Author : Nana Maryama Category : Romantic Hausa Novels
din daya siyo mata yanzu tayi amfani pants din dai ke bata taba ba tasaka riga kafin tadawo kan katifan ta kwanta ta rufe har kanta few minutes bacci ya dauketa, kallonta yayi yaga alaman bacci tayi yafita backyard din yashanya rigan ta dana sh isai bedsheet din, already ta shan inners dinta toilet daman nan suke shan inners
dinsu daga shi har ita basa fitowa waje su shanya, sai da ya gyara parlor yayi moping kafin ya shiga kitchen din ya gyara shi, shima sauran ruwan lipton din daya tafasa mata, shima yahada tea din yahada dawani bread yasha,few plates da cups kawai ke baa wanke ba ya wanke su kafin yafito anan parlor ya kwanta kan carpet,kafin bacci yadaukesa.Yace ya jikin? Tace yayi sauki yace sannu tace yawwa daga haka babu wanda yasake magana cikinsu can yace ko na kara maki slices din apple din? Ta girgiza masa kai tace ah’ah nakoshi yace baki sha fruits din dayawa ba fa hajia tace anjima zan sha,yace har yanzu kina jin ciwon? Ta gyada masa kai tace erh amma kadan kadan yace sannu zai daina kinji ta gyada masa kai.Har sai dayayi shiru kafin yace tau shi waccan dr yaushe zai zo kasar dr ibrahim yace gaskia ban dai sani ba amma dr Faisal din yace ba maganar zuwansa bane ba komai zaa iya yinsa ta cellular, malik yace tau Allah yataimaka ibrahim,dr ibrahim yace Ameen in sha Allah zaa dace malik yayi murmushi yace tau Allah yasa dr ibrahim yace Ameen kafin malik yace ya wajan amarya yace lafiya lau ai danace nan zanzo shine wai zata biyoni nace tayi hakuri akwai inda zan wuce ba nan kai bas ai tabani sako nakawo madam malik yace Allah sarki dr ibrahim yace banji motsinta bak o tana gidan inna ?malik ya girgiza kai yace aaaaa tana ciki bata jin dadine dr ibrahim yace subhanallah Allah yasawwake malik yace Ameen,kafin yamike yace bara na kirata sai ku gaisa dr ibrahim yace da kabarta malik yace aaaaaa kafin yashiga bedroom din tana zaune apple din take sha kallonta yake ko dauke ido babu she looks very good tayi parking hair dinta can keya kanta babu hula wahalan jiya datasha yasata dan fadawa sai wani glow datakara yace ki saka hijab zaku gaisa da Doctor yana parlor kafin yajuya yafita “hijab din tasaka,tafito parlor walking very slow irin na wanda yatashi daga ciwon nan amma sai ka rantse tsaban aji ne da gayu,kusa da malik ta zaune kafin tace ina wuni Doctor ya auntie hibba? Dr ibrahim na murmushi yace lafiya lau madam ya jikin? Tace Alhamdulilah yace masha Allah Allah yakarasa sauki tace Ameen kafin tasake cewa Auntie hibban fa? Dr ibrahim yace tana lafiya tana gaishe ki ga wannan tace nako maki, Aydarh ta karba tace to nagode sosai a gaishe ta, dr ibrahim yace in sha Allah daga haka ta mike da ledan ahannun ta koma bedroom din duk tasakar wa malik kamshin jikinta,dr ibrahim yamike yace yallabai bara nawuce komai ke nan yace zai turo sai ka duba Whatsapp dinka kawai nayi maka sharing ka cike da kanka malik yace tau shknn, dr ibrahim yace ni zan wuce nabarka karasa jinyar yafada yana wani dariyan tsokana malik ya girgiza kai yace Allah yashirya ka ibrahim har bakin kofa yarakasa kafin dr ibrahim yace wai yallabai ya wajan Ramlah ?’malik yayi murmushi yace ana sha drama ai,dr ibrahim yayi dariya yace nan kusa zaka sha mamaki ai, malik yashafa kansa yace tau Allah yasa sallama sukayi dr ibrahim yawuce shikuma yadawo cikin gida,yana shigowa ya rufe parlor yawuce bedroom tana jin karan kofa tayi saurin boye abunda hibba ta aiko mata dashi ita bata san sauran batayi amfani dasu ba balle waennan, kuma kunya take malik yagani batasan yama ga na wardrobe din bas ai dai ya dinga mamakin ina aka samu so can tunaninsa yabasa matan dr ibrahim din, karasa shigowa yayi yazauna kan carpet yasa hannu ya dauke slice daya na apple yasa baki yana sha yarda yake shan apple din take kallo komai nasa a natse, he is real definition of decent can yadago yace shi sakon ba zaa raba damu ba hajiya “ta turo baki tace ah’ah fa,yace rowa ba kyau dai ,tayi shiru kafin tace yatafi? Yace eh tace tau yaushe zaka kaini can gidan? Yace sai Monday kinga gobe da jibi duk akwai islamiya ta gyada
kai,kafin tace Allah yakaimu yace Ameen ,kafin yace what will I prepared for dinner hajiya?tace ai tare zamuyi yace kinji sauki net ace erh yace alluran ba zafi ba?ta gyada kai tace babu yace ai nayi tunanin technicians kawai suka iya allura,ta turo masa baki tace kaidin ma dan kasamu na yarda kamun zaka wani dinga daga shoulder yayi murmushi yace sorry ma,yayi shiru kafin yayi breaking silent din su yace,anjima ma zan fita so, ko gidan inna zan kaiki ki zauna ne? Tayi shiru kafin tace ina zakaje?yace zance ta gyara zamanta “ tace zance fira?ta gyada kai tahade rai tace ina?yace kofan gida manah tace kofan gidan ina?yace let’s cut the story wajan Ramlah “ta kallesa kafin ta dauke kai tace babu gidan innan da zani kai ma babu inda zaka ya wara ido yace tau saboda mi?tace saboda hakanan babu inda zaka fita kuma ma har yanzu Cikina ciwo yake kaman zan mutu nake ji ,yawara ido yace amma dazu kika gama cemun yadaina tace to ya dawo yanzu tafada tana juyan da kanta yace kinga relax ni ai bawani abu nace ba ,bakya son naje ne?ta gyada masa kai yace tau shknn bazanje ba “tayi smile kafin taja cheeks dinsa tace good boy,” yah rabbi “wannan yarinyar na neman zauta ma ummi shi ,bai ce komai ba ta dauke hannunta tace mi zakayi dinner dashi? Ni am okay fruits din sun isa yace nima tace yanzu karfe nawa ya duba wayansa yace mata quarter to six tace,sir kanada nail quarter? Yace mata ehhh tanuna masa white beautiful cutesy nails dinta tace kalli zaka gyara mun? Yace eh tace to muje parlor?yace eh,nail quarter ya dauka suka fita parlor ko hulan bata saka ba gashinta yayi masifan yin kyau yarda tayi masa parlor suka zauna kan carpet kafin tace nima zanyi maka yace kin iya ne?ta gyada kai tace zan iya yiwa wani nice bazan iya wa kaina bayace tau, ya dinga bin fingers dinta da kallo rings din suna masifan karawa fingers din kyau,ahankali yafara yanke mata akaifan duk da bawani tsawo tayi ba kusan 10mins ya daukesa cutting mata nails din bakaramin kokari yayi bay agama saboda yanda hannun ke fizgarsa, yana gamawa tace thanks tana wani cute smile,yace ko mu bar isai gobe kimun ta girgiza kai tace nooo yanzu zan ma, yace tau ai kinga babu nails din amun cutting tace duk da haka sai anyi yace tau gashi,yafada yana mika mata nails dinsa kallonsu take ko dauke ido babu,saboda ita ke ma abba cutting nails, a gida kuma babu abunda ya bambata nails dinsa dana abba komai yayi Wallah isai taga kaman abbanta “can yace ko dai kallon akaifan zakiyi ba yankewa ba?tayi saurin girgiza masa kai tace naga kaman na abba shiyasa “yayi shiru kafin yace miye kaman na abba?tace nails dinka kala daya dana sa yace really?tace yes,yace Allah sarki ai muna kama da abby kuma kinga ai there are bloods tayi shiru tace ai bansan abbyn ba, yace kai haba baki gansa ba?tace ai bana iya kallonsa shida ummi tsoro nake,yayi dariya yace tsoro kuma nami ta turo baki tace bayan ance musu kamun ciki kuma,dariya yayi sosai har da rike ciki,yace ohh shiyasa?tace to miye kuma na dariya? Yace aaaa babu komai sorry tace Allah hadda sisters dinka zasu dinga ganin da haka “yace aaaa sun manta yanzu tace dagaske ya gyada mata kai yace eh tace to kawo nayi maka “ahankali tafara yanke masa,knocking akayi kofan babu key kawai yasa malik cewa a shigo da sallama dr hafsa tashigo parlor suka amsa murmushi tayi tace ah ai bansan anan wannan kaunan ba da ban shigo,malik yayi murmushi yace welcome Doctor ,dr hafsa tace thank you yallabai ya gida ya aiki?yace Alhamdulilah ya naku tace sai godiya yace Allah ya taimaka tace Ameen, aydarh ta dago still hannunta rike da finger malik tace auntie ina wuni?dr hafsa tace lafiya lau mata tagari ya mai gidan?Aydarh ta kalli malik kafin tace he is doing good,tace auntie bara nakawo miki dr
hafsa tayi sauri cewa aaaaaaa nagode Wallahi ki cigaba da aikin lada kawai,inna ma nagaishe ki,aydarh tace ina ansawa “ malik yace ai nace tazo wajan inna tace aaaaaa fa,tace kinji fa auntie wai fira fa zaije dr hafsa tawara ido tace gaskia kwara dakikace aaaaaaa,tayi wani kala da fuska tace firan ma fa wajan wannan yarinya ,dr hafsa tace gaskia ai babu dadi malik yace ita fa tace nakara aure aydarh ta bude ido tace nikuma yaushe
.
Ni yaushe nace haka? Yace ranar ma har ce mun kike ai munyi matching da Ramlah,Aydarh duk ta rikice ta marairaice fuska tace Allah ban fada auntie “dr hafsa tarike baki tace ah eh lallai gaskia “yallabai da nayi niyyar shigan mata fadan amma yanzu nafasa,ina bayanki tunda har itama ke fadin kunyi matching idan ka shirya kawai kafito a fara hadda lefe “aydarh dai sai kallonsu take ko dauke ido babu” Malik yace in sha Allah Doctor tana sona sosai nima haka tau there’s no anytime to waste kawai azo a fara preparations right? Ai yana kai karshe ta sakar masa hannunsa da nail quarter ta watsar ta kallesa kafin tafashe dawani kukan shagwaba sai hawaye batace komai ta mike ta nufi bedroom sai kuka take “ malik kau ya bita da kallo ko dauke babu ya girgiza kai yana murmushi,dr hafsa ta rike baki Wallahi mamakin yarinyar take,komai nata na shagwaba ne “aranta tace wannan ranan dazata haihu sai yallabai yarasa waye mamar waye babyn raino kawai yake, malik yace dr kinsa mun yarinya kuka,dr hafsa na dariya tace kaga yallabai magrib takusa bara nawuce kaje lallashin baby girl dinka,babu ruwana ni “tafada tana mikewa tace kace mata na wuce “malik yace tau Doctor thank you “ bakaramin dadin zuwan dr hafsa yaji saboda ta taimaka mashi, kusan ten minutes kafin yashiga bedroom din walking majestical yazuba hannunsa a pocket din trouser dinsa, yana shiga ya ganta kan carpet ta kwantar da kanta kan katifan sai kuka take,zama yayi kusa da ita ta juya masa baya tana cigaba da kukan ta riganta duk ta tattare daga kasa, ya dinga kallon legs dinta yace tashi “ai kaman tana jira tace”Wallahi sai dai ni kasake ni!kafin ka aure ta ,tafada tana sake fashewa dawani kukan “ Wallahi duk da fadi kawai tayi ba aikatawa yayi ba sai da zuciyarsa tayi wani irin mumunan bugawa, tashi zaune tayi tana facing dinsa tace ai nace bana sonta shine zaka ce zaku fara preparations to ni kasake ni sai ka aure “ ka kaini tasha natafi can adamawa nasan ita ummi bazata koreni ba zan zauna dasu auntie Aysha kawai “kafin oum da abba suyi hakuri nakoma can kai kuma sai ka aureta din “malik was speechless bai ma son ta ina tayi wannan wayon haka ba bai masan ta ina tunanin ta yabata haka ba,ko dan shiga cikin matan auran datakeyi ne tafara wayo ko dai kishi ne? Yadai san ai bata sonshi shine kawai ke haukan banza sa, yace kin fi so nasake ki? Tace erh ni kasake n isai ka aure waccan amma Allah da aurena kanka “shine last abun dazakayi in this earth auranta ba “malik yayi shiru kafin yace tunda tana sona tana kishina ta shirya zaman aure dani duk da bani da kudi ta shirya haihuwa dani duk da batasan ko ni asalin waye ba,komai abunda take duk dan ta burge ni,shiyasa nace zanyi mata hallaci na aureta “cike da masifa Aydarh tace and so? Nice kawai matarka kuma duk abunda ka ce din babu wanda takeyi maka “yace oh haba haka kike tunanin tau indai kiga ban……ai bata bari yakarasa ba tayi wani irin shigewa jikinsa tana rufe masa baki,da hannunta,yarda ta makalesa sai yaji duniyan na neman masa locomotive “ tace karka karasa dan Wallahi duk ranan da ka aureta sai na gudu “kuma sai ka zaba ko ni ko wannan abun !!! Shi fa yau tana kashesa da mamaki duk baiyi tunanin zai ji haka daga wajan ba, hannu yasa yana cire nata haannu yamike tsaye itama tashin
tayi duk tsawonta amma ko shoulder dinsa bata kamo ba, tace itama auntie nafasa bazaka aureta ba tunda har ita kecewa ka aure wannan, nice kawai matarka babu wacce zaka sake aure!! Malik yadinga kallonta ko kiftawa babu , bugun zuciyansa na sauyawa, idonshi har ya kada “soyayyyarta na barzanar hallaka sa, yarda yakeji kaman ya hadiye ta “ ahankali ya fita daga dakin ta dinga binsa da kallo kaman zata fashe da wani kukan toilet tawuce,shima masallaci yatafi saboda magrib “ ake kira. Ko da yashigo gidan kitchen yafara yadaura indomie “ yafito ya shiga bedroom din tana kan prayer mat, zama yayi kan katifa yana kallonta, kafin yace sit kaman bazata zauna ba sai kuma ta zauna din yayi kasa da murya yace,har kin gama mp din? Ta girgiza masa kai tana juyan da kanta tace ni ba sallarh nayi ba, yace ohh kwanciya kawai kikayi anan din tayi masa banza batace komai ba, yayi shiru kafin yace ita Ramlah har yanzu kin kasa bani dalilin dayasa bakya sonta,and kince kuma dr hafsa yanzu kuma kince bazan aureta ba “mi kike so yanzu? Tace bana son komai kawai yarda mu biyu kawai muke rayuwa bamu da kowa let’s continue like this bana son wata ta shigo rayuwanmu yace ASSEIYARH am 35 by now I suppose to build a family nasamu matar da zamu haihu muyi building family understanding wife,mai sona “wacce zata iya zama dani ahaka “ muyi rayuwar mu kinga idan ba yanzu ba ,shekaruna karuwa suke har yakai lokacin da zan wuce wannan stage din so dole nayi aure “ta dinga kallonsa tama rasa abunda zatace masa, kusan ten minutes babu wanda yasake cewa komai cikinsu kowa da irin bugun da zuciyarsa keyi, fatan sa batace tana sonshi ba kawai ta yarda matsayin matar shi, shirun yaga yayi yawa kawai yawuce kitchen yakarasa indomie sa ya juye a warmer lokacin isha”I yayi yawuce mosque,ko daya dawo kitchen din yafara shiga yadauko plates biyu da forks biyu ya dauki warmer yashiga bedroom din ta fito wanka tana daure da towel tana kokarin parking gashinta yadinga binta da kallo ko dauke ido babu “wani kalan pleasures ke shiga ta ko wani vein a jikinsa har wani kara gudu bugawan zuciyarsa yayi bata ji karan shigowansa ba saboda har yabude baki zaiyi sallama kalaman suka kwace masa , ajiye kayan hannunsa yayi yakarasa bayanta kai yasa hannu yakama nata yana karban ribbon din, wani irin firgita tayi dan bakaramin tsoro taji ba addua yakaranta mata kafin voice dinsa so calm yace shiii nine,ajiyan zuciya ta sauke hankalinta na kwanciya amma duk da haka ganin towel ne jikinta sai taji duk she is uncomfortable, ribbon din yasa yayi mata parking gashin kaman yarda yaga tana parking din sa tunda kan su maryam ya iya parking saboda daura gashin su nayi musu wahala tsawo garesa sosai duk da yana ganin tsawon gashin su maryam amma sai yaga nata yayi mugun linka nasu “parking din yayi mata daidai,tabawa tayi taga yarda yayi mata har yama fi yarda take nata ma,saboda wani lokacin bata da karfin daure gashin ma Sosai batace komai ta jawo hijab dinta,tasaka “kanta kasa yace let’s eat, tace nakoshi “yace mika ci? Tace babu komai ,yace zauna k ici abinci malama ‘serving dinta yayi daidai yarda yasan zata ci kafin shima yayi serving kansa ahankali suke cin abinci babu wanda ke magana cikinsu har yagama ita bata gama ba warmer ya dauka da plate dinsa ya fitar kafin yadawo da ruwa a plate ya tura mata gabanta,takusa cinyewa yasa shi kawai fiddo wayarsa yaga miss calls din dr ibrahim har biyu,dialing number yayi tana fara ringing ya daga gaisawa sukayi Malik nabasa hakuri kin daga wayar,yace babu komai daman dr faisal ne yakira sa yana sanar masa da zuwan dr usama ranar Wednesday, malik yace nan da five days kenan? Dr ibrahim yace masa eh in sha Allah,malik
yace Allah yakaimu lapia nagode Doctor a gaishe da madam ,dr ibrahim yace ai gata kusa wai sai ka hada su waya,malik yace ohh bata wayan ai muna kusa da ita,hibba ta karbi wayan “Aydarh nakallonsa alaman mi zatayi da wayan yace mata ai hibba ce wani cute smile tayi tana karban wayan ,kafin tace Allah auntie hibba nayi fushi,daga can hibba tayi murmushi tace afuwan Auntie aydarh naso zuwa ai ko ranan dayazo jiya neb a ?aydarh tace erh naga sako nagode sosai hibba ta kalli dr ibrahim dake kokarin mata zipping zip din gown tana hanasa da ido yayi kaman bai ganinta, kafin tace babu komai Auntie aydarh kin dai yi amfani dashi ko?aydarh tace ah’ah tafada tanayin kasa da murya tace kai auntie Aydarh miyasa kike haka kawai kinfi son wahalan kenan?aydarh dake jin wani irin kunya gani take kaman malik ya fahimce abunda suke cewa, tace in sha Allah zanyi auntie hibba thank you,hibba tace don’t mention auntie aydarh duk fa anzama daya “ ganin dai abun dr ibrahim ba mai karewa bane yasa hibba yiwa Aydarh bankwana tana ce mata sai tazo sallama sukayi kafin hibba takashe wayan “mika masa wayan tayi bata bari sun hada ido ba ta mike tana kwashe plate din data gama cin indomie da wanda yakawo mata ruwa har tafice bai dauke idonsa kanta ba. Hibba tace Allah Doctor ka fa daina yace mi zan daina din tace ko gajiya ma kayi wai?yace yanzu mi nayi miki ina zip kawai na bude? Tace nidai muje cikin tau,yace anan zan zauna tace aaaaaa kaga ranar ma rabiah tazo duk