Author : Maman Mama Category : Romantic Hausa Novels
ki dawowa ya dauko ki ya kawo ki gida,
shima kuma da ya koma na tambaye shi
Muhammad din sai yace bai ganshi ba" na
ajiye kayan sallah ta a inda suke na rufe
ban ce mata komai ba,
Sai ta nuna min kusa da ita a kan kujerar
da take tace "zo ki zauna" na je na zauna
kamar yadda tace na sunkuyar da kaina
kasa ina kallon yatsun hannuna. Tace "Safiyya, Yar war ki Safina tana cikin matsala sosai a gidan mijinta. Allah ya jarabce ta da auren mijin da bai san
darajar ta ba ko kadan ballantana ta
iyayen ta. Tun kafin bikin su na fahimci
haka, amma rabon zata sha wahala da
kuma rabon cikin da take dauke da shi a
yanzu ya saka ban yi kokarin tsayar da
auren ba sai nayi tunanin miskili ne kawai
amma zata shawo kan shi. Sai bayan da
aka daura auren sannan take gaya min
gaskiya, ashe a social media ta ga hoton
sa ta kamu da son sa, sai ta nemi kanwar
sa ita kuma ta hada ta da shi. To
coincidentally sai ya kasance a lokacin su
kuma iyayensa suna son yi masa aure,
watakila da ma kokarin fin karfin su suka
ga yana yi shine suke neman yarinyar da
zasu manna wa, ita kuma Safina rabon
shan wahala ya kai ta".
Tayi shiru tana kallona, maybe tana jira ne
in ce wani abu, jin ban ce komai ba sai ta
cigaba "ni abinda yafi bata min rai shine
idan da yasan baya son ta ai da sai ya
fada, tunda na tabbatar iyayensa ba zasu
yi masa dole ba, amma sai ya karbi auren
yarinyar nan, ita kuma Safina munafuka
tunda ta san daga ni har Daddyn ku ba
zamu yarda da irin wanna auren ba shine
ta kai shi Katsina, su kuma wasu
munafukan, dama ba sonta suke yi ba ba damuwa suka yi da ita ba shine basu
à
tsaurara binciken komai ba dan sunga mai
kudi ne suna saka ran zai ke kai musu
wani abu, basu san cewa ita kanta Safina
ba abinda take samu daga gare shi
balantana su, shine suka daura mata aure
da shi" ta sake yin shiru,na dago kai in
kallon ta nace "Mommy why are you
telling me this?" Tace "why not? Me yasa
ba zan gaya miki ba kuwa Safiyya, saboda
yar uwarki ce ita, ina ganin ya kamata ace
kin san halin da take ciki, kuma ai
hausawa sunce ciwon ya mace na ya
mace ne. Na tabbatar ba zaki so Safina ta
kasance cikin kunci a gidan mijinta ba
ko?" Ban amsa tambayar tata ba sai nace
"Mommy yanzu ni me kije so inyi akan
hakan?" Tace "you are very smart Safiyya,
in fact ni ban taba ganin someone as
smart as you ba, kin san Safina bata da
yawo sam, so nake ki saka kanki in her
shoes kiyi tunanin me take ji a zuciyar ta
sannan idan ke ce me zaki yi a kai. Sai ki bata shawara, na tabbatar in tabi shawarar ki zata samu waraka" na cigaba da yin shiru, sai ta mike "kinji kamar har an fara kiran sallar isha, bara in sauri inje
inyi Sallah, just think about it Safiyya, na
san zaki samo mata solution. Tayi kuskure
na sani, amma yanzu it is too late to go
back a gyara kuskuren tunda already har an fara hada zuriya. So nake muyi standing together as a family mu taya ta gyara gidan ta, kamar yadda muka yi
standing together as a family muka rufe
maganar kaddarar data same ki".
Ta juya, har ta kai bakin kofa sai ta kara
tsayawa tace "in kin gama ki sauka muci
abinci tare. Sai mu bawa Daddy labarin
gidan Safina".
Ta fita tare da rufe min kofa. Na bi kofar
da kallo sannan na dawo da hankali na
kan yatsun hannuna naci gaba da kallon
su, na tabbatar Safina ta gayawa Mommy
wani abu a kaina ni da Muhammad, kuma
na tabbatar ba gaskiya ta gaya mata ba.
Dan wadannan maganganun nata a cike
suke da harshen damo, she meant more
than she said. Har da gori a cikin maganar
and I also felt a threat a karshen maganar
ta lokacin da ta ambaci Daddy.
Na tashi na sauka kasa, na tarar Esther
tana ta hidimar shirya dinning sai na taya
ta, nayi kokarin yi mata hira to make up
for dazu dana ni ignoring dinta tana y min
magana, nace "Esther ya kamata a samo
wadda zata ke taya ki aikin gidan nan
gaskiya, aikin yana yi miki yawa, dama
mun barki ke kadai ne saboda ba zama
muke yi a gidan ba yanzu kuwa naga Daddy kamar yafi jin dadin zama a gidan
nan dan haka bansan sanda zamu koma
Kano ba" ta bude ido "wata kuma
Madam? No dai a bar ni ni kadai. Nafi jin
dadin aikina ni kadai bani da wani
problem. Ana kawo Wata zamu fara
competition for your appreciation. Ni ina
da kishi sosai. Idan something nawa ne
nafi son ya zama nawa ni kadai" nayi
murmushi "that makes the two of us
Esther. Tace "I think that makes almost
everyone. Kowa yana da kishi. Maza da
mata. Na wasu ne kawai yafi na wasu,
wasu suna fitowa da shi fili was suna
boyewa. Ya danganta da halin mutum".
Na tayata ta karasawa Daddy soup din da
ta hada masa, saboda yanzu baya iya cin
solid food irin namu, soup ce da aka yi da
shredded chicken, shredded Irish
potatoes and shredded vegetables aka
kuma dafa su sosai yadda ba zasu bawa
cikin sa wahala wajen digesting ba. Shi ya
fara zuwa dining din kuwa a kan
electronic wheelchair dinsa, naje ina
kokarin gyara masa zamansa sai ga
Mommy ta sauko sannan sai ga Mustapha
shima ya shigo, na zauna tare da su muka
ci abincin trying as much as I can inga
cewa na danne abinda yake zuciya ta
amma da kyar nake samo lomar tuwon da
nake ci take wucewa.
I expected Mommy ta bawa Daddy labarin
abinda ya faru a gidan Safina ko tayi
complain akan halin mijin Safina amma sai
naji bata yi ba, sai labarin abincin da
Safina ta dafa musu ta bayar "yarinyar
nan bata iya girki ba. Suma yaran da na
kai mata duk basu iya ba ashe. Nace
wanna wanne irin kwamacala kike baya
mijin naki? Kuma wai a haka ta shiga
online classes na koyon girki, daga videos
din take kalla tana yi".
Mustapha yayi gyaran murya yace "gwara
dai a samo mata wadda zata koya mata
girkin har gida, tun kafin masu iya girki su
kwace mata miji" ya karasa maganar yana
kallona. Daddy da yake jin su yana
murmushi yace"ai kuwa dazu mijin yazo
gidan nan kafin ku dawo" duk muka juya
muna kallon sa, ya cigaba da magana
fuskar sa dauke da murmushi "yaron kirki
ne. Yazo ya gaishe ni. Yace ya ga kunje
amma babu ni shine yace bara shi yazo ya
duba ni" Mommy tace "what? Lallai
munafunci ba'a mata kawai ya tsaya ba"
Daddy ya kalle ta yace"me yasa kika ce
haka?" Ta girgiza kai tare da cigaba da cin
abincin ta amma kana gani kasan ranta ya
baci tace "babu komai, wata maganar ce
daban".
Ranar da daddare ban iya bacci ba kamar
yadda nayi tunani, babu abinda kwakwalwa ta take yi min tunani sai Muhammad da Safina, ko me suke yi
yanzu? Na tabbatar suna manne da juna.
Munafiki, da rana zai wani ringa nuna wa
duniya kamar baya son ta da daddare
kuma yaje yayi mata ciki. Ina nan kwance in da dark, trying to get rid of tunanin Muhammad da matarsa sai
naji wayata tayi kara, na dauka na ga
bakuwar number and the first thing that
came to my mind shine Muhammad ne.
Shine ya saka sabon sim ya kira ni dan
yasan nayi blocking wadancan. Na rike
wayar ina kallon ta har ta katse, amma
kuma ji nake zuciya ta tana bugawa har a
cikin makogwaro na. Nayi missing din sa
sosai, nayi missing our long night calls da
bamu da mu da nisan da dare yayi ba.
Nayi missing listening to his deep calming
voice.
A lokacin wani kiran ya sake shigowa,
kwakwalwa ta tana gaya min inyi ignoring
ko in kashe wayar ma gabakidaya but my
heart wants to listen to his voice again,
And I followed my heart, na dauka,
pretending ban san cewa shine ba "hello,
who is there" yayi shiru, sai kuma naj
haushin kaina, wata kila ma bashi bane
ba, to ya ma za'ayi ya kira ni a wannan daren bayan na san yana can manne da matar sa?
Har zan katse kiran sai kuma naji muryar
sa "sunana Muhammad Gidado, Please
don't hang up" and all the emotions and
the memories came flooding back to me.
He sounded just like when we were free
and without a problem, kamar babu
abinda ya chanja, yet everything has
changed. Misali matar shi da take kwance
maybe ma a kusa da shi a yanzu, watakila
ya gama lallabata ne ta bata hakurin dazu,
tayi bacci shine zai kira ni, watakila ma
satar jiki yayi ya fito daga dakin su yaje
waje ya kira ni. Wadannan thoughts dinne
suka sa na katse kiran bayan na tabbatar
masa da rabuwa ta da Mukhtar kuma na
tabbatar masa da cewa babu sauran
change of something between us.
Ina katse kiran kuma nayi blocking
number din ita ma. Yaje ya karata da
Safinar sa na bar mata shi
A daren na fahimci cewa rayuwa zata
karayi min tsananin a garin Abuja, sai nayi
tunanin alkawarin da nayi wa Hajiya na
zuwa Umrah daga ni sai ita, ina ganin
lokaci yayi da zan cika mata alkawarin ta.
Washegari da naje gaishe da Daddy ma
gaya masa plan dina, ya amince kuma ya
nuna jin dadin sa sosai, nan take kuma ya kira wani agent da zaiyi mana shirin komai. Sai kuma yace "in kun dawo kuma sai mu shirya muje gabakidaya da
Sa'adatu da yara" nayi shiru ban ce komai
ba, sai ya kira sunana "Safiyya" na dago
kai ina kallon sa amma ban amsa ba sai
yace '"koma menene a tsakanin ki da
Sa'adatu da yaranta ki ajiye shi a gefe, na
dauka maganar zargin da kike wa
Mustapha ne ya saka ki ke jan jikin ki daga
gare su, yanzu wancan issue din is over
but har yanzu you seem even more
distant than before. Akwai wani abun ne?"
Na sunkuyar da kaina kasa ina girgiza shi
sannan nace "babu komai" yace "okay.
Bana son a samu komai din, bana son
wani issue tsakanin ku because without
Ahmad, yanzu su ne kadai dangin da kike
da su a duniya".
Na tashi kenan zan fita sai ga Mustapha
nan ya shigo, ya gaishe da Daddy nima
sai na gaishe shi, zan fita kenan yace min
"zaki je Oasis ne yau Fiyya? In zaki je zan
biki. Na kwana biyu ban je ba" na kalli
Daddy sannan na kalle shi nace "Okay" na
juya na fita a raina ina fatan sanda zan tafi
ya manta ko kuma baya gidan, amma sai
dai ina fitowa na ganshi a zaune a rumfar
motoci yana danna waya, ina shiga mota
kuwa yazo ya shiga ya zauna a
passengers seat, naji kamar zan saka
kuka amma a haka na kunna motar muka fita.
Muna fita guards dina suka biyo bayan
mu. Ya juya ya kalle su yace "seriously! I
am here, what more protection do you
want?" Nace "maybe protection from
you" yayi dariya, "you are kidding right? In
zan miki wani abu baa hanya zanyi miki
ba" nayi shiru na rabu da shi dan na san
dama neman magana ne ya saka shi biyo
ni, ni kuma yanzu magana ita ce abinda
bana son yi shi yasa nake barin gidan.
Muka cigaba da tafiya sai yace "Ban gaya
wa Mommy ko Daddy ba" ban kalle shi ba
nace "what?" Yace'"maganar mijin
Safina" nayi shiru na rabu da shi, ya
cigaba"baki tambaye ni dalilin da yasa
ban gaya musu ba" still bance komai ba,
sai yace "dalilin da yasa ban gaya musu
ba shine exactly dalilin da yasa ban gaya
wa Daddy inda kika je ranar nan ba" nace
"and what reason was that?" Yace
"because I care. I care about you and I
want you to trust me. Ina so ki fahimci cewa I am loyal to you.And I am very trustworthy" nayi ajjiyar
zuciya nace "wai dan Allah Mustapha kai
baka da budurwa ne da zaka je ka dama?
Kai ko zancen nan ma ba ka zuwa? At
& least go out and meet people, maybe
zaka samu mai sonka one day" yace
"yammata akwai su mana, su da kansu suke kawo kansu, but the problem is I already have my eyes and heart somewhere. I just want to be seen. I just
want my efforts to be appreciated".
Sai da muka je nayi packing sannan na
juyo ina kalion sa nace "Mustapha, it is
not going to happen. Let it go. Don't drag
please, we have been through this before.
Ka bar maganar dan Allah" na bude kofar
zan fita sai ya kira sunana, na juyo ina
kallon sa sai yace "and neither will you
and Muhammad happen. Daddy ba zai
taba bari ki auri mijin Safina ba".
Na fita daga motar da sauri na shiga dakin
da nake zama a ciki duk sanda na je gidan
na rufe kofa sannan na jingina da jikin
kofar. Ba maganar sa ce ta bata min rai ba
abinda ya bata min shine the fact that he
is right. Daddy will never let it happen.
Idan da ace Daddy zai samu yadda yake
so to zai so in auri wanda yake kusa da ni,
someone like Mustapha, someone da ba
za'a yi bincike ba idan zaa5yi auren.
lyayen Muhammad ma ba zasu barshi ya
aure ni ba considering alaka ta da Safina,
ko zasu bari ma zasu yi bincike, and
chances are high that they will find out
about my fast, I am sure Safina zata basu
labari ko da basu tambaye ta ba, And as righteous as they are, they will never let him marry someone da take da dan shege. So Mustapha is right. It is never
going to happen.
And just as if to rub salt on my wound sai
ga kira nan ya shigo waya ta from an
unknown number, a take na san cewa
shine, and my stupid heart pick up the
call na saka a kunne na, ya sake yin shiru
irin na jiya, nima kuma nayi shirun, sai
daga baya ya kira ni da sunana shi kadai
yake kira na da shi "Piya" na ji hawaye
naya bin fuska ta amma ban amsa ba, ya
cigaba "I know you can hear me, please ki
bani ko da minti biyu ne inyi miki magana,
I just want you to listen to me" and I
listened to him as he try to pour his heart
out to me, sai da naji kuka yana kokarin
kwace min sannan na katse kiran without
saying a word to him. Sannan nayi
blocking number din ita ma.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya mana,
kullum sai Muhammad ya saka sabuwar
number ya kira ni, farko ina dauka ba dan
komai ba sai dan inji muryarsa in samu
sanyi a zuciya ta, daga baya sai na daina
dauka dan na fahimci sauraron nasa was
doing more harm to my heart than good,
Giving me false hope, Da ya ga na daina dauka sai ya koma turo min messages, kamar dosage na magani
haka ya riga feeding dina da soyayyar sa,
safe, rana, dare, har zama nake yi in saka
waya ta a gaba ina jiran shigowar sakon
sa. And when the nights get lonely sai in
zauna inyi ta bitar messages dinsa kamar
mai dorin karatu.
A haka har muka tafi Umrah nibda Hajiya,
naji dadin tafiyar tamu sosai musamman
peace din da na samu a zuciyata sanda
na taka kafa ta a cikin garin Madina, and
the weight da naji any lifting daga
zuciyata sanda nayi kuka a cikin sujjada ta
a gaban ka'aba.
A ranar ne bayan mun koma masauki
Hajiya ta saka ni a gaba da tambaya.
"Kina da wani problem ne Safiyya? Akwai
abinda yake damun ki?" Na girgiza kaina
da sauri laughing nervously, "bani da wani
problem Hajiya, me kika gani?" Tace
"dazu kukan da kika yi a gaban ka'aba is
not normal. Abu biyu zai saka mutum
wannan kukan, ko dai wani babban zunubi
da kayi nadama akan sa kake neman
gafarar ubangiji ko kuma wani problem da
kake da shi kake neman Allah ya baka
mafita" nayi shiru ina niyyar ce mata bani
da problem amma sai hawaye na yayi
betraying dina,
Ta zauna tana kallo na kawai, sai kuma
tace "kin san yanzu da nake kallon ki me
kika tuna min dashi?" Na goge hawaye na
tare da girgiza kaina, sai tace "mahaifiyar
ki. Ganin da na fara yi mata a duniya.
Ranar da Hajiya Kyauta ta kawo min ita
gida na. I have never seen anyone as
broken as she was, she was so sad.
But you know what? She was also
determined. She had a purpose. Aim dinta a lokacin shine tayi all that she can a rayuwa so that zuri'ar ta, ma'ana you, will not be in her situation. Bata da
komai kuma bata iya komai ba a lokacin,
hatta shara sai da aka koya mata dan bata
¡ya irin ta mu ba. But she worked hard,
harder than anyone I have known. She
took risks, risks that even I couldn't. And
all for you. At the end kuma, she gave her
life for yours".
Nayi shiru ina jin ta, wondering if her
words are to make me feel better or
worst. Sai ta cigaba "but yanzu da nake
ganin ki a wannan halin sai na samu kaina
da tambayar kaina, All that your mother
did are for what? Because you are as
broken and devastated as she was
lokacin da ta shigo Abuja. To hakan yana
nufin all her sacrifices have been in vain kenan?"
Na girgiza kaina "Ammie was mistaken.
Money doesn't buy happiness. It only
creates problem. Well at least it did for
me. Gani da kudin dai yanzu but ba zan
¡ya siyan abinda zai saka ni farin ciki ba"
Hajiya ta girgiza kanta "no Safiyya. You
are mistaken not her. Money doesn't buy
all happiness, yes, amma talauci ma haka.
Money can create problems tabbas,
amma talauci ya fi shi creating problems.
Kowa da kaddarar sa, whether you are
talaka ko mai kudi. Safiyya, happiness can
only be found from within, you are the
only one responsible for your happiness
not abinda kike da shi and not mutanen
da kike tare da su. Only you and the
choices you make can make you happy"
Two weeks muka yi a can muka dawo
Nigeria, and sanda muka dawo I felt a lot
better duk da dai har lokacin ban samu
solution to MG problem ba.
Sai dai kuma a ranar da muka dawo din
muna zaune a falo da kowa da kowa har
da twins sai ga waya anyi wa Mommy,
tace Safina ce ta kira ta "maybe zata ce
zata zo miki sannu da zuwa ne" ta fada
sannan ta dauki kiran, amma kuma tana
dauka sai muka ga ta mike tsaye cikin
tashin hankali "accident? Wanne irin accident? Ban gane ba, Safina ce tayi accident ko mijinta? Tare suka yi? Ni fa ban gane ba, suna ina?" Na mike tsaye ina
kallon ta ido na kamar zai fado kasa.
Ta bi mu da kallo, jikinta har rawa yake yi
"'Ramla ce, yarinyar da na kaiwa Safina,
wai mijin Safina ne yayi accident. Ita ma
kuma Safinan wai tayi accident. Ni ban
gane ba. Kuma tace ba tare suka yi ba".
Na juya da gudu nayi waje, sai da na kama
handle din mota ta sannan na tuna ban
dauko key ba, na koma gurin daya motar
da bata bukatar key na bude ta da
fingerprint dina hannuna yana karkarwa
sannan na shiga na tashe ta na fita daga
gidan a guje.
Him👳🏻♀️
It has been 3 weeks already yana ta bin
Safiyya amma ya kasa samun ko da
response ne from her, ya zama as
frustrated as anyone can be. Ya zama
kuma very