Author : Nana Maryama Category : Romantic Hausa Novels
tuba bamai ma wanka ba mai wanke maka kashi ko fitsari dawaniyya kuma nami banda neman alkaba’I ? Hajajju tace ai yaran yanzu duhun kai dai yayi musu yawa Allah natuba anzama daya duk fameli ne mu “ummi dai nakan one sitter sai dan murmushi take “ hajajju ta waiwayo takalli ummi tace sun gaisa da habib? Ummi tace aaa lokacin dasuka shiga baya nan amma anjima in sha Allah zamu shiga sai su gaisa hajajju tamike tace bara naje na samesa yanzu kinsan shi Batsari bane dashi sam hakanan yake zuwa kasan turan badai kan gado garesa ba daga nan can fita zamuyi da ramda ummi tace tau Allah yatsare yabada sa’a baba kulu tace sai kin dawo “inna ma tace adawo lafiya “hajajju ta amsa su tana maida mayafinta ta dau jikkarta tafice , Dr ibrahim yace tau ko kayi mata magana ko kasaka matarka tayi mata tunda aunt dinta ce?malik yace zai fi sauki zanyi magana da ita sai tafada mata “dr ibrahim yayi murmushi yace Allah ya tabbatar da alkhairi daman dr usama deserves a lot sai inda karfinmu yakare in sha Allah “ malik yayi murmushi yace in sha Allah dr ibrahim yace amma magana tsaftan nan faa??malik yashafa kansa yace itama don baka ganta bane dr ibrahim yace ko ka manta dazu munje mun gaishe su malik yace ohh haka “so in that case kaga halinsu kusan daya “dr ibrahim ya jinjina kai “can yayi dariya yace hala mantawa kayi baka fada mun kunada kaka irin hajiya inna ba? Malik da duk daurewa yake suke firan yayi murmushi gefen baki yace ai wannan tafi inna case Allah yashirya su kawai yanzu haka wurin mijin wata dr take ta zarya wai sai tamayar da auran kaji fa wata rigima dr ibrahim yace wata sabuwa relatives dinku ne malik yabude hannu yace ina fa kawai ta dauki ummi matsayin her elder sister a boarding school su ummi na sss3 ita kuma suna jss 1 shine fa kawai relationship din dr ibrahim yace aikin lada zatayi aie Allah yabada sa’a malik yace Ameen dr ibrahim yace tun safe banga abby ba malik yace amm yaje campany kaman interview sabin ma’aikata zaiyi babu enough time kwara campany yafara functioning dawuri dr ibrahim yace ubangiji Allah yabada saa Allah yataimaka kai kuma Allah yasaka maka da alkhairi malik yace mudai baki daya Ameen summa
Ameen “ suna nan zaune kan mota a kofan gidan sai ga maryam halime aysha da hibba sai dr hafsa looking very good “ dr ibrahim ne yace sai ina haka bayan duk sun gaishe su maryam ce sarkin magana tayi saurin cewa gidansu auntie zamu shiga dr ibrahim yace Allah yatsare adawo lapia suk ace Ameen har sunyi gaba malik yakwallawa aysha kira tadawo yace kice ta kunna
wayan right now aysha tace ohk.
Rufaidarh tace kuje sama yanzu kam takoma can din nayi tunanin ma mijin ne yashigo dr hafsat ace no waje muka barosu auntie rufaidarh tace Allah sarki saman suka wuce rufaidarh ta kwallawa daya daga cikin maids din kitchen kira tashirya musu wani abu takai musu can saman dakin aydarh ‘knocking maryam tayi ‘kasancewan rufe dakin tayi bata son magana yau dinnan sam she is not in the mood ga maganin da auntie rufaidarh ke bata yana sata jin duk wani kala Wallahi ‘ahankali tace who’s here?maryam tace mune auntie ‘gently tasauko daga kan gado tadauki veil din white abayan dake jikinta ‘dan fadawan datayi ma ta ciko gawani irin kamshin da take fitarwa yau hadda powder tasaka da pink lips ga idon yasha kajal asalin dan sudan ‘tayi parking gashinta can keya tayafa veil din akayi bude kofan akaiyi maryam ce a gaba tayi murmushi tace sorry auntie bacci ma kikeyi ba?aydarh ta girgiza kai tace ah’ah zaune nake ma har nayi tunanin babu wanda zai shigo ma yau “hibba tace dole mu zo kam aydarh tayi dan murmushi tace kushigo auntie duk shigowa sukayi ta tura kofan dakin ta dawo ciki “dr hafsa da halime sai maryam suka zauna kan sofa aysha da hibba suka zauna a gadon aydarh ma tazauna can, tace auntie hafsa ina wuni ya gajiyan hanya?dr hafsat ace Alhamdulilah mrs malik ya jikinki aydarh tayi kasa da kai tace dasauki alhamdulilah kafin ta gaishe da hibba itama tana tambayarta ya jikinta “ duk suka gaisa dasu aysha kafin tamike tace bara nakawo ruwa dr hafsa tace ai da kin zauna ma kin barshi aydarh tace noo bara nasa akawo maryam tamike dasauri tace muje natayaki auntie aydarh tace thank you yah mariam tafada tana murmushi,fita sukayi tare suna daidai sauka stairs sai ga maids su biyu dauke da tray ahannu lemo da ruwa ne sai snacks akai aydarh tasa hannu tana karban tray daya maryam ma ta dauki dayan suka juya “dr hafsa dake kallon aydarh tace ni har kullun sai nakasa gane wani kalan perfume kike using kaman kece kawai mai kalan this scent a duniya gaskiya idan bake ba mijinki gaskia dai hibba tace Wallahi kuwa auntie hafsa nima dai haka nace ai dawani kalan speed aysha tace nabani yayah fa yabani sako amma kinga namanta ban fada bak i rufa mun asiri ki kunna wayanki yace yanzu nan please “Aydarh tayi kasa dakai tace kunne yake aie Hibba tace maybe network ne shiyasa yakira yaji a gaishe maryam tace bara nafita sai nafada masa,dr hafsa tace ah’ah bara nakira sa idan magana ne basai yashigo cikin gidan ba tafita suyi? Aydarh dai batace komai ba,halime tamike tace tau Allah yakara sauki auntie daman muyi sallama gobe zamu wuce nida maryam school “Aydarh tawara ido tace lah daman baa nan kuke schooling ba?maryam tayi sauri tace noo bamu fara ba daman sai yanzu yayah dawowan nan naku yanema manah base university a can abuja aydarh tayi murmushi tace masha Allah freshers wannan dai ba sallama bane kamata yayi dasafe sai ku shigo muyi proper sallama,maryam tayi wani kala da fuska tana dariya tace wai fa flight zamu bi “Wallahi yanda tayi magana dole tabaka dariya aikam kowa sai dayayi dariya a dakin aysha dai cannot take off her eyes daga kallon matar yayan nasu Allahumma bareek kowa nayi mata kyau shi kansa yanda take dariya abun kallo ne she is damn cute kaiiii “ halime tace ke kam dai baki ji
dadi ba gaskia sai wani faman fadi kike zaki hau jirgi Dallah can sabon shiga cike da tsiwa maryam ta turo baki tace naji din ina ruwanki ina dazu hadda kiran salis dawani fada masa zaki tafi base uni ko tsaban kauyanci yaron da bama auranki zaiyi ba miye na ki dinga magana dashi halime tamike har kwalla yacika mata ido tsaban haushi daman sauri hayaka gareta tace Allah yau sai fadan mun dalilin dayasa kike shiga abunda babu ruwanki “ita dai aydarh dariya suke bata basa gajiya da rigima kaman wasu tom and jerry “dr hafsa dake faman dariya tace yanzu dai kuyi hakuri acan hostel din ma haka zaku dinga kalan this silly rigima haba yanzu fa kun zama yan gayun abuja you are not longer halime and maryam you are now haliii and arya “dariya maryam tayi tace nice arya din right auntie?aydarh tace erh manah ai naki sunan yafi na yaya halime “halime tabata fuska tace Wallahi duk kaman gaban yayah kuka fadi haka Saboda kalan son dayake ma suna nan yace first born dinku ma zai saka mawa aydarh tayi dariya kawai tace noo wasa yake sunan yah mariam zamu saka “hibba tace rabu dasu halii ni zanyi miki wannan karan ma kinga ita ko cikin ma babu har anfara miki nuna bambamci ni kinga gashi ke keda dahir “halime tayi wani cute smile tazo taba hibba wani side hug tana kissing cheeks dinta tace thank you auntie hibba Allah yarabaki da abunda kika dauka lafiya in sha Allah yayah ibrahim bayanke babu macen dazai kara gani hibba tayi dariya tace Ameen Ameen halii,dr hafsa dai takasa daina murmushi duk abun nan aysha batace komai ba dariya kawai tayi tana girgiza kai “maryam tabata fuska tace wai dagaske auntie babu?aydarh tayi saurin sukunyan dakai batace komai ba don kunya take ji ma Wallahi “ aysha dataga abun nasu yayi yawa tace wai yanzu ba karasa shirya kayanku zakuyi ba? Maryam tace ehh addarh yanzu zamu tafi “ kafin tajuyo tace auntie dan Allah anjima zamu tafi tare dake? Aydarh tace ina? Maryam tace wai fa waya yayah zai siyan manah nida yah halime sai provision zamu yu “kinga dagani sai halime bata iya siyan komai bas hi kuma yayah baya son ana bata masa lokaci idan anje siyayya aydarh ta gyada kai maryam tayi murmushi tace mungode auntie aydarh tagyada “fita sukayi halime tace auntie mi zan fadawa yayan? Aydarh tayi shiru kafin tace akunne wayan yake “halime tace tau “aysha tamike tace bara naje dakaina auntie Allah yasa kar yace laifi na ne yaran can basu da saitin kirki akansu “dasauri aydarh tace ah’ah addarh aysharh babu abunda zai fada zanyi masa message daman abu zan basa a cikin box dina idan yashigo zai karba zanfada masa ba laifinki bane aysha tadawo ta zauna tace yauwa tau shknn ma “dr hafsa dake kallon aydarh fuska bawasa tace ki kirasa yanzu manah kinsa zai iya fushin fa kindai san halin yan kayanki gently ta dauki wayan tamike tanufi hanyar closeted din dake cikin dakin wanda babba ne sosai har tashige kafin Hibba ta girgiza kai tana murmushi tace kullun kaman yar yarinya “dr hafsa tace ai mijin ma har yasaba ahaka kiga ya shagala yana kallonta aysha tayi murmushi tace wai auntie zuwan yayah can garinku naga yarage daure fuska da fada ma baki daya dr hafsa tayi murmushi tace matarsa zaku gode mawa “daya fara zata fashe masa da kuka shiyasa yanzu duk yazama haka “ta gyara muku shi sosai tafada tana dariya “hibba tace ke kam aysha ai dole kanwar taki ce duk ta saita muku shi ai shagwaba dayake sha kawai ya isa aysha tayi murmushi tace naga alama kam “tana shiga closeted din kaman kar tayi dialing sai kuma tadaure tayi daman numbersa ne asa wayan ma babu wani number bata masa kowani lokaci yasamu sim din Nigeria yasaka mata ba kawai dai sai ganin message tayi ranar a asibiti yatura mata “ yana fara ringing yakalli wayan ganin sunanta
ne saving din dayayi mata ya rubuta “wudd “da imoji mai kaman zakayi kuka sai red heart da rings har uku “har ya katse bai dauka ba tawani tura baki tana bude hannu alaman shi yasani “dialing yayi yakirata maybe saboda isa yayi hakan har takusa katsewa kafin tadaga kai kunne tayi shiru shima shirun yayi bakajin komai face sautin numfashin su daga ita har shin shine yayi breaking silence din yace duk ranan dana sake tuna miki ki gaisheni sai na karya ki tau “ murya can kasa tace kai ma ai baka gaishe ni din “dayake snake ears garesa har yaji ta “yace mikaka ce tace ina wuni murmushi yayi yana shafa kansa, kafin yace ita aysha datazo batace nace ki kunna wayanki ba tace tace faa kuma ni Allah kune yake yace so am lying kenan danace a kashe yake tace ah’ah fa ni ai bakaji nafada ba yace get ready anjima zamu je wajan abba abby yafada mun yace muje nidake Wallahi sai da gabanta yafadi daram tayi shiru “ kafin ahankali tace “to”yace and bayan nan zamu fita da maryam da halime gobe flight dinsu zai tashi zuwa abuja tace Allah yakaimu lapia “ yace Ameen kince abinci?tagirgiza masa kai yace na’am?tace ah’ah yace why tace nasa oat “ yace ohk bara nakarbo miki tuwo wajan ummi naga hadda shi sukayi yau tace na koshi “yace inna da ummi da oum ma sun fita aie “ tace yaushe?yace nima dai bansani ba, tace auntie rufaidarh na nan ita yace ehen cuddle bug zamuyi magana ma kan auntie rufaidarh tace Alright yakashe wayan “ aysha tace auntie hafsa kenan am 28 yanzu nan said ai mu ta addua duk wanda yazo mostly su ba auran ke kawo su ba,dr hafsa tace amma kullun gani aka mun ki aure hibba tace Wallahi fa mutanan ne sai ahankula yanzu sun mata da aure lokaci ne ni fa a can kinga am 24 fa kuma kowa yasan anyi alkawarin aurena da dr amma karku so ku ga yarda ake cewa naki aure dr hafsa tace wanda ke 24 ma kenan ina ga mu masu 34 fa aysha tace Wallahi abun ni baya damuna sam daga ummi har abby babu mai cemun naki aure “hibba tace ai su da illimin su kuma fa ma kuji wani ikon Allah mutun baya daukan dawaniyyanka da komai parents dinka kema amma sun sa ido kaki aure su parents din naka basu takura maka bas ai su “ dr hafsat ace Wallahi fa hibba kudai ku godewa Allah Alhamdulilah “Aydarh tafito daga closeted din kamshinta yarigata karasowa duk da tabar shi ma a dakin suna jinsa duk bata dakin “tadawo ta zauna inda ta tashi dr hafsa ta cigaba dacewa both you and aydarh are very lucky Wallahi kinga ke you are just 24 kinyi aure hadda ciki kuma kinsamu miji nagari miji mai sonki na gogan jigida “Hibba tace hakane auntie Alhamdulilah “ kuma in sha Allah Allah zai kawo nagari mai albarka,dr hafsa tace in sha Allah “ Aydarh kumaa 22 take tayi auran living very peaceful da mijinta “ Aydarh tayi kasa da kai tace Auntie muje kasa sai mu ci abinci tana cikin fadin haka akayi knocking dakin “ aysha ta mike tabude malik ne tsaye jikinn kofan yasaka white cotton yard an masa kaftan yayi kyau bana wasa ba hadda hula yasaka hannunsa rike da dan karamin warmer mai kyau tace sannu yayah ya gyada mata kai yace kira muni ta Tace ohk”juyawa tayi dakin tarufe kofan tace yayah ne auntie aydarh tayi shiru kafin tamike dr hafsa tayi murmushi tace love birds “yakasa hakuri kenan “hibba tace ke kam auntie kina bata kunya, aydarh dai tayi kasa dakai ta fice daga dakin “tana budewa yana nan tsaye ta kallesa kadan shikam ya dinga kallonta kaman zai hadeta “yace waya ce ki saka kalan kayana murmushi tayi bata masan tayi ba murya can kasa tace kai kam ka cika rigima ni fa banganka ba duk yau taya ma nasan kayanka na yau “yace heart dinki tabaki labarin kalan kayana shine kema zaki sa tace ai na rigaka saka kayan yanzu kayi wanka ma ai nasani hannu yasa yana jawota jikinsa yace kinsan nib a kazami bane na
yarda dai yanzu nasaka kayan shknn aydarh ta kyalkyale da dariya Wallahi yanda yake kallonta kaman zai hadeta white clean teeth dinta sun fito ga hakuri gwal din dayakara musu kyau “tace shknn nayi maka wayau ,dariya yayi smile yace kinyi kyau kuma tayi wani kala da ido batace komai ba yamika mata warmer takarba ahankali tace miye?yace tuwon ne na kawo miki and promised me ke kawai zaki ci kwara daya mane nakawo su duk sun ci aydarh tace “to “har zata juya yakira sunanta “tajuyo ahankali yace idan Abba yace miye ra’ayinki zaki ce nasake ki?tambayan tazo mata suddenly tayi kasa da ido yace darl kinyi shiru!tace sai anjima tashige dakin tabarsa nan tsaye yakai 10mins jikin karfen staircase din kafin yajuya yasauka yabar gidan daki yazauna shi kadai ko hulan bai cire bahaka ya kwanta a gadon zuciyarsa fal tunanin abunda zai faru yau din yau ne zai san ahalin dayake “ .DR hafsa tace shine yakawo miki tuwon nan aydarh ta gyada kai tana dan murmushi Hibba tace aie gani yayi ita bataci ba aysha tace shi fa yazuba da kansa ina ganin lokacin dayasa abincin warmer aydarh batace komai ba tamike tafita daga dakin a dining tazauna ta tass ta cinye tuwon she cannot stop smiling yanda ta tuno yanda yayi da fuska wurin fadin shi ba kazami bane
.
Dakin takoma dr hafsa dake kokarin shimfida abun salla tace har yatafi?aydarh takara sa ta zauna murya can kasa tace tun dazu yatafi fa auntie,dr hafsa tace nayi tunanin tare kuka ci tuwon aydarh dai batace komai sai murmushi kawai datayi aysha tamike tace bara na wuce gida su ummi sun raka oum gaisuwa gidan barrister sham yamma nayi nasan su halime bawai daura girki zasuyi ban asan halinsu sarai hibba tace nima bara na biki nasan mijina na nema na “ Aydarh tayi dariya tace auntie hibba mai miji “bazaki jira auntie ba?hibba ta girgiza kai tace bara dai naje wajansa first “itama auntie hafsa din fada zatayi mun wuni daya bama tare aydarh tace gaskia fa “Agaishe sa tom “Hibba tace zaiji in sha Allah har kofan parlor taraka su, kafin tajuyo anan suka hadu da rufaidarh zaune cikin parlor tasaka wani ubansu Turkish abaya tayi kyau bana wasa ba irin hadaddan kyau din nan “ Aydarh takarasa kusa da ita ‘tace auntie rufaidarh ta waiwayo tana kallon aydarh from head to toe ganin gyara na aiki ta isa isa ta mayar da jikinta fatan nan daman baa magana tabarakallah “rufaidarh tace wai baby mantawa kike kinada aure ehh? Aydarh tawara ido kafin tayi kasa dakai tana wasa da yatsun hannunta “ rufaidarh tacigaba dacewa perfume dinki har yawuce misali baki san kinada natural skin aroma ba?kinfa sani no need of spraying too much perfume kuma kalan wannan designer ma karasa inda ma kamshin yake zuwa duk kala daya ma muke amfani nidake da uktiee amma naki yafi nakowa “shi Abdoolmalik din baya fadane? Tau billahi shiyasa ba daya tashi kusantarki baije miki dasauki ba yakusa kashe sa “wannan irin fizgar hankali dakikeyi, aydarh dai tayi shiru rufaidarh tace zauna miya faru?aydarh tazauna kusa da ita “tace auntie wai cewa yayi abba na neman mu?rufaidarh tace kaii haba yaushe tace yace mun zai shigo kawai maybe yanzu ko anjima kadan ba?rufaidarh tace tau idan aka tambaye ki decision dinki mi zaki fada?aydarh tayi shiru tana kwantar da kanta shoulder din rufaidarh muryanta