Author : Nana Maryama Category : Romantic Hausa Novels
mutun? Malik yace babu gaskia,inna tace tau nan da kake ta sauri daman dai ba kayi niyyar zuwa gidan nawa ba kenan? Malik ya girgiza kai yace aa fa daman dai da yamma nayi niyya zanzo aie, inna tace tau shikenan amma yanzu sake sa man lambar sai ka kirani gabana naji kar ka sake sa wata kuma na kira ama kulle layin baki daya ka cuceni, malik yayi murmushi yace tau shikenan,sabowar number shi yasaka ya kira sai da tayi ringing inna ta yarda kafin ya kashe tace tau yi man sebin yace tau mi zan saka?tace rubuta audu kawai da manyan baki daman hafsa ce ke gano man, itama dai sai ahankali ba yarda nake da itama ba,sai kuma tayi kasa da murya tace inaga itama fa ba wani iyawa tayi ba karatun nan Amma kafin tagano man lambar mutane sai nashiga ukku shidai malik yayi shiru bai ce komai ba,inna tace tau sai anjima sai kazo ka gaishe da mai dakin naka,bata jira amsar sa ba tayi gaba. Suna fitowa daga sallar azahar shago ya wuce yasiyo flour da yaji dakake a rubber sai groundnut oil da star kwai yasiya kwara 4 yabiya kudin yatsaya wajan mai cefanan daya siya dazu suka gaisa dashi dan ya gane sa,fresh tomatoes ya siya da albassa anan yake tambayar mai cefanan idan zai siyi kuka da kanwa mai cefanan yace masa yaba yaron sa yashiga gidan dake kusa dasu ana siyarwa ya siyo masa,10mins sai ga yaron yadawo yasiyo godia yayi ya karba ya wuce, ruwa ya tara ya daura kafin ya kwaba flour danwake zaiyi wanda favorite food din sa ne ya iya danwake sosai abubuwan da bai iya ba kadan ne a girki yana tafasa ya jefa dan waken 30mins ya dauka yagama
ya wanke tukunyar tunda kwara dayace Bayan ya juye danwaken a warmer ya mayarda da tukunyan ya wanke kwan ya saka kafin ya yanka tomotoes din da albassan kanana yarda yaga ummi nayi idan anyi dan wake tass ya hada komai kafin ya zubawa aydarh a plate ya bare kwai kwara uku ya zuba mata a nata plate din,zaune take kan carpet, kallonta yayi ya dauke ido kafin ya aje mata plate din agabanta bata dago ba kanta nakasa amma taga abunda ke cikin plate din, this time ma kamar dazu ledan drugs dinta ya kawo mata kafin yaje kitchen ya dauko mata r
uwa .
Inna tace oyoyo ga audu ga audu ga audu maraba, ganin har angama la’asar baka shigo ba nayi tunanin ma baka zuwan,malik yace aaa zan shigo daman barin nayi yamma tayi kafin nazo, daki tashiga ta sai gata da jug da cup a hannu fura ce ciki mai kyau tasha Nono sai kamshin kayan yaji ke tashi ta zuba masa a cup tace gashi kasha daman kai na dama ma ita,karba malik yayi yabi furar da kallo yace nagode kwarai inna, da sallama dr hafsa tashigo cikin shigarta tsaf da lab coat sai jikkarta da wayanta a hannu masa mata malik yayi inna ta tsaya tana kallonta ko kiftawa babu, sai ta dauke kai,dr hafsa tayi murmushi daman dr ibrahim yabata labarin komai itama kanta ba karamin mamaki tayi ba jin wai har inna taraka malik din siyan gas,tace yallabai ashe dai anguwarmu daya,ina wuni ya mai jikin?shima malik dan sakin fuskar sa yayi yace Alhamdulilah Doctor,inna tace wacece wannan kuma, sai kuma tayi kasa da murya tace ina kasan wannan kuma?ita fa haka take a duniya burinta taga nasan wani itama tace tasan shi,malik yayi murmushi yace a asibitin su aka kwantar da mai dakina,inna tace ohh ,sai kuma ta kalli Doctor hafsa da ta daure fuska tace nan dakika tsaya kamar wata yar sanda bazaki shigo ba komi? Doctor hafsa batace komai ba tawuce tashiga daki “inna tasake kasa da murya tace itace nake gaya maka dazu nidai ba ruwana jikata ce diyar babban dana ce daya rasu,nake riko Malik yace Allahu akbar Allah yayi masa rahama inna tace Amin, babu ruwanka da ita rashin mutunci wanda ta mance ne kawai ke bata mun ga girman kai,kaii hakuri nake kawai billahi amma daya yanzu na kai kaina gidan marayu na bar mata nan din, malik yayi murmushi yace bazaayi haka ba ai
.
Inna tace yanzu fa nan da ta shiga kafin ta fito sai wani iko daga Allah, malik yace hutawa take kinsan gajiyar aiki “inna ta bi malik da kallo kafin ta kalli kofan dakin dr hafsa tace tau mutun idan iko da sarauta yake ji ai sai yatafi can gidan sa yayi “Amma babu katuwar da ta isa ta dinga man mulki a gida “malik dai yayi shiru yana sauraron inna,mikewa tsaye tayi tashiga daki,can sai gata ta fito hannunta rike da kula da kuma jug “tayi kasa da murya tace bara nashiga na kai mata abinci saboda idan bani na kai mata ba saidai fa yunwa ta kashe ta wallahi bazata fito ta dauka ba,malik dai nata kallon drama inna, inna ta kalli dr hafsa tace nasan daman dawuri zaki taso shiyasa nace bara nayi kokarin gama girkin da wuri ita dai dr hafsa bata kalli inna ba ta cigaba da linke lab coat dinta, inna tayi kasa da murya ta kalli kofa tace wai zararra ce ni ko mi ina magana kinyi shiru kin maidani kamar wata yar iska dai, dr hafsa tace wai ba naga bak’o gareki ba? Ki fita ki same sa manah abinci ne dai kin kawo kuma nagode, sai nafara yin wanka kafin,inna ta tsuke bakin ta tace tau Allah yabaki hakuri bara na fita kafin ki zage ni kuma”,tana fitowa tace yawa daman ai na gaya maka nice daidai da ita, malik yace ayi hakuri dai ni bara na koma naga magrib ta kusa, inna ta washe baki tace tau ba laifi ka gaishe da mai dakin naka nima nasamu lokaci sai nashigo na dubata, har kofar gidan inna ta rako sa labari kau kamar kar yatafi inna takasa shiru. 6:00pm daidai yashigo gidan ,Ramlah na zaune a ventilation dinsu ita da mahaifiyar
ta sai dayar matar part din fadila da yaranta biyu maza da mata, su biyar ne wurin amma kamar mutun dari fada suke sosai kan Ramlah ta bige yaron fadila musa aiken sa tayi bai je ba tayi magana yace bazaije aiken karuwa ba,ta dakesa uwarsa tace bazata yarda ba ai gaskia ya fada, shine suke faman wannan masifar, ko kallon su bai yi ba yayi wucewar shi part dinsa, dawani irin mayyan kallo Ramlah ta bisa ta mance ma shaf da abunda sukeyi, har sai daya shige building din part dinsa ta daina hango shi domin an zagaye ma kowa ventilation dinsa, fadila tayi gyaran murya tace haka fa aka yi, Ramlah ta maka mata wata wani shegen harara tace tau uban miye yayi ruwanki da ni?maman Ramlah tace duk ba wannan ba kuyi shiru, tayi kasa da murya tace ma fadila “ shin fadila kinga abunda nake gani kam? Fadila data saki baki tana kallon maman Ramlah tace nagani tun jiya abun ke ci na hakuri nayi kawai banyi magana ba wallahi, maman Ramlah tace tau wai balarabe ne ko mi wannan din? Fadila tace wallahi tun jiya dana ganshi nake tambayar kai na tau baki nan shiyasa na ja bakina nayi shiru (kamar basu bane ke fada yanzu) Ramlah ta tabe baki tace ba fa balarabe bane kawai dai haka yake, maman Ramlah tace ki bari baban musa yadawo kila ma ji magana daga wurin shi,fadila tace in sha Allahu saidai idan basu hadu dashi ba amma nasan sai ya tambaye shi wayeshi,kin fa san halin sabo, Ramlah tace ku kwantar da hankalin ku zan binciko maku komai ni fa ai naga miji wurin nan, fadila ta tabe baki tace ko makaho yasan wutsiyar ragumi tayi nesa da wuyan zakara “ maman Ramlah tace aa fadila mi kike nufi?fadila tace babu komai ba
ra na tafi kafin sabo ya shigo,
Sai daya fara shiga kitchen ya daura ruwan zafi kafin ya fito knocking yayi saboda ya taba kofar yaji ta a rufe, sai dayayi almost 8mins atsaye yana knocking kafin a bude kofar ahankali ta bude masa kofar ta juya ciki, bin ta yayi da kallo ganin abunda tayi masa a rayuwa baya son raini ya tsani rashin kunya,bai ce mata komai ba itama hakan ko kallon sa batayi ba kanta na kasa tana wasa da Expensive diamond ring din hannunta,plates din daya kawo mata abinci yabi da kallo ba laifi taci sosai saidai ga yajin nan gefe guda da alama bata son yaji dan bata ma taba shi ba saidai star din kawai eggs din kuma daya kawai tace ga sauran two din nan danwaken ma gashi nan ledan maganin ta ya dauka yanzu ma tasha daga yau ya kare daman na 3days ne kawai, kallonta yake ko kiftawa babu so yake ta dago idonta yayi mata concrete warning kan rashin sallama amma tak’I baya jin kuma sai iya yi mata magana tayi shiru ta kyale sa saboda ko saar maryam auta bata wuce ba bazaiyi tolerating shits ba, bai ce komai ba ya kwashe plate din ya fita dasu da harara ta bi bayansa a ranta tayi karamin tsaki , kwanciya tayi ta rufe idonta daman can bata saba zama cikin mutane ba ,shiyasa bata jin kadaici ‘Ko a gida sai ta wuni bata fito ba,a can school Cyprus daman idan ba lectures zatayi attending ba bata fita daga campus dinta, her life is always private bata da friends bata jin magana ya hada ta ko sau uku ne dawani a school din tun zuwan ta duk da yanda school din yake akwai yara masu yawa yaran masu hali ne,amma bata gani akwai wanda zata iya zama dashi balle har a kai da wani abu wai friendship.sai da ruwan yatafasa kafin ya dauko bucket ya juye mata, this time ma bata amsa sallaman shi ba, bai ce komai basai da ya kai ruwan toilet yafito ya zuba mata ido mistakenly ta bude idonta suka hada ido dashi wani irin fadi gabanta yayi tayi maza ta saukar da kanta kasa, ya kafe ta da waennan idon nashi , cikin tsare gida da muryan nan tasa babu alamun wasa yace “baki iya amsa sallama ba hala ? Sai taji wani iri da tambayar tasa abun yazo mata wani kala,shiru tayi batace komai ba,
yace “daga yau kar nasake sallama naji kinyi shiru “ bai jira amsarta ba yayi ficewar sa daga dakin, sai time din ta dago kanta idonta cike da kwalla , umarni yake bata kenan? Ita yake ba umarni ? Saboda yaga bata da kowa sai shi babu inda zata je sai wajan shi? Who is he? Mi yake daukar kanshi? Mi ma yake nufi da ita ne wai? Tayi ma kanta tambaya kusan goma amma bata da amsar ko daya,hawayen ta tasa bayan hannu ta share tass tayi ma kanta alkawarin baza ta sake takura kanta ba ko daura ma kanta damuwa,kuma shima bai isa ya daura mata damuwa ba ko ya juya ta,idan girman kai yake ji dashi ta fisa idan izzgili yake ji dashi ta fisa, hararar datayi ma kofan dakin sai ka rantse da Allah malik ne tsaye a gabanta, toilet ta shiga nan taga bucket din ruwan zafin da ya ajiye mata, kallon bucket din take ko kiftawa babu ita yakawo ma wa kenan? Tunda taga shi baya using da wannan toilet din,tsaki ta saki kafin ta fito cikin dakin ta cire kayanta ta dauki towel ta daura, Sai da tayi wanka tsarki dan tagama period kafin tayi wanka ta fito, kamar dazu yanzu ma Vaseline da tashafa da perfume din abayar ta mayar ta koma ta kwanta. Daga masallaci daya fito garin dinke yake da hadari tunanin abunda zai yi masu na dinner yake mai awaran daya gani a gefen gidan su kawai ya yanke shawaran siyan masu,sallama yayi yarinya ta amsa wurin a share yake tass da alama awaran na da tsafta na 500h yasiyan musu ya wuce. Kofar dakin ya tura this Time bata saka key ba sallama yayi yaji shiru bata amsa ba,karasa shiga dakin yayi ya ganta tana salla,murmushi yayi iya lips dinsa yafice daga dakin a plate ya saka mata awaran kafin ya zuba tasa a warmer , sallama yayi ta amsa sa can kasan makoshi kamar wace throat din ta ke ciwo mamakin halin yarinyar yake,ta idar da sallan still kuma tana zaune kan prayer mat din “ bata tashi ba ajiye plate din yayi ya fita
.
TWO WEEKS LATER
Zuwa yanzu malik ba karamin sabo yayi da inna ba sosai suka saba kullun ne da yamma sai yashiga gidan indai kau baije baya tare da dr ibrahim suka fita wanda yanzu ya zamar masa kamar wani dan uwa tsakanin sa da aydarh har yanzu babu mai ma dan uwansa magana, kullun ne sai yadafa ma ruwan wanka ya kai mata abinci kau babu fashi kullun sai ya girki duk wani gyaran gida shi yakeyi,ya fuskanci abubuwa dayawa game da ita,wani lokacin idan tayi wani abun dariya take ba sa akwai ranar da inna ta matsa mashi sai sunje ta ga mai dakin sa, suka tafi tare shiga yayi daki yasame ta tsaye inda take tsayuwa kullun tana kallon mutanan gidan,bai san mi zai ce mata ba kawai yasa shi cewa ga innata nan zaku gaisa batayi magana ba dan batasan wace inna ba. Kayan ta kala biyu ne daga gown din atampha sai abayar ta wllh ta gaji da saka su bra daya take using idan tayi wanka ta wanke sai ta zauna haka har sai ta bushe sannan ta mayarda,abayar ce jikinta ta daura kallabin akai fita parlor tayi wanda bata cika zama a nan din bas ai idan baya nan ko kuma an dauke nepa tazo ta tukure kanta waje daya shidai yana ganin abunda takeyi baya tankata ya fahimce yarda take tsoron duhu hakan yasa shi siyan mata torchlight indai babu nepa ta dinga haske haske kenan, Ahankali take tafiya har ta iso cikin parlor kasancewar yamma ce akwai nepa hasken globs din parlor sun haske fuskarta tarr kullun kara kyau take sometimes malik har mamakin ta yake yakan tambayi kansa wai mata haka suke ko kuwa? Wani lokacin dr ibrahim neke yawon kawo masa zancan mata da zamantakewar aure har wani zakewa yakeyi shima yakusa shigo daga ciki yaji abunda suke ji, shidai malik saidai
yayi murmushi kawai har mamakin dr ibrahim yakeyi shi baya kunyar ko wace magana “. Murmushi kadan a fuskar ta,ta zauna kan carpet din parlor tana gaishe da inna dake ta faman zara ido kamar wacce aka tsikara haka inna ta mike tsaye tana kallon malik da aydarh tasake bude idonta sosai kafin ta koma ta zauna tace Allah mai halitta sai kuma ta kalli malik tayi kasa da murya tace audu ashe kafini gaskia danace boyun matarka kake ashe dole ka boyeta, masha Allahu sai kuma ta washe baki tace tsali yo Allah na tuba audu ku wannan kamar dai ku aka hada ma wa, sai kuma taja bakinta tayi shiru tace ah babu ruwana balle ace nayi sabo amma wannan dai wannan dai sai kuma tayi shiru,shidai malik sai kallon inna yake aydarh ma tarasa abunda zata ce mata, inna tace ya sunan ta kace?ahankali malik yace ASSIEYERH yarda yafadi sunan kamar da larabci yasa inna kasa fahimta yarda yafada , zata sake magana akayi knocking kofan part din nasu malik yace waye muryar dr hafsa suka ji tana fadan ita ce, bude mata malik yayi inna tadafe kirji tana kallonta tace yanzu kuma haka kika zama ni hajara nabani, tayi kasa da murya tana kallon aydarh tace kiji bala’I daga taji labarin nazo nan har ta biyo ni, dr hafsa dake gaisawa da malik ko ta kan inna bata bi ba, ta kalli aydarh tace patient daga rana ban sake ganinki ba kuma saidai yallabai murmushi aydarh tayi tace ina wuni dr hafsa ta amsa tana tambayar ta ya jiki, labari sukeyi duk da inna ce mai labarin ita dai aydarh murmushi ne nata,malik kau da har yasaba fira da inna biye mata yayi suna fira, ana labari da dr hafsa tayi magana sai inna ta kwale ta sai wajan six suka yi sallama zasu tafi har waje suka rako su dr hafsa da ta daga waya tayi gaba sai inna a bayanta aydarh a bayan inna malik ke can bayan su, har suka fito building din parts dinsu inna batayi shiru ba, ganin tana neman fita yasa shi jawo………
Kallonta yake ko kiftawa babu itama ido cikin ido take kallansa ,kasa yayi da murya cikin tsare gida yace duk ranar da kika kara kokarin fita a haka babu hijab sai na karya ki,yasake ta yafice “anan tsaye yabar ta mamaki ya cikata har kofan gida ya raka inna sannan yadawo, bata parlor yasan cikin daki ta koma, hakan yasa shi yin zaman shi a parlor kwana biyun nan kudin hannunshi sun kusa karewa,shiyasa yake so idan anjima suyi shawara da dr ibrahim kan abunda zaiyi.Dakin yashigo ko kallansa batayi ba yana tsaye kanta “ta turo baki “tace nan da ka tsaya mun akai fa? Malik mamaki ne ya cikasa, sai yaji kamar bai ji da kyau ba, yace dani kike duk yarda gabanta ke faduwa na masifan tsoron shi da yanzu ta yarda tanayi bai hanata ,mikewa tsaye ba tace erh, bai ce mata komai ba ya fice daga daki “ . Kallonshi yakeyi har sai da yayi shiru yace tau shknn na fahimta Allah yakaimu lapia, dr ibrahim yace Ameen “shiru ya biyo baya dr ibrahim yamike tsaye yace bara na fita na jira ka kar time ya wuce,malik ya kalli watch din hannunsa yace har na kusa mantawa ma fa ashe yau ana wasa “ dr ibrahim yace sure kayi sauri mu tafi, fita dr ibrahim yayi kofan gida,shi kuma malik ya juya yashiga kitchen indomie daya dafa masu ya zuba mata a plate sauran tasa kuma ya zuba a warmer, salla take