SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 113

39K to 42K   out of 336.6K words

sannan ya wuce ciki. Dakinsa ya shige zauna a kan kujera, staring into nothing, babu abinda yake gani idan ya rufe idonsa sai hoton Safiyya da ciki, cikin wani, waye wanin amma? Waye mijin Safiyya. Ya tuno da maganar da Mama ta fada sanda ya gaya musu cewa Safiyya tana da aure, she said wanda Safiyya take cewa Daddyn ta ne, wanda take zuwa kasar waje gurin sa, shine mijinta.

Ya san pictures din Daddy, tabbas ya haife ta ko ma wadda ta fita, amma kuma yana da kuɗi, yana da bala'in kuɗi, yammata kuma a wannan zamanin sukan auri sa'an kakansu ma saboda kuɗi. But Safiyya doesn't look like a gold digger, she never sounds like a gold digger. He just couldn't picture her and that man as husband and wife.

Yayi kokarin kawar da tunanin daga ransa dan gudun illata zuciyarsa. Ya fara mayar da tunanin kan issue at hand, issue ɗin wannan yarinyar Safina. He regretted cewa ya zabe ta. Bai san dalili ba but he just doesn't like her tun kafin ya ganta, kuma in zai gaya wa kansa gaskiya ya san aibunta kawai shine dan sunanta Safina, which is not fair to her. She couldn't possibly be Safinar Safiyya, like is not that cruel is it?

Ya tashi ya koma kan study table dinsa ya bude laptop dinsa, in da akwai inda zai samu aibun yarinyar to tabbas a social media ne, anan zai samu abinda zai nuna wa iyayen sa yadda zasu yarda a fasa auren ba tare da sun jingina fasawar da Safiyya ba. Ya bude goggle sannan ya tsaya yana tuno sunan da ta gaya masa "Safina Ibrahim" amma da ya fara typing sunan sai ya samu kansa da typing "Safiyya Adam Muhammad" "damn it" ya faɗa a fili, subconsciously yana son yin bincike ne akan Safiyya.

He saw a lot of results da basu da dangantaka da Safiyyan da yake nema, he saw her Instagram account with the few posts she made most of which na abinci ne. Yayi murmushi "acici" sai kuma yayi sauri ya fita ya cigaba da binciken sa amma bai ga wani abu da zai yi linking dinta da aure ba ko kuma ya yi directing dinsa to mijinta. Ya koma search engine din sannan yayi typing "Alhaji Adam Muhammad" a cikin results din ya ga wanda yake nema, ya gane hotonsa from the pictures dinsa da yake gani a wayar Safiyya. Anan yaga biography dinsa da aka yi publishing, ya shiga idanunsa suna searching abinda ya ke nema, anyi rubutun ne akan a lot of achievements dinsa da irin tarin arzikin da yake da shi da kamfanonin da ya mallaka, he was even listed a cikin manyan masu kuɗin Nigeria. Yayi ta wucewa har yazo kan abinda yake nema, a cikin biography ɗin nasa anyi listing spouses dinsa, sunan farko shine "Safiya" sai kuma "Sa'adatu".

Ya kife fuskar laptop din da karfin da shi kansa ya san ta lalace. Ya mike sannan yayi jifa da kujerar da yake kai a zaune. Sai kuma ya zauna akan gado tare da rintse idanunsa. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya furta a hankali. How much more pain does he have to endure. How much more pain can his heart take. When will this end?

Ya koma da baya ya kwanta yana kallon sama. Ba san me zai yi tunani ba, bai san me zaiyi ba, bai kuma san tsahon lokacin da ya dauka a haka ba. Daga baya ya koma ya zauna sannan ya jawo wayarsa ya bude number ɗin Safina sannan ya kira. Ba'a jima ba aka dauka "alhamdulillah. Allah shine abin godiya. Tunda nayi sallah nake zaune akan sallaya ina gaya wa Allah bukatu na akan ka. Gashi kuma ban tashi ba sai da Allah ya amsa min ya juyo min da hankalinka gare ni".

Yace "listen Safina. If we are going to do this, then we are going to do it the right way. I am really heartbroken right now. I am in love, deeply in love with someone else, someone that I cannot have. Wannan ne dalilin da yasa aka matsa min akan auren nan. Bana son shiga hakkin duk wacce zan aura, so I want you to know what you are getting yourself into. Babu rufa rufa. I will marry you saboda ina son in farantawa iyayena rai, but chances are I might never love you, or anyone else. Me kika ce? Kin amince?"

Sai da tayi shiru na wasu lokuta, daga dukkan alamu maganar ta sa ta dake ta sosai. Sannan tace "I don't know what tomorrow will present to us. Babu wanda ya san gobe. Yanzu na sani, abinda na sani a yanzu kuma shine ina son ka, ina matukar son ka. Na kuma san cewa in na aure ka zan baka dukkanin kulawar da miji yake bukata daga gurin matarsa. Na kuma san cewa ita zuciya an halicce ta ne a bisa son mai kyautata mata, so chances are high that you will love me. Maybe one day in ka tuna da waccan har sai kaji haushin kan ka ma kana tunanin what made you love her. So yes, I am going to take my chances. Na amince, a bisa alkawari guda daya, cewa you will try your best akan sauke dukkan nauyin da addini zai gindaya a tsakanin mu. Kuma ba zaka wulakanta ko goranta min soyayya ta ba".

A cikin sati biyu aka gama bincike, kuma a iyakacin abinda aka samu babu wani abu da zai hana aure a musulunci. An gano asalin ta, an kuma yi bincike akan tarbiyyar ta. Daga nan uncles din Gidado, Uncle Habib, Faruk da kuma mijin aunty dinsa Maimunatu suka je har Katsina suka nema masa aurenta, a take kuma kanin mahaifin ta ya basu auren ta. Aka saka rana sati shida yadda zai zo dai dai dana Mufida kamar yadda iyayen angon suka nema. Daga nan kuma sai aka cigaba da gudanar da shirye shirye a duk bangarorin biyu.

****.     ****.    ****.    ****.    ****     ****

*Her🧕🏻*

Sama sama muka yi magana da Mukhtar, nayi kuma iyakacin kokari na na ganin cewa banyi masa wulakanci ba tunda yanzu ni ce da kaina na neme shi, sai dai kuma na katse maganar da cewa akwai abinda nake yi amma zan kira shi idan na gama. Na mike ba tare da na kalli Abdul ba nace "zan shiga ciki, thank you for...... For listening" ya mike shima "amma da zaki ji shawara ta kar ki koma ciki yanzu, ki dan basu space ki bari su huce tukunna. Ke ma ki huce" na tsaya amma ban ce komai ba, ya mike shima "let me take you home" na juyo "ba gidan ku zamu koma ba, mun samu gurin zama for the time being" yace "I know, amma zaku dauko kayan ku daga gidan na mu ai ko? Let me take you there sai ki debo muku kayan ku".

Ban cigaba da musu ba saboda nima bana son komawa gurin Mommy da Daddy a lokacin. Muka shiga motar sa muna tafiya a hankali na jingina kaina a jikin window tare da rufe idona, hoping ina ma dai mutum yana iya hana kansa tunani? Na jima a haka sannan naji yace "Fiyya. Wata tambaya nake son yi miki. Ban san yadda zaki dauke ta ba. Please kar ki ji haushi bana nufin komai sai alkhairi. I will only ask the question dan naga yau mun samu fahimtar juna. You can choose not to answer it if you will" na dago kaina tare da bude ido nace "ina jin ka" kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "akan wannan da kika gaya min kina so, shine baban babyn ki?"

Nayi sauri na kalle shi. Ya daga hannu "am sorry. In ba kya son amsawa forget I ever asked it" na juya kaina na cigaba da kallon gefe, sai da na jima a haka sannan nace "ba nashi ba ne ba. But kasan wani abu? Sometimes in akayi min irin wannan tambayar I wish cewa nashi ɗin ne. It would have made everything easier for both of us. Da sai dai Daddy yayi fadan shi ya gama, maybe ma ranshi ba zai kai yanzu baci ba, shima nashi iyayen in suka ji ransu ya baci suyi fada, but duk kan su ba zasu iya disowning din mu ba saboda suna son mu, at the end zasu nema mana mafita ne, which would be to get us married, muyi aure mu rike babyn mu, and live happily ever after. The end".

Ban jima a gidan Aunty Hajjo ba na gama hada mana kayan mu, tare muka tafi da ita zuwa gidan da Daddy ya kama mana muka danyi gyare gyare kafin su Daddy su zo. Ita ta kira Mommy ta gaya mata muna tare. Da furnitures da komai a gidan dan haka kayan sakawar mu kadai muka shiga dashi, sai yan few abubuwan da naga babu nayi mana order za'a kawo mana har gida.

Tunda su Daddy suka zo daga shi har Mommy babu wanda ya kula ni, Mustapha ne ya kai shi dakin da aka shirya domin shi sannan ya shirya masa kayan sa da duk abubuwan bukatar sa. Ni dai da naga na gama abinda zan yi kuma babu wanda yake yi min magana sai na wuce na tafi dakin da yake a matsayin nawa nayi kwanciya ta.

Sai dare sannan Mommy ta shigo. "Ki tashi ki ci abinci" tace min. Na mike zaune kawai bance komai ba, sai ta zauna a bakin gadon tana kallo na tace "Safiyya wannan ita ce magana ta karshe da zanyi miki a kan auren ki. Duk da cewa yanzun ma ba wai zanyi miki maganar bane ba dan ina saka ran zaki chanja ra'ayin ki ba, zanyi ne kawai dan in nuna miki irin yadda rai na ya baci akan maganar. Ba kiyi halacci ba Safiyya, daga ke har mahaifinki ba kuyi min halacci ba wallahi. Ai na san kin san komai, duk da dai ni ban taba zama na gaya miki ba dan bana son ki dauki maganar kamar gori amma na san duniya ta gaya miki, kin san irin halaccin da nayi wa Safiya, ni na dauke ta a matsayin yar aiki sannan na mayar da ita mutum, duk abinda Safiya ta zama a rayuwar ta wallahi ni ce sila. Haka kema kuma, tun kina zanin goyon ki na dauke ki na rike tamkar nina haife ki amma yanzu ni ce abin gudu a gurin ki. Shi kuma mahaifin ki ya goya miki baya as always. Babatun sa da fadansa na banza ne in dai a kanki ne baya iya juya ki sai abinda kike so shi kikeyi. Ba'a saka ki ba'a hana ki. Kuma kowa ya dan dalilin da yasa kika samu kanki a halin da kike ciki kenan. Amma har yanzu bai dauki darasi ba. Da wasu iyayen ne ma har wanni zaɓi za'a baki? Bayan abinda kika aikata kuma ace sai an baki zabin mijin da zaki aura? Da wasu iyayen ne da tuni baki fadi uban shegen cikin ki ba? Kuma na san abinda zakuyi nan gaba, tunanin ku yanzu shine in an haifi shegen a dauko shi a kawo min ace in rike shi saboda ni ce karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ko?. To wallahi kar ku sake ku doso ni da shi ma. Na fada miki wannan ne dan ki sani, zan cigaba da sauke nauyin ku da Allah ya dora min daga ke har mahaifin ki amma na daina going extra for any of you. Na daina saka bukatun ki a saman na ƴaƴan da na haifa da cikina. Tunda kun tabbatar min da cewa bani na haife ki ba. Kun tabbatar min da matsayina na matar uba kuma na dauki matsayin nawa".

Har ta gama bance komai ba, tana gamawa ta mike ta bar dakin ni ma kuma na koma na kwanta na cigaba da kallon ceiling. Shin da gaske na yiwa Mommy butulci?

Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min, har tsahon sati uku, Mommy ta janye jikinta sosai daga gare ni haka Mustapha ko magana baya yi min, nima kuma dama ba so nake yayi min maganar ba, Daddy ma kamar ko da yaushe sama sama yake min magana in dai har munyi doguwar magana to faɗa ne. Kullum dakina ne gurin zama na akan sallaya ta, anan nake sallah ta, anan nake kuka na, anan kuma nake bacci na. Na cigaba da zuwa asibiti ganin likita, na tabbatar masa da ra'ayi na na bayar da ɗan cikina for a closed adoption idan na haife shi.

A ranar da muka cika sati uku a gidan ne bayan na tashi da safe na fita da niyyar gaishe da Daddy da Mommy kamar yadda na saba kullum, ina fita parlor sai naga Daddy shi kadai a zaune akan electric wheelchair dinsa da kofin tea a hannunsa. Na karasa na gaishe shi ina lura da bacin ran da yake bayyane a fuskarsa, a raina har na fara lissafin ko nayi wani sabon laifin ne. Amma sai naji bai yi min faɗa ba bayan amsa gaisuwa ta da yayi. Na mike ina dube dube. Na shiga kitchen na fito na kuma shiga dakin su Daddy na fito amma ban ga Mommy ba. Daddy naji yace "she is gone" na juyo ina kallon sa. "Gone? Gone where?" Yana kallona shima yace "home. Sun tafi Nigeria ita da Mustapha. Wai auren Safina za'a yi. Safina ce wai aka bayar da ita ba tare da ko faɗa min anyi ba. Suka shirya tafiyar su ba tare da sun gaya min ba. Sai da safe kawai suka fito da akwati wai Nigeria zasu tafi bikin Safina. She said wai na nuna mata cewa ke ba yar ta bace ba shi yasa ita ma ta nuna min cewa Safina ba yata ba ce ba".

Not edited. Forgive the typos please.
[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: *❤‍🩹 Safiyya ❤‍🩹*



*By*



*Maman Maama*




*Episode Ten: Soul Mates*



Free Episode

Na zame na zauna akan kujera cikin mamaki "aure Daddy? Safina ce zata yi aure amma ni ban sani ba? How? Why? To wa zata aura ma?"

Yace "ba ta gaya miki ba kema? Kuna magana kuma?" Na gyada kai. Na san mun dan samu falling out da Safina kwanan bayan nan, and must issue din mu na san laifi na ne saboda yadda na zama very rude to her a watannin nan, hakan kuma yan ada dangantaka da mood dina da kullum bashi da kyau. Amma ban dauka har zata iya yin aure ba tare da na sani ba. And ko shekaran jiya munyi chats da ita. We even talked about magana ta da Mukhtar.

Nace "muna magana Daddy, amma ko alama bata nuna min ba. Wa zata aura kuma?" Ya girgiza kai "ban sani ba, they didn't tell me and I didn't ask tunda sun nuna ban isa ba. Ba ki san samarin ta ba?" Na yi shiru ina tunani "Safina bata da saurayi. Ni dai ban san wani saurayi da take kulawa ba" na tuno da yadda takan takan yi min kallon zautacciya duk sanda muke tare in taji muna waya da Gidado. Tace soyayya irritating dinta take yi.

"How can she do that?" Na fada a fili. Daddy yace " ba laifin ta bane ba. Am sure Sa'adatu ce zata hana ta fada dan tana so ta bata min rai, tana so ta nuna min nata ikon" nayi ajjiyar zuciya "babu komai Daddy kar ranka ya baci, we don't need them. We can do this alone. Su je suyi mata aure, Allah ya sanya alkhairi. All we have to do now is hire someone, kamar a nurse haka that can take care of you, sai kuma mu nemi a house keeper da zata ke shigowa ko da twice a week ne tana kula da gidan, and I can drive, duk inda zamuje zan iya kai mu" yayi shiru yana kallo na da murmushi a fuskarsa, sai kuma ya girgiza kai "Safiyya kenan. Kin dauka damuwa ta kenan? Wanda zai kula da ni? Damuwa ta shine wanda zai kula da ke idan babu ni. I don't want any enmity between you and them saboda ko babu dangantaka ta jini su yan'uwanki ne, ba na son in babu ni ki rasa wanda zaki yi turning to. Ke ba yanuwan uwa ne da ke ba, and in akayi auren ki da Mukhtar yan uwans sun zama na mijin ki, ke ba older siblings ne da ke ba. In na mutu ya zaki yi?"

Na koma na zauna ina jin wani kadaici yana lullube ni. Tamkar Ni kadai ce a duniya. Ya cigaba "shi yasa da farko naso auren ki da Mustapha, at least it will strengthen the bond between you kuma ba zasu yi spilling secrets dinki ba. And you will still have Ahmad a matsayin uba ba matsayin uban miji ba, zai kuma saka ido ya ga cewa basu cuce ki ba. But now, now I don't know what to do sai dai addu'ar Allah ya kara ara min lokaci"

Na gyara zama "amma Daddy ba ka ganin wannan tafiyar da suka yi suka barmu ta nuna true intentions ɗin su? Ta nuna cewa ba soyayyar Allah da Annabi suke yi mana ba?" Yace "Allah kadai ya san abinda yake ran bayin sa. I don't know abinda ke ran Mustapha, amma na san Sa'adatu is not cruel, stupid but not cruel, she is just scared that she will loose everything" nayi kokarin gane maganar amma ban fahimta ba sai na chanja magana "I still have the twins" yayi murmushi "yes, and they are the more reasons why dole in gyara tsakanin ku kafin in bar duniya, if not, you will loose them too, dan babu yadda za'a yi su juya wa uwarsu baya saboda ke".

Daga nan na tashi na shiga kitchen na hada wa kaina smoothie na zauna ina sha ina jimamin abinda ya faru, har lokacin na kasa yarda wai da gaske Safina ce zata yi aure amma wai daga

14 / 113