Da So Kamane Complete Hausa Novel By Nana Maryama.docx

Author :  Nana Maryama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   62 / 111

183K to 186K   out of 332K words

manufar oum ba kan hakan “oum ta kama hannu abba dake nan tsaye yayi shiru yama rasa mi zai yi next murna zaiyi ko akasin haka shidai yasan last abunda zaiyi a duniya kenan yabar wannan auran “mikewa yayi Still hannunsa na cikin na oum har suka fita daga asibitin abby na jingine jikin motarsa abba dai yadauke ido murya can ciki yace Allah yabata lapia zamu wuce abby yace Ameen Ameen “sai anjiman ku fatima oum tace sai anjima yayah ,motar suka shiga suka wuce abby yakai five minutes tsaye a wurin bayan tafiyarsu kafin yashiga cikin asibitin anan reception yatarar da hajajju wacce fitowar ta kenan daga office din dr raudarh ta iske su oum sun tafi zama tayi ta buga tagumi ita daya a reception din kasancewan baba kulu da ummi da malik din duk suna cikin dakin da aydarh ke kwance wanda har yanzu ma bata farka ba “abby ya karaso ya zauna kusada hajajju yace sannu hajiya “hajajju tayi mitsi mitsi da ido tace bayan rashin kaunar Allah hala habib da wannan larabawan matan sun fara bankar wiwi da sauran su?abby yace subhanallah miya faru har haka hajiya tace ahtau daga shigata ofis din dafta ramda,magana fa kawai naje muyi da ita asan yanda zaa taimaki yarinyar nan daga hannun mutunmin can shine na fito suk ace daukarmu inda kika aje mu shegiya “ abby yace ayi hakuri kila wani uzurin zasuje suyi su dawo hajajju tace uzurin banza dana wofi har yafi lafiyar diyarsu “tsaban rashin kan gado mudai muna haduwa da jarabawa kala kala a famelin mu daga wannan jafa’I sai wannan bala’I kaman dai mun zage sama haba ina dalilin rashin lissafi da rashin kan gado abby yace ayi hakuri dai yanzu ya mai jikin ta farka? Hajajju tayi kasa da murya tace Wallahi ibrahin akwai firoblem ‘abby yace nami hajiya hajajju tasake yin kasa da murya tace dakyar idan habibu bazai saka ya sakar masa yarinya ba saboda kasan shidai bawai hankali yacika ba sam bashi da lissafi ahaka wai turai yake zuwa haba “abby yayi shiru yace saboda mi hajiya hajajju tace ga babban dalili nan baya son zumuncin yafi so a rabu abby yace idan hakan

shine alkhairi sai muyi fatan Allah ya tabbatar idan kuma bashi bane Allah yahana faruwan hakan “hajajju tayii wani kala da baki tace taso dai muma mu shiga kar ma daftan taga mu bamu da matsayi a wurin su an shanya mu nan kaman dai wasu yan hau abby ya girgiza kai kawai yabi bayan hajiya suka shiga hajajju ta rafka sallama baba da ummi suka amsa mata shidai malik ganin su ummi bai sa ya dauke idonsa daga kanta b abaya son yayi missing daidai second daya wurin kallonta son ta zai mishi illa Wallahi bai san abunda kaddara ta tanadar mishi ba nan gaba amma koma miye yana son abarshi da ita a duniya har ma can kiyama ‘yaga jarabawa kala kala a rayuwarsa yaga abubuwa da yawa a duniya kuma duk ya dauke abu dayane yasan zai zamo datsewar numfashin sa shine rashintw don dafin sonta ya mamaye duk wani parts na jikinsa tazamo jini da jikinsa “daya bayan daya yake recalling duk wani moments dinsu na waccan daran hakika tayi mishi kyautar da duk duniya babu wanda ya taba masa tayi masa sillar da duk duniya babu wanda yayi masa “yana jin duk duniya baya ummi babu mace mai matukar daraja da girman a idonsa da ma zuciyarsa kamanta yana sonta yana kaunarta zaiyi mata bauta ta har karshan rayuwarta zai yazo mata miji irin mijin nunawa a duniya da kuma lahira , hajajju tace anbani ibrahin ji bi wannan kalar abu tau wai audul kodai dan banza kazama duk ba asani ba? Shidai abby yayi shiru malik kam ko alaman ma yasan tanayi bai nuna ba shidai hankalinsa na kan matarsa baba kulu ta kalli abby tace kuje da asiya gida sai ta dauko duk abunda yadace tunda inaga ai nan zaa kwana suma yaran sai ka biya ka dauko su ka mayar dasu gida “kafin kuma in sha Allah yarinyar taji sauki sai a tafi gida duk ayi maganar “ abby yace tau shknn ba damuwa,hajajju tace nima muje ka saukeni a gidan habib zuwa anjima sai mu dawo don anan zan kwana “abby yace tau bismillah hajiya muje ummi takarasa gaban aydarh gentle take shafa mata fuska kafin ahankali tayi mata pecky a goshi “tayi addua tana shafa mata malik yakalli ummi yayi wani kala da fuska kaman irin dan yaron nan ummi tayi masa wani kallo tana maka masa harara ta wuce tace baba in sha Allah bazamu jima bas ai kema kije gida ki huta “baba tace tau asiya sai kun dawo fita sukayi ya rage daga baba sai malik a dakin “ahankali baba tace dawo nan abdulmalik ‘cike da so baba tayi masa maganar tashi yayi yana sakin hannun aydarh sai dayayi mata addua kafin ya gyara mata duvet din daaka rufeta na asibitin kafin yaxauna kusada baba kasan carpet “ kusan 2mins baba na kallonsa ahankali tace abdul kazama babban mutun sai kamanin ka da habib suka sake bayana “murmushi yayi kadan yace itama haka take fada baba tadan bude ido tace ita wa? Malik yashafa kansa yace ASSEIYARH baba tarike baki tana murmushi tace tau yanzu nan da larabci ko da turanci ka fadi sunanta malik yayi shiru yana dan murmushi yace both “baba tayi yar dariya tace kai kasan wannan bani ba, yace kema din kinsani “baba tayi shiru kafin murya cikin ruwan sanyi wanda ko da akwai wani dakin daga ita sai malik zasuji maganar saboda kar aydarh tafarka tace kana son matarka!?malik da kaman jira yake yace Wallahi baba Bayan ummi babu abunda nakeso sama da yarinyar nan baba tayi shiru tana karantu gaskiyar abunda yake fada daga cikin idonsa zallar gaskiya yake fada kuma irin mugun son nan yake mata ga dukkan alamu baba tace naji bayan barin ku adamawa sai kuka nufi ina?malik ya fesar da numfashi kafin cike da nutsuwa yafara bawa baba labari tunda ga farkon tafiyan su har dawowar su yau kaman yanda yabawa abby bayan yayi shiru kawaisai kwalla yacika idon baba tayi kabbara “ ta zuba ma waje daya ido ko kiftawa babu, malik ya dinga kallon

baba kafin yace baba tau kina ganin abban zai barmun ita? Baba tayi murmushi underneath her breath tace in sha Allah tunda kuna son juna babu wanda zai rabaku da yardar Allah malik yakama hannun baba yace kinga nagaya miki kwana bakwai kawai zanyi dan Allah kiyi kokari nidai kar su rabani da ita Wallahi bazan iya sakin ta ba nidai ina son mata ta Allah “baba tace ja’iri kenan tunda kayi aika aika ai dole kafadi haka,malik yashafa kansa yayi shiru baba tayi murmushi ta girgiza kai.Abby dake kallon ummi bayan tagama linke hijab dinta tasaka cikin yar jakka data saka kayan aydarh “yace tau haka dai baba tace mun “ummi tace Allah yasa muji alkhairi dai abby yace Ameen amma dan naki ned ai yace bazaiyi sakin ba ummi tace marar kunyar karya kawai abby yayi dan murmushi yace muje yaran can sun gama girkin dare nayi itama baba taso ta tafi gida daman hajiya tazo ummi tace ohk “maryam dake tsaye tsakan gida tasaka jalbab blue yayi mata kyau sosai tabarakallah, takalli ummi tace dan Allah ummi zan biyo I want to see her har ummi zatayi magana abby yace muje aysha halime ku kula baza mu jima ba “aysha tace tau abby a gaishe da mai jikin dasafe za muzo muma ummi “ummi tace tau Allah yakaimu lapia ‘,hajajju ce zaune a reception din sai baba da ta shimfida prayer mat da alama anan tayi sallarh ummi ce agaba sai abby maryam a baya “ ummi ta sukunya har kasa ta gaishe su tana tambayar su ya mai jikin baba tace dasauki alhamdulilah “hajajju tagyara mayafinta tace shi fa karya kowa yasan babu kyau a musulunce ma Wallahi “ahtau wani sauki yarinya dai angama nakasata saboda har yanzu ko dan farkawa batayi ba sai dai ta dan motsa baki ko ta taba fuska “baiwar Allah ina ma dalili, Maryam tace ina wuni hajajju “hajajju tace lahiya lau anmairo ya gidan?maryam tace fine ya jikin auntie aydarh? Hajajju tace wacece kuma haka? Maryam tayi shiru tace nidai nuna mun dakin nakai kayan hannuna hajajju tayi mitsi mitsi da ido tace tau daga gidan Habib abinci ne na larabawa kaca kaca a ciki dana turawa baki daya duk an jibge a ciki yanzu ba jimawa ma suka tafi abby dai yayi gaba maryam tabi shi a baya suka shige “ummi ma tashiga malik na zaune gaban gadon ya kura mata ido kaman kalan yasamu t.v dinnan ahankali ya amsa sallamar su tareda gaishe da abby da ummi kafin ya amsa gaisuwan da maryam ke masa tana tambayar sa ya mai jiki “ummi da taki kallonsa saboda bata son yaga rahama a idonta kowani taji tausayin sa saboda bakaramin bata mata rai yayi ba abunda yayi ma yarinyar nan tace ta farka? Yace ah’ah tayi shiru batace masa komai ba,abby yace kaci abinci ne?ya girgiza kai yace taso muje gida kayi wanka sai kaci abinci dasafe sai kadawo malik yayi shiru kaman zaiyi kuka bai so tafiya ba amma babu yanda zaiyi “maryam ta matso gaban gadon tana kallon aydarh for few seconds kafin tayi ma ummi sai dasafe ta fita ahaka malik yabi bayan abby kaman yafashe da kuka tsaban haushi,abby na fitowa baba tamike tace bara nayiwa asiya sallama ‘sallama sukayi saida abby yafara ajiye baba kafin suka wuce gida a hanya ya tsaya ya siye duk wani abunda zasu bukata wajan making breakfast.tunda hajajju taci ta koshi ta kwanta kan carpet din take bacci ummi kau na nan kan plastic chair kaf hankalinta na kan yarinyar “ahankali take bude idonta da kadan kadan ta dinga kallon celling din dakin tunda ta farka ummi tamike tsayi yunkurin tashi tayi kawai tafashe da kuka billahi tasa mutuwa tayi ba suma ba ummi a rude takama ta tana mata sannu har tasamu kukan ya lafa kafin ahankali ta kwantar da ita ta mike ta dauki flasks din data zuba ruwan zafi ta cikin bathtub din toilet din tahada ruwan zafin sai dayayi daidai daidai yanda zatayi mata sit bath kafin ta fito cikin dabara ta shiga toilet din data ita “duk

wani kunya ummi ciresa tayi ta mata sit bath taji tausan yarinyar sosai saboda duk yanda zaa gaya maka bazaka gane kalan wuyan data sha a wajan sa ba,ummi tace sai na rama mata fita tayi tabar aydarh tayi wanka kafin tashiga tasaka mata towel ta kamo ta suka fito wani plain gown ta dauko ta cotton mai kyau tasaka mata yanda take mata kaman kwai tea tahada mata da kyar tasamu ta karba kafin tabata magani Wallahi wani kalan kunyar ummi aydarh ke ji bana wasa ba “komawa tayi ta kwanta “ummi tace baby ko na kira dr dai akwai inda ke miki ciwo?aydarh ta girgiza kai tace ah’ah,ummi tace sannu aydarh ta gyada mata kai “ko baccin kirki ummi batayi ba saboda aydarh ko motsi tay isai ummi tayi mata sannu wani irin jin ummi take har cikin ranta,karshe ma ummi komawa tayi kan gadon ta kwantar da kan aydarh kan laps dinta itama aydarh wani abun ma da gangan takeyi ga masifan kunya datake ji

.

Har kusan asubah ummi batayi bacci ba duk da aydarh kam data gama yan koke koken nata bacci tayi ita kam ummi idonta biyu hajajju daman tunda tafara bacci ko farkawa ma batayi ba kaman wacce bata da rai “ ana kiran sallarh ahankali ummi ta zare kan aydarh dake bisa cinyanta “ ta daura kan pillow “ tamike tashiga toilet alwala ta dauro ta shimfida prayer mat ta kabbara sallarh “har tagama hajajju bata farka ba daman tasan aydarh zaiyi wuya ta farka tunda bata wani jima da fara baccin ba “matsawa tayi kusa da carpet din da hajajju ke kwance tace hajiya ku tashi anyi sallarh hajajju tabuda ido tace kai kwanan asibiti kam da wuya Wallahi “tunda dare yayi na kwanta anan ko baccin sakwan banyi ba tunanin halin da yarinyar nan ke ciki yahana ni sakat billahi abun duk ya daman duk ina jin motsin ku kasa tashi nayi karmu gallabi sauran al’ummar dake kwance rai a hannun Allah sauran dakunan “tunda hajajju tafara magana ummi ke kallonta da mamaki,bacci fa tayi kaman an yanka ta shine zata ce haka yanzu ummi bata ce komai ba ta mike ta koma jikin gadon tana tunani ta tayar da aydarh tayi salla ko ta qyaleta tunda bata jima da samun baccin ba “ Ahankali yaturo kofan kaman wani marar gaskiya yashigo without making any sound “daidai hajajju nafitowa daga toilet din tayi alwala jikin kofan bayin ta tsaya ta dafe kirji tace yau naga jaraba daga ina aka aiko wannan kuma ?? Sai lokacin ummi ta juyo suka hada ido da malik yayi saurin sunkuyan da kansa ummi ta dauke idonta ta cigaba da gyara wa aydarh duvet din da ta rufeta “yashigo yace ina kwana yafada yana kallon hajajju,hajajju tace lahiya lau hala a can risefshon din ka kwana?malik ya girgiza kai yace ah’ah a gida na kwana yanzu na fito hajajju tace bala’I dai yasameka kai kam “yoo wannan ai har sai a dinga jin tsoron lamarinka “malik bai ce komai ba yakarasa gaban ummi yaki yarda su hada ido yace ina kwana ummi?ummi tace Alhamdulilah tafada bata ko dago ta kallesa ba ‘yakai five minutes a wurin bai sake cewa komai ba ummi tacigaba da lazimin ta hajajju dake salla tagama tace tau ko aikin gadi kasamu malam?malik dai bai ce komai ba tace tau idan bahaka ba ka taimaka ka wuce ka samu gu kazauna dan sonka da manzon rahama “malik dai Still bai ce komai ba kuma bai da alamar matsawa hajajju tace tau ai shknn tafada tana sake komawa kan carpet din data tashi tasake kwanciya ko 10 seconds bata kara ba bacci ya kwasheta ganin babu sark isai Allah kuma ummi taki ko da kallonsa yasa shi jawo plastic chair din kusa dashi ya zauna “ya dago kansa ya daura kan cinya ummi kallonsa tayi don mamaki yabata duk da tasan zai iya amma batayi tunanin hakan ba a yanzu “ kaman ta dauke kansa a wurin sai kuma taji bazata iya ba ta kasa,wani irin sanyi taji a jikinta ganin su biyun kusa da ita is turning her up “rufe idonsa yayi yana jin wani

reliefs a all his body part cikin few seconds bacci ya daukesa jin yanayin saukan numfashin sa ya sa tagane cewa yayi bacci rufe idonta tay isai kwalla suka cika mata ido Wallahi tausan danta take ji har cikin ranta take iya jin kalan wahalan dazai shiga idan aka ce yasaki yarinyar nan saboda ko baka tsoron Allah kana iya hango tsananin kauna da son dayake mata a idonsa .Bude idonta datayi da yanzu ya rage mata nauyi kanta ma ya rage ciwon sosai saidai kadan kadan but still tana jin jikinta kaman irin bana ta ba, adduan tashi tayi daga bacci tana bin dakin da kallo kafin ta juyo tana kallon ummi da har yanzu kan malik na bisa cinyanta kallon sa datake da mamaki batasan ya akayi ba taji wani kala murmushi tayi kadan kafin ta turo baki tana harararsa ita fa bata sonsa,daman can kawai tasan he is all what she has “shiyasa amma yanzu dayayi mata wannan mugunta taji she didn’t like him anymore ta bata dashi ma wllh “kishin yanda ya kwantar da kansa a cinyan ummi taji yasata kama hannun ummi muryanta a mugun shagwabe tace ummiiii zanyi fitsari dasauri ummi tabude ido tace sannu baby kin farka sannu kinji “Ummi ta kalli malik kafin tasa hannu ta tayar dashi yana tashi ta mike tana kama aydarh sai faman jera mata sannun take shi kam kaman zai cinyeta tsaban kallo ko kallonsa batayi bai ta kam ahankali ummi ta saukan mata da kafanta “ummi a ranta tace barakallah ganin lallan kafan aydarh, ummi tasaka ta jikinta suna tafiya har toilet malik na biye dasu har kofan bayin kafin ummi ta juyo tace fita “ta karasa shigewa da aydarh cikin bayin “shikam anan kofan ya tsaya kaman wani dan yaro yana bata rai “Wallahi aydarh tsoron sit bath din take ga kuma kunyar dake taji “ummi ta tara ruwa a bathtub din kafin ta fito ta bude handbag dinta ta dauki ledan wani fresh sassake na icce wanda pure maganin gyara ne ta koma toilet din tasaka cikin bathtub din yauma dai kaman jiya batareda an cire rigan bad uk yarda taso ta daure yau kasawa tay isai datayi kuka ummi dai sai hakuri take bata yarinyar tariga da tagama wahala ne Wallahi fita ummi tayi bayan ta chanza mata ruwa tasa ta yin wanka da alwala “malik na nan tsaye bakin kofa tausai yabata batace komai ba ta fice daga dakin ta bar shi yanata tsayuwa reception ta zauna da tunani kala kala ranta .kusan 20 mins yana nan zaune can yaji cikin cute baby voice dinta takira sunan ummi “dasauri yabude yashiga tana ganin shine duk taji ta tsorota matsawa yayi kusa da ita yana kallonta ko kiftawa babu kaman zai hadeta tsaban so kyaunta na fizgarsa body structure dinta nakai sa cloud 7 ji yake kaman yayi hauka saboda ita kaiii Wallahi he loves ASSEIYARH murya very slow and calm yace cuddle bug rufe idonta tayi yanda yafadi sunan har tsikan jikinta sai daya tashi “wani masifan kunya da tsoronsa take ji “ita yanzu bayan shi a duniya babu wani abunda ya zamar mata kaya a rayuwar nan “a dan tsorace tama rasa abunda zatayi kawai murya na shaking tace in..a..kwa..na? Malik bai amsa ba yacigaba da kallonta rigan asibiti blue gown din yayi mata kyau bana wasa ba kallo daya yayi mata yasan jikinta babu bra yasan daman ai babu pant daga nan tsayen

62 / 111