niger kace niger ta yi maka kadan sata yanzu? Me yasa ake samun gawarwakin bayin Allah a gidajensu? Masu aikata min haka baki ne! Da sun san idan na damke su zasuna kururuwar na kashe su da abinda nake masu da basu shiga gonata ba! Wardugu ya karasa yana dukan table din glass din dake falon ya yi wani jijiga aman bai fashe ba domin irin wannan mai masifar karkon ne, sai bindiga mai tsini ke tarwatsa shi Rhissa ya mike tsaye ya ce" ba ni bane, kuma ba yarana bane, abinda ya sa na tsayar da hankalina kennan har na baro aikina na garzayo dan ganawa da kai! Kar ka shiga yaki da ni ba ni bane! Na yi bincike tsageru ne, kan harkar siyasa ne, kuma na ga makwoncinsu, suna cancanza waje ne ina son sannin tsarin canza wajen nasu, Wardugu nima sai na yi maka maganninsu Wardugu ya girgiza kai ya ce..... 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣3⃣ Wardugu ya girgiza kai ya ce" ka taba gannin na nemi agaji? Kokowa ai ya dace mutun yayi abinsa! Ka bani hanya kawai ka barni da sauran ai na san tsarin tsagerancin yan tsagera, idan ka yi yaki a kambacina kana so gobe su afko su aikata abinda ya fi haka? Domin sun san ba zan iya tarbansu ba? Aa ba dai Wardugu ba Haka tataunawar Wardugu da Rhissa ta kare, kowa na ji da kansa da kuma ikirarin kansa, Rhissa ya san abu guda Wardugu ba wai cika baki yake ba, yana fadin abinda zai iya aikatawa ne, ya san da in dai suka yarda ya ci masu kamar yanda ya fada ne sai sun gwamace mutuwarsu da rayuwarsu a hannunsa, Wardugu ya ga damar ya fitar da su jeji su fuskanci juna wanda hakan kuwa ba zai gyara su ba! Wannan kennan Bayan kwana biyu .......AMERICA Docteur Mu.azam ne ke zaune yana dadana computer, Can ya dago kansa ya duba time, A hankali ya ajiye ya mike ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa Yana fitowa ya dauki kayansa ya saka ya saka vest dinsa ya dauki agogonsa ya daura ya fito fallonsa dan madaidaici ba wani tarkace sai kujeru da dan table da tv tankamemiya, sai hoton wasu fararan mutane mata da miji ga dukan alamu suna murmushi a hoto Kamar yanda ya saba zuwa ya yi ganan hoton ya tsaya ya ce" Abi, amy asalamu alaikum, yauma na tashi lafia, sai dai har yanzu ya kasa hakuri ya daina fushi da ni, gashi aiki ya taso min a kasarsa banda shi da mahaifiyarsa da mahaifinsa da suka dauke ni tamkar dan cikinsu bani da kowa, Zan kuma gwada kiransa ku taya ni da adu.a daga inda kuke, ina mai kara yi maku adu.ar Allah ya sa kuna cikin Aljannah Shi kadai ya tsaya ya yi zubarsa kafin yake zuwa wajen wayarsa ya zauna yana dan murmushi ya shiga doka kira Yana kallon wayar na haske ya ki dagawa, Walyn ce ta fito daga wanka ta zo ta mike abinta saman lafiyayan bed din hotel din itama tana duba saman screnn din dan gannin wa ke kiransa yake sharewa haka? Murmushi ta yi ta juya abinta ta shiga neman baci a kasan zuciyarta tana ayanna toh fa da shima yana gaba bare ni? Can dai ya daga ya saka a handsfree Soja kake Ya fada yana danne dariyar farin cikin ya daga kiransa Murya ciki ciki ya ce" Docter kake, kuma dan rainin hankali kake Murmushi ya yi ya ce" baka hakuri ne? Baka mantuwa ne??? Wardugu ya kawar da kansa ya ce" haka, ka san ba nine na watsa taron aurena ranar aurena dan wani gudiri nawa na shirme daga shiga ka ga amarya kafin a daura aure zaka fito ka watsa taro? Kai mahaukaci ne! Mu.azam baka da nutsuwa Mu.azam ya bushe da dariya ya ce" Wardugu, abinda ya sa na tsalako fararan fatar, na yi doguwar tafiya niger ba dan ina son na samu *BAK'A* bane?, ni bak'ar mace nake so, ita ce ra.ayina, ita nake son zaman aure da ita! Kar ka manta ni likitan mata ne, idan ka ga na kuke abu kaima ka gwada abokina Tsaki wardugu ya ja ya ce" kiran na menene? Mu.azam ya kuma yin dariya ya ce" kai ka dena jin haushina mana, ai ni ban shaki mahaifin matana ba Da sauri wardugu ya kai dubansa wajen Walyn wace ke kwonce, ta ji sarai dan haka ta yi saurin mikewa tana kallonsa, Fuska ya hade idannuwansa cikin nata ya ce" eh haka ne na shake shi, domin a lokacin ban san mahaifinta bane, kuma na tarar da shi ya zabgawa mamanta mari , idona ya rufe ban tsaya wata wata ba na shake shi, kai dan ubanka sai yanzu ka tina????? Ajiyar zuciya ta sauke, tana tine da ranar .....dalilin wannan action din da yayi na ta haukace kansa, wardugu jarabar duniya....komawa ta yi ta kwonta ta ja bargo tana rufe jikinta Wardugu ya fice a dakin , yana fita ya ce" Mu.azam?? Mu.azam ya amsa da na.am? Wardugu ya ce" kana son kashe min aure ne? Tana jinka fa Mu.azam bai ji dadi ba aman ya ya iya har ta ji, dan tsam ya yi kafin cikin yannayin mamaki ya ce" Wardugu yamzu tsareka ake idan zaka amsa waya ko me? Lale dole na auri batuba Kai banza ka nutsu ka ji!! Mu.azam ya yi murmushi ya ce" dadina da soja zagi, ni dai ka fadawa Ayyata in sha Allah ina nan ina faman gama abinda nake zan shigo Niger, ka san bani da masauki sai kusa da ita dan ita ta iya kula da cikina, zan zo ba zan dawo ba sai na samu macen aure na kuma gama abindq zai kawo ni Wardugu ya ji dadin haka dan haka ya amsa shi da murnar hakan Satin su wardugu hudu a garin Agadez yana faman aikinsa wanda tun Anna na fada har ta kawo ido ta zuba masa, gashi ta yi ta yi aminiyarta ta barta ta koma wani wajen ta kiya ta ki fir sai ma fada da ta dauka cewar masarautar ai girma ne da ita, ba ita ba ko baki ta kawo suna da wajen zama har lokacin da suke so a masarautar Agadez A yau suke saka ran komawa bayan ya fada masu su kiyaye, ya basu magungunna, ya kafa masu sharuda kan lafiar Fatimata, Jirgin da ya kawo su an basu takarda dan haka suka kai aka saka su a layin wa.inda zai mayar garin agadez bisa jagorancin docter Fannata Sun sauka lafia inda Fatimata ke dan takawa a hankali daga nan suka nemi abin hawa dan karasawa Timiya............ Timiya.....me aka kwaba? Me aka yi me ba.a yi ba? Me ake cikin yi? Timiya gari mai abin mamaki, Timiya garin bak'a, Duka na kawo wuka a yanka Algabitt ya yi mata bisa taki shafa man da ya fitar da kudi ya saya, Rai bace ya ce" sai na tsine maki in dai baki shafa man nan ba Cikin kuka ta ce" Aba, ka yi hakuri ka ji? Bana son canza kalar fatana ka yi hakuri Abanna Ni ban haifeki ba, ke ba abin alfaharinki bane yau har na yi hakuri na dube ki na nemi intaki aman ki butulce min? Uban wa ke hure maki kune ne ni? Aba ba kyau, ba kyau, mu ji tsoron Allah Hannu ya saka ya dake bakinta ya ce" ki rufe mini bakinkin nan mai bakin jaraba! Ke sai kin shafa Kokarin shaketa yake dan ya shafa mata Mariama ta fito da gudu tana ihu tana nuna dakinsu Dakatawa ya yi yana binta da kallon meye ke kuwa Hankali tashe ta ce" Ashta ce, ashta ce, tun da ta ce maka in dai ka yi mata auren nan sai dai a kai gawarta kai kuwa kace sai me ba dai ka daura mata auren ba? Ita ce gata can sai wani abu take daga baya ta fasa motsi Fancakalar da Bak'a ya yi, shi da amaryarsa suka nufi dakin da gudu Daidai wannan lokacin Su Anna da sukai doguwar tafiya suka shigo gidan da salama bayan su Dogarai ne da suka tarbo gimbiyarsu wace sarki yake hakimce yana ji tamkar ya zo ya tarbi abinsa Jin kururuwa ya saka gaban Anna ya yanke ya yi wani irin faduwa, cak ta tsaya tana sauraron magangannun dake tashi, ihun kuka yayanta biyu suke inda Bak'a ke jingine jikin garu ta daga hannunta ta dora saman kanta ta yi tamkar status tana kallon kofar dqkin nasu , Muryar amaryar Algabiitt ce ta tashi ta ce" ta kashe kanta, ta kashe kanta Wani irin luuuuu Anna ta yi wanda ba wanda ya ganta sai faduwarta da aka ji , nan mutanen gidan suka ankara da dawowarsu wanda nan da nan gidan kai dama anguwar ta cika da dukan jama.a ana ta daga maganar, tabas Ashata ta rasu, ta rasu ne da bakin ciki, tana da ciwon zuciya ne wanda ya yi mata tashin kai tsaye, wanda amaryar Algabitt ta yi kazafin ta kashe kanta, Tashin hankali! Mota ce katuwa irin ta sojoji, direba mai iya janta kawai ya dauka kai tsaye suka karasa gidan Sarki Ayya na zaune tana gyara akaifunta labari ya zo mata cewar ta fito su tafi Mikewa ta yi fa hanzari tana murnar yau kam Allah ya sa , Tafia suke cikin mota, Walyn na zaune tunda ta cewa Ayya ina kwana bata kara magana ba sai shanshan kamshi take domin da yar tsamarsu da Ayya, gani take Ayya ke zige mata miji yana wulakantata Tafia ce suka yi mai tsayi, cikin jeji ne sosai kafin suke shigewa sahara gaba da baya Wani kara motar take a cikin kasar nan tana cin tafiyar wace kana ganni ka san karfi ne ke aiki Duda a cikin mota suke aman sun yi budu budu da su domin kura sosai ke tashi sanadiyar gudun da suke a motar da kuma kasa A hankali ya ratsa yar gadar da ta kai mutun cikin kauyen, wato *TIMIYA*.............. YA RAYUWAR ANNA? ALGABITTTT FA? BAK'A????? SU WARDUGU DA AYYA DA WALYN ME YA KAWO SU TIMIYA??????? MU JE ZUWA ...........................................................na yi imanin da ba dan Allah na sakawa bawa hakuri da dangana a zuciyarsa a lokacin da ya rasa wani mutun mafi kusanci da shi da Anna ta samu tabuwar hankali ga wannan lamari na mijinta, kar ku manta na fada ba labarin mutun na dauko ba aa labarin abinda ke faruwa ne, (YA FARU!)...... 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣4⃣ Bayan sun shiga garin timiya mutane suka ringa gudu suna kururuwa, wasu na fadawa gidajensu wasun kuwa na nufa gidan sarki wasu kuwa na kokarin neman hanyar da zata fitar da su daga garin ta barauniyar hanyoyi domin dai garin ba wani rufe yake ba Da mamaki suke kallon reaction din mutanen, Warsugu da sojan dake jansu ne kawai basu yi mamaki sosai ba duba da yannayin garin motar lafia dai bata shiga sai ta sojoji ko kuwa motar mugayen mutane masu zuwa su kai hargitsi su kashe mutane Kallonsa ya maida wajen Ayya wace ta dafe habarta ta wara idannuwanta tana mamakin nan yake mutumen kuwa? Aman gudun me suke? Labari ya kaiwa sarki a yar fadarsa, Tabas gabansa ya fadi da jin wannan lamari, ba a taba ba, mota har nan bata fara shiga ba, Mikewa ya yi da dukan kokarinsa ya tatara karfinsa inda dogarawa suka shiga kabara sunai masa kallon jarumi mai tausayin talakawansa da kuma kallon marigayi Du a bayansa suke inda yake daga kafafuwansa da kyar yana kara tunkarar motar, gannin motar ta sojoji ce hankalinda ya kara tashi, domin dai shi ya san motar tunda yana shiga gari kai gaisuwa fada, kai harma ya tafi kasa mai tsarki, me ya kawo motar sojawa Timiya? Shine tambayar da yake yiwa kansa, To ko dai sojojin ne a cikin motar ko kuwa mugayen mutane domin idan sun kai hari ai suna karbe motocin sojawan Wardugu ne ya bude gefen da yake zaune ya karbe hannunsa daga rikon da walyn ta yi masa ya diro daga cikin motar tsaye kan kafafuwansa Jibgi, dankari, in ba wardugu ba zaka shiga kauye sai ka je da wando tree Carter? Sai rigar sojawa irin body din nan damatsunnan hannayensa a fili, yar karamar bindiga marar karan sautin harbi ce a kugunsa inda ya rufeta da wannan rigar ta jikinsa ya saka belt kalar kayan sojojin ya daure tam abinsa Kansa sanye da hula baka kalar wandon sai takalminsa sandal wanda ya daura abinsa Sun karbe shi, sun amshi jikinsa, sun kawata shi Taku ya shiga yi da karfin jiki ya nufi Sarki da ya ja ya tsaya jikinsa na bari, ta faru ta kare, jita jitar Ashta kanwar matarsa ta kashe kanta wani ya kai birni an zo kama sirikinsa, mutuwar yau har kwana takwassss tabas wani ya kai, shikennan Alghabiitttt ya bani domin a hoto kuma a tv a birni Yana gannin wannan mutumen, an ce shugaban sojoji ne, shi da kansa ya zo kama algabiit? Algabitt ya ji haushin rayuwarsa, tunanin da Sarki ke yi kennan inda ya daskare da tare da bugun zuciyar ko wani taku na Wardugu dan nufo shi (🤦♀ in ba kauyanci irin na sarki ba, a rasa mai zuwa kama Algabiit karamin kwaro sai Wardugu? Za dai ka san waye shugaban sojojin nan hangensa kake!) Yannayin shigarsa ta tabatarwa da Wardugu shi ne magabacin garin, dama irin haka idan an zo sarkin gari ko mai garin gari ko kuwa tsageran gari wanda ya gagari uban kowa ke zuwa ya tarbi mutanen, in da karar kwana a kansu ake farawa Salama ya yiwa sarkin yana mika masa hannu sannan tar yana kallonsa ido cikin ido Jiki na bari Sarki ya karbi gaisuwarsa yana tambayarsa hanya da zarcewa da magana kamar haka" mai gida, na san ba auren iri ka zo nema a wannan jeji namu ba? Koma wa ka zo kamawa ka yi hakuri, a yi mana sasauci kar a kashe mu, a kama iya mutumen a tafi, ni kaina inada kankannan yara da mata, idan aka tsame masu ni wa zai ji da su? Da mamaki Wardugu ke kallonsa , aman da yake Wardugu dan duniya ne sai ya ce" Kai, baka san Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi ba? Ai kuwa gaba daya sarki ya haukace, jiki na bari ya saki kuka ya duka kasa ya rike kafafuwan wardugu ya shiga magiya Ayya dake cikin mota ta dake lebenta na kasa ta kali sojan nan ta ce" ka karasa da mu, na san wardugu wani lamarin ya shiga na tsawatar masa tun kafin abin ya birge shi Walyn ce ta juyo da sauri ta kalli Ayya, a ranta ta ayanna wai ta tsawatar masa, sai son ta nuna ita kadai ta isa ta juya shi, ta ja tsaki a ranta a fili kuwa ta ce" Hum tana tabe bakinta sosai Sojan ne ya juyo ya ce" Hajia, ki yi hakuri, nan ya ce na ja na tsaya idan na matsa bai bani umarni ba ni da shi ne Da haushi haushi ta shiga bude motar wanda sojan bai ankara ba har sai da ya ji ta bude ya juyo da sauri , har ta sauke kafarta guda ta ga Wardugun ya dawo da saurinsa gefen da take Yana zuwa ya ja ya tsara mata ya ce" Ayya maman Wardugu, kece ikon mai sanya Wardugu cire wando ta kai, Ayyana kar ki yi fushi kin ji? Koma motar mu karasa sai ki yi masa tambayar ai sarkinsu ne Da mamaki ta saki baki tana kallonsa, sarkinsu? Aman me ya saka shi kuka da dukawa ya kama kafar wardugu? Dan murmushi ya yi bayan ya saka mata lafayarta ciki ya rufe ya bada umarnin su karasa inda sarki yake Suna karasawa Ayya ta bude tana shirin fitowa sarkin na karasowa ya dan risina yana gaisheta, Ayya ta kalli wardugu ya dan sakar mata murmushi Kai ta girgiza ta sauka sosai ta gaishe da sarkin kafin take fada masa abinda ya kawo su Wata ajiyar zuciya ya sauke a bayane, ya ce" A garinnan Sofo mai bada magani kwaya daya mukeda, ya sufa sosai, gidansa da dan nisa da kasuwarnan sai mun shiga gari sosai Ayya ta amsawa sarki da ba damuwa su je A cikin motar nan sarki ya shiga inda yake dan hangen Wardugu ta madubi lokaci zuwa lokaci, ya yarda da ake cewa sarkin sojojin fa masifafe ne , bashi da dar, in ba rashin tsoro ba du irin yanda ake tsoron abzinawa da asiri shi a gabansa sai dai ma shi sarkin ya ji gabansa ya fadi maimakun na wardugun ya fadi, lale yaron ya sha ya jiku ya tada kai , rabonsa da kuka tunda aka zo masa da sakon Gaishat ta tafi baban birnin niger inda ya yi tunanin shikenan ta gudu me ta bar shi.....(wani lamarin dan gyara nvl dina ne fa, sarkin abzin ba wasa walahi🤣🤣) Basu zame ko.ina ba sai anguwar baba Sofo Suna tsayawa mutane suka cika wajen, tunda sun ga sarkinsu a tare da mutanen ai shikenan sai suka sakin jikinsu da su harma ake matsowa a shafa motar sai a kwala ihu da yaren buzanci a ce" nima na taba, mota mota a garinmu, mota har gidanmu, Du ja sukai a lokacin da mutanen ciki suka fito gaba dayansu, suna masu binsu da kallo, girma da yannayin tsarin halitar wardugu ta basu mamaki, suna da mutane dogaye sosai sai dai ba masu fafadan kirji da manyan damatsuna haka ba, sai kuma matan dake tare da mutumen da dayen sojan, kun san dai Ayya gwadar ado ce, bale Walyn farar mace alkyabar mata, walyn farar batuba ce tas tas
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN