daukeni tamkar uba nakan yi mata nasiha, nakan tsoratar da ita, nakan nuna mata karara rayuwa da abinda Allah ya bani ikon sani Annar yara , Ba zan tirsasa maki ba, ba zan saka ki daukan abinda zaki yi ta nisawa zuciya bata da tabas, aman ina so ki yi tunanin gaba da bayan lamarin, in da hali ki dauki Agaishat ki baiwa wannan mata riko da zuciya daya, ki yi kyakyawan zato, ki saka a ranki alkhairi ne sannan ki bi da adu.a, na yi imanin koda mugaye ne Allah zai saka mata kaunar yarinyar shari ya juye wa khairi Wardugu ya yatsina fuska ya dubi Ayya dake zaune tana kallon su, da yaren tubanci ya ce" Ayya, yarinyar nan fa wannan mahaifiyarta ce , kuma ina jin shegiya ce shi ya sa wancen yake zazaginta haka! Ayya me ya sa suke faman rabuwa da yarinyar? Ayya Wardugu ya isheka haka , Ayya ta fada tana zaro masa idannuwanta, murya a kausashe ta ce" baka lura da abinda ke faruwa ne? Ba zato ba tsamani muryar Anna, cikin yaren Tubanci ta ce" ba shegiya bace, wannan da ka gani ya shige daki ya labe shine ubanta, yana kyamatarta ne dan ta zo duniya *BAK'AR FATA* Da mamaki du suke kallonta, Ayya ta taso ta karasa kusa da ita, hannunta ta kamo tana kallonta ta ce" batuba ce ke????? Anna ta lumshe idannuwanta sai ga hawaye sharsharshar ta dan jijiga hannun Ayya ta ce" ban sani ba, ban san ko mecece ni ba, Damko hannun Ayya ta yi da dan karfi ta saka idannuwanta cikin nata ta ce" ban san ko dan ina jin yarenki ba? Sai kawai nake ji zan iya sadaukar da y'ata wa ke, zaki rike mini yarinya da gaskiya? Ayya ta ji gabanta ya dan fadi, matar na tare da wani banban lamari, Ayyan ta jijiga hannayenta itama tana kallonta ta ce" mudin raina Algabiit dake ciki sai zaro ido yake, ya shiga ukunsa, ya aka yi Anna bata manta yaren nan ba? Aman abinda ya yi mata *Harta sunnanta ta manta*! Domin kafin ya lulo timiya da ita sai da ya tabata ta iya yarensa, ta iya saka kaya irin nasu, ta iya yan dabi.unsu, shigewa ya yi ciki ya zauna jikinsa na dan rawa rawa Anna ta lumshe idannuwanta, ta ce" thank you, Wardugu dake tsaye ya kalo su , Inglish kuma? Inglish ta yi? Hai san ya karasa shigowa dakin da kyau ba sai da ya karasa, inda shigowarsa ya saka du yan matan suka tsaya kallonsa da mamaki, Bak'a kuwa ta lafe da tsoro jikin baba tsoho jikinta du yayi wani sanyi tana son fahimtar maganar tafiya da wa wai ake? Ina ai ita ba inda zata, ba zata bi wasu mutanen da bata sani ba bata taba gani ba ta je a kasheta, ya zata iya tafia ta bar yan uwanta da annarta da baba Sofo? Wa zai ringa kawo masa ruwa? Wa zai ringa saya masa gogo yana gurza masa a karfen gurje goro? Wa zai ringa koya mata karatu? Wa zai ringa ce mata itama mutun ce dan tana baka Haka Allah yake son ganninta ? Wardugu yana karasowa ya dan duka yana kallon Anna ya ce" di u speak Inglish? Anna ta dago ta kale shi, ta amsa masa da kanta, a ranta tana nanata inglish? Wani yare ne shi kuwa? Ba irin wanda suke yi da matar bane kennan? Wardugu da mamaki ya ce" ya aka yi kika iya inglish? A ina kika koya? Wa ya koya maki? Daga wani gari kika zo? Anna da kanta ya fara sarawa ta dafe kanta da sauri , muryarta ya fara rawa rawa ta ce" i...i...i don't know ! Ta fashe da kuka tana rungume hannayenta da sauri Gaishat ta karasa tana rungumo Annarsu itama tana kukan za.a kuma raba su da yar uwarsu? Domin ta sani ne , a yanda anna ke jin zafin irin abubuwan da ake yiwa Agaishat , a yanda aba ya tasota a gaba da man bleating kan sai ta shafa ya yi kudinta itama , anna na neman koma waye ta bashi aurenta ta tafi ta huta, ta gwamace ta tafi ta auri koma waye da aba ya yi kudinta itama kar a je ta fada irin rayuwar da fatimata ta fada ko ma wace ta fi ta Sai da Anna ta yi kuka mai isarta, suba bata hakuri kafin take share hawayenta ta yafito Bak'a sake kukan yan uwanta da mamanta na kuka A hankali ta taso ta nufo Anna Tunda ta taso suka sauke idannuwansu kanta Wardugu ya tsura mata ido, a ransa ya ayyana " Eh lale baka ce, tana da baki sosai da kuma kazanta, a rayuwar kauye dole su tsangwameta domin gari ne mai bambace bambance Kawar da kansa ya yi, jikinsa ya yi sanyi da lamarin uwar yarinyar, tabas akoy bamban al.amari a tatare da ita, da farko ya so ya cakula abin, ya kasance an watse su yi tafiarsu ba tare da Ayya ta kwaso masu wani jangom din ba, sai dai ina yanda matar ta yi yarensa tar tar tamkar nata, sannan ta shiga turanci tamkar yarenta shima, kuma ta furta bata san bama sunnan yaririkan da ta yi, harma ta shiga wani yannayi dan za.a takurata da tambayoyi ya saka shi yin sanyi, a hankali ya furta" sai na san su waye ku! Anna ta kamo hannunta ta zaunar da ita daf da daf, ta dago fuskarta, abinda bata taba yi ba irin kusancin nan da yar tata, tana so ta yi tana mugun tsoro da kunya Murya a raunane ta ce" Agaishat, Ina son ki Da sauri Agaishat ta kara kallonta, Anna ta sakar mata murmushi ta ce" sosai, ina son ki, kuma ina so ki samu canjin rayuwa, bana so ki kare a haka bana so ki kare a ciki duhun rayuwa Gaishat ta ce" Anna, Anna Anna ta kallota ta ce" menen Gaishat? Kar na raba ku da yar uwarku? Na san muna cikin jimamin mutuwa, muna cikin rudu, aman ku kun fi kowa sannin rayuwar da muke , mutanen nan na tafia in dai ba da ita ba na yi imanin ba zai barta ba tunda ya saka wannan lamarin a ransa sai ya aikata Da wa zai hadata? Ina zata fada? Mai yiwuwa idan aka tsilira da ita wani wajen koda ta so guduwa ishrwa ta kasheta a hanya, Agaishat ta fashe da kuka jikinta ya kwashi rawa ta ce" Anna aa, aa Anna, kar ki bada ni haka Anna, ku kadai na sani Anna, kar ki raba ni da ku, kar ki yi mini haka Anna, ki barni ina ganninki har in mutu, ki barni ina gannin baba Sofona ina kai masa ruwa yana kiya mini karatu, ni ba ruwana Aba ya yi ta dukan nawa ba komi Anna in dai ina ganninki ina gannin yan uwanna ina gannin Baba Sofo ya isheni Anna, kar ki rabani da abinda nakeda a duniya wato ku........ To jama.a ya zama kwashe ne? ............m 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣7⃣ Anna zuciyarta ta yi mugun karyewa Hawaye yana shatatar mata muryarta na rawa ta ce " Agaishat, ki yi hakuri ki bi su, ba mugaye bane Agaishat ta buda idannuwanta da kyau ta ce" kina da tabacin ba mugaye bane? Kina da tabacin su din mutanen kirki ne?? Jikin Annan ya yi sanyi ta sada kanta Gaishat dake hawaye itama ta matso ta dafa hannun Agaishat ta ce" Agaishat.... Anna ta dago ta ce" bani da tabacin halayensu, ba zan ce su din mutanen kirki bane kuma ba zan fadi akasin hakan ba Agaishat, ni da na haike ki, ni da na yi rainon cikinki, na haife ki , tunda kika ji na ce ki je, toh ki je din kawai....ba zaki fahimci girman maganana ba sai ranar da Allah ya nuna maki kin haihu, soyayar dake tsakanina da ke na iya cewa ki je to ki yarda da na yi imani na barwa Allah komai ne, a nan kike ko a wani wajen dama shi ya halice ki, ko wace rayuwa zaki fuskanta shi ya kadaro maki, ni ban isa na hana ko na saka ba sai dai na yi ta kai kukana wajensa ina neman jin sanyi daga wajensa Agaishat ta rintse idannuwanta, ita bama bin nasu ba, wannan mutumen da suke tare wanda yake tsaye tunda suka zo wanda fuskarsa bata ga saki ko tausayi a tatare da ita ba, shi take tsoro, in dai mugaye ne ta san shine mai yanka mutanen domin wannan da gani shine bamban mugun Algabiit dake daka sai sintiri yake, haka zata tafi? Ba.a bashi komai na kudin tafia da ita ba? Koda ba yarsa bace ai shi yake ciyar da ita tunda aka haifeta, ya isa a yi shawara da shi sannan a biya shi! Sai dai yana ganin yanda wardugu ya diro daga motar nan ya nufosu, tun a lokacin ya fara sakin fitsari domin shi yama yi tunanin an zo kashe shi ne, ba zai fita gaban wannan mutumin mai kwarjini ya yi wani abin ba, aman ta yarda ta bada Bak'a haka zata gane bata da wayo! Bak'a na ji tana ganni, tana gurzan kuka mahaifanta da rai ba babu ba, ba aure ba ba dangi ba aka fitar da ita tana waiwayen Anna da ta koma da sauri ta shige bayi ta rufe ta shiga rizgar kuka, aka shiga da ita cikin motar da bata taba gani da idannuwanta bama bale ta shiga, Tana ji tana ganni matar nan ta shiga ta riko hannunta tana dan murzawa Alamar rarashi Tana kallon baba Sofo har aka sako shi motar shima kafin da kyar sai da Wardugu ya yiwa Walyn tsawa ta shiga motar wai karni take ji na bak'a, ya shiga suka tayar tana ji tana ganni aka bar anguwarsu gidansu yara sai bin bayan motar suke suna ihun murna sun ga mota manya sai daga hannu suke har sai ta bace da ganninsu aka je kofat baba sofo aka tsaya suka sauke shi Agaishat ta kara rikicewa gannin da gaske sun bar baba Sofo wanda ya tsaya yana daga mata hannu idannuwansa sun kara kodewa alamun kuka yake na zuci sai dai ya fi farin cikin hakan da zamanta a garin Haka suka dauki hanya ba tare da sun huta ba ko sun sha ruwan garin ba suka dibi hanyar komawa garin Agadez Kukan take tana fadin"" Anna, Sofo, Anna, sofo Walyn ta ja tsaki ta ciro ecouteurs dinta ta saka a kune, Wardugu dake gaba ya rufe idannuwansa a tunaninsa zata gaji ta yi shiru ne aman ina sai kara boda Agaishat ke yi Ayya na tausarta tana bata hakuri da tubanci bata san ta dan iya hausa ba ita kuwa bata iya buzanci ba Juyowa ya yi, da yaren buzanci ya ce" Ke ki rufe mini baki a nan tun kafin na saukeki na yi maki dukan tsiya, shiiit bakin nan naki ya mini shiru ko na ciro maki shi a hannunki Wa ya ga hadiya, Agaishat hadiye kukanta ta yi, tana zaro ido tana kallonsu daya bayan daya tana sauke ajiyar zuciya, Ayya tana magana tana yi mata nuni da ta yi hakuri ta yi shiru ta daina kuka A hankali Agaishat ke ajiyar zuciya sannan ta damke hannun Ayya wace ke rike da nata itama, tana kallonta, a nan ita kadai ta dan hangi laushi a tare da ita Tafiya suke suna ratsa sahara har suka baro suka debi titi, Agasihat ko dis ba baci a tare da ita sai kallon titin da take , tsoro fal ranta haka idannuwanta suka nuna, mamaki take dama Shukoki na gudu? Domin yanda motar ke gudu sai take gannin suma shukokin gudu suke tun karfinsu Walyn dake takure tana sakin numfashi sama sama ta shiga yinkurin amai tana kakari Ayya ta kai dubanta wajenta da mamaki, lale walyn bata da mutunci, yanzu du irin yanda ta fafeshe su da turare tana jan tsaki kuma ta kai amai zata yi dan warin Yarinyar da suka dauko Ta girgiza kai kawai ko ci kanki bata ce da ita ba Wardugu dake zaune a ransa ya ayanna Walyn bata son zaman lafia, in dai Ayya ce ta isheki ba abinda ya dame ni! Ba su su karasa cikin gari ba sai can wajen karfe goma na dare Abinka da agadez ma ba wani banban gari sosai bane sai ya kasance shiru garin sai yan mata da samari wasu na tafe a kafa wasu a mota wasu a mashin suna dan yawansu na yau da kulun wasu sun nufi gidan rawa, wasu sun tafi gidan cin abinci, wasu suna yawatawa dan shan iskan gari kuma suna hirarsu Idan ta juya can sai ta juyo nan, kallo take irin na kauyawa sosai jikinta kuwa har zuwa wannan lokacin bata saki ba, sai dai ta rakube jikin Ayya wace take kara rike hannunta dan ta saki jikinta Direct gidan Sarki aka kai su Ayya, har ciki suka shiga da motar suka sauke su Ayya Walyn sai sauke ajiyar zuciya take ta rabu da alkakai Har sun juya motar Wardugu ya ce" tsaya Sojan ya ja ya tsaya , Wardugu ya juyo wajen Walyn ya ce" sauka ki kwana wajen Ayya Walyn ta dago da sauri daga kakabe kakaben jikinta ta zaro ido ta ce" me me ka ce? Wardugu ya tsareta da wani kallo na kar ki raina min wayo Walyn ta ce" aman Wardugu , wani irin na sauka na kwana a wajen Ayya bayan ga mijina wajenka na sauka kayana a wajenka komaina na tare da kai? Yama zaka raba ni da kai ka hada ni shakar iska daya da wannan mumunar yarinyar mai siffar aljannu Yatsina fuska ya yi, a ransa ya ce wai siffar aljannu, ko a ina ta san aljannun ita? A fili kuwa ya ce" Haka na yi ra.ayi Walyn ta ce" Wardugu kar ka yi min haka, me na maka? Kar ka yi min irin horon nan! Wardugu ya kalli sojan nan ya ce" sauka mu je Sojan dai bai ce komai ba ya bude ta fita da bindigarsa yana kallon ikon Allah Wardugu ma ya fito ya rufe ya tafi wajen sojan ya fara tafiya, sojan ya waiwaya ya ga a yanda suka ajiye motar a bakin hanya, bayan wannan matarsa a ciki, sannan tsakanin fadar da hotel din sojojin akoy tazara, kuma idan mutun ya tunkaro wajen haka kai tsaye daga bakin karfe goma na dare ordre da aka baiwa sojojin shine harbi ba ji ba gani in dai ba a mota ko wani abinda yake malakinsu ba wanda da ya tunkaro wajen akoy adadin odar da aka ce su yi dan shaida su ne wada kowace safiya ake canzawa Shi dai biye yake da shi da sauri yana hadawa da fan gudugudu suna tafiya har suka fita daga gidan suka dauki hanya (🤔 sisi kika ce zaki iya da wardugu ko?🤣) Walyn wani ihu ta saki a daidai lokacin da ta fahimci wardugu bara mata ya yi motar gaba daya ya tafi a kafa da ya je da ita, Wardugu ita yake wulakantawa? Toh ita kuwa ba zata shiga wajen wannan uwar tasa da wannan yarinyar mai karnin jini ba! Sai dai ta kwana a motar! Haka ta takure a motar nan ta ki kunna hasken waya dan a gaskiya tsoro take ta kunna waya wani abin ya lura da mutun tun bama dare da ya tsala maguna suka fara kukan jarirai ba, Kawata, tsakaninki da Allah ke haka rayuwarki wata irin mace ce bahaguma? Yanzu yarinyar nan da kika kwaso kin san asalinta ne? Ayya ta yi murmushi tana kallon kawarta aminiyarta matar sarki, ta ce" mamanta ta iya tubanci Anna matar sarki ta dafe kai ta ce" dan ta iya tubanci sai me? Dan ta iya yarenki shikennan sai ki wani kwaso yarta? Kin ce a gidansu kuka daukota Ayya ta ce" ki gane kawata, lamarin mahaifiyar yarinyar da yarinyar ne akoy sarkakiya, wai kawai dan kalar fatarta shikenan take fuskantar tsangwama, ita kuwa uwar sai kawai ki ji tana yare kuma wai tace itama bata san sunnan yaren ba, kuma ni na yi haka ne dan cika alkawarin bawan Allahnan, baki ga yanda ya tsufa ba aman haka yake nisa lamarinta, Anna matar sarki ta dafe kanta da hannunta dake cike da zobunnan zinari ta kalota ta ce" ai idan kin lura yanzu wannan matsakar ta zama ruwan dare, a kauye suna kin bakar fata tare da jahilci a birni suna kiyaye bakar mace dan dogon buri irin nasu sannan suna hakan ne da dabara, kina ganni daidaiya zaki ga a yanzu mutun ya tashi ya dauko bakar mace, sai ki ji suna fadin Allah ya basu farar mace koda maya ce, banza idan ta cinye su fa? Ayya ta dora kafarta daya saman daya tana ajiye tufar da ta gutsura ta ce" ba ko.ina ba, ban ki maganarki ba aman nima nace maki ba ko.ina ba, Du macen da kika ga ana yi mata duban marar kyau ko anai mata wani gani gani ina mai tabatar maki ita ta saki kanta, Mace du muninta idan ta iya wanka ta iya kula da jikinta ta iya kwaliya daidai da yannayinta sai ta kara da adu.a kawai Sannan ita bakar mace da kike ganni baiwa ne da ita, bakar mace tana da kwarjini, bakar mace nada juriya a kowani fani, bakar mace na da kyau mai fuzga, idan bakar mace ta sakar maki tsararen murmushi zaki hangi haske ne a tatare da ita, ke kawata zaki sha mamakin yar amanata in sha Allah Anna matar sarki ta yi murmushi tana jujuya kanta ta ce" oho dai, kina kare bakar fata dan kina da ita bayan taki mai kyau ce, na rantse maki ko ni na samu taki ina so domin bakinki mai kyau ne, ba gashi
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN