Da So Kamane Complete Hausa Novel By Nana Maryama.docx

Author :  Nana Maryama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   83 / 111

246K to 249K   out of 332K words

hafsa tayi murmushi tace eyyerh sorry ahankali aydarh tace aunty duk kunci abinci? Dr hafsa tace no nan kawai mukayo aydarh tace lah ai da kun ci abinci first bara nasa a kawo tafada tana mikewa walking very slow irin na marar lafiya tayi hanyar kofan “daidai zai shigo zai bude yaji ana budewa yatsaya budewa tayi bata lura dashi ba aikam sukayi karo dasauri ta dafe goshinta tace ouch wayyo oum kamata yayi yajawo kofan a rikice yake shafa mata goshin “yace shshsh sorry baby girl Allah ban san kina nan ba trust me kinji ta balla mai harara tace shine bara kajira nabude ba kaji kuma alaman zan bude ba?yace tau yanzu dai ayi hakuri dan Allah “ ta marairaice fuska tace eyyerh sir kaga har su aunty ma sun gane am pregnant ‘malik yawara ido kaman irin gasken nan yace subhanallah yanzu yazaayi? Tace Wallahi nima dai ban sani ba “yace kinga karki damu itama matan ibrahim ba kinga tanada ciki ba?ita bata boyewa babu ruwanta tunda tasan is normal kawai dai ki daure ki dinga cin abinci idan kika samu karfi babu wanda zai gane ma kinada ciki ta gyada mai kai yace tau yanzu ke ina zakiji “tace abinci zan saka akawo musu basu ci ba “malik yace nima abincin nazo mu ci nan din “bara nashiga nace musu ummi tace nakira su “Aydarh tace kai sir miyasa yace babu komai ina zuwa tarike hannunsa tace nidai dan Allah ka kyalesu su ci abincin su anan yace sai fa sun tafi cuddle bug kedai tsaya anan “tayi raurau da ido zatayi masa kuka yayi murmushi kawai yashiga dakin sallama yayi suka amsa kafin fuska ba wasa yace hafsa ummi na kiranku “and anjima bana son bata lokaci zamu fita dr hafsa tace ohk yallabai “fita yayi ‘dr hafsa takallesu tace mu tashi

mu tafi mikewa sukayi duk suka fito suna nan corridor yana tsaye cikin karfen stairs aydarh na gefensa magana yake mata tana sauraron sa “dr hafsa tace Aydarh bara muje wajan ummi anjima mayi magana “Aydarh tace to auntie suna juyawa yakama hannunta suka shiga dakin yace anjima zasu tafi sai nasa driver yadauke su “tace miyasa bara mutafi tare dasu ba yace driver dai nace zai kai su tace Alright “ yace mi aka dafa yau?tace nikam ban sani ba ‘yace tau mi zaki ci ta girgiza kai tace ai bana jin yunwa yanzu anjima zan ci tace fadamun have you eating?yagirgiza kai yace aaaa tace zauna ina zuwa ‘ tafada tana mikewa “kasa tasauka ganin su oum basa nan sai uban souvenirs din da aka gama packaging “ta nufi hanyar kitchen din tana shiga maids din suka juyo suna gaishe ta ta amsa su ahankali kafin ta matsu tana bude warmers din fried rice ne sai pepper chicken da beef sauce kwata kwata aroma abinci baiyi mata ba “batace komai ba tafice daga kitchen din “duk suka bita da kallo upstairs tahau tashiga kitchen din sama maids daya ce a ciki tana diluting mayonnaise “ ahankali ta amsa gaisuwan datake mata kafin takarasa tabude warmer abinci abba “ white rice ce sai curry soup da salad “plate ta dauka tazuba rice din daidai yanda tasan yana ci kafin tasa soup din gefe sai salad spoon ta daura kafin ta dauki wani plate din ta kifa kai ta fita “yana zaune a wurin data bar sa wayanta a hannunsa ko mi yake gani a wayan oho “ karasawa tayi gefen gadon ta zauna tabude abinci kafin gently ta sa hannu ta karbi wayan ta daura mai plate din a laps tamike tayi takoma kan sofa ta zauna yadage gira Yace you “bazaki ci bane?ta girgiza kai tace zan ci anjima yace look wife dole fa sai kina cin abinci zaki samu karfi kuma kinga you are not only one now ‘you have to be cared karki je kuma wani ciwon yazo “let’s eat please duk bata so haka ta dawo kusa dashi yajuya abinci ahankali yakai mata a baki sosai abinci yamata dadi shima yaci ahaka yacigaba da feeding dinsu can tamike tace ta koshi ganin taci dayawa yasa shi barin ta fridge din corridor tanufa “ ta dauko masa bottle water da glass cup anan kan dining tadawo ruwan tabasa kafin yace where your drugs? Tanuna masa bedside drawer ledan drugs din yajawo yabude ya ciciro yabata tana daure fuska dai ahaka takarba “yace good batayi niyyan smile ba amma sai datayi yace gobe su uncle zasu zo so I thinks I will be much busy mamana dan Allah Ki kula da kanki ki sha magani kici abinci I know bakya son hayaniya so don’t stress yourself for my sake dan Allah “ tagyada masa kai ya shafa kanta yace and anjima sai mu ma mom transfer kudin ko zamu bawa oum tabata ne?aydarh tagirgiza masa kai tace kawai mubata sir yace ohk princess now am leaving ibrahim najirana zamu karbi dinkin uncle na daurin aure “gyada tace shine zaka koran mun yan fira while kaima tafiya zakayi yace pardon me ranki dade abunda ko 1hr bazan kai ba zandawo mu fita ma “did you start caring about me like that tajuya masa kai tace sai kadawo yayi murmushi kawai kafin ahankali yace yaushe zaki ce kina sona dan Allah?yafada kaman mai shirin kuka tace sirrrrrrrrr dawani irin tone dayaji from head to toe dinsa na neman fara waka-waka yah rabbil alameen “tace kaje kar ya gaji da jira bye “yayi gathering courage dinsa yace ohk dear I love you yafada yana mata blowing kiss “tace take care yace tau darl “fita yayi tabishi da kallo tana girgiza kai kawai mikewa tayi takarasa gaban mirror tana kallonta kanta mamakin yanda tayi wani fau tagani cream dinta dai shine take using har yanzu “dazu data na drying gashinta bata tsaya ta kalli kanta da kyau basai yanzu daman can haka shape din yake buh yanzu saidai taga kaman irin tasha magani kalan irin kara budewa datayi said ai tafada a ido da fuska kana kallonta kasan she

is sick manya kuma kallo daya zasuyi mata su fahimce ciki ne kaman irin yana jiran ace akwai shi saiduk wata alama tayi showing gently tayi placing white clean soft hannunta a cikin bakaramin kyau diamond rings dinta ke kara wa hannun ba “ ta lumshe ido bata san ya akai yi ba jitayi she is feeling the baby ma a cikin kusan five minutes tana tsaye a wurin tana kallon kanta wai yau ita ne keda aure kuma hadda ciki “maganar sa ke mata yawo a kunne yana dawo mata fresh a brain “ when zaki ci kina sona?dole tafada ma kanta gaskiya ita kanta bata san abunda takeji ba akan malik itadai tasan ko dawasa bata son ganin wata a wajan shi “ idan ta wuni baya nan ko bata ganshi ba tunanin sa ke hanata sakat yana mata kyau idan yayi kwalliya duk da by nature Allah yadaura mata tausayi amma tausayin datake wa malik na daban ne “ko da zata wahala bazata taba bari taga yana ciwo bako gajiya yayi daga wurin aiki zataji duk abun ya dameta “when it comes to sex bata so bata so amma idan ta tuna zai iya yin rashin lafiya bata iya hanasa ko da tagaji tana daurewa “idan suna tare zataji ta very safe!to mi hakan ke nufi tana sonsa ne?dasauri ta girgiza kai wata zuciya nace mata keda baki san so ba “komawa tayi tazauna kan gadon ta rike kanta tunani na neman zauta ta salama ta samar ma kanta tacire tunanin a zuciyanta idan ma bata son sa ya zatayi?tunda ko zata mutu tasan babu wanda zai ce yarabu da ita bama zancan rabuwa Ai a yanzu “kawaii dan shine kaddaranta shikenan ta karba Allah ya cigaba dabasu zaman lapia that’s it,tunda a da ne tayi tunanin yasaketa amma a yanzu kwata kwata bata ma son kalman ko tunawa ne tayi “ita wa zata tambaya akan abunda take ji kansa ko dai shine son? Ko ta tambayesa tunda duk duniya bayan shi babu wanda zata iya sakin jiki suyi labari ko magana sosai a daa dai sai salma!sai yanzu ma zuciyanta yatuna mata da salma ta ina ne ta daina zuwa gidan ne ko dawasa daga oum har mom babu wanda yamata maganar salma yau kam taji tana son taji labarin salman “a da ko bindiga aka bata akace wa take son ta kashe zata iya cewa salman amma yanzu kiyayyar datake mata ragu sosai batasan miyasa ba “wayanta tadauka ganin inda ya shiga yana kallo kai kawai ta girgiza tana murmushi wayan ta ajiye tamike tashiga toilet bata jima dayin wanka ba amma wani zata kara saboda ji take jikin duk babu dadi (nikam nace su cuddle bug ai hakuri ake) . Driver ne ya dauko halime da Maryam daga airport sun isa isa sun zama classy yan gayun abuja cikin abunda bai fi one month ba sunyi kyau “kyansu yasake fitowa ankara zama yan mata duk suna zaune parlor lokacin dasuka shigo ai maryam bata tsaya wata wata ba da gudu tafada jikin ummi tafara kukan shagwaba ummi ta ture ta tana murmushi tace ohh bazaki chanza bake koh? Maryam tace ai missing dinki fa nayi ummi tabude hannu suka shiga jikinta both halimen da maryam din tace I missed you to yaran kirki “dr hafsa tasaki baki tana binsu da kallo ta ajiye mug din hannunta tace wai wa nake gani haka kunga yanda kuka zama irin yan gayun Twitter din nan yah Allahu tau oyoyo tafada tana bude musu hannu hugging juna sukayi tana tambayar su ya school suk ace Alhamdulilah aysha dai sai kallon su take batasan haka tayi missing Lil sisters dinta bas ai yanzu data gansu “ihu sukayi suna nufar ta halime tace oyoyo addarhnmu “aysha tawashe baki tace oyoyo freshers ya school din halime tace not fine my aysha we missed tace I missed you more than words yaran ummi “ halime takalli hibba tarike baki tace shine bara kiyi manah magana ba saidai kiyi murmushi Ko auntie hibba ? Hibba dai tasake murmushin tace tau kuzo halime tafada jikin hibba tace ina wuni aunty ya jikinki hibba tace Alhamdulilah “ girlies ya school din? Maryam tace ina yayanmu ina auntie

aydarh ummi tace sun fita shida ibrahim “ baby kuma na gida “ halime tace ina my loves ina hajajju da inna ina babata kuma?aysha tace inna sun fita da hajajju baba kuma na ciki tayi baki ku shiga kuyi wanka ku ci abinci sai ku duba baby da jiki “maryam tace eyyerh ummi dan Allah nidai zanfara ganin auntie kafin nan ummi tayi shiru kafin aysha tace aaaa fa Maryam yayah nadawowa fita zamuyi gaba daya fa Wallahi “ dr hafsa tace nooo kibarta taje Ai mu duk mun shirya basai a jirata ba halime tace tau kije ke daya kawai ni idan zamu fita zan mata ya jiki “maryam ta dau wayanta tafice duk suka bita da kallo kowa na murmushi halime takalli hibba tace auntie bangane wannan ba ta nuna rabiah dasuka gaisa wacce tafito yanzu hibba tayi murmushi tace she is my sister “halime tace kai haba Masha Allah kuma Wallahi sunyi kama da yayah ibrahim aysha tace idiot tau ai kanwar sa ce she is his only sister dayake dashi “ halime tace wow barakallah mai kyau da ita itama tana murmushi tasake ma rabiah waving hannu tace hey sis sannunki miye sunanta ayshat ace she is rabiah halime tace nice to meets you rabi “ rabiah tayi murmushi tace nice to meets you too sissy “halime da daman sun fi shiri da hibba maryam kuma dr hafsa “halime tace aunty hibba bara nayi wanka nafito ke kawai nayowa tsaraba sai yayah ibrahim aysha tace ohh wow daman ansaba nuna manah wariya itama aunty hibba ko yayah ibrahim din yasiyo abu saidai ta bawa halime babu komai ummi na murmushi tace tau ina ruwanku dr hafsa tace nima dai shi nagani ummi aysha ce da bata gajiya aie “rabiah Wallahi abun birgeta yake ashe rayuwar rashin kunya da rashin bin nagaba ba wayewa bane ba birgewa bane “rayuwar wayewa shine jan mutane a jiki bawa babba girmansa dakuma kunya shiyasa har yanzu dr hafsa bata wani sakin jiki da ita sosai duk saboda halinta nada “,Lokacin da maryam tashigo gidan su oum sun dawo duk suna zaune a parlor da oum da rufaidarh sai aydarh dake zaune da MacBook din wedding planner a hannu tana duba deco daaka chanza

.

Maryam tace Assalam alaikum “Aydarh tadago ido suka hada ido da maryam tayi cute smile tace ahhh ga yan base oyoyo “maryam na murmushi tace oyoyo auntie ‘takara so parlor zata zauna kan carpet oum tace no tazauna a kujera gaishe su tayi ita da rufaidarh suna tambayanta ya school din tace Alhamdulilah oum tace yan mata duk antaho biki Ko maryam tagyada kai tana murmushi rufaidarh tace masha Allah uktiee kiga kuma maryam yacce takara zama Allahumma bareek oum tace Ameen “Aydarh dai sai murmushi take taji dadin ganin maryam din gently ta tashi tana mikawa matar MacBook din tagama hannun maryam suka wuce sama can dakinta “zaunar da ita aydarh tayi a sofa itama tazauna kusa da ita tace welcome back my yah mariam ya school ya flight? Amma baku jima da landing ba right?maryam tace Alhamdulilah auntie ina wuni?ya karfin jiki?aydarh tace Alhamdulilah “ maryam tayi wani kala da fuska tace masha Allah auntie kinyi kyau aydarh tayi dan murmushi kawai batace komai ba, kafin maryam tace kuma aie sai nan da two weeks zaku koma right aydarh tace erh fa in sha Allah “ tace banga yayah ba auntie ko ya fita? Aydarh tace Erh yace zasu fita “maryam tace eyyerh Allah sarki “ kafin tace ni auntie sai naga kin kara yin kyau amma kin fada ma aydarh tace kai yah mariam kinci Abinci kam maryam tagirgiza kai tace kingani nan babu abunda nayi isowan mu kenan nace wajan ki zanzo aydarh tace Hun nagode sosai bara nahada miki ruwa sai kiyi wanka kafin nan sai akawo miki lunch maryam tace lah aaaa auntie zan mayi a gida yazaayi nayi miki wanka a bayi ahh ba ruwana aydarh tawara ido tace shine miye yah mariam ai toilet dina ne kuma nin

ace ki shiga babu komai fa “ maryam tace idan yayah yashigo fa yayi fada nazo natakura ki aydarh tayi kasa dakai tace bazaya ce komai fa yah mariam nidai kawai kiyi don Allah kinga bayace fita zaayi ba and you know baya son jira yazo yadinga manah masifa yanda aydarh tayi magana yasa maryam takwashe da dariya tace nidai babu ruwana kun fi kusa amma kibarshi basai kin hadamun ruwan wanka ba auntie naga yanayin ki sai ahankali I will do it by myself Allah aydarh tace to shknn kije “ mikewa maryam tayi tashiga toilet din sai bin toilet din take da kallo “ganin set set na shower gels kala kala ga set din baths perfumes da liquid dollber kala kala “bin hanger towels din dakeyi da kallo kafin taciro daya tadaura tafara wanka “ kaiiiii dole ma ne Wallahi auntie aydarh tayi kamshi don Allah ji ta yanzu yanda take kamshi balle ita auntie aydarh dake amfani dasu ko yaushe wow! Fitowa tayi taga aydarh bata dakin sai wata silver abaya mai mugun kyau sabowa dal da sabon pant da bra hadda undie duk sabbi ne “ murmushi kawai tayi Wallahi tana son auntie aydarh tana da mugun kirki ‘ tana tsaye bakin mirror tana bin kayan sama da kallo tarasa wanda ma zatayi amfani dashi itakam so take ma taje Washington taga dakin auntie aydarh yanzu fa nan ba gidanta bane gidansu ne kuma zuwa take a yanzu “ amma ji wannan uban kayan “bude dakin akayi aydarh tashigo da waya kare a hannu da alama waya take kuma kaman da yayansu ne sai ga maids a bayanta da tray anjera abincin a kai “ aydarh tanuna wa matar idan zata ajiye abincin akai tana ajiyewa kanta kasa ta gaishe da maryam maryam ta amsa mata matar tajuya tafita “Aydarh ta zauna gefen gadon tayi shiru kafin tace kayi hakuri to “daga can yace shknn ku shirya din yanzu zamu taho tace ohk “takashe wayan maryam tace auntie wane zan shafa aydarh takalli mirror tace kowane yah mariam akwai wanda kike amfani dashi anan? Maryam tabude baki tana girgiza kai tace ni banma taba ganinsu basai dazamu tafi base kika siyan manah shigen su aydarh ta mike tadauki wani strawberry fields lotion tamikawa maryam tace use this maryam takarba tana budewa taji zallan kamshin strawberry fara shafawa tayi aydarh dai sai juya abunda malik yafada mata arai anya uncle din dr usama baiyi wa auntie hafsa tsufa ba taya ma zaayi ace bama friend dinsa ba uncle dinsa ita dai saidai sir yayi fushin amma sai tasake masa maganar ai kwara dr faisal din “maryam nagama wa tashafa perfumes the scent is different ouuuuu “maryam tace auntie Allah perfumes dinki akwai abunda kike karawa “ Aydarh tayi smile tace nope babu fa komai Allah idan kina so ma zaki iya dauka ma maryam tagirgiza kai tace aaaaa auntie aydarh tace ba wasa ba fa “maryam tace zan dai dauka amma wannan “tanuna wani dan karamin oil perfume designer “Aydarh tadauki abayan dake kan gadon tamikawa maryam din tace gasshi sai ki shiga closet din ki saka maryam takarba tana murmushi tace thank you my auntie Allah yasaka da alkhairi yakawo manah pikin’s masu albarka “aydarh tayi kasa da kai batace komai ba “maryam tashiga tasaka abayan yayi kyau sosai masha Allah “ fitowa tayi aydarh tace ga abinci nan maryam tace tau auntie nagode aydarh tayi murmushi kawai “ fried rice ne da chicken sai chivita da bottle water ga glass cup a gefe maryam tace yanzu haka fa baki ci ba ke? Aydarh tagirgiza kai tace naci fa “ maryam tace Allah yasa abincin take ci sai faman surutu take wa aydarh

83 / 111