Author : Nana Maryama Category : Romantic Hausa Novels
dayasa komai ya cika tamkar gaske? Hannu abba ya daga yana nuna abby cikin rawar murya da tsoro yake furta ya..y…yarh ya…y..yarh kaine ko idona ne daman yayah kana adamawa har yanzu? Malik dake kallon su tamkar idonshi zasu fado yarasa gane kan komai hankalinshi da tunaninshi baki daya sun gaza fahimtar komai anan tsaye yake ko zama yakasa haka shima abby a tsaye yake yana jinjina girman da kuma ikon Allah wacce kaddara ke son tadawo baya wacce gaskia ke son bayanna kanta ashe suna da rabon sake ganin juna a duniyar nan Duk da yasha mafarkin hakan kuma kullun cikin ba ummi kwarin gwiwar faruwar hakan yake amma sam baiyi tunani yanzu ba baiyi tunanin kwana ku saba,Mikewa tsaye hajajju tayi tare da gyaran murya tace duk ku tsaya kowa sai wani gwale gwalan ido yakeyi ku da ko abunda yakawo mu nan din baayi ba har kun fara wani yan sane sane ku zauna kuji abunda yatara mu nan kafin ku cigaba da wannan ya tunane tunane ahtau ku tsaya kuji jafa’in da yaran ku suka kwaso zama sukayi kowa na mamakin maganganunta cikin abby da abba da ummi baki dayansu ta daure masu kai wasu yaran nasu?oum dai kanta na kasa itama rufaidarh haka while baaba hajajju take kallo tareda yi mata alamar datayi shiru ita zatayi magana dasauri hajajju tafashe da kuka tace aaa yayah wllh aaa dole nayi magana ki daina hanani dole nayi magana kowa ita yake kallo cikin su,kafin takira sunan abba tace habibu kaga wannan sai sannan abba yakalli direction din ummi da aydarh da hajajju ke nuna mashi, nagani hajajju kiyi magana manah kin sani a duhu mitsi mitsi da ido hajajju tayi tareda gyara zama tace tau tunda ga farko har karshe zan zayyana duk abunda yafaru domin niba’a munafurci dani ba oum kadai ba hatta rufaidarh da baaba saidai da hankalinsu ya tashi sun san halin hajajju tsaf zata iya watsa duk wani shiri nasu ta fadi gaskia amma kau da sunyi dana sanin involving dinta a case din sake fashewa da kuka tayi cikin muryar dattako abby dasai yanzu yayi magana tunda suka shiga yace hajiya kamata yayi kuyi magana ba ku dinga kuka ba duk kun bar mu a cikin duhu wani abu ya farune mutuwa akayi ko mai? Yoo Allah na tuba ibrahin ba kwara mutuwa ba da zagin da yaran nan suke shirin jawo manah
.
Jawo manah ba still dakin babu wanda yayi magana kowa kallon hajajju yake banda rufaidarh oum da baaba da gaban su ke ta lugude hantar cikinsu na kadawa jiran jin abunda hajajju za tace, suke. tana matsar kwalla Takai 5mins ahaka sai tayi kasa da murya tace tau Alhamdulilah haka naso kuma haka na bukata mu hadu baki daya pameli domin mu yanke hukunci tare na’am shine abunda abby yace tare da gyara zama yana kallon hajajju gyaran murya tayi “tace tau saidai fa kuyi hakuri ita zuciya bata da kashi yara ne ka haife su baka haifi halinsu zamani ne yazo da haka habibu mai mace kuma kullun mai mace shi ake cuta kai zaka lallaba ka rufawa kanka da rayuwar ka asiri ka zubda makaman yakinka ka bada hadin kai abba dai bace komai duk a birkice yake sauraran bayanan hajajju, “sai kuma ta kalli abby tayi kasa da murya tace kai kuma sai ka goye bayan gaskia kayi adalci “zuwa yanzu jikin abby yagama yin sanyi yace in sha Allah hajajju zan zamo mai adalci a duk hukunci da zaa yanke,wayar ta fiddo daga cikin katuwar jikkarta keypad ce anyi mata mugun daure da rubber bands bugu daya tayi aka daga sannan tace bismillah ku shigo,within 2mins sai ga salma da doctor ashraff sun shigo gaishe da kowa na parlor sukayi sannan doctor ashraff yafara magana cikin nutsuwa Alhaji ayi hakuri I didn’t wish abubuwa su zo ahaka I have no other option but to spared the truth a min afuwa cikin tsawa abba
yace doctor just talk “daidai ta nutsuwar shi doctor ashraff yayi yace last week nayi ma aydarh medical checkups abunda nagani ba karamin daga mun hankali yayi ba nasamu salma nayi mata bayanin komai duk cikinmu babu wanda yasan abun yi yasa muka sami hajia rufaidarh da maganar da kuma ita oum, will you just go straight to the point doctor shiru doctor yayi can yace am sorry sir but I found out aydarh is pregnant for almost two months wani irin zabura aydarh tayi kanta nawani irin juyewa tasan abunda yake nufi tasan mi kalmar ke nufi da yare kala kala da turanci hausa larabci da kuma fulanci,malik kau tsaki yayi a ranshi daman yasan wannan yarinya salihan cin karya take ( nikau nace kabari rabo yazo kanka) Ummi ta rike ta sosai ganin yarda tayi din. Da wani irin mugun speed abba ya mike tsaye yayi ma doctor ashraff wani irin mugun kallo yace did you know what you just said doctor kasan abunda ka fadi kuwa? Baby? This is serious ina tunanin baka san waka ke magana kai ba girgiza kai doctor ashraff yayi yace nasan abunda nake fadi ga result din ma ka duba sir yafada yana fiddo paper daga pocket din suit dinshi ya mikawa abba hannu na rawa abba yakarbi takardar ya bude kallo daya yayi ma paper ya maida ta kan kujera banda yana namiji yanada karfin zuciya da tuni zuciyarshi ta buga maganar da hajajju tayi yasa shi dawowa daga shock din daya shiga “tace tau ai komai yazo da sauki tunda cikin ba rayayye bane Allah yakarbi abinshi yanzu haka ibrahin kafin mu zo gidan naka daga asibiti muke nida yarinya dashi uban cikin audul gashi nan zaune ya sadda kai kamar wani waliyye alhalin shine mai laifin, da wani irin duba ummi ta kalli hajajju domin bata ma gane abunda take fadi ba malik uban dan as how? Ganin haka yasa hajajju cewa kwarai da gaske asiya audul shine uban cikin dan ya gantalle yau kuma ga shaida nan naga ke ma kika rike yarinyar kamar kinsan danki yacuce ta ya zalinceta! da zaa auna jinin ummi kila yakai trillion 100 wannan wacce irin kaddara ce wannan wani sabon bala’In ne ya kunno kai inalilahi waina illahil rajiun adduar samun sauki daga wurin ubangiji kawai ummi ke domin dakin juya mata take komai biyu biyu take gani and still yanda take rike da aydarh bata sake taba duk da yanzu kusan hali daya suka shiga ita da aydarh ,kokowa aydarh tashiga yi da numfashin ta alamar asthma ta ke nima tashi “ tunda yazo dunia bai taba shiga tashin hankalin da yashiga yau ba bai masan yanayin dazai fassara kanshi ba shidai yasan rabi rai rabi mutuwa haka yake ji, wasu irin hawaye masu zafi ke sauka daga
.
Id
on abby bai taba tunani faruwar komai ta haka ba bai taba kawo ma ranshi malik zai aikata abu irin haka bai san adadin lokacin da ya dauka ba zuciya sa na juya zancan hankalin sa ya gaza auna lamarin ji yake kamar mafarki ko almara ABDOOLMALIK ne yayi ma wata ciki watan ma diyar dan uwanshi uwa daya uba daya wanda duk duniya su biyu iyayansu kawai suka haifa “son zuciya da kuma son duniya irin na dan uwan nasa yaraba su da juna tsawan shekara ashirin da biyu wannan wacce irin kaddara ce mike shirin faruwa da rayuwar su? Oum kau wani irin ajiyar zuciya ta sauke rufe idonta tayi ruf tana jiran ji karashan zaman, ummi da har yanzu bata dawo daidai ba ji take kamar duk duniya babu wanda ake jarabta kamar ita ashe kuka rahama ne ashe,ashe wani lokaci dadi ke sa ayi kuka . Hajajju tace tau nan da kuke ta wani yan kuke kuke abunda dai yafaru ya riga faru kuma dai iyakar yamu yamu kawai muka sani kunga kwara asan yarda zaayi kafin wasu rubabbun su sani su samu a bakin duniya yanzu ma fita day ace tattara su a hadasu “AURE”kalmar auran da tafito daga bakin hajajju sai yazamo tamkar wani miki ne ta
famo a azuciyar ummi harbawa zuciyar tayi tana barazanar fitowa waje bazata zamo marar aldaci ba bazata so kanta da zuciyarta ba ko itace a wannan matsayin da wani yayi wa yar ciki karshan hukunci da zata yanke mashi kenan shiyasa taji wani kalar yanayi farin ciki ko bakin ciki ( bakin cikin dai
🙄
)ba karamin karfin hali abba yayi ba wajan sauraran maganganun su bai taba tunanin abu mai haka da wannan ba zai faru a rayuwarshi ashe duk wayon ka duk dabarar ka Sai Allah ya jarabceka mutanan dayayi nisa dasu mutanan dayayi kaura daga rayuwarsu mutanan daya binne gaskiar dangantaka tsakanin su ashe zanan gudun kaddara su atare suke ashe gudun kaddara guzirin iske ta ne inalilahi waina illahil rajiun zufar dake keto masa tamkar yana cikin oven tamkar bai taba shiga inuwa ba,aydarh dake ma salma wani irin kallo hawaye ke zuba a idonta sosai ko da bata taba tunanin salma da doctor ashraff zasuyi mata abu irin haka ba kuma da wanda ma batasan ko waye ba kuka take sosai a jikin ummi, oum tamike ta nufi abba ta durkusa ta rike kafanshi cikin kuka “tace abban aydarh kar son zuciya ya rude ka kasa zatar da hunkunci ka dubi rayuwar ka ka dubi rayuwarmu ka yi abunda musulunci yace tunda har bataji kunyar yi manah haka nima a matsayin mahaifiyarta na yafe ta wani irin kuka ta fashe dashi ,dasauri hajajju ta mike tace aaa zara’u yoo Allah natuba babu katon da ya isa hana wannan mutuman auran yarinyar nan sai kuma tayi kasa da murya tace tau tunda bai ji kunyar taba masu diya ba mu ma ai bamu jin kunyar aurar masa da ita,malik ya mike tsaye yana girgiza kai yace enough hajajju ya isa haka mi nayi maki dakike kokari bata rayuwa ta mi nayi maki da kika zabi yi mun wannan sharrin ?’wani wawan mari abby ya dauke shi dashi kamar jira ummi take ta taro shi ta dayan side din cikin kuka ummi tace wallahi duk duniya idan gatanka ne sai ka aure yarinyar nan mugu azzalumi marar tsoron Allah indai ni ce mahaifiyarka sai ka aure yarinyar dabas ta zauna kasa ta fara wani irin kuka,zuwa yanzu aydarh mutuwar ta kawai take jira ciki! Aure! Kalaman da suka zautar da tunaninta bin kowa take da kallo domin batasan abun fadi bakoo abun yi sauraran yanda numfashi ta ke fita da yarda zuciyarta ke over racing kawai take.Baaba tace kuyi hakuri shi daman duk yanda bawa ke kokarin gujewa kaddararshi sai ta riski shi wannan wani ikon ne daga Allah wayau ko dabarar bazata iya kwatar mu ba daga rubutatciyar kaddara ba “Don haka a matsayi na na babba a kaf ahalin nan nake umartar ku da kuyi hakuri ku hadda auran yaran nan ya yanzu kuma a take! Abba daya lula duniyar tunani sai yanzu ya dago kai ya zubawa aydarh ido kallonta yake irin kallon kin ban kunya kinbani mamaki,aydarh da bata fahimtar komai batasan ma irin kallon da abban ke mata ba,Abby yayi gyaran murya yace habib ina neman alfarma ka yafewa abdool abunda yayi na biyu ka yarda mu hada auran su suyi nesa damu domin ganin su a kusa damu ba karamin ciwo zai jawa zuciyoyin mu ba musamman kai abby ya karasa maganar yana Kafe abba da waennan manya idanun nashi,har ga Allah lokaci daya abba yaji ba aure ba komai ya cancanci yayiwa aydarh bai taba tunanin zatayi mashi wannan tabon ba kuma ma a mutanan daya dauka mafi kaskantatu a rayuwar shi mutanan daya guda saboda a ganinshi abun kunyarshi ne yayi kudi kuma mutane su sam asalinshi talaka bane tsawon shekara 22 ba taba tunanin akwai ranar da zasu dawo rayuwarshi ba,mikewa tsaye yayi yace ni Alhaji habib nabawa yaron wurinka auran Aseeyarh akan sadaki mafi kankanci sannan matsayi na mahaifinta na yafe ta har…. Dasauri baaba tace aaa habibu kar ka karasa hakan ma ya isa zasuyi nesa daga gareku in sha Allah har sai zuciyoyin
ku sunyi sanyi,Abby ya fiddo 20k daga aljihun shi ya mikawa rufaidarh yace taba aydarh sadakin ta ne sannan ta kira limamin massalacin gidan yazama waliyyin aydarh! .cikin yan mutunan liman yakara so aka farad uk wani abunda musulunci ya shar’anta kafin daurin aure gaban duk wanda ke parlor aka daura auran ABDOOLMALIK IBRAHIM MAIDO DA ASEEYA HABIB MAIDO kan sadaki naira dubu ashirin wani irin sanyayan ajiyar zuciya oum tasauke bata taba tunanin abun zai faru duk yanda suka shirya ba hajajju kau wani irin arna smile tayi irin boss din nan rufaidarh kau ga farin ciki ga tausai dukka sun hade mata ,salma dai kanta na kasa.Doctor ashraff yayi bankwana yatafi abba bai jira komai ba ya mike yanufi part dinshi oum ta bishi da ido tasan yau akwai aikin lallashi koma miye mai sauki ne tasan yarda zata saita mijinta abby ma godiya yayi wa oum ya sake bata hakuri kan abunda yafaru yayi mata sallama yafita,ahankali ummi tamike ta rike hannu aydarh da still takasa tsayawa tsaye tace mungode fatima Allah yayi albarka oum itama godia tayiwa ummi ta bisu da ido zuciyarta na tsinkewa aydarh kau da batasan duk abunda ke faruwa ba sai bin su take kamar status da sauri rufaidarh ta mara musu baya domin yi musu rakiya hajajju ma jikkarta ta diba tana cewa oum zuwa gobe zata zo ta karasa hutun nata anan,wata irin faduwa aydarh da jiri ke kwasarta tayi daidai kofar fita parlor oum na ganin haka ta juya dasauri tay hanyar part dinta kukan dake cin ranta na kufcewa dasauri ummi tayi kanta ganin yarda ta fadi kamar ba rai tsawa tayi wa malik tace yadauke su tafi “kamar bazai tabata ba ya dai daure ya dauke ta yanufi hanyar waje hajajju ta gwalo ido ta kalli rufaidarh tace anya kau ba mutuwa tayi ba?rufaidarh tashare hawayenta tace aa hajajju ina tunani rudun da tashiga ne in sha Allah zata tashi tau Allah yasa dai mudai bara mutafi sai kuma tayi kasa da murya tace yau dan dole kawai zai sa na kwana wannan kuturun gida na ibrahin gashi audul din dake siyo man abubuwan da bazaa rasaba yau ko bindiga aka bashi ni zai harba yoo Allah natuba daga taimako sai abu yadawo kai na shi hwa taimakon shi nayi dana sa aka bashi yarinyar ita dai rufaidarh kallon hajajju kawai take batayi magana ba dasauri hajajju ta bi bayan ummi. Babu yarda rufaidarh batayi ba su bari driver ya mayar dasu abby yace babu komai sun gode zasu samu dan sahu, hajajju da bata so haka ba tayi mitsi mitsi da ido tace kai kuji tababbe tau a ina kaga alamar dan sahu anan anguwar salon aganmu cikin dan sahu kamar wasu yan iska ace manah mayu yan kwakwa munzo maula kamar wasu zararru ina dalili da kyar dai aka shawo kan hajajju suka samu napep suka tafi ummi da abby suka shiga daya Malik dake dauke da aydarh kamar baby a kirji wanda riqe ta dayayi yanayin shi ya chanza bai fahimce komai abun dunia ya taru yayi mashi yawa tare suka shiga da hajajju,fuskar nan tashi kamar hadari dinki tsab idonshi kamar zaiyi aman wuta turaranta ya takurawa rayuwar shi.
Assalam babyn habeebe’s
💖
nace bara na gaya muku ina yan mata? Ina haddadun mata?ina manya mata?ina yan gayu? Da zawarawa baki daya
🥳💖
nesa ta zo kusa kina neman musulmin turare mai kamshin rahama turare mai musulmin kamshi
💖💃🏻👌
wanda zai sa duk idan kikaje a kalli ki domin kamshin shi cikin nutsuwa yake fita
💃🏻
tau nesa tazo kusa come one
☝
️
come all to real scent perfumes
💃🏻
nake gaya muku karshan kamshi ake magana just dm me and purchased yours
😉💖
muna da air fresheners masu kamshin oud
👌💃🏻
Turaranta ya takurawa rayuwar shi, hajajju ta kauda fuska tace uhm “ tau banda ma neman bala’I irin na ibrahin mi yayi zafi daga wannan dan abun sai ya danna maka auran yarinya “tayi kasa da murya tace tau wai da kake ta wani daura fuska kamar wani afta mi zakayi aure ne an riga an cuce ka an Baka ma yarinya ,ga yarinya kuma ba lafiyaya ba , Allah na tuba ita kuma asiya ta dauka da zafi tasaka gaba da masifa kamar wani dan iska shidai malik bai ce komai ba domin bai ma da abun cewa , hajajju tace ohh dan ka daukeni zararra ina ta magana kayi shiru kana ta bina da ido kamar wata tababba Still malik was quite da tasan yanda yakeji da bata dameshi da wannan surutun nata ba marar kan gado ba da tasan yarda yake ji datayi shiru, har suka sauka gida hajajju na mashi masifa wai tana magana yayi mata shiru, suka sukayi abby ya biya masu keken kudinsu ko gida bai shiga ba ya wuce masallaci ba lokacin sallarh bane amma yana bukatar dayaje ko yasamu nutsuwa ‘ko kallon shi ummi batayi batace ya wuce ya kai aydarh dakinta aysha da su halime kallon ikon Allah kawai suke sun rasa abunda ke faruwa Yarinyar da suka zo dazo da hajajju ce tau ya akayi yayansu ya dauke ta miye hadani su da ita dazo ta shigo da kafanta yanzu kuma an kawo ta? Basu san wanda zasu tambaya ba hakan ya sa suka zubawa ikon Allah ido , ummi da still idonta ke jawur ta kalli aysha tace daura man ruwan zafi yanzu ta sa kai tashiga dakin kan gado ya kwantar da aydarh har yanzu kuma bata bude ido ba! Ummi ta cire hijabinta ta linke ajiyar zuciya ta sauke har yanzu bata gama dawowa daga shock din da ta shiga ba abu ne wanda ya faru tamkar a flim lalle Allah abun tsoro ne shike juya alamari a duk yarda ya so ,ahankali taje kusa