsu irin ta yara ce, Wardugun ma dubansa yake har ya karasa wajen bed yana dana waya ya ce" Wardugu, yanzu kayan buzaye ne zamu nada , kawai kai tamkar diarhee kake idan ka tashi abu yi kake? Bamu wani shirya ba, bamu zo da datijo ba zamu je a bamu aure? Ni dai kar ka ja iyayen yarinyar su hana min Agaishat ba zan jure hakan ba , zan haukace maka ne! Tsuru ya yi masa daga kwoncen yana jin wani iri da maganarsa, wani irin tashi ya yi zaune yana dubansa ya ce" kai zo zauna mu yi magana! Mu.azam na dubansa ya karaso ya zauna yana kara kare masa kallo, Wardugu ya ce" dan tausayi zaka aureta ko dan so domin Allah? Mu.azam ya yatsina fuska ya ce" ina sonta mana, meye a tare da ita na tausayi? Nine ma ai abin a tausayawa, Wardugu ya ce" kana ji, bana son ka yi auren nan da wata manufa, Mu.azam, ba zan jure gannin hawayenta ba koda kai ka jawo shi ranka zai bace, ka kara tunani ! Yana gama fada ya muke ya nufi bayi dan ji yake kamar ya yi ta ihu, sam baya jin dadin duniyar, Yana kasan shower idannuwansa rintse, zuba take da karfin gaske ga ruwan sanyi karara da su, Idannuwansa da sukai ja ya bude ya barsu haka ruwan na shigar masa ido , hanunsa na dama ya jimke ya daki bangon yana wani irin nishi mai nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki, A kadan Wardugu ya kai minti arba.in a bayin nan sai da ya saisaita kansa ya kashe gudun showern ya dubi hannunsa da ya daki bango a kala sau uku wajen ya dan tashi abinka da farar fata, Towels ya dauka ya daure jikinsa ya fito ya nufi bed ya kwonta rigingine yana adu.a a cikin ransa Da ido Mu.azan dake saman salaya ya bishi, kansa ya dukar ya ci gaba da jan carbinsa yana tunani barkatai a kasan zuciyarsa.......... Bayan ta gama ibadarta , zuwa ta yi ta hada complet dinta biyu ta saka a jakar computerta, ta duba kudin dake jakarta , ta kuma duba wayarta da passport dinta ta koma bakin dan madaidaicin bed din da take kwana tun zuwanta ta dauki carbinta fari kar ya fito tana mai kuma kiran docter Elisabeth Dagawa ta yi suka gaisa, nan docter Khadija ta yi shiru, Docter Elizabeth ta ce" kina ji, sati biyun nan shi dai kawai na iya sama maki domin kin ga aikinki ya kasance aiki mai daraja, bangaren zuciya bama so koda wasa masu kula da lamarin mu rasa daya koda na minti daya ne, na yi iya yina a haka aka tsaya, dan haka ki hanzarta zuwa niger din ki gama komai kafin likaci ya cika, ni dai fatana ki yi ki dawo da shi mu shiga aikinsa , Kanta kawai take gyadawa , bata san ya zasu kwashe da masoyin nata ba, ta so ta samu lokaci isashe sai dai hakan bai samu ba , zata je da wannan din ma Allah ya sa ya amince. *Timiya* Tunda suka iso suka sauka wsjen baba tsoho suka fada masa abinda ke tafe da su, Baba kam tsufa ya kara rufe shi, bawan Allah daga ringeshe yake binsu da kallonsa domin idannuwansa ramram suke ganni, murya irin na datijai ya ce" na ji dadi na yi farin ciki, aman me zai shaida min da gaskiyar maganarku? Ina mahaifiyar taku? Ina agaishat? Ina alwalin mai neman auren? menene shaidar da zata saka na aminta da ku? Wardugu dake dubansa ya karaso a hankali kusa da shi, kai shi yanzu yana jin nauyin tsohon wanda a da nauyin bai kai haka ba, Yana karasawa ya kama hannun Baba tsoho cikin yaren buzanci ya ce" bamu zo da su ba, sai waya da na dauke su suna magana, mai neman auren Agaishat abokina ne , aminina, shine wannan , ya nuna Mu.azam, ya ci gaba da fadin" Allah ne shaidar mu, shi ne alwalin kansa, idan kuwa ni zaka baiwa amanar yarka zan dauka baba domin ina jinta tamkar kanwata ta jini, Baba tsoho yana dubansa da wani yannayi, a lamarin Agaishat du idan ya yi istihara yakan hango wani duhu kafin ya ga haske, , dubansa yake ta kaiwa kan samarin biyu, Mu.azam da bai sani ba , da kuma Wardugu da ya zubawa ido, ya rasa me ya sa bai ji wani zumudi ba, Bashida ikon hanawa ko sakawa a lamarin agaishat duda shine silar zuwanta da mutanen nan, bai isa ya yanke hukunci ba, sannan idan ba zaka fadi alkhairi ba ka yi shiru, Shiru ya yi ya yi masu jagora inda suka talabe shi sosai suka shiga motar aka nufi gidan Ba Zaune suka same shi kofar gida , ya tisa sansaninsa a gaba yana zaune kan tabarmar kaba yana ta gyara sansanin yana kukulewa da zaren daure abu yana kashi kashi , shi nan sana.a ce ya fara, Da ido ya bisu har suka firfito infa ya hade rai yana hararar baba tsoho Daidai wannan lokacin suka karaso inda sukai masa salama, Wani kallon ya bisu da shi, yana tatare sansaninsa, Wani uabn tsaki ya ja ya ce" ai ko ba.a birne gawarta ba sai na siyar da tabata , ka ga bakin ciki, du ranakun nan baku zo fada min ta mutu ba sai ranar da zan fara sana.a? Ni na san *Bak'a* bata son ci gabana, wato dan ubanta mutuwarma ba zata yi ba sai ranar da zan fara sana.a Baki dayansu dubansa suke, wardugu da tunda gari ya waye jikinsa a mace yake bai iya ce masa komai ba sai sakin baba tsoho da ya yi wajen Mu.azam ya karasa saman tabarmar ya zauna , Hannunsa ya mika wajen sergent, Da sauri ya karaso ya dire wata bakar jaka ya koma wajen da suke tsaitsaye, Bude jakar Wardugu ya yi ya shiga fitar da daurin daurin kudi cefa yan jika goma goma yana direwa gaban Ba, Du daurin nan million guda na cefa ne, sai da ya dire ashirin wanda zuwa lokacin Ba sai zufa yake jikinsa na rawa yana fitar da harshe tamkar kare shi ya ga kudi, Wardugu ya ce" bata mutu ba, da ranta da lafiarta, aurenta zaka bamu, ga gudin auren nan idan kuwa sun yi kadan a karo! Domin *Darajarta* ta fi karfin a yi cinikinta! Ta fi karfin a aureta dan kudi, *Agaishat* na da daraja a idannuna! Gaba daya dubansa suke, magana ne yake daga zuciyarsa, fuskarsa ta nuna wani yannayi mai wuyar fasara, ba zai iya jure wulakancin Ba a wannan halin ba, sannan ba zai iya biye masa su yi ba dadi ba ko dan albarkacin haihuwar Agaishat da ya yi, Wani irin rawa jikinsa yake, auren bak'a da sadakin da ba.a taba bashi ba na sauran yayansa? Wani irin zama ya gyara yana fadin" ai kawai a matso a daura domin kuwa ya shirya, ba ruwansa da tambayar da wa za.a daura, ina take? Tana so? Ina zata zauna? Waima da ranta? Jiki na rawa Ba ya umarci baba tsofo ya yi alwalin Agaishat inda nan da nan sarki ya karaso da jama.ar anguwa ana ta yaba sadaki (kar abin ya baku mamaki ko ya girgiza ku, na gani da idanuwa sadakin buzuwa million arba.in na kudin nigeria bama niger ba, ana amsan karamin sadaki kamar jika hamsin aman yawanci auren garinmu kama daga agadez da kauyukan bugaje ana kashe kudi na mamaki wanda ba.a dauki hakan a matsayin laifi ko wani almubazaranci ba,), A wannan rana , gaban duban shaidu, Mu.azam ya zama alwalin kansa inda Baba tsoho ya zama na agaishat, aka daura auren Mu.azam da Agaishat bisa sadaki mai tsoka lakadan, Sai bayan an gama daura aure Ba ya tatare kudin nan jiki na rawa ya zube a cikin rawaninsa ya daure, bai wani tsaya ya bi ta kansu ba ya yiwa gidan tsinke sai washe baki yake yana ihun kiran sunnan Anna inda ya yi fatali da sansanin, Da amarya ya fara cin karo sai murkashi take ymtana rauda kai domin cikin nata mai matukar bata wahala ne, tana ta fama da kanta du ta lalace, Tsayuwa ya yi ya tofa mata yawu a fuska ya ce" ke kadarara, jeki na sake ki! Daidai lokacin da Anna ta fito tana dubansa sai kiranta yake yana kashe murya irin za.a tuna da din nan, Yana karasowa ya ce" ashe *Agaishat alkhairi ce?* Da mamaki take dubansa tana jiran karin bayani, Agaishat kuma? Ita tana tunanin rabonsa da ya kama sunnanna da daraja haka tun rada mata shi da ya yi, me ke faruwa? Ina yarta ? Innalilahi wa ina ilaihi raj.une, sam bata daukan fara.ar Ba a alkhairi, hakan ya sa ta fito da sauri ta yi waje ko zata ga Agaishat din Baba tsoho ta tarar yana yiwa Wardugu magana kansa a sade yana sauraronsa inda jikinsa ke fitar da hucin zafi gaba daya bashinda laka tamkar wanda ruwa ya daka zazabi ya rufe shi, zuciyarda kuwa ba dadi, dandannon bakinsa daci firit, sam baya jin dadin yannayin ranar nan. Tana zuwa ta tsuguna infa suke, Muryarta na rawa cikin yaren buzanci ta ce" me ya same ta? Idannuwansa ya dago ya sauke kan fuskar Anna, duda turkudi ya rine mata fata ba wani kula take samu ba, aman idan kana neman ainahin kyau, tsararan kyau ka ja ka tsaya wajen Anna, Agaishat kama take da ita sai dai hasken fata da ya bambanta, yaren tubanci ya juye da shi inda ya shaida mata komai cikin nutsuwa da sada kai da girmamawa, Kunyarsa ce ta kamata, har ta hanata yi masa wata tambaya, Kanta ta sada bayan ta hangi Mu.azam dake tsaye ya rungume hannayensa yana kallonsu ta kawar da dubanta ta mayar wajen Wardugu, Muryarta a nitse ta ce" *kar ka damu da bani hakuri d'ana, na saba da gannin auren yayana a wulakancema bale ita nata kun mutunta, ai dama halal malak na baiwa Ayya Agaishat, koda a can kuka daura mata aure bani da ja, fatana zaku ci gaba da riketa da amana, sannan ba sai ka kawota ba, ka barta a can kawai bara na kawo maka sako ka bata, ka fada mata Ayya uwa ce a wajenta, ta yi mata biyaya!* Asalamu alaikum, Rayuwa ce da aka yi nake bi maku, duda na rufe abu dayawa, na kuma gyara wani dan labarina ya yi ma.ana, aman kar ku manta rayuwar nan an yita, kuma a gidan bak'a akoy Alhinayett dake yayata uba daya, team Mu.azam da Wardugu,,.....ku biyoni sanu zamu ji meye sirin, sanu zamu yi murmushiπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜… Hhhh yau kam na cika da yawaπŸ˜•πŸ˜•πŸ˜•πŸ˜• 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4️⃣5️⃣ Yana kallonta ta shige bata jima sosai ba ta fito da yayun Agaishat, inda Mariama ta hade rai tamkar ta zunduma ihu dan bacin rai, Sai dai suna zuwa wajen Wardugu ta ji ba zata iya yi masa wulakanci ko kashedi ba, dan haka ta sada kanta ta ce " Amana kanwata, Kalonsu kawai yake har suka koma inda Anna ta bashi wani zani a kule wanda bai san ko menene ba, Kamar bashi da laka haka ya mike jiki a sake inda su Mu.azam suka kama baba tsoho suka saka shi a motar suka dauki hanya, Mu.azam na lure da yannayin Wardugu, inda gabansa ya yi ta faduwa kan lamarin, tambayoyi me cike da zuciyarsa *Me ke damun Wardugu? Me ke adabarsa haka? Bashi da lafia ne? Me ya fauke murmushinsa?* Sai dai bashida mai bashi amsoshin tambayoyinsa domin rabinsa da jin muryar wardugu tunda suka baro kofar Baba tsofo inda baba ya baiwa Wardugu wani kuli a baiwa Agaishat shima harda carbi fari ya shaida masa cewa ya fada mata bata da gata sai na Allah. Rike yake kamkam da sakon Baba da Anna, carbin kuwa sai ja yake yana duban hanya har suka karaso garin Agadez, Fir Wardugu yace qi sai dai su tashi a jirgin sojoji , inda nan da nan aka taso daga garin niamey aka zo Agadez aka dauke su su biyu tal aka juya da su duka a cikin awowi hudu har jirgin ya sauke su inda dare ya fara tsalawa, Tunda ya fito a jirgin ya daga kansa sama, garin niamey da yannayin zafi hakan ya sa ya fara jin har kamar ya cire rigar nan ya yar, Dubansa ya kai wajen Mu.azam ya kirkiro murmushi ya ce" zan karasa gida, zamu hadu gobe in sha Allah, Mu.azam ya amsa shi da kai yana kallonsa har ya bace masa da gani, Wardugunsa ne ya juye haka lokaci daya? Hannayensa ya dora saman kansa ya furta" innalilahi wa ina ilaihi raj.une, me na aikata haka? Na kutsa wajen da ba nawa bane ko me? Da sauri ya kawar da zacen nan ya nufi wajen da ya tabata ba za.a rasa motar wardugu ba dan yawan tafiye tafiyensa yakan zo da mota ya bari a aeroport, Yelemun kuwa ya samu ya shiga ya tayar ya nufi gidan Ayya ransa cike da tunani, Wardugu bai zame ko.ina ba sai kofar gudan su Alhinayett A lokacin karfe goma na dare ya kusa, anguwar ana dan kai kawo domin ba laifi suma anguwar yan gayu ce, manyan yan mata da samari sai kai kawo suke suna bada kala. Wayarsa ya danna mata kira, tana dagawa ya ce" ina kofa, Da sauri ta mike ta daga labulen tagarta, hango mutun ta yi duke a kofar gidansu, Da sauri ta fito da zumbulelen hijabinta infa kanwarta dake kusa da ita ta nace ita sai ta bita, Dubanta ta yi da kyau ta ce" *Tghmass*, wajen yaya Wardugu ne fa? Thgmass ta turo baki ta koma saman bed tana kunkunnin je ki, ba zan biki ba ya yi min muhunta wannan katoton da bai san yara ba! Murmushi ta yi ta fice da sauri ta fito ta karasa da sauri tana fadin" Wardugu lafia? Me ke damunka? Me ya faru? Baka taba zuwa gidan nan a wannan lokacin ba, menene? Wani ne ba lafia? Wardugu ya dago kansa daga duken ya kamo hannunta na dama murya a dake ya ce" Alhinayett, zuciyata ke min ciwo, ina jina tamkar zan mutu, ina jin dari sosai, na kasa tabuka komai, ina jin tamkar na rasa wani baban abu a rayuwana, ina jin iskar duniya ta yiwa kofofin hancina kadan, ji nake tamkar jikina na gasuwa da wani irin azabeben zafi da sanyi, ina jin jikina ya yi min nauyi, Alhinayett me ke damuna? Menene wannan? Ban taba jin wannan abin ba, mutuwa zan yi! Da sauri ta dafe kirjinta gabanta na bugawa, A hankali ta duka inda yake ta ce" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Wardugu baka da lafia ne? Jikinka zafi, ka je asibiti ne? Daga ina kake yanzu? Ayya ke ce min ka je Garin su Agaishat nemawa Mu.azam aurenta, ko ka yi gamo ne? Bara na kira Abanmu, Kokarin tashi take ya riko hannunta ta dawo gwarab kusa da shi tana share hawayen amininta yayanta a wani hali, a firgice ta kuma fadin" ka bari na tado abanmu ya baka magani ya yi maka turare ko ka yi gamo da wani mugun ne Wardugu Wardugu ya ce" bana tunanin hayaki, tashin hankali, likita, kudina, ko mulkina zasu warkar da ni, tabas zuciyata sakara ce banza ce da take da gagawar yanke hukunci, ke kin fi kowani makusancina saurarata , na zo ne dan nima yau ki saurareni kamar yanda nake sauraronki, Alhinayett, a yau da inada mace nutsatsiya da na kwontar da kaina saman cinyarta ta taya ni saisaita bugun numfashina, Alhinayett halayen Walyn na tayar min da hankali, ina sane, ina hankalce, kawar da kai ne nake dan ta kula da kanta ta gyara, Alhinayett nima mutun ne, kuma inada rauni fa, ina da zuciya, ita a kulun hirarta da ni tuhume tuhume da zargi ne, a jiya jifana ta yi da maganar wai ina tare da watatsinaniyar? Ni ba mashayi ba, ni ba mazinaci ba, aman ta ki godewa Allah sai fata take yiwa kanta? Yau da zinar nake ta isa ta hana ko ta yi wani abin? *Wani lokacin nakan dauki niyar zuwa na yin na ga sai me?* (hatara mata, walahi yawancin lokuta mu ke jawowa kanmu masifa da bakinmu da banzan tunanin mu), sai dai har yanzu ban aikatan ba, Alhinayett sauraronsa take cike da yannayin tashin hankali, ko me ya firgita mata Wardugu ba karami bane, meye shi da yace ba zai iya masa ba? Ya fi karfinsa? Meye wannan? Gashi ya hanata kiran Aba, Sai da ya gama ya ce" ki daina kuka, yau nima na yi jajen abinda ke raina ne. Alhinayett ta ce" me ka fada bayan komai a dunkuke ka fada Wardugu? Me ke damunka a ranka? Tsai ya yi yana tambayar kansa takamaiman damuwarsa har haka? Kan matar wani ko me? Da sauri ya mike ya mikar da ita ya jata har kofar gidansu ya tura ya turata ya ce" asuba alkhairi Alhi........, A wannan rana Wardugu

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 24

WAReaders TGUpdates