Author : Nana Maryama Category : Romantic Hausa Novels
sake kallon aydarh wannan karon kanta a kasa yake idonta rufe amma ba bacci take ba tayi wanka duk a takure take jin ta har wani kyankyanmin jikinta take ji ( ah
🙄
abun naki yayi yawa aydarh) asalin abayar ta ce da tafito daga gida tun farko ta mayar domin tak’I mayarda wanda ta cire, ta fada sosai sai asalin kyauwun fuskarta yafito tarr gashin gabanta kanta yayi luff luff kasancewar veil din abayar da ta daure kanta yayi baya “ can nurse din tace please can I asked you ma’am? Bude idonta tayi kamar bata taba kuka dasu ba wani irin haske da kyau garesu mai matukar daukar hankali da fizga, washe baki nurse Saratu tayi tace dan Allah daga
Qatar kuke ko Egypt ni nakasa gane da yan wace kasar larabawan kukayi kama wallahi kunada mugun kyau ke da mijinki kai har kama ma kukeyi auran zumunci ne hala? Aydarh dai tayi shiru domin surutun nurse saratu ya dameta ko gane abunda take fada ma batayi,ganin aydarh bata amsa bay asa nurse saratu tace ko dai ke bakya jin hausa amma naji shi mijin naki hausa raddam a bakinsa wallahi daman baya son yawan magana, still aydarh was quite ganin bazata amsa ta bay asa nurse saratu kama kanta tayi shiru tace mata zan fita idan kina bukatar wani abu sai ki kirawo ni bara nayi ma maigidan naki magana yasamu maki abunda zaki ci, daga haka ta juya ta fita, sai sannan aydarh ta bude ido tana bin dakin da kallo. Dr ibrahim yayi murmushi yace kai kam baka son magana sam sai muna labari sai ka fada tunani, ko dai duk halin da mai dakin naka ke ciki ke damun ka nagaya maka babu wani damu ko zuwa gobe ma zamuyi iya sallaman ku, dan murmushi malik yayi yace tau Allah yakaimu “nurse saratu ce tashigo da sallama office din cikin girmamawa takalli malik tace yallabai asamo ma madam abunda zata ci zuwa yanzu alluran sun sake ta nasan ta isa tafara jin yunwa, kallonta yay isai kuma yace tau a ina zan samu wurin siyarda abinci? Da sauri dr ibrahim yace aa abokina bara nayi waya yanzu a ba yaro yakawo muku daga gida “ kallonshi malik yayi zaiyi magana dr ibrahim ya girgiza kai yace aaa babu komai gidan ai babu nisa kuma ance bakon ka annabin ka duk da ba wajena kazo ba amma ai garin mu kazo, murmushi malik yayi tareda shafa sumar kansa yayi kasa da murya yace tau angode Allah yasaka, Ameen dr ibrahim yace tareda fido android phone dinshi yayi dialing contact din da yayi Saving da iya, bugu biyu aka daga cikin nutsuwa yayi sallama daga can bangaran aka amsa mashi yace iya idan rabi’ah na nan a bata abinci takawo mun yanzu, amsa mashi akayi sannan yayi godiya ya katse wayar, Ko 12mins ba ayi bas ai ga wata matashiyar yarinya kamar aysharsu tashigo da warmer abinci kwara biyu cikin leda sai jug da cups biyu a hannu, tana tsananin kama da dr ibrahim koba a fada maka bak asan sister shi ce ta kalli malik ta gaishe sa ya amsa ta, tace yaya ga abinci amsa yayi yace mata sannu, yauwa tace tana satar kallon malik dayayi kamar bai office din dan ko motsi bayayi, duk abunda take dr ibrahim na kallonta. Kallon malik yayi yace gashi sai kaje ku ci don kaima tunda kuka zo banga ka kai komai bakin ka bah, hannu yasa ya dauki kayan abinci yafita zuwa dakin da take. Bayan fitar malik rabi’ah takalli dr ibrahim tace yaya a ina kasan shi please? Wannan ba balarabe bane kam? Ibrahim ya kalleta yace aaa ba indiye ne karewa! Wait miye hadinki da shi? Girgiza kai tayi ta mike tace ni natafi sai ka taso “:bata jira amsar shi ba ta phecee daga office din yaraka bayanta da harara,
b
ayan sun dawo sallarh malik ya kalli dr yace dan Allah a ina ake samun gidajan haya? Shiru Doctor yayi sai can yace idan ba damuwa akwai wani gida can kasan anguwar nan babu nisa gidan mai clinic din ne da a ciki yake zaune kafin a mayar dashi kaduna aiki compound ne sauran parts din akwai mutane wannan ne kawai babu idan ya tashi da yace nashiga na zauna baya son barin shi hakanan tau yanzu tunda ga ka sai muje ka gani idan yayi maka, malik was speechless he is out of words tun haduwar shi da dr ibrahim yake masa kirki kala kala……..
Dr ibrahim yace zuwa gobe dasafe kafin a sallameta sai muje tare ka ga gidan daga nan din zuwa can 200 ake zuwa a keke,
malik yace tau shknn Doctor Allah yakaimu nagode “ dr ibrahim yace babu komai yanzu lokacin tashi na yayi daman bama kwana a nan din mu uku ne kawai ke aiki a nan din sai shi mai clinic din da ai chemist ne sai kuma mayarda wurin clinic ,malik ya danyi
murmushi zuwa yanzu har yasaba da surutun Doctor ibrahim din. Sai da yafara shiga dakin da aydarh ke kwance ya sake gwada bp ta kafin suyi sallama da malik nurse saratu da 8 tayi take tafi sai dayar ita Doctor ce ita kawai ke kwana itama ba kullun saidai in har akwai patient din da aka kwantar basu ma cika kwantar da mutane ba a clinic din, Akwai wadatacan haske a clinic din, da sallama mai gadin clinic din yashigo hannu shi rike da tabarma dakuma prayer mat sai bargo da pillow mikawa malik yayi dake zaune a reception ,” da mamaki malik ke bin mai gadi da kallo shima mai gadin kallon malik yake kamar yasamu t.v bai taba ganin mai irin Kamar shi a zahiri ba saidai a indian flim “ ganin yarda yake kallonshi ko kiftawa babu yasaki baki yasa malik mikewa tsaye, yace lafiya dai? Sai sannan mai gadin ya washe baki yace aaaa lafiya lau yallabai dakta ibrahim ne yace a kawo maku wannan hannu malik yasa yakarba yana jinjina kirki irin na Doctor ibrahim, mai gadin yace ina waje ranka ya dade idan akwai abunda ake bukata ayi man magana “ko rufe baki bai yi su kaji takon tafiya a bayansu mai gadin ne ya waiwaya yace ahh barka da zuwa dakta yanzu nake zancan ki a raina nace ko dai dakta ibrahim bai gaya maki da marar sa lafiya bam asu kwana “dan murmushi wacce yakira Doctor din tayi tace aaa ya fadamun ina hanya bana jin dadin jikina ne sam ,cikin jimami yace Asha kam Allah yabada lafiya,Ameen kawai tace tayi gaba ko kallonta malik baiyi ba ya kwashe kayan da Doctor ibrahim ya aiko masa yashige dakin. Ahankali ya tura dakin ta takure kanta waje daya bacci take amma a wahale da alama ma sanyin damuna da akeyi garin na damun ta domin ta kudundene kanta cikin hijabi kallonta yayi for few seconds yadauke kanshi ya ajiye kayan, bargon yasha jiki amma duk da haka fess yake a wanke sai kamshin klin yake “ warware shi yayi tass sannan ahankali ya matsa kusa da gadon karamin tsaki yasaki kafin yasa hannu gently ya kwashe hijabin, dasauri ya dauke kanshi ganin yarda zip din abayar jikinta ya dan bude har kana iya ganin whitest boobs dinta wanda skin din ke kamar madara har wani shining yake , tsaki yasaki a fili kafin ya yafa mata bargon “komawa yayi ya zauna kan rubber chair dake dakin yayi alkawarin mantawa da komai yayi alkawarin karbar kaddararshi shiyasa ko kadan baya son sake tuna komai. Without making any sound ya buda warm din yana kallon abinci bazai iya tuna when last yaci abinci ba irin mutanan ne shi wanda sam basa wasa da cikin su amma yau gashi baya son ko kallon abinci, white rice ce da stew sai kifi cikin jug din kuma zobo ne still akwai ice a ciki batayi melting ba kadan yaci abincin ,yana tuna yarda take cin Abinci dazo kamar magani batayi three spoon ba ta aje, girgiza kanshi a ranshi yana tunanin ita din amanace a wajanshi ita din ticket ce ta yafiyar da mahaifiyarshi zatayi masa kan laifin da bai aikata ba “cike da kwarin gwiwa yayi ma kanshi alkawarin fuskantar sabuwar rayuwar shi da kuma gogaya tsakanin shi da kaddararshi.
Tabarmar ya shimfida yasaka pillow ya kwanta sam baya jin bacci amma wata irin gajiya ke tattare dashi, Almost thirty minutes yana ahaka idonshi rufe amma ba bacci yake ba,knocking kofar akayi ahankali yamike yace who’s that? Daga waje Doctor hafsa tace Doctor ce zan duba ko drip din yakare, “bude kofar yayi tareda bata hanya tashigo zata kai saar shi koma tafishi, ahankali tace ina wuni ya mai jikin? Lapia, da sauki kawai yace ya koma kan kujerar ya zauna ,duba drip din tayi taga still da saura, sannan ta dan yaye bargon kadan tashafa goshin aydarh taji temperature din jikinta normal normal kafin ta mayarda da bargon ta rufe ta, tunda
Doctor hafsa tayi knocking ta farka taki buda idonta tana sauraron duk abunda ke faruwa, Doctor hafsa ta kalli malik tayi murmushi ahankali ta saukar da muryar kamar mai tsoron yin magana tace is she your sister or your wife sir? Malik yayi shiru har ta fidda ran zai amsata can yace “both” Dr hafsa tace Allah sarki Allah yabata lapia ,anan anguwar kuke ne? Malik ya girgiza kai yace aaaa , dr hafsa tace alright idan drip din yakare please let me know am in the office, Alright yace “daga haka Doctor hafsa ta juya ta fita. Har wajan 12 na dare malik ya nemi bacci yarasa itama aydarh sam ba bacci take kasancewar kadan kadan drip din ke sauka shiyasa har yanzu bai kare ba, har yanzu idonta rufe yake and bata fito da fuskar ta waje ba,ganin ya kasa bacci hakan yasa shi shiga toilet ya daura alwalla ya fito ya shimfida prayer mat din ya kabara sallarh, sai wajan one kafin drip din yakare lokacin malik ya sallame sallarh, sai sannan ya tuna da zancan kiran dr hafsa idan drip din yakare mikewa yayi tsaye ya matsa kusa da gadon yaga drip din yakare,without making any sound ya buda kofar yafita zuwa office din dr hafsa sai da yayi knocking sau uku sannan cikin muryar bacci dr hafsa tace am coming, bai sake cewa komai ba ya juya ya koma dakin, Dr hafsa ta kalli aydarh tace ko zaki shiga toilet din? ahankali ta gyada mata kai sai kuma tayi kasa da murya kamar zatayi kuka tace I need to change kuma ina son warm water,ita dai Doctor hafsa kallonta take ko kiftawa babu ganin yarda take magana cike da shegen shagwaba da tsananin izza da kuma aji gauraye a muryan ta kar ma aje batun kyau wannan zata ce tunda Allah ya hallice ta she never meet a beautiful persons irin aydarh da malik duk da bata da lapia amma asalin gayu ya bayyana a jikinta asalin hutu yanuna ajikinta babu abun da take kallo a sai diamond rings din dake hannun aydarh masu masifar kyau da daukar ido, murmushi dr hafsa tayi tace alright am coming, bayan fitar ta shima malik ya tashi ya kasake kabara sallarh ita dai aydarh har yanzu bata yarda ta sake hada ido dashi ba . Dr hafsa tadawo dauke da flask a hannunta ta wuce toilet ta hada ruwan toilet din is very neat daman bawani amfani ake dashi ba, fitowa tayi tace muje na hada, bata ce mata komai ba ta tashi ahankali tana wannan tafiyan nata mai daukar hankali,dr hafsa dai sai kallonta take yah rabbi duk shape din nata ne ko na ciko ne this girl fine finish Allahumma bareek, fitsari tayi dr hafsa ta mika mata pad da pant duk malik na kallon su bayan ya sallame sallarh har su kagama sannan dr hafsa ta kalli malik tace yallabai sai dasafe,sannan ta juya ta kalli aydarh itama tayi mata murmushi tace sai dasafe madam Allah yakara sauki aydarh bata ce komai ba, sai malik ne yace angode kwarai Allah yasaka , babu komai dr hafsa tace sannan ta fita ta ja musu kofa, Malik ya kalleta bai san sunan da ya dace ya kirata ba, Ahankali yace how was your body? Shiru tayi kanta na kasa tace fine, babu wanda yasake magana cikin su.
Hajajju ta kalli oum tace to pah, wanene abba? Oum ta gyara tsayuwar ta tace habib, hajajju tace shi habibun yace zaku tafi can kasar din? Oum tace ehh ba jimawa zamuyi ba , hajajju tayi kasa da murya tace tau nidai ina nan bazan koma wannan kuturun gidan na yaya ba gaskia,oum tayi murmushi tace tau shknn nima na fi son ki zauna nan din tunda rufaidarh na nan itama hajajju dai tayi shiru bata ce komai ba oum tace tau idan gari ya waye ma karasa maganar tau Allah yakaimu hajajju tace,oum ta fita. Wajan karfe 10 flight dinsu ya tashi zuwa kasar spain hajajju dai hada kukanta,tace Allah sarki rayuwa famelin Habibu duk sun yaye sun barmu daga mu sai halin ko awani hali yaran can ke ciki Allah kawai yasani andai cuce su an cuce rayuwar su ita
yarinya an banka mata aure da wannan basamudan mutumin, shikuma an lika mashi yarinya ga ba isassar lafiya Allah dai yasaka masu, rufaidarh dai sai kallon hajajju take inda sabo har tasaba da halin hajajjun. Hajajju tashiga kitchen ta iske daya daga cikin maids din gidan ts
aye tana goge kitchen cabinet.
Hajajju tayi mitsi mitsi da ido tace hup dai an gaya maku matsayina a gidan tau idan baku sani ba daga yau kusani daga yanzu har su habibu su dawo nice zan dinga bada umarnin duk abunda zaayi a gidan nan , ita dai mai aikin na tsaye da dan karamin towel a hannunta tana kallon hajajju, ko kiftawa babu “can hajajju tayi kasa da murya tace wai ita waccan dayar balarabiyar ita bata da mai so ne komai? Allah na tuba tunda nasanta ban taba jin labarin wani na neman auranta ba gaskia, mai aikin tace wacce balarabiyar ? Hajajju ta juya ta juyo Kamar mai gudun wani ya ganta tace waccan abun manah watake yauwa rufaidarh, “mai aikin ta girgiza kai tace aaa mama tanada masu so sosai amma kila ita ce dai bata bada fuska”hajajju tayi shiru can kuma tace kai kuji rubabba yoo Allah na tuba bata ga ita yar uwar ba ma da auranta kuma tafita komai ma,amma sai ita tau nidai ba ruwana bara nakama bakina nayi shiru kingan ni nan babu abunda yashafe ni da rayuwar mutune, ni ko maganar mutane bana son ana mun, shiyasa kullun nake zamana lapia,kema ga shawara ki kama bakinki ba ruwanki da maganar bil’adama “ ta sake kasa da murya tace kinga habibu duk cikin mu shine kawai ba rubabbe ba da kudinshi tau sai ni din nan dakika gani tsaye a gabanki famelin mu duk sun yaye sun rasu daga ni sai wata mata da muke uwa daya uba daya muka rage sai kuma ibrahin da ya’yanshi “ ta gyara tsayuwar ta tace wai fa shine dan tsoron Allah da kaunar ma’aiki da yanzu ba ‘ayi za a hadani da jafa’I wai wani abu na koma kuturun gidan matar da zama “ita a wa?ita ame? Da zasu hadani da zama waje daya da ita babu iskan kirki gidan ba kai babu kugu haka take rayuwa ba da ba jikah daman mu famelin mu munada tsari bama sakin jiki mu dinga zazaga yara kamar tsuma shiyasa kikaga bamu da yawa ma “ ita dai mai aikin har ta gaji da sauraron hajajju she see no reason da zata dinga mata wannan zubar, bata ce mata komai ba har tayi shiru “sannan tace tau Allah ya kyauta mama”hajajju tace haram haram badani ba aikata wannan baqin kantameman zunubin miye wani mama, sau biyu ina zuwa makkah fa wanda a famelin mu bayan ni sai habibu da wannan matar tasa dakuma diyarsu wanda a halin yanzu bamu san inda suke ba, still dai maid din she is eager hajajju tafita takarasa aikinta tun tana bata dariya har labarin yafara fita kanta nan fa take ce mata ita bata maganar mutane amma tun dazu take bata labarin abunda bai shafe ta ba “ can wani dabara ya fado mata tace am hajiya mi kike bukata na kumallo “hajajju ta washe baki tace daman tun jiya rabo na da sa ma cikina wani abu tashin hankali ya hanani sakat billahi “maid din tace Allah sarki, hajajju tace shayi zaki hadaman ki suya dankali da kwai takwas sai sabon biredi da farfesu yanzu ina jiranki ,maid din tace tau shknn hajiya dana gama sai na kawo maki a nan dining hajajju bata ce komai ba ta juya tafita.
Doctor hafsa ta kalli malik tace ya jikin nata tasamu bacci kuwa? Sai da malik ya sace kallon aydarh dake zaune ta rabe waje guda kamar marainiya kallo daya zakayi mata kaga alamar tana cikin damuwa sosai she is helpless and she’s alone,can ya kalli dr hafsa yace jiki da sauki alhamdulilah amma ina ga gaskia batayi bacci ba, duk maganar da suke aydarh na jinsu ko kallo
basu ishe ta ba,ahankali dr hafsa ta taka kusa da ita tace good morning ma’am how was your body? Kamar bazata magana ba kamar batagane da yaran da dr hafsa ke tambayan ta ba , bata motsa ba kuma bata dago kanta ba jikinta na cure waje daya daidai numfashinta ahankali take shakar sa take kuma fidda shi, dr hafsa dake kallonta ko kiftawa babu bata gaji ba tasake maimaita tambayar da take mata, kusan 2mins lokacin dakin yayi shiru malik kau bakin ciki kamar ya kashe shi ji yake kamar ya rufeta da duka ganin irin yarda ta maida dr hafsa kamar wata shashasha tana tambayar ta tayi mata shiru, dr hafsa tayi murmushi ta girgiza kai tace Allah yakara sauki bara na hada