SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   81 / 113

240K to 243K   out of 336.6K words

sallar la 'asar
sannan na fita.

Hassan ne ya tuka mu a motar Daddy
wadda take ajiye baya hawa, dama twins
ne suke hawan ta yanzu idan sun zo gari,
Hussain yana gefensa ni da Daddy muna
baya, muna tafiya muna hira, and Daddy
used the opportunity to talk to us about
hadin kai da kuma son juna. "Be each
other's keepers" he said.

"ku kar kuga ita macece ku raina ta, ku yi
mata biyayya kamar ni kuke bi, duk
abinda zakuyi ku nemi shawarar ta. She is strong and she will take care of you, bani da shakka akan wannan. Ke kuma kar kiga su kanana ne ki raina su, ki saka su a cikin dukkan al'amuran ki, kiyi shawara da su a
kan dukkan abinda ya shafe ki. In kinyi
haka you will be enough for each other".
Na kama hannun shi a rike da hannayena
biyu ina jin wani nauyi a kirjina. He looked
at me and smiled.

Muna zuwa asibitin suka dauko kujerar
Daddy a bayan motar suka dora shi akai
sannan suka tura muka shiga ciki. Muna
shiga dakin da Safina take muka tarar da
wasu kawayen ta sunzo dubata, da suka
gan mu sai suka yi mata sallama suka tafi.
Na samu guri akan kujerar two sitters da
take gefe a akin na zauna bayan na
gaishe da Mommy, ina zama Mustapha ya
shigo, ya je ya gaishe da Daddy sannan
ya dawo ya zauna a kusa da ni, nayi
kamar ban ganshi ba na dauko waya ta na
fara daddanna wa.

Daddy yaje har gaban gadon Safina ya
duba ta, ta tashi zaune ta gaishe shi. Ya
duba hannun ta da kafarta da taji ciwo
sannan Mommy ta zo tana nuna masa
fuskarta "ka ga marin da yayi mata? Ka ga
irin cin mutuncin da yayi mata? Ko mu
bamu taba dukan ta ba amma wani kato a can ya kusa ya kal ta lahira, Wannan yaron ba mutumin kirki bane ba Daddyn Mustapha. Wallahi ba mutumin kirki ba ne
ba. Na tabbatar da kai ka bada auren
Safina ba zaka ba shi ita ba. Na tabbatar
da kai ne zaka yi bincike kuma zaka san
halin sa. Ita dai Safina iyayen ta sun cuce
ta, ita ma kuma ta cuci kanta tunda ita ta
kai kanta gurin su. Amma yanzu ba zamu
kuma irin wancan kuskuren ba".

Duk mukayi shiru babu wanda yace
komai. Safina ta fara kuka kasa kasa,
Daddy ya dora hannunsa akan kafadar ta
a hankali cikin muryar sa ta rashin lafiya
ya fara rarrashin ta. "kiyi hakuri Safina
kinji? Kaddarar ki ce haka. Amma za'a
dauki mataki akan abinda ya far, zamu
tabbatar haka ba ta sake faruwa da ke ba
ko kuma da wani daga cikin yayan mu ba."
Mustapha yace "wallahi dan Mommy ta
hana nine amma da yaron nan dazu ba
zai bar asibitin nan ba dan sai na karya
masa hannu ko kafa" Daddy ya juyo yana
kallonsa yace "ban amince ba. Kar ka
taba shi. In ka taba shi kai ma ka zama irin
sa kenan" Mommy tace "ai na gaya masa
kar ya taba shi, matakin shari' a zamu
dauka akan sa. Da dai iyayen sunce min
zasu dauki mataki shi yasa nayi shiru na
saka musu ido, amma yanzu naga basu
da niyyar daukan wani mataki a kai dan haka mu zamu dauka" Daddy ya girgiza kai "'a ba za'a yi karar sa ba. Akwal martabar aure al a tsakanin su. A fara
kokarin sasanta maganar a gida tukunna,
sai in anga abin ya gagara tukunna sai a
shigar da sharia ciki. Tunda duka da
kuma ture wa da mota ai domestic
violence ne".

Ina jin su ni dai ban ce komai ba, A lokacin
kuma na kara zargin daga Daddy har
Mommy sun san tsakani na da
Muhammad kuma suna fada min magana
ne a fakaice. Suka cigaba da maganganun
su Safina kuma ta cigaba da kukan ta sai
kuma kawai naga Mommy ta mike, tace
"ni in abu yana cina bana iya zama
wallahi, Safiyya zo ki raka ni gidan su
yaron nan, Mustapha zo ka kai mu. Gwara
inje inji inda binciken nasu ya tsaya dan in
san abunyi a akan maganar nan".

Na dago kai da sauri ina kallon ta sai
kuma na girgiza kai and ban san sanda
nace "no Mommy, I don't want to go
there" wani kallo da Daddy yayi min shi ya
sa na mike na fita ba tare da na sake yiwa
kowa magana ba amma ji nake kamar in
ruga da gudu in samu mota in koma gida,
like why? Me yasa zata je dani gidan du
Muhammad akan rigimar sa da Safina? Al
wannan maganar manya ce and I am not manyan Satina duk kuwa da cewa ni nayi mata kayan daki.

Ina jin su suka fito ita da Mustapha suna
maganganun su, yana bude motar nayi
sauri na shige baya na zauna. Suka shiga
gaba tana cigaba da mita tare da fadar
maganganu akan Muhammad, sai na saka
hannayena biyu na toshe kunnuwana na
jingina kaina a jikin kofa. A haka muka je
gidan raina a matukar bace, ni ban taba
zuwa gidan su Muhammad ba sai ranar. Muna yin packing ta juyo tace min fito muje, na sake girgiza kai na kamar zanyi kuka "Mommy I rather stay in the car"
tace "da a motar zan barki ki zauna ai da
ba zan taho da ke ba. Ina sane na taho da
ke din ai'". A dole na fito daga motar ina ji
ina gani ta tusa keya ta zuwa cikin gidan,
my mind was telling me to call one of my
guards da na tabbatar suna waje ya zo ya
kwace ni daga hannun Mommy ya mayar da ni gida.

Muka shiga ciki, and I saw Muhammad da
wata da na fahimci Mufida ce, sai kuma
ga Mama ita ma ta shigo. Haka naje na
zauna and I was literally forced to listen to
maganganun su akan rigimar Safina da
Muhammad har daga baya aka kira shaida ta kuma tabbatar da cewa Safina ce mai
laifi concerning zubewar cikin da kuma
raunukan da ta samu not Muhammad.
Amma dai tabbas Muhammad ya mare ta.
But that doesn't made me feel better dan
kirikiri nake ganin kiyayya ta a idon Mama.

Haka Mommy ta gama borin kunyar ta ta
tashi muka fito, da zamu fito ta saka aka
kira mata Ramla tace tazo mu tafi tare.
Muka sake komawa mota muka juya zuwa
asibiti. Mustapha yana ta tambayar yadda
aka kare, Mommy ta fara "sun goyi bayan
dan su. Wai ba da sanin sa bane ba. Har
da kuma cewa wai marin da vavi mata ma ai ya bata hakuri. Kuma ta gaya min bai bata hakuri ba sai ma maganar banza da ya ke gaya mata".

Na nemo ear piece na toshe kunnuwana
har muka je asibitin, zuwa lokacin ana ta
kiraye kirayen sallar magrib, muna zuwa
muka tarar Daddy yana jiran mu na dauka
juya wa kawai zamuyi mu tafi but he said
"Safiyya kiyi wa Safina sallama" na ji
kamar zan fashe da kuka, na je gaban
gadon nace "zamu wuce. Allah ya kara
miki lafiya" tace "Amen. Thank you" sai
na wuce na fita da sauri ina jin alamar duk
yan dakin ni suke kallo.

ina zuwa mota sal gain Mommy nayi ta
biyo mu, wai gida zata je ta kwana shi
yasa ta taho da Ramiah ta kwana a wajen
Safina. Ni dal har muka je gida ban sake
magana ba, Muna zuwa na wuce dakina
da sauri na kuma rufe kofa ta sannan na
shiga toilet nayi alwala na fito nayi sallah,
na rufe kofar ne saboda na san Mommy
zata iya cewa zata shigo ta sake yi min
irin maganar ranar nan ni kuma raina a
matukar bace yake ina tsoron kar in gaya
mata bakar magana.

Ina jin ta tana taba handle din kofar amma
nayi kamar bana kusa na cigaba da zama
na akan sallaya. Ni na san har lokacin my
mental health is not okay, in dai har zata
zauna tana zagin Muhammad a gaba na
anything can happen. Na tuna sanda
Mukhtar ya zage shi a mota na bude kofa
zan fita. Ina nan zaune har akayi sallar
isha na tashi nayi sannan aka sake
knocking kofa ta sai kuma naji muryar
Esther. "Madam Daddy yana kira".

Na ajiye charbin hannuna sannan na tashi
na bude kofar na fita, na wuce Esther na
sauka kasa. A dinning room na same su
gabaki daya suna cin abinci, ina shiga
Mommy tace "ina sane nace da Esther tace miki Daddy ne yake kira ai, gashi nan kin sauko, Tun dazu nake hawa ina miki magana amma o amsa baki bani ba" nace mata "ina sallah ne" sal kuma na
juya gurin Daddy nace "Daddy ganj" ya
nuna min kujera "ki zauna ki ci abinci tare
da yan'uwan kj" na girgiza kai nace "na
koshi" yace "ki zauna ki ci abinci nace"
sai na ja kujera na zauna na zuba abinci a
plate na fara ci kamar yadda ya umarce ni.

Mustapha yana kallo na yace "wai ke me
yake damun ki ne?" Mommy tace "fushi
take yi, dan dazu na matsa mata ta shiga
gidan surukan Safina" Hussein vace
"Mommy to me yasa za'a matsa mata?
Tun da ta nuna bata so ai da sai abarta
ko" ta zabga masa harara tace "to uban
iyawa, ka fi mu santa ne ko kuma ka fi mu
sanin abinda yake dai dai. It was for her own good" Hassan yace "we just don't like seeing her sad. She have been through a lot. She should be happy" sai naji abincin da nake ci ya tokare a makogwarona, Hassan is right, I should be happy. But I am not. Ban kuma san ranar da zanyi farin cikin ba.

Haka na cuccusa abincin, ina jin shi
gabakidaya yana tsayawa a kirjina baya
wuce wa ciki na, sal da na ga kamar zanyi
wa kaina illa sannan a daina nci na
cigaba da zama akan kujera ina kallon su
har suka gama, Ina jin twins suna bawa
Mommy labarin nace zan kai su kasar
waje karatu, a take naji tana yiwa
Mustapha maganar ya zauna da su ya
taya su zabar makarantar da ta dace da
fannin da kowa a cikin su yake son
karanta. Daddy ne ya fara cewa zai shiga
ciki ya kwanta, Mustapha ya tashi ya
taimaka masa ya shiga dashi cikin part
dinsa, ina ganin sun wuce na mike da
sauri na fita nima na hau sama zuwa
dakina. A hanya na hadu da Esther, sai na
ga ta bini a baya amma bata ce min komai
ba har na shiga dakina sai ta shigo ita ma
sannan ta rufe kofa tana kallo na.

Na tsaya ina kallon ta da alamar tambaya
sai ta fara magana cikin inda inda "uhmm
Madam, dama wani abu nake so in gaya
miki" na zauna ina kallon ta with serious
face nace "what? Wani abu ya faru ne?"
Tace "I am not sure, but I just want you to
be careful" na ji gaba na ya fadi, nace
"careful about what?" Sai ta shigo ciki
sosai ta zauna akan gado tana kallona
tace "da akwai wani ex boyfriend dina, to
yana ta so mu shirya ni kuma naki yarda"
na cigaba da sauraron ta duk kuwa da cewa bani da interest in her relationship
with her ex boyfriend, Ta cigabe "sal
dazu, na ganshi a gidan nan bayan na
dawo daga aiken da Daddy yay min,
lokacin ba kwa nan kuna asibit!, I asked
him me yake yi anan farko sal ya ki fada
min yace it is confidential, Sal na cigaba
da insisting sal naji. And in his attempt to
get back to me sal ya gaya min" na gyara
zama nace "ya gaya miki me?" Tace
"dama yana aikin saka CCTV ne. To wal
Daddy ne ya saka shi ya saka a ko'ina a
gidan nan. Kamar Daddy yana zargin
something us happening amma ba'a gaya
masa, yana son sanin komal da yake
faruwa a cikin gidan nan. Shine dazu ya
fita da ku gabakidaya ni kuma ya aike ni
dan ya bawa mai aikin damar yin aikin ba
tare da kowa ya sani ba. He told me ya
saka small cameras da ba za'a gani easily
ba a koina a gidan nan except for bedrooms and toilets. Sannan yayl connecting komai zuwa wayar Daddy, duk abinda za'ayi yanzu a gidan nan Daddy
zai gani kuma zai ji".

Nayi shiru ban ce komai ba sai ta sake
cewa "na gaya miki ne so that you should
be careful in da akwai wani abu da ba kya
so Daddy ya gani ko ya ji. Ni ma yanzu
dole in rage saka kida a kitchen in ina
aik™️" ta karasa tana dariya, Nayi mata
murmushi "Okay Esther, Nagode sosal for this. I won't forget your kindness" tayi murmushi ita ma tace "you deserve it" har ta kai bakin kofa sai ta juyo tace "bazan gaya wa kowa ba bayan ke. And I wish
Daddy zai kama duk me laifi a gidan nan".

Bayan ta fita na jima a zaune ina juya
maganar a raina sai kuma na tashi a kalli
agogo sannan na fita na sauka kasa da
sauri na tafi bangaren Daddy. Na tarar har
an gama yi masa shirin kwanciya yana
zaune akan gado da dan karamin
Alqur'ani a hannun sa yana karantawa, sai
na zauna a bakin gadon ina kallon sa har
ya gama ya shafa, Da dauki Alqur'anin na ajiye a inda ake ajiyewa sannan na dawo na zauna

Yana kaliona yace "Safiyya, akwai
maganar da kike son gaya min ne?" Na
sunkuyar da kaina sannan ace "Daddy
fushi kake yi da ni ko?" Yace "akwai
abinda kika yi wanda zai saka inyi fushi da
ke?" nace "I am sorry Daddy, jiya nayi
maka karya, nace zan je asibiti kuma ban
je ba" ya daga hannun sa a hankali ya
dago fuskata yace "tunda kin yarda baki
je asibitin ba, ina kika je?" Na sunkuyar da
ido na kasa ina wasa da hannu na, ya kira
sunana "Safiyya" na dago kai muka hada
ido sai na sake mayar da kaina kasa, yace * understand life has been hard, and
cruel to you, I understand I haven't been
as good a father as I planned to be for
you, But you must put the past behind
you and face your future. Na san cewa
yanzu is too early in fara yi miki maganar
aure, but I do not have time Safiyya. And I
so much want to see you married and
happy before I go, Ina so ki samu mutumin kirki mai hankali
wanda zai soki kuma ya rike ki tsakani da
Allah, wanda zai zame miki gata bayan
babu ni ki aura, dan Allah Safiyya" nayi
sauri na dago kai tare da rike hannunsa
"Daddy don't beg me, abinda duk kake so
shi zanyi, If you want me to get married I
will get married, Ni dai so nake ka daina
fushi da ni dan Allah, Na kwanta na kasa
bacci. Ina cikin damuwa Daddy" na fada
murya ta tana karyewa, yace "menene
damuwar ki? Dan ina yin fushi da ke ko
kuma akwai wata damuwar da ban?" Nayi
ta kokarin fitar da maganar amma na
kasa, sai daga baya sannan a hankali nace
"Muhammad" yayi shiru yana kaliona
sannan yace "wanne Muhammad din?"
Sai naji na kasa kiran sa da sunan mijin
Safina kamar yadda suke kiran sa da shi,
Sal na gyara maganar "wanda muka je
gidan su dazu" yayi ajjiyar zuciya, "mijin Safina?" ya fadi sunan da bana so din.

Nayi shiru ban amsa wannan ba, sai ya
sake tambaya "what about him? Me kike
so ki gaya min akan sa?" Nace "uhmm,
dama ..... Jiya da banje asibitin ba, muna
tare da shi" yace "I know. Malam Ya'u ya
gaya min. Abinda nake so inji shine
menene a tsakanin ku da har zai bar
asibiti a halin rashin lafiya, ya tsallake
matar sa da iyayensa ya taho wajen ki?"
Na cigaba da kallon yatsun hannu na
sannan nace "Daddy, Muhammad
shine ....... Shinake........Wannan
maganar........." "Shi kike so zaki aura" yayi
summarizing duk maganganun da nayi
niyyar yi masa. Nayi shiru bance komai ba
ina jin yadda zuciya ta take bugawa a
kirjina. "Haka ne?" Ya tambaya, na gyada
kai na ba tare da na kalle shi ba.

Ya jima shiru yana kallona sannan yace
"out of the billions of maza da suke
duniyar nan Safiyya babu wanda yayi miki
sai mijin da Safina take aure?" Naji
hawaye ya fara taruwa a idona. "ba
haramun bane ba tunda ku ba sisters
bane ba, zai iya auren ku ya hada ku ku
biyo Safiyya but common........ You are
smarter than this Safiyya you are above
this. Ta yaya ma hakan zata yiyu? Ta yaya
ma kike tunanin zan aikata hakan?"

Na dago kai ina kallon shi hawayen ido na
yana karasa gangarowa kan kuncina,
"Daddy shi nake so. I don't know anything
else, I don't know yadda za'a yi ko kuma
me hakan xai jawo I just know that I love
him" ya dakatar da ni yace "and that is
where you are wrong. Very wrong, Love is
just not enough. Just because you love
him and you think he loves you saboda
yana dukan matarsa da wulakanta ta
saboda ke doesn't make him the right
choice. He is all shades of wrong for you.
And ni ba zan aura miki shi ba".

Na fara girgiza kaina hawaye na suna
karuwa, "Daddy...." Ya daga min hannu,
"dalilai uku ne ya saka ba zan aura miki
shi ba kuma ban amince ko da ace gobe
na tashi babu rai ki aure shi ba. Na farko
saboda yana auren Safina, Safina tamkar
yaya take a gare ki mahaifiyar ta ita take
amsa sunan uwa a gare ki, Tun daga kan
Sa'adatu har kan Hussain babu wanda zai
amince da wanna shirmen da kike
shiryawa and if you insist you will loose
them just like you lost Ahmad, Dalili na
biyu shine Muhammad ba mijin kirki bane
ba, bana miki fatan ki auri miji mai irin
halin sa, ance idan zaka aura wa yarka mill
mai mata ka bincika kaga yadda yake treating matar sa ta gida saboda exact treatment zai yiwa second matar, Watarana kuma hannu zai daga ya mare ki
" you provoked him, Dalili na blyu shine iyayensa, if you insist on marrying him har iyaye suka shige maganar they will dig and they may find out, abinda muka yi
sacrificing a lot to bury, Gidan su kuma babban gida ne, How do you think they will treat you? How do you think, they will look at you?",

Na rufe fuska ta da hannayena ina cigaba
da kuka kasa kasa, Ya kamo hannun ya
rike, naji yadda nasa hannun suka yi zafi
yace "Safiyya, in daí na isa da ke ki
hakura da yaron nan. Kiyi addu'a, nima
zan yi miki addua, Allah ya baki wanda ya
fishi, Sa'adatu is still insisting on Mustapha but I told her like I did before that ba zan matsa miki ba, But you should think about that too", Na karbe hannuna
ina girgiza kai na tare da jin duk duniyar
tayi min kunci, ji nake kamar numfashi na
zai bar jiki na, Na zame zuwa kasan gadon na zauna sai kuma na mike nayi hanyar waje da sauri,
ina jin shi yana kira na da muryarsa da
take fita da kyar amma ban juya ba, ina zuwa dakina na tarar da missed calls din Muhammad a waya ta. Sai na zauna na rungume wayar a kirjina ina ta rusar kuka, gani nake yi babu abinda yayi min saura kuma a duniya. Babu wani sauran farinciki daya ragemin a duniya. Muhammad shine farin ciki na. Shi nake so

Ranar kwana nayi ina aikin kuka. Kaina ya
toshe na kasa yin tunanin komai
ballantana in hango wa kaina hanyar da
zata bulle da ni. Da assuba bayan nayi
sallah ina zaune akan sallaya ta naji ana
buga min kofa da karfi,

81 / 113