Author : Nana Maryama Category : Romantic Hausa Novels
ba “ ASSEIYARH promise me please ko bayan mun koma gida you will continue seeing me as your own biological brother tunda bakiyi accepting auranmu ba “har cikin brain dinta take jin maganarsa tone din yake maganan bakaramin ratsa ta yayi ba shiru yayi taji lema na sauka a fuskanta tana dagowa taga kuka yake “sai taji wani irin rauni da tashin hankali at same time “ bata son ganin wani na kuka balle shi wanda a yanzu duk duniya bata dakowa bayan shi ahankali tasaka gefen veil dinta tana goge masa hawayan sa itama kaman zatayi kuka batasan dalilin kukansa ba amma har cikin ranta taji yanzu bata son rabuwa dashi bata taba zama so free tayi magana dawani a rayuwanta ba kaman shi bayan oum rufaidarh babu wanda yasan wani abu da yashafeta sai shi “yasan dariyanta yasan kukanta yasan jikinta yasan adadin cin abincin ta yasan adadin shan ruwanta yasan adadin kwananki mp dinta alluran dayake mata har yafi na dr khaleel ma bata taba jin ta damu wani a rayuwarta ba kaman shi hakanan kawai she cares about him “ganin duk tazama so disturb da maganganun sa da kuma hawayan sa yasa shi yin murmushi yajawo ta jikinsa tayi lamo shima lamo din yayi kowa na sauraron bugun
zuciyar dayan “,Dr ibrahim yace kinga muje dare nayi hibba tace tau kar mu katse musu soyayyya kuma, dr ibrahim yace rabu dasu sun karasa a gida “ tura kofan yayi aydarh tayi kokarin tashi daga jikin malik amma yaki bata dama ahankali malik ya daga idonsa yana kallon hibba da dr ibrahim kafin yace mu wuce right?dr ibrahim yayi murmushi yace ehhh sai a karasa soyayyan a gida kama hannunta yayi yasata a jikinsa sosai har kofan gidan dr ibrahim yakawo su kafin suyi sallama “kofan part din ya bude suka shiga fitan su kaman wani wutan soyayyan Aydarh aka kara masa ita kuma wani irin tausayin sa taji “duk motsin dayayi sai ta bisa da ido duk yana lura da ita “lokacin da ta fito daga wanka baya bedroom din vaseline din tashafa sama sama kafin tasaka wata gown marar nauyi tashafa perfume sama sama hula tasaka kafin ta kwanta kan gadon tana rufe har kanta da duvet “ ahankali yaturo kofan dakin yashigo kashe hasken yayi kafin walking very slow yakarasa kan katifan kusa da ita yakwanta kafin yajawo ta jikinsa yasauke wani ajiyan zuciya “itama lamo tayi a jikinsa tana jin wani irin nutsuwa duk lokacin datake jikinsa ko da kau tana jin tsoro sai taji kaman she is safe “ shiru shiru tana jiran taji ko zaiyi mata wani abu sai kuma yaji shiru,har bacci ya dauke ta shima baccin ya daukesa zuciyarsa na tayi mata azalzala dafin sonta na mamaye masa zuciya. Yace ko zaki je gidan dr ibrahim din?dasauri ta gyada masa kai yace tau je ki shirya ina jiranki kan carpet din yazauna itakuma tawuce bedroom din da sauri “can sai gata tafito tasaka doguwan riga tayafa veil akanta yama kasa dauke ido a kanta wallahi shidai sai kallonta,yamike yace go back and put on your hijab cuddle bug langwabar da kai tayi kaman zatayi kuka tace pleaseeeeeeeeeee muje ahaka lumshe ido yayi yana girgiza kai yace zan tafi nabarki fa “turo baki tayi kafin ta juya tasaka hijab din hadda nikkab ma ta dauko gani yayi ma Wallahi tafi yin kyau da hijabin “batace komai ta mika masa nikkab din tana turo baki murmushi yayi aranshi yace na tabo rigima fa nikkab din ya daura mata kafin yayi kissing goshinta yakama hannunta “suka fita rufe kofan yayi kafin suka fita bakin kofan gidan zasu samu keke “wani irin bacce ranta yayi ganin Ramlah she forgets when last da ta ganta kawai hannu malik kawai takama sukayi gaba kafin ma Ramlah takaraso “ganin tajasa yasa sa dinga kallonta har sukayi nisa kafin yace naga dai acan muke samun keke yau ko dai ance miki babu keke a can?aydarh ta hade rai duk da a cikin nikkab ne sai daya lura kafin tace ai wannan yarinya nasan data karaso sai tayi maka magana nikuma bana son Allah, malik ya dinga rike dariyar sa amma sai data fito kafin yace kinga yi hakuri nifa babu ruwana da ita ke kadai ce kanwata kawai kinji?ta dinga kallonsa kafin dai takasa hakura tace kuma ni kadai ce matarka “baki bude yake kallonta shi mamakin kishinta yake ya lura akan kishi zata iya komai, murmushi yayi ransa yace Allah nagode maka zanyi amfani da wannan hanyar ganin yanata murmushi tace the smile is for? Ya girgiza kai yace no finest batace komai ba har suka samu keke “malik yafada masa inda zasuje suka shiga “yakalleta yace ke da wakike kama? Oum ko abba?tawara ido tace both of them yayi murmushi yace bangane ba kaman ya both of them fa? Tace to ni ai bansan ma da wanda nake kama ba “yace nidai da abby na nake kama tace ai kasa kallonsa nayi to bazan ce ga kaman sa ba yayi murmushi kafin ya riko hannunta yasa ana shi yacigaba da kallon titi “can tadago tace ehen aiki wani kala sir?yace as a medical doctor tace congratulations sir all your hard work has finally paid off am so excited for you! Ya jinjina kansa yace thank you my priority “tayi murmushi tana dage nikkab tace did you just said am your
priority?ya girgiza kansa yace sure batace komai ta maida nikkab dinta tana murmushi, kofan gidan su dr ibrahim din aka ajiye su yabiya mai keken kudinsa “ suka wuce cikin zauran gidan suka ci karo da rabiah “ai yau ko damar gaishe da malik aydarh bata ,bata taja hannunsa suka wuce sai da suka shiga bangaran iya suka gaisa tayi masa murna kafin suka wuce bangaran dr ibrahim din “hibba ba karamin murna tayi ba ganin aydarh batayi tunanin tare zasu zo ba dayake dr ibrahim din ma already yashirya malik yake jira suje duba plot din ko zama basu yi dr ibrahim da malik suka wuce addua hibba tayi musu har sun fita kafin malik yadawo yarada ma aydarh yace karki ga bana nan ki kince bazaki ci abincin ba kinjini? Ta gyada masa kai tana murmushi sai kuma yace be a good girl “yayi mata waving hannu ita dai hibba sai kallonsu take “yana fita hibba tace ohni auntie aydarh wannan tsaban so har ina?aydarh tace kai auntie tafada tana cire nikkab dinta hibba ta dinga kallonta tace Wallahi auntie aydarh da sirrin dakike boye mun kan wannan glow din naki kodai wani lotion kike amfani dashi ko kuma yallabai yayi ajiya “Aydarh tayi dariya tace ba wata fa ajiyan dayayi auntie hibba yace bama yanzu ba nikuma I support my husband “hibba ta rike bacci tace ahh yayi masoya watau har yanzu ba a gama cin amarcin ba kenan tau Allah dai yasa adawo daga Washington ba a zo manah da triplets ba “Aydarh dai tayi dariya duk da bata fahimce maganar hibba ba tace “yace am still a baby fa tafada tana rufe ido hibba tace kid ai ce shi zai fara shanye milk din kafin babies din aydarh tayi saurin rufe fuskan ta da hijab tana dariya “kafin tace auntie kenan a da fa nafi haka Hibba tace wai lokacin da kina budurwa? Aydarh ta gyada kai tace wai shi yallabai soyayya kuke ko haka kawai aka hada ku “Aydarh tayi shiru bata son fada mata abunda yafaru gani take wannan sirrinsu ne “can tace shine fa yace yana sona kawai akayi manah aure Hibba tace Wallahi yayi daidai Allah yakara bada zaman lafiya yakawo cutest masu kama daku aydarh tayi kasa da kanta “Hibba tace kwana biyun nan daurewa kawai nake amma sai na dinga tashin zuciya shima ya lura kawai dai sai nace masa ba komai, aydarh tace eyyerh auntie ko fever ne?ki fada masa sai yayi miki test ba “Hibba ta girgiza kai tace kema dai auntie aydarh ina tunanin kawai har nayi gamo “ Aydarh tayi shiru tace like?don bata fahimta bah ibba
tace ina jin kaman inda ciki ne.
Aydarh tace congratulations auntie Allah yasauke ki lapia “Hibba tayi murmushi tace Ameen Ameen aydarh banda tabbaci sai dai anyi test din aydarh tace to auntie idan yadawo sai ki gaya masa ayi test din,Hibba tace in sha Allah ya islamiyan?aydarh tace Alhamdulilah muna ta fama fa exams zamu fara next week “hibba tace Allah yataimaka kila ma daga wannan week din bazaki sake zuwa ba idan kun tafi aydarh tace ana karatu Sosai amma kin sami auntie?hibba ta girgiza kai aydarh tace classmates din nawa sai ahankula kullun komai nasu a fade komai na gidansu sai sunyi sharing a islamiya kuma which is not good at all “hibba ta jinjina kai tace kinsan wasu matan kaman basu da hankali ko mi ma zance “ace baki da sirri komai na gidan ki sai kin gayawa kowa sai kowa yasani “ aydarh tace shine fa auntie “Hibba tace Allah yasa su gane aydarh tace Ameen kafin ta mike tace auntie bara nayi sallarh hibba tace tau shknn shiga nima banyi sallan ba aydarh tace ina ma da alwalla fa hibba tace tau shigo bedroom din “ Aydarh ta girgiza kai tace kibani prayer mat zanyi anan kawai hibba tace tau shknn abun salla takawo mata kafin ta wuce bedroom din ita sai datayi alwalla kafin tayi sallan “har ta fito aydarh na zaune kan prayer mat zama hibba tayi kan kujera tana kallon aydarh tace auntie aydarh ko muyi
wainan flour shi nake son ci? Aydarh ta gyada kai tace tau shknn auntie hibba tace tau yallabai yana ci ne? Aydarh ta girgiza kai tace erh yana ci amma ba sosai ba gaskia ranan auntie hafsa ta yi manah amma bai ci ko biyu ba nidai kam ina so sosai, hibba tace dr kam na so Sosai ko sai ki girka masa ko jallof din macaroni? Aydarh tace ah’ah auntie kawai ayi wainan idan mukaje gida nayi masa girkin “hibba tace aaaaa aydarh kar nasake ji kar ki sake barin mijinki yawuce lokacin cin abinci bai ci ba saidai idan baya nan yanzu kinsan sai sun kwaso yunwa ga rana kafin su dawo kuma har sai kunje gida kafin kiyi masa girki?aydarh dai tayi shiru tana wasa da rings din hannunta bata ce komai ba Hibba tace muje sai kiyi greating kayan miyan akwai vegetables ma hadda kifi sai ki saka masa “Aydarh dai tace thank you auntie kitchen din suka shiga Hibba ta ba aydarh duk wani ingredients din da zata masa girkin “ kafin ta cigaba da harkan wainan flour ta “Hibba dai takasa dauke idonta daga kallon aydarh ganin yarda take girkin komai tsaf komai cikin kwanciyan hankali, sunayi suna fira aydarh dai sai kokarin rike numfashin ta take saboda kamshin wainan flour dake damun ta “can dai tafara jin numfashin ta na seizing ta dai daure tayi shiru hibba kam sam bata ma lura da abunda aydarh keyi ba labari kawai take bata cikin kwanciyan hankali duk da aydarh bata amsata tacigaba da labarin daman tasan haka aydarh keyi “ can dai tafara tari ahankali ahankali hibba tace sannu auntie aydarh mura neba?aydarh ta girgiza kai tana cigaba da tarin ta hibba tamike ganin yarda aydarh ta rike chest tana tari non stop ga zufa dayafara keto mata dasauri takashe camping gas din datake suyan wainan flour daman takusa gamawa,karasawa tayi kusa da Aydarh tana tambayar lafiya ko sarkewa tayi cike da karfin hali aydarh ta girgiza kai idonta yayi ja tana jan numfashin ta dakyar “har tama kasa breathing din da kyau hibba data gama rudewa tace aydarh ko dai kinada asthma??????da kyar aydarh ta gyada mata kai aikau dasauri hibba takama ta suka shiga parlor banda inalilahi waina illahil rajiun babu abunda hibba ke fada sai jera ma aydarh sannu take tama rasa yarda zatayi ita Wallahi ganin yarda aydarh ke fighting da numfashin ta yasa hankalin hibba karasa tashi kama aydarh tayi tana kara gudun fanka kafin ta sake ta duk ta rude tana dage curtains din parlor da wani irin speed tashiga daki tayi dialing number dr ibrahim bugu daya ya dauke “yawani langwabar da murya yace did you just started missing me roohi?a rude tace dr kuyi sauri ku dawo Wallahi banyi tunanin aydarh is asthmatic patient ba kaurin wainan flour yasa asthma tashi dan girman Allah ku dawo “kashe wayan tayi ta koma parlor tacigaba da jera ma aydarh sannu Wallahi iyakan tashin hankali Hibba ahankalin ta yatashi bata masan taya zata taimaka mata ba kafin su iso duk ta gigice “ addua tacigaba da tofa mata “ .wallahi malik gani yake mai keken baya sauri du kinda hankalinsa yayi dubu yatashi dr ibrahim ke ta basa karfin gwiwa yayi hakuri ba abunda zai faru da ita amma ina bayaji sai ruwan masifa yake zubawa mai keken “shidai bawan Allah sai iyakan bakin kokarinsa yake daga mai keken har dr ibrahim sun masa uzuri saboda ganin duk yarda ya gigice “sunata basa magana “ ai suna isa kofan gidan dr ibrahim ko jiran mai keken ya tsaya bai yi ba ya dire “cike da sarfafa yake tafiya daga kansa kaga cikaken karfafan namiji mai ji da karfi gashin kansa har kwantowa yakeyi “sallama yayi yashiga aydarh na rungumai jikin hibba duk ta gama galabaita, tana ganinsa “kwalla yasauka idonta ai hannu yasa kawai yayi sama da ita kafin hibba ta mike ta zira mata hijab dinta “kaman baby haka ya fita da ita rike hannu dr ibrahim da bai sallami mai keken ba yabasa hanya shiga da ita rike a
hannunsa duk ya rude ya gigice dr ibrahim yashiga gaban keken ,mai keken ya tayar suka wuce clinic”dr ibrahim yakira hibba yace ta rufo gida tasamu keke ya kawota clinic kafin kashe wayan “ Wallahi malik kaman ma ba dr ba don yakasa yin komai ma kallonta yake kawai har suka isa clinic din yafito da ita 2k dr ibrahim yafito ya mikawa mai keken yayi masa godiya da adduan Allah yabata lafiya dr ibrahim ya amsa masa kafin ya rufawa malik baya ,emergency room din malik yashiga ya kwantar da aydarh kan gado hawayen dake fita a idonta da yanda take fighting da breath dinta yasa jin wani irin rauni kawa isai hawaye sharrr Wallahi dr ibrahim kasa boye mamakinsa yayi malik kuma kuka?ganin malik bai ma da niyyar yin komai don dr ibrahim ya fahimce malik yamance waye shi yasa kiran nr saratu dake nan reception dr hafsa bata kai da zuwa ba,bai ce wa malik Komai yabarsa nan rike da hannuta yayi kasa da kansa itama ta rike hannunsa sosai kaman zaa kwace mata shi, dasauri dr ibrahim da taimakon nr saratu sukayi kokarin daidaita numfashin aydarh cikin few minutes sukayi mata allura cikin abunda bai fi ten minutes bacci ya dauketa ahankali tafara ajiyan zuciya a wahale kadan kadan sai lokacin malik da idonsa yayi jawur ya dago kai,yana kallonta ko dauke ido babu hannunsa yasa yagoge mata hawayen dake nan a fuskan ta kafin shima yadago hannunta yarike yadinga goge hawayen fuskan sa da hannunta “ sai kallonta yake wani irin kyau tayi masa mai daukan hankali lashes dinta sun tattare wuri daya wanda ruwan hawaye ya jikasu, dr ibrahim daya shigo dakin ya kalli malik yace katashi muje masallaci in sha Allah she will be alright yallabai ai kasani dai malik kaman bazai tashi ba dan kona second daya baiyi missing kallon fuskanta ba ahankali yasaki hannunta kafin yasaka Hijab dinta ya rufe mata jikinta dr ibrahim dai sai kallonsa yake, ahankali yake bin bayan dr ibrahim duk yayi wani kala a bakin kofan clinic suka hadu da hibba dauke da basket din Abinci gaishe su tayi kafin fuskanta cike da damuwa ta tambaye su ya jikinta dr ibrahim ne ya amsa mata da sauki kafin ya nuna mata dakin yace tana ciki ta samu bacci hibba tace musu tau kafin da sauri ta nufi hanyar dakin dr ibrahim yabi ta baya yana karban basket din hannunta shidai malik yayi shiru ya lumshe ido,sai da yakai mata basket din kafin yadawo ya tarar da malik nan inda yabar sa suka wuce masallacin magrib,hibba na shiga ta zauna kan plastic chair din dake dakin tayi shiru Wallahi duk tadamu sai taga kaman ita tasaka ta cikin wannan halin gani take kaman ita taja mata duk wahalan,basu suka dawo bas ai da aka gama Isha’I ,hibba nayi musu sannu da zuwa dr ibrahim kawai ya amsata yana tambayar ta ya mai jikin ta farka?hibba ta girgiza kai tace aaaaa bata farka ba fa bacci kawai take dr ibrahim yace tau masha Allah Allah yakara lafiya Hibba tace Ameen kafin tace bara nasaka muku abincin dr ibrahim yace bara muje office nan kar motsin mu ya tayar da ita, yakalli malik yace yallabai muje office “sai sannan malik yadago ya girgiza kai yace kuje ibrahim zan zauna da ita zanci abincin anjima in sha Allah dr ibrahim yayi shiru yace tau shknn yallabai Allah yabata lafiya, malik yace Ameen hibba ma addua tayi masa kafin ta dauki warmer wainan flour da plate sai rubber yaji tabar dayan warmer shape pasta dasauran plates din tabi bayan dr ibrahim bayan fitarsu malik ya kwantar da kansa bisa gadon ya lumshe ido ,har wajan ten bata farka ba lokacin har dr hafsa ta iso “dr ibrahim yayi masa sallama yace zasu tafi in sha Allah gobe daga masallacin asuba zai shigo ya sallamesu ya mikawa malik sauran drip da alluran ta na daran tunda in sha Allah da angama dosage din suke nan hibba ta kalli malik kafin tace am sorry yallabai bada gangan nayi
ba,malik yayi murmushi yace ba komai amarya mungode sosai Allah yasaka da alkhairi hibba tace babu komai y
allabai Wallahi duk anzama daya.
Sai wajan karfe sha biyun dare aydarh tafara bude ido ahankali kanta yayi mata masifan nauyi “ahankali tasauke idonta kansa hannunsa rike da hannunta dake da karin ruwa,ya kifar da kansa kan