Da So Kamane Complete Hausa Novel By Nana Maryama.docx

Author :  Nana Maryama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   30 / 111

87K to 90K   out of 332K words

time da wannan abun zata cigaba da kawo abu nan gida idan bahaka bazan sake pardoning dinka ba Allah,tayi folding hannunta a kirji tace miye ma ruwanka da ita da har zata dinga yin girki tana baka? Ya ajiye plates din hannunsa yayi yadaga hannunsa alaman yayi surrounder yace nikam har nagaji ma dafada miki waye ita batace komai ba ta wuce cikin parlor har ta kai bakin kofa zata fita haka babu kallabi, dawani irin speed yajawo ta har sai data tsorata tana kallonsa yace Ko bakinsa kanki babu kallabi ba? Batace komai bay ace da ina zakije haka? Tace fita zanyi na ga warmer din ko tazo ta dauka “sakin baki yayi yana kallonta kafin yace tau dawo ta dauka ma tun dazu “ ya dinga binta da kallo har ta kusa shiga bedroom yace gobe Wednesday da yamma zamuje gidan dr ibrahim “tace “to”kawai kafin ta shige ciki abinci ya zauna sai daya cinye tass sosai yake mamakin yarda ta iya girki har idan yana cin girkinta yana tunuwa da ummi babu sallan dazaiyi ba rok’I Allah ba ya mayarda su wajan familyn sau dayawa yana tunanin komawa amma yasan har yanzu abby bai huce bay asan har yanzu da tabon abun a ransa ahankali ya furta I prayed for the best and I want to prove the best inshaAllah “ kitchen yashiga ya wanke few plates da tukunya datayi girki kafin ya share kitchen din duk da ba dirty yasake mopping,bedroom din yashiga ya iske tana toilet “wankin toilet din take yadinga bin kofan data bari bude da kallo daga waje yace kibani aron bucket dinki zanyi wanki batace komai ba ta karasa wankin bayin kafin ta fito hannunta rike da bucket din sai detergent missing step tayi suddenly ta fadi dabbas akasa, wani irin kara ta yi hankalinsa yayi mugun tashi dasauri ya karasa yadaga ta sai faman kuka take a rude yake tambayan ta taji ciwo ita kam tayi masa banza sai faman rike wrist dinta tana kuka daf ya dauke ta bai sauke ta ko’ina ba sai saman katifa yakai hannunsa inda nata hannun yake kara tasaki saboda yanda yakama wurin da dan karfi hakan yasa shi gane nan ke mata ciwo, dasauri ya mike yabude wardrobe dinsa yafito da man zafi wand abaya rabuwa dashi ko a gida “ dawowa yayi kafin gently yasa hannu yafara dage rigan duk dana jin zafi hakan bai hanata rike masa hannu ba tana girgiza kai ko sauraron ta baiyi ba yakarasa daga riga very irin hadaddan scent ya dage hancinsa kamshi mai sirin dadi very clean undie ta yabi da kallo white, ta runtse idonta sosae gabanta na wani irin faduwa kamar zai fito ta kirjinta,yarda ya taune lips dinsa kaman zai fasa har wani irin zufa yake daurewa tayi har ya kwashe rigan yana kallon inda ta fadin wurin har yayi wani irin red ahankali yabude man zafin yafara shafa mata wani irin ajiyan zuciya ta sauke kafin kuma ta fashe dawani rigimaman kuka zufa ahancinta da gaban goshinta yarda yake shafawa kamar irin yana mata susa amma tsaban rigima take masa irin wannan kukan kusan 25 mins yadaukesa yana abu guda tun tana kukan har tayi shiru Still idonta a rufe gam tana sauraron ikon Allah, har sai daya gama da kansa yamayarda rigan kafin ya mike ahankali yace sannu zai bari,fita yayi daga dakin ya koma parlor kan carpet ya kwanta yana sauraron bugun zuciyarsa dayake ji Kaman an kara sa lumshe idonsa yana karanto addua har sai dayaji bugun zuciyansa ya daidai anan ya dinga zama,sai can ta bude idonta kafin tasa hannu ta goge sauran hawayen kafin tayi lamo tana kifta ido kaman wace tayi wa sarki karya,yaga sama yaga kasa inalilahi waina illahil rajiun sai wani hawayen yasake balle mata duk duniya bayan ita babu wanda yataba ganin mata boobs sai shi ko oum bata taba sai shi gashi yau kuma yaganin mata laps kadan kadan take kukanta har aka kira magrib tana nan kwance,kiran sallarh dayaji yasa ya farka daga baccin daya dauke sa “ahankali yake

motsa bakin yana tasbihi mikewa yayi yashiga toilet sai daya sakar ma jikinsa ruwa kafin yayi alwalla yafito bedroom din yawuce yabi katifan da kallo bata sa karan ruwa yaji alaman tana toilet bude wardrobe dinsa yayi ya saka jallabiya kafin ya saka perfume har zai fita sai gashi ta fito daga bathroom din fuskanta da ruwa alamun tayi alwalla kallo daya tayi masa ta dauke ido, tayi kasa da kansa shima bai kalleta ba yakarasa abunda yakeyi ya wuce masallaci ,ba laifi wrist din yasaki amma har yanzu akwai pain din, samu tayi tai sallarh, ta zauna nan kan prayer mat din bata tashi ba “ ,Da sallama yashigo bedroom din hannunsa rike da leda ya ajiye bai ce komai ba yafita,ledan ta dinga bi da kallo kafin tasa hannu gently ta dauko drugs ne a ciki ‘ sai manya chocolates biyu sai perfume designer kwara daya ta dinga bin ledan da kallo kafin ta ture ledan ta tashi tana bin bango ahankali ta koma ta kwanta kan katifa har kundundune cikin hijab dinta.

Sai wajan nine yashigo da pure water a hannunsa, ya dinga binta da kallo kwance take kan prayer mat bacci take da alama tunda tayi isha’I bata tashi ba, Ahankali ya zauna wajan kanta kafin yasa hannu ya shafa cheeks din ta,yasan bata da nauyin bacci,shiyasa bude idonta tayi ahankali ta daura kan fuskan shi,murya can kasa yace wake up tashi tayi tana ya mutsa fuska da alama har yanzu wurin nayi mata zafi zama tayi ta dauke kanta,ledan da ya ajiye “yasa hannu ya dauka kafin ya ciro drugs din ya balla yabata hannun ta ya dinga bi da kallo har yanzu lallan kamar yau akayi sa kullun kara budewa yake yana kyau, maganin ta karba kafin ta rufe ido sai datasha dukka biyun kafin ya mike ya fita binsa tayi da kallo har yafita kafin ta jingina jikin wall din ta sa kanta cikin gwiwa ta fashe da kuka kamar wace aka daka, shi ya tashe ta sallarh yau har yaje masallaci yadawo bata farka basai da ya shiga dakin yasame ta kan carpet tana bacci girgiza kai yayi yace sturbborn bea “long nose dinta yaja tasa hannu ta rike hannunsa, yace tashi kiyi sallarh sallan ta tashi tayi, breakfast yahada kafin ya gyara gidan duk da babu wani dirty dayayi, dakin yashiga yasame ta tana gyaran katifan “bata kallesa ba kanta kasa tace Good morning “shafa kansa yayi kafin yace morning ya jikin yadaina ciwon yandaa yayi mata tambayan cike da kula sai taji wani iri kaman yanda abba ke mata idan bata da lapia kallonsa tayi kafin tayi raurau da ido tace har yanzu da zafi fa,ido yazuba mata kafin ya matsa kusa da ita yace mugani girgiza masa kai tayi kafin dasauri tace ah’ah, bai ce komai ba yasa hannu ahankali ya jawo ta yasata a chest dinsa ya zage ta, hannunsa yasa ya dage rigan “ kafin yabude wurin yayi tunanin akwai ciwo wajan sai daya bude yaga babu wani ciwo red din ma dawurin yayi yawashe sai kadan “ babu wani kumburi wurin “ hannunsa yasa yashafa kadan tasaki wani kara bai ce komai ba ya mayar mata da riganta yasake ta kafin yahade rai yace eyyerh tunda har yanzu ma akwai ciwo wurin sai mu hakura da zuwa can gidan dr ibrahim din wajan hibban dasauri ta rike masa hannu kafin wani kasa da murya kaman zata fashe da kuka tace ah’ah fa zai daina zan sha maganin “malik yamayarda fuskan shi babu yabo babu fallasa yace tau ko na siyo allura ne nayi maki? Dasauri ta girgiza kai tace ah’ah Allah ya daina kadan nake ji, malik yace tau shknn muje ki ci abinci tare suka fita parlor ta zauna yashiga kitchen yafito da breakfast din a tray tea ya hada mata rabin cup sai eggs dayayi frying ‘ yasa mata a plate, ya ajiye mata gabanta ya tura mata bread sai daya hada nashi kusan cup daya kafin yabude bread din yafara ci, ahankali take shan tea din egg din ma kadan taci, yana lura da ita, bata shanye ba ta ajiye bai ce mata komai ba har yagama kafin yace kije ki dauki maganin ki sha kitchen din ta shiga, ta dauki ruwa tawuce dakin.

Hibba tace dana ga har two nayi tunani baza ku zo ba,Aydarh tayi murmushi tace ah’ah zamu zo, dr ibrahim yace nasan ai cewa zaiyi baza ku zo ba,malik yace sai gashi munzo nabaka kunya koh? Hibba tace yanzu dai tunda kunzo ka goge laifinka dasai dai ku ganmu malik yace ahh amarya bata fita ai , hibba na kallon dr ibrahim ta gefen ido tace aaa yau fa kwana nan five lafiya lau zan fita dr yace ai ke da fita sai kuma wani year din dariya akayi kafin hibba ta shiga kitchen tayi serving dinsu abinci da chops sai drinks din da dr ibrahim yasiyo saboda zuwansu malik din anan parlor ta ajiye musu nasu kafin ta kai ma aydarh nata bedroom ,hannuta ta kama suka shiga,hibba ta bi aydarh da kallo kafin tace kugun ke ciwo ne naga yarda kike tafiya? Aydarh tace erh faduwa nayi, hibba tace eyyerh sorry aydarh tace yauwa fira suka cigaba da yi kafin tace yawwa aydarh ya magani

n nan ni ai wllh kamar.

Kaman zan mutu hannu mutumin can babu kalan rokon da banma Doctor ba amma bai ji bai gani abun har yaso yafi karfina ma “tafada kaman zatayi kuka ,aydarh kanta nakasa tsaf ta fahimce labarin hibba zuwan yanzu yawancin abubuwa tasani ba kaman da,da hausar ma bata fahimta sosai, batace komai ba tayi shiru hibba tayi murmushi tace hala ke har baki so ki tuna nasan nawa mai sauki ne kanki dan Wallahi har tausayin ki nake idan na kallesa “ Aydarh ta dago kai tana kallon hibba kafin tayi kasa da murya tace,korh? Hibba tace Aydarh amma ai tunda kin saba shikenan tunda dai mijinki ne babu yarda zakiyi dashi, aydarh tayi shiru kafin murya cike da rauni tace ,jiya ma dana bige wrist sai kuma tayi sauri tayi shiru kaman wace ta tunu wani abu,hibba ta wara ido tace kikayi shiru ohh jiyan ma duk da ciwon abun nashi ba sauki?aydarh da har hawaye sun fara sako mata ta gyadawa hibba kai,hibba ta girgiza kai tace hakuri zakiyi tunda Allah yasa haka yake daya tafi yana neman wasu a waje fa kinga ai kwara ke ki daure koh?aydarh ta gyada kai kafin tashare hawayenta “tana so ta tambayi hibba wani abu amma kunya da nauyi sun hanata tambayar ta cigaba da wasa da zoben hannunta hibba tace k ici abincin fa kar ya huce naga tun dazu kadan kika ci,aydarh ta girgiza kai tace ah’ah ya isa,hibba ta bita da kallo tace yanzu dan abincin nan dakika ci har ya isa? Hibba tace tau auntie aydarh ko dai ciki ne gareki? Aydarh ta girgiza kai tace Allah ah’ah kawai na koshi, hibba tace tau shknn bara na ajiye chops din su sai nayi maki packaging a leda idan zaku tafi gida sai ki tafi dashi aydarh tace to “nagode “ abinci hibba ta dauka tasanya hijab dinta ta fita suna parlor suna kallon kwallo sannu tayi musu suka amsa ta wuce sai data dawo malik yace madam yarinyar nan bata cin abinci yau cikin ta tun rabin kofin shayi ne ko zaki taimaka kisa taci?hibba tayi murmushi tace Wallahi nagani kadan taci nayi nayi da ita takara tace aaaaa malik ya gyada kai kafin ya juya ya cigaba da kallonsa,dr ibrahim ya kalli matar sa yace tau ko wani abun zaa samu mata ko fura can wajan iya sai nakira rabiah ta miko?malik ya girgiza kai yace ko ankawo bazata Sha ba kawai a rabu da ita “hibba tace aaa yayah malik ko a jaraba karbo mata manah?malik ya sake girgiza kai yace tunda tak’I bazata cin ban e komi aka kawo “dr ibrahim yace tau shknn,hibba dai ta koma bedroom din tana kallon Aydarh kafin tace ohh ni ke kam abinci ne makiyinki tau ana haka mutun yadinga zama da yunwa har kin saba shiyasa ga cikin ki nan kullun kaman babu hanji yanan a shafe very flat, Aydarh tayi murmushi kawai kadan bata ce komai ba,hibba ta zauna tace tau baki da kawa anan kano aydarh ta girgiza kai kafin tace erh auntie hafsa ce kawai muke magana sai inna sai few students a class din mu, hibba tace Allah sarki islamiya? Aydarh ta

gyada kai hibba tace ai yafi sauki aydarh naji dadin da baki ma da kawan, amma Banda nan gidan da gidan inna shima bai zuwa ko’ina,aydarh tabude hannu alaman bata sani ba, hibba na kallonta tace baku da saurin sabo da mutane ne kawai “Aydarh ta gyada mata kai,kafin hibba tace idan zaku tafi zan baki wani perfume ki dinga amfani dashi kinji?aydarh ta gyada kai tace to nagode “.malik yayi shiru har sai da dr ibrahim yagama bayani kafin yace kayi kokari ranka ya dade dr ibrahim yace amma fa har tsoro naji nayi tunani ta suma fa Wallahi,malik yawara ido yace kai haba Allah yakare dai Dr ibrahim yace Ameen ni fa har bana son hutun nan yakare na koma clinic Allah,malik yace tau ai sai kadawo gida da zama kabar musu aikin “dr ibrahim yace kai wuyanka bakan magana kaman wani mai nama lallashi na naso kayi malik ya hade rai kafin yace tau sannu ASSEIYARH “dr ibrahim yayi wani kalan dariya yace oh ita kawai zaka iya lallashi kenan malik ya gyada kai bai ce komai ba ya cigaba da kallonsa dr ibrahim yace kai dinnan da shegen masifa har ita din baka wani lallashi hakuri kawai take dakai “Malik ya mike ya zuba hannunsa a aljihu yace tau idan batayi hakuri ba sai tayi hauka tunda duk duniya bayan ni bata dawani mijin aie “dr ibrahim yabisa da kallo har yafice kafin shima yadauki wayansa yabi sa baya,a kofan gida ya gansa yace wai tun yanzu zaka tafi can din?malik ya gyada kai yace tau muje tare “bai ce komai ba suka juya suka tafi,Allh musa yace malik kaji kiran gagawa ko?malik yace ehhh sir ‘Allh musa yace tafiya zanyi na kusan five months abuja “malik yace Allah sarki Allah ya tsare yabada sa’a Allh musa yace Ameen kafin yace malik saidai fa kayi hakuri amma zaa tsaya da aiki “ har sai na dawo sauran works din duk nayi musu bayani a jiya already daman duk karshan shekara ina wannan tafiyan sun sani, kafin nadawo sai kasamu wani dan abun yi saboda ka samu abun rike kanka da mai dakin ka,malik yayi shiru kafin yace Alright sir “Allh musa yatashi ya shiga daki kusan ten minutes kafin yafito hannu 20k ya mikawa malik yace gashi ba yawa Allah yasa maka da alkhairi yabaka abun yi nagari dr ibrahim yace Ameen yallabai sallama sukayi suka fita, dr ibrahim yace yanzu miye abunyi yallabai? Malik yayi shiru yace ni kaina ban sani ba dr ibrahim yace in sha Allah,Allah zai kawo mafita let’s keep praying yafada yana patting shoulder dinsa, ba gida suka wuce bas ai dasu ka biya general hospital zasu duba wani abokin dr ibrahim dake jinya can.

Cikin firan dasukayi yau aydarh kaman wani sabon class ne tashiga domin kau hibba ba ruwanta babu wani abu datake sayawa ko boyewa aydarh komai yazo fada mata shi take abu dayawa mamaki yake bata wai duk shi malik din ke da wannan matsayin? Ikon Allah akwai questions dayawa datake son yiwa hibba amma nauyin ta yahanata duk firan yawanci hibba keyin abun ta, hibba tace duk irin fa wahalan dazaa baka labari baka tunani yakai haka sai kaji da kanka billahi,mudai Allah ya tsallakan damu,aydarh tace mi? Hibba tace shi wajan disvirgin din Aydarh tasauka da kanta kasa gabanta yayi wani irin faduwa batace komai ba tayi shiru hibba tace hmmm ni har bana son tunu zafin Doctor kanshi yaji tausai na shiyasa har yau said ai a tsaya sama sama Amma can kam sai nakara hutawa “duk nasan yau dawuya ya hakura jiya dakyar nasamu yayi bacci fa shima sai da boobs a bakin shi Allah,Aydarh tawara ido bata masan ta maimaita abunda hibban tace ba tana bude manyan idonta tabarakallah,hibba tace Wallahi kinsan dai zafin da ake jib a,ita duk tunaninta aydarh saboda zafin ne ta firgita Ko tausayinta taji,hibba tace Ku ai inda sabo ma kun saba mu ma zamu saba ahankali, aydarh tace eyyerh sorry tafada

tana sukunyan da kanta kasa, can hibba tace auntie aydarh kinji dadin jikinki ke kam Allah “Aydarh tace kai haba, hibba tace Wallahi fa kiji ki fa idan ba rashin tsoron Allah na maza ba shikam ya malik mi zai gani ajikin wata Allah natuba billahi ban taba ganin structure mai kyau ba irin naki ban taba ganin skinny mai kyau ba kallan naki ke wllh ban taba ma ganin abu mai kyau ba irin ki, Aydarh tayi wani dariya hibba tasaki baki tana kallonta kafin tasa hannu ta rufe bakinta Still takasa daina dariyan tace you are funny Wallahi auntie hibba, ke kam ai kinada kyau ku kullun kullun sai ku dinga cewa abu daya, tafasa tana rufe fuskanta, tana dariya “hibba tace ai yayah malik nasan a rana sai yafada sau dubu kema haka shima ai yanada kyau da kinga sa kinsan jinin ku guda wannan yaran ku ai said ai ku dinga boyesu billahi saboda baki, aydarh dai batace komai ba can ta mike tace auntie hibba sun fita ne?hibba ya gyada mata kai kafin tace ehhh fita sukayi amma nasan zuwa anjima kadan zaki gansu,aydarh tace eyyerh daman auntie hafsa c eke zazzabi zan mi shi magana muje mu dubata hibba tace Allah sarki Allah yabata lafiya aydarh tace Amen. Sai wajan 5:00pm suka dawo suna dawowa ko shiga ciki malik baiyi ba yace wa dr ibrahim yace ta fito su wuce, hibba ta

30 / 111