SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 113

78K to 81K   out of 336.6K words

kirkiro murmushi nace "dan inje dinner
din nan na taho tun daga Germany da sabon
yanka a cikina, bana jin akwaí abinda zai
hana ni zuwa",
17
11
7:46 PM
Na shiga toilet na tsaya ina kallon kaina a
madubi, saí a lokacín na kara fahimtar
abinda twins suke nufi da suka ce I looked
terrible dan da gaske I really looked terrible.
Idona ya kara fadawa kasa ya kuma loosing
all the light da suke cikin sa, fatar idon ta
yamushe tayi baki, fatar lips dina ta bushe
har tana neman tsagewa, ba zan iya tuna
rabon da in shafa mai a bakina ba, ko a
sauran jikina, Na tuna da da a gurina babban
abu mai muhimmanci shine skin care routine
dina, bana taba yadda inyi missing. Amma
yanzu da rayuwa ta nuna min shege banga
na fahimci komai ma guri yake samu. na fahimci komai ma guri yake samu.
Sanitary pad din jikina na chanja na sake
gyara kaina sannan na fito nace musu "na
shirya, ku zo mu tafi" suka kalli juna sannan
suka kalle ni, Hussein yace "yaya dinner ce
fa. Kuma dangin angon nan naga manyan
mutane ne sosai. It is going to be
extravagant ....." Na yafa mayafi na nace "ba
zuwa zanyi dan in burge kowa ba, zuwa
zanyi dan inyi wa yar uwata murnar sabon
auren ta. Wanda yaga ni ko shigata basu yi
masa ba sai dai ya rufe idon sa".
Doguwar riga ce a jikina ta yadi. Rigar aunty
Hajjo ce ta bani na saka da zamu taho
saboda tana da girma sosai kuma yadin
yana da laushi ba zai ke min famin ciwo na
ba. Rigar duk ta chukwuikuye saboda zaman
jirgi. Dankwalin rigar na daura a kaina na
rufe dankararren gashina da na manta rabon
da in taje shi. Sai kuma wani mayafi da ko
kadan bai shiga da yadin ba dana dora a
kafada ta.
Ganin basu da niyyar tashi mu tafi sai na
wuce su na ce "in kun gama ku same ni a
waje", A parlor na zauna ina jiran su, Esther
ta zo da sauri ta kunna min tv da ac, ni duk
basu dame ni ba, so nake inyi sauri inje in
aiwatar da abinda yake raina, Wajen 7:30
suka fito, still da alamar basa son inje, na
mike tsaye "kun gama?" Suma basu chanja
kayan jikin su ba, Hussain ya sake kokarin
hanani fita "yaya bedrest fa aka baki" ban
amsa ba nayi hanyar waje, sai kuma na dawo. amsa ba nayi hanyar waje, sai kuma na dawo
da baya nace musu "a ina ne gurin? Akwai
gatepass a hannun ku? Na iya mota ai zan
iya kai kaina in ba zaku kaini ba".
A dole suka fito muka shiga mota muka tafi,
sai da muka yi nisa nace musu "kar ku gaya
wa Daddy naje" basu ce komai ba.
Muna zuwa mukayi packing a inda aka
tanada, na zauna a mota ina kallon mutane
suna ta shiga gurin, ga kida har ya fara
tashi. Sai na rufe ido na ina kokarin karfafa
zuciyata. Yau zan ganshi. Amma a matsayin
mijin wata. A matsayin mijin Safina. Yayin da
ni kuma nake matsayin matar wani. Matar
Mukhtar. Sai da naga alamar gurin ya cika
sosai sannan nayi karfin halin fita daga
motar, tunda na fita naji alamar jiri yana
neman dibana amma na daure dan bana son
twins su sani, na taka a hankali naje har
bakin kofar na bayar da katin da twins suka
bani sannan na shiga. A gurin muka rabu da
su su suka tafi bangaren maza ni nayi na
mata. Dama abinda nake so kenan. Ina
kallon security din yana bina da kallo, maybe
ya dauka almajira ce, Daga can karshe na
samu guri na zauna saboda bana son wanda
ya sanni ya ganni, Duk da dai nasan a yadda
nake din nan ba kowa ne wanda ya sanni zai
gane ni ba, A haka har guri ya gama cika aka
fara gabatar da event, Ina ji aka yi
announcing zuwan iyayen su Muhammad da
Mufida, suka shigo cikin isa da burgewa.
Sannan aka shigo da iyayen angon Mufida,
suma suka wuce, sal iyayen amaryar. suma suka wuce, sal iyayen amaryar
Muhammad, wato Safina, Mommy ce a gaba
da yan uwanta suna take mata baya, nayi
ajjiyar zuciya, wato ta baro mijin nata a
asibiti ta taho dinner. Daga nan kuma sai aka
y announcing shigowar angwaye da amare.
Na mike tsaye daga inda nake ina hango
kofar da zasu shigo ta cikin ta. Su
Muhammad ne a gaba. Ido na fuskarsa ta
fara gani. Yayi kyau iyakacin yadda dan
Adam ya kamata yayi kyau. Gefensa ga
yayata nan Safina, taci kwalliya ta ajin
karshe, fuskar ta dauke da murmushi idonta
a kasa kamar mai jin kunyar mutanen gurin.
A bayan su abokan Muhammad ne, most of
which na sansu, da kuma kawayen Safina,
gabadayan su na san su. Kowannen su cikin
kwalliya ta alfarma kuma cikin farin ciki. A
raina nace gabakidayan su munafukai ne,
tun daga kan Muhammad din har zuwa kan
securities din gurin, duk munafukai ne.
25
14
7:46 PM
Sai naji a raina ina fatan ina ma dai ginin
gurin ya rushe ya fado a kan mu gabaki
dayan mu mu mutu kowa ya huta.
Ina na tsaye har suka je suka tsaya a
tsakiyar fage, aka ringa kiran iyaye suna yi
musu ruwan kudi, daga inda nake ina hango
yadda Mommy take watsi da kudi. Kudin da
ba ita ta nema ba, Sai da aka gama aka ce
suke su zauna. And those minutes daga
shigowar su zuwa zaman su, zan iya cewa
are one of the most terrifying minutes of my. are one of the most terrifying minutes of my
life.
Suna zama aka yi announcing shigowar
Mufida da angon ta. Nan da nan sai hankalin
mutane ya koma kansu. I took my chance.
Burina shine in hargitsa bikin ba tare da nayi
calling attention din mutane zuwa kaina ba,
not that I care about mutane, but bana son
Daddy ya sani. Bana son yasan komai.
Na bi ta gefen mutane har sai da na wuce
inda mutane suke zazzaune. Ina jin jiri yana
dibana amma na cigaba da daurewa. Daga
inda nake ina hango Muhammad da Safina
akan kujerun da aka tanada saboda su.
Idonsa yana kasa yana daddanna wayarsa,
ita kuma tana magana da wata kawarta
Husna. Na taka a hankali na tafi inda suke
idanuna a kansa, zuciya ta tana jera duk irin
zagin da ta iya tana yi masa. "Munafiki.
Mayaudari. Maci amana" sai dai kuma kiran
tasa zuciyar take yi, so take ya amsa, so
take ya dago ya kalli cikin idona ya gaya min
dalilin da yasa ya auri yar'uwata.
Tamkar wanda tasa zuciyar taji kiran tawa,
sai ya dago idonsa a lokaci daya suka fada
cikin nawa. Ina kallon sanda wayarsa ta
zame daga cikin yatsun hannun sa ta fadi
akan carpet din gurin. Ya mike tsaye a
hankali kamar wanda ake jansa da zare. Na
cigaba da tafiya idona a cikin nasa har sai da
naje na tsaya a gabansa tsakanin mu bai fi
taku daya ba. taku daya ba.
Sai a lokacin Safina ta ganni, ta zabura
kamar wadda aka watsawa wuta. Na dauke
ido na daga cikin nashi na mayar kanta nace
"hello dear sister. Na taho daga Germany
nazo nan gurin musamman dan ke, dan inyi
miki HML. Happy Married life to you" na
mayar da ido na kansa, har lokacin ni yake
kallo da idon da ban san yadda zan
kwatanta shi ba. Nace "and Happy married
life to you too".
Sai na juya a hankali na sauka daga kan
stage din, doing everything in my power dan
ganin na hana kaina faduwa a gurin, bana
son Daddy ya sani. Wata kofa na gani a kusa
da stage din, kamar masu rabon abinci ne
suke fitowa daga ciki. Nayi sauri na shiga, na
wuce su suna ta hidimar su, na ga wata kofa
na sake shiga sai na ganni a waje, kamar filin
bayan gurin ne. Na tsaya ina tsakar
numfashi da sauri dan in samu in daidaita
bugun zuciya ta,
Ji nayi an finciko ni da karfi an juyo dani,
saura kadan in karasa shidewa, Muhammad
na gani a tsaye a gaba na fuskarsa da yana
yin da ban taba ganin ta cikin sa ba, yanayin
da ba zan iya kwatantawa ba, EPISODE EIGHTEEN
15
> 5
3
owner
2
7:43 PM
Safiyya
Episode Eighteen: New Couples
Paid advert
*Contact Bojuwa HERBAL'S for all your*
*kayan mata for*
*Amarya*
*Uwargida*
*Bazawara*
*Mai jego*
*Saiwowin sanyi gangariya da na dahuwar
kazar sababi har da na tattabaru da ciccibi
all from Chad.*
*Kayan gyara masu kyau da inganci kala
daban daban, special maganin sanyi for
women of class*,
*Contact Surayya HALIN YAU on*
*08032773332*, Sai da nayi amfani da dukkanin karfin halin
da rage a gare ni sannan na iya cire idona
daga cikin nasa na sauke su akan hannu na
daya rike sannan na sake kallon sa nace
"careful, ni matar aure ce" ya kalli hannun,
daga alama shi kansa bai san ya rike ba,
sannan ya sake shi da sauri yace cikin daga
murya "then what are you doing here? Me
kika zo yi nan?"
Nace "kamar yadda na fada muku a ciki kai
da matar ka, zuwa nayi in taya ku murnar
auren ku, ko kaga nayi wani abun ne bayan
haka?" Ya fara girgiza kansa "no. no. no,
nasan me kika zo yi gurin nan. Na san me ya
kawo ki. You came here to torment me. Why
me? Me nayi miki? Shin soyayya ta koma laifi
ne ni ban sani ba? After all the yaudara ta da
kika yi for years before kika ce min kina da
aure and you asked me not to contact you
again and you were pregnant and ......."
"Ya
kare min kallo "where the hell is your
pregnancy?" Ya fada looking as confused as
ever.
Nace "wrong question. You asked the wrong
question, Babu hadin ka da cikina and you
have no right to asked for it. Now I will ask
you the right question, Shin saboda kana
tunanin na yaudare ka...."
"Tunani?" Ya
tambaya "kina magana kamar baki yi ba. Kin. tambaya "kina magana kamar baki yi ba. Kin
yaudare ni kema kin sani, kin......" Na katse
shi "is that why you marry my sister?
Saboda kana tunanin na yaudare ka or do
you really love her?" Nayi masa tambayar da
ita ce take keeping dina awake all these
hours.
Ya tsaya yana kallo na kamar a lokacin ya
lura da ni a gurin. Ya bude bakin sa a hankali
"your....
." Sai kuma ya juya ya kalli hall din
da muka fito daga cikin sa "your sister?" Ya
tambaye ni kamar wanda bai ji abinda nace
ba sosai. "She is your sister" ya fada as a
statement, not as a question "she is your
Safina" ya sake fada a hankali, more like
talking to himself. And in that moment I
realized the truth. Bai sani ba. Bai san wa ya
aura ba.
And ni kaina ba zan iya cewa ga abinda naji
a zuciyata a game da hakan ba. Yes I felt a
relief, relief that he didn't intentionally do it.
And then a surge of pity, pity for him. Wani
tausayinsa naji ya lullube ni. He is innocent,
his innocence yana daga cikin dalilan da
yasa nayi deciding rabuwa da shi so that he
can continue to live his innocence life. And
now he got dragged back into it and tangled
in a web da ni bansan yadda zanyi in
warware shi and set him free ba.
Na fara girgiza kaina a hankali ina ja da
baya, sannan kuma na fara sauri zuwa bakin
titi nayi sa'ar taxi ta sauke wata na shige
ciki. Na rufe ido na ina mayar da numfashi ciki. Na rufe ido na ina mayar da numfashi
na a hankali hannuna a dage da ciki na gurin
da akayi min aiki dan ba jaramin azabar ciwo
yake yi min ba saboda tafiyar da nayi da
sauri. Sai da mai motar ya tambaye ni sau
biyu sannan na samu na bude baki na gaya
masa address din inda zai kaini.
A hanya sai na samu kaina da kasa zabar
tunanin da zanyi. Tun sanda na ga hoton
Muhammad da Safina babu irin lissafin da
banyi ba na abinda zanyi musu, a cikin jirgi
kuma babu irin plan din da ban shirya ba na
yadda zan hargitsa dinner din su. A cikin
plans din nawa har da petrol nace zan siyo
gallon daya in zazzaga a hall din in kunna
wuta. But I didn't do any of my plans. But
still I feel satisfied. My mission has been
accomplished. Dan a yadda na bar
Muhammad nasan dinner din nan ta kare a
gurin sa shi da Safina. Shi da kansa zai
hargitsa bikin nasu da kansa.
Da kyar na iya shiga gida bayan an sauke ni
saboda azabar ciwo, ina zuwa na samu na
sha magani na kwanta a parlor, har wani
gumi ne yake karyomin saboda azaba, a
haka bacci ya dauke ni. Cikin baccin naji
hayaniya, na farka amma ban bude ido na ba
sai naji muryar Mommy tana masifa,
13
7
2
1 7:51 PM
"Wallahi ba'a isa ayi mana wannan
wulakancin ba, chafdi, Basu san wace
Sa'adatu ba. Ba'a haifi wanda ya isa yayi min. Sa'adatu ba. Ba'a haifi wanda ya isa yayi min
wannan wulakancin in yi shiru in barshi ba".
Naji Muryar kanwarta da muke cewa Aunty
karama "dan Allah ki bar maganar nan
Sa'adatu. Tunda mun dauko yarinyar mun
taho ba shikenan ba, dole ai zasu bio mu
har gida su bada hakuri in dai suna so a kai
musu ita".
Na bude idona a hankali na kare musu kallo,
Mommy ce tayi kicin kicin, daga dukkan
alamu tafi awa daya tana fada, sai kanwarta
Hajiya karama da wata kawarta. Sai kuma
Safina a can gefen su ta kwanta ta kifa kanta
akan kujera, da kawarta Husna a zaune a
gabanta. Na mayar da ido na na rufe. Suka
cigaba da maganganun su, a cikin maganar
na fahimci suna fada ne akan wai tunda
Safina suka shiga da mijinta gurin dinner
suka zauna, shikenan ya tashi yayi tafiyar sa
ya barta ita kadai a zaune. Mufida tana
zaune da mijinta ita kuma Safina tana zaune
ita kadai. Anyi ta nemansa an rasa inda yayi,
anyi ta kiran wayarsa a kashe. Ita ma Safina
tace bata san inda yaje ba. Dan haka sai
concentrating bikin aka yi akan Mufida, ita
kuma Mommy ta gaji da ganin yarta tana
zaune a high table kamar decoration ta
dauko kayarta tana masifa mutane suna
bata hakuri ta fito daga gurin dinner din.
Mommy ta cigaba da fada "kuma wallahi
banga wanda ya isa ya kai min ya gidan sa
ba a yau, Idan kinga an kai yarinyar nan
gidan sa sai yazo har cikin gidan nan ya
bamu hakuri tukunna", bamu hakuri tukunna".
A yadda aka tsara bikin nasu a yau za'a kai
amare gidajen su, daga gurin dinner za'a
wuce dasu, amma Mommy yanzu tace ba
za'a kai Safina ba sai Muhammad yazo ya
bada hakurin tafiya da yayi ya barta a stage
kamar flowar decoration.
Na tashi na zauna ina jin ciwon ya danyi min
sauki sannan kuma hayaniyar su tana
kokarin saka min ciwon kai. Na gaishe su
suka amsa min babu yabo babu fallasa dan
duk rayukan su a bace suke, muka gaisa da
Husna ita ma tayi min sannu tace taji ance
bani da lafiya. Na amsa mata da "da sauki ai
sosai. The worst is over insha Allah. Na kusa
inyi getting my life back insha Allah" Na
mike nace da Mommy zan koma daki in
kwanta ta gyada min kai kawai. Ina jin Hajiya
karama tana tambayar ta "wanna yarinyar
wanne ciwo take yi ne haka Sa'adatu? Kinga
yadda ta koma kuwa?" Mommy ta tabe baki
tace "ulcer ce ta sako ta a gaba, tayi mata
mugun kamu har sai da ta kai ani mata aiki
a hanji. Yara ne kayi ta fama dasu akan suci
abinci ba zasu ci ba wai su dieting suke yi,
wai su sunfi son su rame, gashi nan ai ta
jawo wa kanta rama mai guarantee". Ni dai
na wuce na shige dakina tun kafin a fara yi
min fada akan laifin da ban aikata ba.
One thing da nake respecting mommy akai
shine ko yanuwanta da suke uwa daya uba
daya ba ta gaya wa abinda ya same ni ba,
kuma ba ta bari sun ganni da cikin ba, kuma ba ta bari sun ganni da cikin ba.
Ina shiga dakin na shiga toilet nayi wanka na
gyara jikina nayi shirin kwanciya bacci, ina
jin yunwa but I did not feel like eating
anything and did not care. Sai kawai na
kashe fitila nayi kwanciya ta, somehow I was
satisfied with tafiyar da Muhammad yayi ya
bar Safina, my bad girl part wanted more
than that but na san idan da akwai abinda
yake so kuma yake respecting a duniya sune
iyayensa, ba zai taba disrespecting dinsu a
gaban mutane ba. And at least she gets to
sleep alone in her room today, maimakon a
dakin Muhammad kamar yadda ta saka rai.
Ina nan kwance idona a rufe naji motsi an
shigo dakin nawa, sannan aka kunna fitila.
Na bude ido naga Safina a tsaye a bakin
kofa, idonta da alamun tayi kuka. Na koma
na kwanta na mayar da idona na rufe. Naji
alamar ta zauna akan gadon sannan naji
tace "Safiyya….... An samu
misunderstanding. Na san kina gain kamar
nayi miki laifi. Amma ina so in gaya miki
cewa coincidence ne. Ni ban san wanda na
aura shine tsohon saurayin ki ba. Tunda ni
dai baki taba hada ni da shi ba ban taba
ganin sa ba sunan sa kawai na sani. Suna
kuma yakan....
.." Na bude ido na na mike
zaune na zuba mata ido sai tayi shiru ta
kasa cigaba da maganar, na nuna mata kofa
nace "Safina, with all due respect, get out of
my room, Ke karyar ki ko sallah ma bata yi, it is making
me nauseous, dan Allah ki fita tun kafin
karyar ki ta saka ni aman takaici"
Ta yi shiru tana kallona. Na sake nuna kofa
"out I said. In na cigaba da ganin ki ko jin
muryar ki tabbas za'a fitar da gawar daya
daga cikin mu daga cikin akin nan". Ta mike
tsaye har takai bakin kofa kuma sai ta sake
juyowa tana kallo na tace "it is obvious kin
dauki maganar da zafi da yawa, kar ki manta
amma na farko ke a yanzu matar aure ce. Na
biyu ya gaya min ke kika yi breaking up with
him. Yes, na san yana son ki har yanzu
amma kar ki manta shi namiji ne, namiji yana
iya son yaya ya dawo kuma yaso kanwa ko
da uwarsu daya ubansu daya, ballantana mu
da babu hadin jini. And a matsayi na na
mace, making him fall in love with me is
going to be the most easiest thing ever. Ina
miki fatan alkhairi ke da naki mijin." Nayi
murmushi nace "mun gode, now go and
open your room ki shiga ki jira har sai yazo
gida ya baku hakuri sai kije ki saka shi ya so
ki din".
Na koma na kwanta na rufe idona ina jin
zuciya ta tana tafasa, da gaske idan Safina
ta cigaba da tsaya wa a gurin nan ta kuma
cigaba da kiran kanta matar Muhammad
za'a iya rasa daya daga cikin mu. Addu'a
nake a raina ta fita din, ba dan ina gudun
abinda zanyi din ba sai dan ina tunanin. nake a raina ta tita din, ba dan ina gudun
abinda zanyi din ba sai dan ina tunanin
mahaifina daya ke kwance bashi da lafiya.
Bata fita ba din kuwa sai ta cigaba da
magana. "Haka ne, zan jira shi kamar yadda
Mommy tace. Na san kuma zai zo, kamar
yadda na san cewa zai so ni kuma zai manta
da ke, musamman idan ya san abinda kika
yi, abinda na tabbatar ba ki gaya masa ba,
abinda na san kunyar gaya masa ne ya saka
kika zabi rabuwa da shi"
Na sake mikewa zaune da sauri, sai da naji
ciwona ya amsa, sannan na bude abin da na
rufa da shi na mike tsaye ina kallon ta "are
you threatening me?" Ta ja da baya, daga
alama taji

27 / 113