SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   84 / 113

249K to 252K   out of 336.6K words

nan?” Nace "Mommy al ba kya nan ne shi….” Tace kin san bana nan ne? Na tabbatar baki sani ba kuma baki neme ni ba saboda ke yanzu kin zama yar kanki ko? Ba'a isa ayi miki fada ba sai ki dauki fushi da mutane. Ina daukan ki me hankali
ashe kema shashasha ce irin Safina. To wallahi bari kiji in gaya miki, abinda kike nema will never happen. Babu ta yadda za'a yi miciji ya sare ni a kafa daya kuma
in sake mika masa daya kafar. In zaki dawo hankalin ki ma ki dawo tun kafin lokaci ya kure miki. Shashasha". Sai na juya nayi hanyar stairs. Tace "ai ba ce miki nayi na gama ba" na juyo na dawo amma sai na zamu guri na zauna danna fahimci ba yanzu zata gama fadan ba. Ta kuwa cigaba yin abinta. Ni dai na zauna
kaina a kasa, ina yi ina kallon agogo ina lissafin lokacin meeting dina yayin da ita kuma ta cigaba da juye fadan ta a akaina.

Allah ya taimake ni sai ga Dr Ma'aruf ya shigo, shigowar sa ce ta saka tayi shiru ta amsa gaishe ta da yake yi sannan ya zauna ya miko min wata takarda yana yi min bayanin bills ne na dukkan expenses din da aka kashe a wanna karon da kuma kudin machines din da akayi order. Na dudduba tare da sauke ajiyar zuciya nace "same account da wanda na tuna muku last month?" Yace "eh" Na mike nace okay, zan hado maka da salaries dinku for this month, shikenan sai mu gama dasu. Yayi murmushi "that will be good. Thank you"

A haka na samu na zame na hau sama kamar zuwa zany in yi transfer din amma kawai sai na ajiye takardar nayi kwanciya ta na rufe idona. I knew I have achieved something with Mustapha amma kuma
maganar komawar Safina gidan Muhammad tana neman dagula lamari na. Ba wai na saka ran ba zata koma ba ne ba amma kawai da najinta koma din sai naji kishin ya motsa. Ni kaina ban san yadda
za'a yi wannan lamarin ba. Na dai san kawai cewa ina son Muhammad. Ban kuma saukowa ba sai da na gama dukkan meetings dina da na gabatar online. Ina gama wa na rubuta wata takarda na tura e-mail din Uncle Ahmad sannan nayi refreshing na saka riga da
skirt na atampa na daura dankwalin atampar sannan na saka mayafi na kuma feshe jikina da turaruka masu tsada na fito.

Dakin Daddy na fara shiga. A zaune na same shi Dr yana ta yi masa wasu bayanai shi kuma yana gyada kal alamar fahimta, Na zauna sai da suka gama sannan na karaso na gaishe shi, Ya amsa min, yanzu
muryar ta fito amma can kasa, Nayi murmushi, Dr yace "jiki alhamdulillah, Kar ki damu kinji?" Na gyada kaí tare da kara matsawa kusa da Daddy na rike hannunsa nace "Daddy zan fita, Zanje gidan uncle
Ahmad. Yanzu zan dawo insha Allah", A idonsa naga alamar yaji dadin magana ta, sai ya danyi mun murmushi kadan, Ina fita daga parlourn a na dauko shades a cikin jaka ta na saka a idona, Ina fita
harabar gidan naga guards dina sun tashi zasu tafi gurin motasu sai na kira su da hannu na, suka karasa and I said "I don't feel like driving today" da sauri daya ya koma ya kawo motarsu zuwa inda nake,
daya kuma ya bude min baya na shiga sai ya zagaya ya shiga gaba kusa da dan uwansa muka tafi, A hanya na gaya musu address din inda zamuje, gidan uncle Ahmad, Na dauko waya ta na a duba naga missed calls from Muhammad amma sai na share shi,
Haushin sa nake ji duk da bai yi min komai ba. Amma kuma sai nayi amfani da lokacin wajen saving number din sa da sunan da yake kai tun da "Pyar💕”na kuma bata lokaci wajen zaban hoton sa a cikin hotunan sa da nayi retrieving na saka akan number din sa, na kuma zabi ring tune mai dadi mai cike da kalaman
soyayya na saka masa, sai dai still da ya Kira ni ban dauka ba. A raina nace *kaje Matarka tana gida tana jiran ka*.

A kofar gidan uncle Ahmad muka tsaya muka yi horn aka bude gate muka shiga, amma sai na zauna a mota nace su tambaya suji ko mukhtar yana ciki, suka
dawo suka ce baya nan sai na fita sannan nace musu idan ya dawo kar su barshi ya shiga ciki har sai na gama na fito.

Ina shiga cilkin parlour da sallama naga Umma ta fito daga Kitchen. Sai kawai ta tsaya tana kallona. Na cire shades din idona na durkusa na gaishe ta. Ta amsa still fuskar ta da mamakin ganina sai nace "Umma ina su Salima, ina Uncle?" Sai ta kalli dakin Salima sannan ta juya ta kalli hanyar part din uncle Ahmad amma still
bata de komai ba. Sai na mike tsaye nace *Umma uncle din yana kusa? Zan iya ganin sa?" Ta dan gyara fuskarta tana kokarin cire mamaki daga cikin ta tace
"bara inyi masa magana. Salima tana cilki zaki iya shiga" nace "zan shiga, bara in ga uncle tikunna".

Sai ta juya ta shiga part din uncle Ahmad da sauri, Ina nan zaune sai ga Yaya ya shigo, nay kokarin gaishe shi sai naga yayi min kallon banza ya wuce yana cewa
*dama ke kika ajiye mana wannan bakar motar da wadannan bakaken mutanen a kofar gida kenan" ban ce masa komai ba sai ya shige dakin Salima. Yana shiga sai ga ta ta fito, ta tsaya a bakin kofa tana
kallona kamar yadda nima nake kallon ta. *Fiyya" ta fada a hankali. Na dan yi mata murmushi "hello Salima" ta karaso cikin falon tana murmushi itama. Kafin ta zauna uncle Ahmad ya fito tare da Umma. Na
mike tsaye cikin girmamawa sai da ya zauna sannan na zauna nima a kasa, Umma ta zauna a gefensa tana kallo na fuskarta da expression din self pity. Na
gaishe da uncle, ya amsa min idonsa a kasa sai nace "'Uncle dama zuwa nayi in tuna maka da cewa Daddy ba shi da lafiya. You should be with him. He misses
you. Na san kuma kaima kana missing dinsa" yayi shiru sai kuma yayi magana muryarsa tana rawa "me zance masa idan naje?" Nayi sauri nace masa "kace masa ya jiki? Sai kuma ku cigaba da maganganun ku yadda kuka saba" duk muka yi shiru sai na sake cewa "tun kafin ku san zaku same mu kuke tare, you shouldn't be apart because of us" Umma tace "haka ne. Nima na gaya masa, Kin gan shi nan kullum yana kwance a daki cikin damuwa. Amma insha Allah zai je in an jima* nayi murmushi nace "ke ma ya kamata kije Umma, Kera ai kanwar Daddy ce. Ya kamata kema ki je ki ga jikin sa zaiji dadi.

Ban jima sosai ba saboda babu abin magana sosai., Sun kasa sakin jiki suyi min magana sai na mike nace zan tafi, amma sal na kalli Salima nace "ki zo mu tafi tare Salima. In sun je in an jima sai ku taho tare" ta juya ta kalli Umma sannan sai ta koma dal da sauri ta dauko mayafin ta ta fito. Sai da zan fita nace da uncle Ahmad "uncle na tura maka sako email dinka. I will appreciate a response as soon as possible. The management misses you.

Tare muka koma gida da Salima. Muna ta hira sama sama sai dai daga dukkan alama ita ma tsintar kalimomi take yi wajen yi min magana, Mostly akan lafiyar Daddy take min tambaya ina amsa mata. Tayi magana akan wayata da take ta hasken kiran da Muhammad yake ta jera min. ana ta kiran ki fa* na kalli wayar "share shi kawai" "shi?" Tace tana murmushi, nayi murmushi kawai bance komai ba sai ta dau wayar tawa da wani kiran ya shigo ta amsa ta saka a kunnen ta, na dago kai tare da bude ido ina kallon ta cikin mamaki. Sai naga tayi dariya tana rufe bakin ta da hannun ta sannan tace ba ita bace ba. Kanwar ta ce" eh muna hanya ne, naga kamar kayi laifi ne kana ta
Kira ank dauka shine na taimaka maka na dauka* *okay to gamu nan karasowa" ta fada dai dai lokacin da muka sha kwanar shiga layin mu. A take na hango motar Muhammad a tsallaken gidan mu. Na juya
ido na sannan na dauko shades dina na mayar dasu ido na nace da driver din ya tsaya a waje, muna tsayawa Muhammad ya bude motarsa ya fito ya tsaya a gaban ta tare da saka hannayensa a cikin aljihun
sa. Na cigaba da zama a motar ina kallon sa, yayi kyau sosai cikin dinkin shadda ruwan toka mai duhu, rigar mai kananan hannaye ce wadda ta fito da damatsen hannunsa da naga sun kara girma fiye da
yadda na san su, Fatarsa tana kyalli, iska tana kada yalwataccen gyararren gashin kansa. Salima ta taba ni sannan tace min a hankali "he is hot" nayi murmushi
sannan na bude kofa na fita, a tare security din suka fito sai nace musu su wuce ciki kawai,

I purposely cat walked toward him. Irin tafiyar da na tabbatar ta karasa susuta sauran tunaninsa. Sai dai yadda ya zuba min ido ya saka naji ina kamar zan fadi
amma na samu da kyar na karasa inda yake. Ya danyi gyaran murya yace "you look stunningly beautiful. You took my breath away", Sai na daga gira na dauke
kai gefe daya. Ya zagaya side din da na juya fuska ta tare da hade hannayensa a guri daya yace "ban san laifin da nayi ba. Whatever it is. Na dauki laifin 100 percent and I am sorry" na murguda masa baki sannan na sake dauke kaina "ni gida zan shiga yanzu" yace "not until you tell me me nayi" nace "ya kamata kai ma ka koma gida, Matarka tana jiran ka., Gwara kaje da wuri kar ka yi laifi" and I saw him smiled har sai da hakoran sa suka bayyana "my sweet Piya" ya fada a
hankali. Na juya ba tare da nace masa komai ba zan tsallaka in shiga gida sai ya biyo ni ya sha gaba na sannan ya saka hannu na cire shades din idona "there is no way da zan koma gida ba tare da na kalli idon ki ba" na watsa masa harara trying so hard not to smile and kamar ya sani sai cewa yayi "now smile" and my
stupid heart obeyed her master and I smiled at him, har da lumshe ido da budewa. A hankali yace “much better” sannan ya mayar min da shades dina yace “now I can go home and eat” yajuya yana tafiya da baya da baya yana kallo na har sai da bayansa ya taba motarsa sannan ya juya ya shiga ciki, blew me a kiss.

Maman Maama ✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹SAFIYYA ❤️‍🩹


Episode Fifty Six: The Talk

Har na shiga gida da murmushi a fuskata, ina jin sansa a raina sosai sannan kuma at the same time ina jin haushinsa saboda komawar matarsa gidan sa, sai dai ni kaina nasan kishi ne ya saka ni jin haushin ba komai ba, and I asked myself "idan auren ya tabbata, am I ready to share him with Safina?" nayi sauri na kawar da wanna tunanin daga raina sannan nayi replacing dinsa da tunanin ciwon Daddy. Part din sa na wuce, na tarar yana zaune akan gado an saka masa pillows a bayan sa yana kallon tv yana sauraron karatun Alqur'anin da yake fitowa daga ciki, a hankali bakinsa yana motsawa alamar yana bin karatun. Na zauna a kasa a gabansa nima na cigaba da binsu. Sai kuma na tuna da Salima da muka zo tare, na dauki waya ta na tura mata message na gaya mata inda nake na kuma gaya mata zata iya shigowa. Ba'a jima ba sai gata nan ta shigo, ita ma ta samu guri ta zauna a gefe na ta cigaba da bin karatun kamar yadda ta tarar muna yi.

Hussain ne ya shigo, ya sanar mana da cewa lokacin sallah yayi sannan ya dauko bowl yazo ya fara yiwa Daddy alwala, daga nan muka koma cikin gida muka tafi dakina tare mukayi alwala muka yi sallah, Bayan mun idar ne Salima ta tashi tana ninke sallayar da tayi using tace "wai safiyya da gaske wancan gayen kike jawa aji?" na danyi murmushi nace "shi waye da ba za'a ja masa aji ba?" Tace "ya hadu, nake gaya miki ya hadu, most girls will sell their kidney to have him look at them" nayi dariyar yadda tayi maganar nace "Allah ya basu sa'a, now forget about him mu sauka kasa mu ci abinci. I am hungry" muka sauko muka zauna a dining amma still bata daina maganar sa ba "dan kuka
yi aure wato za'a ga kyawawan yaya" nayi murmushi kawai bance komai ba dan bana son yin maganar anan sai ta sake cewa "I wanted auren ki da Yaya Mukhtar ya dore, I was even picturing the nephews and nieces da zaki haifa min, amma Allah ya fi mu sanin dai dai. I wish you happiness, where ever and with who
ever" naji dadin maganar ta nace "ameen, thank you", Na fahimci siblings din Mukhtar basu san gaskiyar abinda ya raba mu ba, ban san me iyayen suka gaya
musu ya faru ma. Maybe shi yasa na fahimci yaya yana jin haushina dan shine ya tarar da yadda na daure yayansa tsirara akan gado.

Da sauri muka ci abincin muka koma wajen Daddy, muka tarar Mustapha yana bashi abinci sai na zauna a gefen gadon ina kallon su har yace ya ishe shi aka ajiye bowl din. Salima ta gaishe shi ya amsa mata tare da mika mata hannu yana murmushi, taje ta saka hannunta a cikin nasa ya tambaye ta ina Salim sai tace
yana school, da yake boarding yake yi a Lagos, sai ta kama yiwa Daddy hirar Salim din da irin dramar da suke sha idan yazo hutu, yana shekarar sa ta karshe ne yanzu. Daddy yana ta murmushi amma baya iya yi mata doguwar magana sai ita ce take tayi.

Fahimtar da nayi cewa yau surutu take ji sai na fara tsoron kar ta bawa Daddy labarin hadadden gayen da yazo gurina dazu, Allah ya taimake ni dai bata bashi labarin ba har su uncle Ahmad suka shigo tare da Umma, bisa jagorancin Hassan. Suna shigowa Mustapha ya gaishe su ya fita. Na sauko kasa nima na barwa uncle Ahmad kusa da dan wan sa ya zauna ya
gaishe shi, Daddy ya hade rai ya amsa sannan ya dauke kansa gefe, Umma ma ta galshe shi tare da duba jikin sa ya amsa mata itama babu yabo babu fallasa. Uncle Ahmad ya fara inda indar bashi hakuri dan ya fahimci fushi yake yi, Umma tana kokarin taya shi. Daddy yace "sai da Safiyya taje tayi maka magana sannan zaka zo ka duba ni?" Umma tace "yaje asibiti ai, lokacin baka sani ba", Daddy yace "bai san gida na ba kenan sai asibiti ya sani? Ke ma baki san gida na ba?" suka cigaba da bashi hakuri mu dai sai muka tashi muka koma cikin gida.

A parlor muka zauna, su Mommy duk suna zaune banda Mustapha, na gaya wa Mommy zancen zuwan su uncle amma sai naga ta dauke kai tana bata fuska tare da magana kasa kasa. Muka cigaba da zama muna hirar mu da Salima tana bani labarin ita ma shirye shirye graduation dinsu da suke tayi, sai
na samu kaina da tunanin nima fa da yanzu ina shekarar karshe a jami'a, ko zan koma watarana? Na samu kaina da tunanin kawayen da nayi a MD wadanda yanzu duk na watsar da su saboda yawan
tambaya ta dalilin barin makaranta ta da suke yi da kuma tambayata ranar da zan dawo. Nayi ajiyar zuciya ina tuna shekaru bitu da yan watannin da nayi a makarantar, they were the most carefree days of my life,

Muna nan zaune sai ga Mustapha ya shigo, yana zama sai naga ramla cousin din Safina da take gidan ta ta shigo itama tare da wadansu mata da na lura yan aikin Safina ne, na cigaba da baza idon ganin Safina sai naga bata shigo ba, na mayar da hankali na kan Mustapha sai naji yana. ce da Mommy, "gasu nan na dauko su, jikin ta zai gaya mata ai" Mommy ta bisu da kallo suna gaisheta tana amsawa dai dai sai ta kira Esther tace ta kaisu dakin da zasu zauna, tace da Ramlah ita kuma ta kai kayanta sama inda suke sauka in sun zo. Sai da suka tafi sannan tayi kwafa tace "zata san da ni take yi ne. Bani na kai mata yan aikin ba? To na dauke kayana, sai inga yadda zata kula da gidan da kuma kanta da hannu daya da kafa daya" Hassan da yake gefe yayi dariya "Allah sarki yaya Safina, yau ta taro match da Mommy" Mustapha yace "ita ta ja wa kanta ai, ni bana tausayin ta, har da
hawayen ta kuwa da nace nazo daukan su, nace mata tazo mu taho tare amma yarinyar nan ta ki" Mommy tayi kwafa "ba zata zo ba ai, babu yadda banyi da ita ba nima fa, Dazu ma sal da na kira ta a waya na kare mata zagi tas amma kamar da dutse nake"

Sai na koma kan kujera na kwanta na rufe har kafafuwana da hijab din jikina, jikina ya bani dalilin komawar Safina gidan Muhammad ba wai dan shi ko dan ita bane ba, ta koma ne dan ni, dan ta san hakan zai bata min rai kuma tana ganin cewa in dai ta fito to zata rage mana wahalar convincing iyayen mu akan
maganar mu, zaman ta a gidan zai karawa shiga ta gidan wahala. Mommy dai ta jera tsaki da kwafa sun kai cikin charbi, aka jima tace "kuma wannan dan iskan yaron ba taimaka mata zai yi da komai ba wallahi, Allah ya sa ma ya zauna a gidan" babu wanda yace komai sai kuma tace "Hussain ka shirya ka je ka kwana a gurinta, yau dai

84 / 113