Author : Nana Maryama Category : Romantic Hausa Novels
da ido gabanta na faduwa domin ba karamin wahala take bah idan tana cramps har allura ake mata sometimes har dayan ciwon nata yake tasowa watau asthma hakanan taji tana so daga curtains din window dinta Allahumma bareek yanayin jikin su aydarh shi ake kira da package shape gyara zip din gaban abayar nata tayi boobs dinta dake cure waje guda suka fitar wani shape mai kyau da daukar hankali fatar wajan tasamu Hutu da tsabata game da kulawa ciza lips dinta take tana takawa ahankali zuwa yanzu ta fahimce ciwon marar ne take komawa tayi ta kwanta kan gado.
Kasancewar garin da alamar hadari yasa ummi fitowa tashiga dakin su aysher zaune suke halime ce ke gyarawa maryam (autarh) kallabar da aysha tayi mata take complain din yayi zafi har aysha ta saba da complain dinsu na zafin hannu da suke cewa tana dashi tun tana biye musu suyi chapter har takoma idan sunyi saidai tayi shiru tana kallonsu gyaran murya ummi tace tau fadan da bai karewar ne kuka dasa koh?takarasa maganar alamar tana tambaya dasauri maryam tace wallahi ummi adda zafin hannunta kullun karuwa yakeyi halimai ta turo baki tace ummi adda pah da gangan takeyi saboda ace ta daina yi kitso daman ai bataso aysha tace ummi ni duk banda lokacin wannan abun nasu abinci zaa daura ne? Eh ummi ta amsa mata tare da bata umarnin abunda zaa daura din ko da ta fito saida tafara shiga dakin malik ta mashi ya jiki tareda tambayar shi ko akwai abunda yake da bukata maida duban shi yayi gareta cikin wannan muryar tashi kamar mai magana dan dole yace mata tea tasan daga wannan babu saura abunda zai ce mata kasa tayi da murya tace wai yayah itama auntie tamu haka kake magana da ita?mugun kallo ya watsa mata da gudu ta fito daga dakin saboda tasan sauran ma ko bayan fitar aysha maganar tace tadawo mashi akai kalmar ‘ auntie’ tana nufin budurwa murmushi yayi yana shafa salkakiyar suman kanshi bakaa sol shi kam bai ga ranar bah ma kan murhun gawaye ta daura mashi ruwan zafin 5mins tagama ta hada mashi ta mika mashi daki idonshi na rufe amma ba bacci yake bah ta ajiye ta fita domin cigaba da aikin girkinsu, oum ta maida dubanta ga rufaidarh ganin cikin plan dinsu wani yazo dasauki domin kau harda gudun zuwa wajan hajajju garesu domin itace zata nuna masu kofar cikan burinsu madaidaicin gidan dake shafe da cement ko ina tsab a gyare gida tsofi ne babu wani hayaniya sam mama Rabi wace matsayin kaka take ga abba ita daya ta rage musu shi da dan uwan nashi kaf dunia amma rashin son zumunci irin na abba dakuma ware
kanshi dayayi tun farko daga lamarin familyn shi tun bayan rasuwar mahaifinsu mahaifiyarsu ta jima da rasu tun suna yara
Wanene dan uwan abba?
Wane irin plan oum da rufaidarh garesu wanda suke ganin zasu jifi tsuntsu biyu da Dutsi daya?
Miya kawo su wajan kanwar kakarsu abba wacce ke matsayin kakarsu?
Salma tace ankusa maganin aydarh wani irin magani?
Mi yajawo kamar da malik keyi da abba?
Tun suna yara cikin tattare kwarin gwiwa da karfin zuciya oum ta fara ma baaba kulu magana tunda ta fara magana hajajju ke kallon oum da baaba kulu da rufaidarh baki daya kallonsu take kamar wasu zararru tana mitsi mitsi da ido tana jiran taji iyakar idan oum zata tsaya cikin sanyi murya game da raunin zuciya da sarewa oum ke magana tunda tafara baaba kulu ke kallonta cikin tausaya da tsabar kauna baaba har yaushe zamu bar cigaban wannan gaba da kiyayya dake tsakanin yan uwa biyu har yaushe zan cigaba da jure ganin ASEEYARH a wannan yanayin baaba fashewa tayi da kuka mai taba rai rufaidarh tacigaba da magana baaba maganar damuka zo ita itace mafita maganar da muka zo ita tace makama itace wukar dazata yanke duk wata damuwa da kowanin muke ciki! cikin gamsuwa da fatan cikar buri baaba tace rufaidarh kuyi saurin fadin abunda ke tafe daku kuyi saurin yin man bayani cikin gagawa kuyi saurin bani haske in sha Allah nayi alkawarin goyan bayan ku,bayanin duk plan dinsu sukayi ma baaba shiru yabiyo bayan rufaidarh takai ayar maganar ta ajiyar zuciya baaba tasauke domin ta yarda ta amince ta gamsu da duk bayanin da rufaidarh tayi mata zata fara magana kenan hajajju ta mike tamkar wacce kunama ta harba salati tagama tamkar wacce aka aiko ma sakon mumunan accident tace hala oum dai kun chanza addini daman ance waennan rubabbun larabawan sudan din ba hankali gareku ba Jama’a kuji wata maganar dauri tayi kasa da murya tace amma dai gaskia kulu baku da imani keda waennan masu zubin abzinawan nijer din haka kawai ku bankawa bayin Allah sharri saboda baku kaunar Allah wai wani saboda a gyara zumunci ita kuma adar ta gyara halinta tau sam babu ni a wannan bakin zunubi wannan sharrin ko a fim sai haka fashewa da kuka tayi tamkar wata tababba cikin daka tsawa da daga murya baaba kulu tace ke wai hajajju mahaukaciyar ina ce ina nan naga basu sa dake ba cikin wannan lamarin kuma saboda sun ga cikin mu guda dake yasa basu ce ke bamu wuri bah,haba dan Allah ki dinga abu kamar wata zararra ina amfanin wannan abunda kikayi haka tau ba ruwanki idan bazaki goye bayan wannan baiwar Allan ba a wannan sadaukarwa da tsoron Allah nata ba ba’a zage ta ba share hawaye hajajju tayi tareda fesar da majina ta mike tsaye tace tau gaskia kun zama abun tsoro tun zuwana yola nake ganin jafa’i kala kala babu irin mugun abun dake ban gani ba shiru sukayi babu wanda batayi mamaki bah domin a tunaninsu itace mutun ta farko dazata amince ta nuna yardar akan lamari amma har cikin rai rufaidarh tasan hajajju daga baya zata chanza magana ta amince domin idan da sabo kowa yasaba da wannan halin nata sosai baaba kulu ke jinjinawa oum wata irin kauna da soyyayarta na sake karuwa har cikin ranta addua tayi musu
sosai da fatan alkhairi dakuma fatan cikar burinsu batare da wata matsala bah hajajju kau daki tashiga tayi zaman dirshan ta cigaba da hada kayanta a ghanan ta yau ban kwana yola gaskia duk idan dare yayi man yau a kano zan kwana ah ni binta ina zan iya zama cikin masu zuciyar kafurai da mugun abu ina zaman zamana wannan tsohuwar ta taso ni wai nazo batada lapia bancin kaddara da mi zai ma kawoni wannan gida nata kamar zuciyar talaka gida ko farin glop babu sai ja kamar dai bamm,Har hajajju tagama hada kayanta su oum na zaune suna cigaba da tautaunawa da baaba kulu fitowa hajajju tayi da katon ghanan ta tashare hawaye ta nemi kujera ta zauna ta mike kafa tayi kasa da murya kamar ba ita tagama kuka yanzu ba tace a gaskia rufida’u ban taba sanin kunada hankali ba irin yau idan bahaka har miya hadaki dasu dazakiyi musu irin wannan halaccin tau ko ni nadake ciki guda da kakarsu habibun bazan iya wannan abunda kikayi bah gaskia kinyi kokari Allah yayi muku albarka ahankali kuma tace amma shi mai zubin yan fim din indiyan ya amince itakuma diyar wurin naki hwa?murmushi oum tayi daman tasan daga karshe hajajju zata sako tace in sha Allah hajajju komai zai zo manah cikin sauki tunda gaki murmushi hajajju tayi tace aikam nasan ta kan tsiya daman tun sauka ta jiya na kira shi audul din nace mashi gani a yola yace zai zo tau nasan wannan bahillatanar uwar tashi zata hana shi zuwa shikuma rubabben ibrahim din daman bana san ran zaizo idan nake saura yaran dama ba fita suke amma ki bari ya shigo sai nasa kulu ta kiraki kituro man ita adar shima habibun ki tada mashi hankali ki nuna wani jafa’i ke shirin faruwa a najeriyar yayi gaggawar dawowa yauwa tunda tafara magana baaba kulu yake murmushi domin tasan halin yar uwarta tsaf saidai ta shirya yarda komai zai tafi daidai daman tasan sai ta amince da zancan daman kowa yasan halinta shiyasa tayi mata wannan gorin
.
Karar kiran wayar yasake shigowa a wayar tashi a karo na ba adadi yasan mai kiran kuma ko daya daga bai san abunda zai fada ba bai shirya daukar darun mai kiran ba shiyasa bai daga ba so yake kawai ya cika alkawari yaje dasafe Idan Allah ya kaimu ummi na lura dashi saboda tasan da maganar sai tayi murmushi tace miyasa ba zaka daga ba? Shafa sumar kanshi yace so nake kawai naje zuwa dasafe in sha Allah,Allah yakaimu tace babu wanda yasake magana acikinsu har kowa yagama cin nasa abinci bayan sun kammala halime ta kwashe plates din tayi kitchen dasu shirin tafiya makarantar dare sukayi amma sai malik din yace su bari saboda har yanzu garin akwai alamun hadari ya yayi musu kari a gida godia sukayi mashi aysha har cikin ranta taji dadi saboda sam bata cika son zuwa makarantar bah saboda malamin su dayafiye takura mata da sunan soyayya har ummi takawo ma zancan tashare ta tareda fadin Allah yakyauta kawai babu abunda tace wajan takwas daidai abby yashigo gidan hannunshi dauke da bakar leda wanda fura ce a ciki da fresh nono mai kyau irin na fulanin adamawa gaishe sa sukayi tareda masa sannun da dawowa tambayar su yayi abunda yahana su zuwa karatun dare maryam tagaya masa bace komai sai shiga daki dayayi gidan a tsabtace yake sai tashin kamshin tsintsiyar tsinke yake abinci shi ummi tashigo mashi dashi tareda wajan dazata dama mashi furar
Zarah bansan abunda yasa kika takurani cewa gobe sai nadawo Nigeria ba ajiyar zuciya oum tasauke tace amma kasan abbyn baby ba karamin abu bane zai sa nace kadawo nigeria zuwa gobe wani tarihi ne na kaddara wani salo ne da tashin zaune tsaye gaskia ce dakuma asalin
rayuwar farko zai maimaita kanshi duk bai fahimce kalaman ta ba saidai gaban shi yayi mumunar bugawa har sai da glass cup din dake hannunshi yayi mumunar fashewa kokarin daidai ta kanshi yayi sannan yace zan biyo private jet around 10:00am in sha Allah munyi landing katse wayar yayi batare da ya jira amsawar oum ba sauke wayar tayi daga kunnata ta zubawa wayar ido tamkar mai son gano karafan daakayi amfani dasu wajan kera wayar wasu irin hawaye suka sauko mata bazata iya fasallata yanayin datake ciki ba farin ciki ko bakin ciki sam ta kasa fahimta bad room tanufa tasakar ma kanta shower ko zata samu saukin abunda take ji a ranta shirya tayi cikin v gown tayafa mayafin gown dinta inner cap ta rufe gashin kanta daya sha gyara da ita tayi matukar kyau duk da yanayin da take ciki yasa ta dan fada sai tayi matukar kyau yarintarta tafito kamar bata haifi aydarh bah dakin aydarh tawuce da sallama tashiga tasame ta tsaye jikin window wannan karon ta Chanza kaya tasaka soft gown baby pink tayi matukar karbar jikinta kanta babu dan kwalli amma ta daure shi tsaf da ribbon kasan kai kallonta oum keyi ko kiftawa babu ganin irin kallon da oum keyi mata yasa tayi rau rau da ido ahankali cikin sanyin muryar nan nata tace oum ina wuni ashe fita kukayi oum banda lapia pah takarasa cikin dan karyar da wuya duk tunanin laifi tayiwa oum dayasa ta tsayawa tana kallonta haka itama oum babu yabo babu fallasa tace
Mafarin faruwar komai kaddara zane ne shikuma tarihi ajiya ne babu gaskiar dake boyuwa duk yanda aka so rufeta shin DA SO KAMANE ba iyakar soyayya zata bayanu a labarin bah faruwa da taushan komai zai fara gudana Allah shine masanin daidai hikima da dabara na iya aiki ne kawai akan abunda Allah yasa zai dawo daidai zai dawo hanya yah rabbi kasa mu ci dukkan kaddarorin dake shimfida a littafin kaddarar mu
Tace mike damunki ?kasa tayi da murya tace cramps ne ta fada tana rau rau da ido kallonta oum keyi ko kiftawa babu tace tun yaushe da yamma nafara ji kuma drugs din duk sun kare sannu oum tayi fita har cikin ranta taji wannan ma wata dama ce duba da yarda cramps din ke wujujuga aydarh numfashi ta fesar tayi hanyar dakin rufaidarh domin sanar da ita halin da aydarh ke cike kasancewar daman duk sanda aydarh ke cramps rufaidarh ce ke dawainiya da ita duk sanda take cramps saboda acewar oum bazata iya da rakin aydarh bah tsaye tasamu rufaidarh tana jera kaya cikin wardrobe dinta kamar ko ina na gidan shima dakin rufaidarh hakan ya kasancewar mai matukar kyau komai a tsare yake daidai da daidai murmushi tayi tace nikam uktiee ko dan gobe abban aydarh zai dawo ne naga kin wani chanza kamar wata yar shekara sha takwas miye sirrin takarasa cikin sigar tsokana tayi sosai oum tayi tace kinga ki koh uktiee miye wani sirri bayan kinsan komai nikam babu wani sirri kuma ma ai wannan ba irin normal zuwa bane zuwa ne mai dalili hakane rufaidarh tafada agajarce sannan tace akwai abunda kike da bukata ne uktiee no babu yarinyar ki ce ba laifi nazo nagaya maki subhanallah mike damunta cramps?gyada kai oum tayi batareda tayi magana murmushi rufaidarh tayi tace Allah maji rokon bawa Allah mai yarda yaso a duk sannda yaga dama kinga hanyoyin nasara na ta zuwa ta ko ina ta hanyar da bamu zato bah koh zama oum tayi kan Italian bed din dakin tace uktiee nadai zullumi ko fargabar wayewar gobe zuciyata ta dake da duk abunda zai faru goben nayi i’mani kuma nayarda da ubangiji in sha Allah komai zai zo yanda muka tsara komai zai zo cikin sauki da yarda Allah ya maganar doctor
ashraff salman tayi magana dashi ne eh uktiee salma tace ta tsara duk yarda abun zai kasance kuma bata samo matsala dashi ba wajan fahimtar yanayi domin shi kanshi shaida ne Alhamdulilah oum tace tareda kwanciya sosai kan gadon tana rufe idonta wani irin sanyi ke ratsa dukkan sassan jikinta dukkan wata kafa ta veins dinta sanyi ke ratsawa jini take jikin na kara yawan gudu a cikin veins din so take ta samu bacci sosai kallonta rufaidarh tacigaba dayi tana tsananin tausan yar uwarta ta hakika ba kowane dan adam bane zai iya aikata abunda oum ba kowane mai rai bane zai iya wannan sadaukarwar ba uktiee bara naje wajan baby kiyi kokari ki samu bacci sosai anan din daidaita gudun Ac tayi tareda sakin duk curtains din dakin kofa taja mata ta fita ko da ta shiga dakin aydarh kwance tasame ta idonta rufe amma tasan ba bacci take ba domin a wannan halin allura kawai ke saka aydarh bacci ahakan ma yanzu da sauki sosai domin kaf Europe countries babu wanda abba bai zagaye ba da aydarh ba saboda case din nan duk da idan asthma ta taso ba karamin wahala take sha ba amma ciwon marar yafi dagawa kowa hankali domin duk rashin tausan ka dole ka ji tausayin aydarh tunda rufaidarh ta zuba mata ido bata dauke ba ji tayi kamar ana kallonta ahankali ta bude ido,idonta dayayi laushi Sosai ba karamin kyau tayi ba duk da tadan fada a wunin hakan sai ya taimaka Sosai wajan fito da asalin zatin fuskar tata kokarin tashi tayi rufaidarh tace no dear kuma ki kwanta no need kamar jira take tafashe da wani shagwababan kuka tamkar wacce aka do’ka ahankali rufaidarh ta taka gaban gadon zaune ta mikar da ita cikin sigar lallashi tace sorry cutie pie maran ne gyada kai tayi ta rike hannun rufaidarh tace second ma gabana faduwa ban san miyasa ba ina jin tsoro I didn’t to be alone please stay Sosai rufaidarh ke jin tausan rungume tayi a jikinta ta cigaba da sauke ajiyar zuciya samun kanta tayi da tambayar zuciya shin ko dai aydarh taji a jikinta akwai alamarin dake shirin faruwa da ita?bata da amsar tambayar tata hakan yasa ta cigaba da tofawa aydarh addua tana shafa bayanta kusan 10mins suna haka sannan rufaidarh tasauka tahadu mata abinci a tray da bottle water marar sanyin ta shigo dakin dashi dakyar tasamu aydarh taci kadan ta turo ganin zatayi amai yasa rufaidarh barinta hakanan magani ta bada tareda gyara mata kwanciya ta rufe da duvet kallonta tacigaba dayi cike da tausayi da kuma kauna kusan 5mins ta bata tana kallon aydarh sannan ta fita tayi bangaran masu maids din gidan saboda akwai abunda take bukata.
Sosai suka ji dadin karin da malik din yayi musu kowa yagane Sosai duk wani kurakuran su sun gyara kuma alhamdulilah Allah yayi masu baiwar fahimta da kuma gane karatu hakan nada nasaba da tarbiyya mai kyau da kuma good background din karatu dasuka samu saida suka sake maida komai mahallinshi a gidan kafin suke shige daki su kwanta (yan uwa a kula dan adinga kauda komai kafin kwanciya bacci kama daga takalmi kwanuka dasauran su saboda mutanan boye dare shine time din hidimomin su kuma suna iya sakar ko wacce kalan cuta a jikin kayan amfanin mu)zaune suke shi da abby da ummi a dakin abby din murmushi abby yayi yace tau ka daure kaje manah tunda dai an zabe ka kamar tumun dare shima murmushi yayi kadan yace in sha Allah abby zanje ummi tace ahtau kafin kuma ka jawa kowa cikin saboda kasan halin yan kayanka Sosai sun dan bata lokaci suna fira sallama malik yayi musu yawuce daki ko daya shiga dakin sake fitowa yayi waje yayi alwalla domin yana san raya daran yana sallarh,sai wajan 2:30sannan ya kwanta
Gyara daurin kallabin ta tayi tareda matse biredin dake hannunta wanda yaji kwai Sosai ga roman kai dayaji kayan kamshi a gefe sannan tayi kasa da murya kamar mai tsoron wani yaji ta tace wai yaya hof kin fahimce duk yarda na shirya filan dina koma kallonta baaba kulu tayi tace na fahimta hajajju kuma na gamsu Allah yasa komai yatafi daidai Ameen tace sai ta cigaba dacewa wai kuma yaya babu son