SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   43 / 113

126K to 129K   out of 336.6K words

yi kama da abinda
kake fada ba, kama take yi da matan
masu kudi. Ka sani ko mijinta ne? Ko aure
ta yi? Safiya kiyi min magana mana ina ta
yi miki magana".

Still Safiya bata ce komai ba, ta wuce ta
tsakiyar su taje ta hau ta kan kasar da
shekaru suka saka ta zaizaye ta zama
bata da yawa, ta fita daga gidan ta koma
mota inda ta bar Adam.

Yana tsaye a jikin motar yana kallon cikin
gidan, daga dukkan alamu hankalin sa
ba'a kwance yake ba, yana gain ta fito
yayi ajiyar zuciya sannan ya bude mata
kofa ta shiga ta zauna a dai dai lokacin da
yaya Malam ya kawo kai yana kokarin
shiga gidan, ya tsaya yana kallon motar
daga alama bai gane wacce ta shiga cikin
motar ba, Safiya ta bishi da kallo, yana
nan kamar yadda ta san shi, ssi dai
shekaru da suka karu akan na da, sai
kuma shekarun suka saka taga yayi mata
kama da baban su. Ta rufe ido tana
kokarin tuno wa da fuskar Baba, suna
kama sosai da yaya Malam, ta bude idon
tace da Adam, "Drive, please" ya taka
motar a dai dai lokacin da yaya Malam ya
gane ta yace "Safiya?" Amma bata amsa
masa ba kamar yadda bata amsawa kowa
a gidan ba.
Gidan Hajiya Kyauta tayi masa kwatance
suka je, Hajiya Kyauta tayi murnar ganin
su sosai dan dama bata samu zuwa bikin
nasu ba saboda bata jin dadi sosai. Suka
zauna suka yi hira da ita sannan suka ci
abinci. A lokacin ne take bawa Safiya
labaran abubuwan da suka faru a gidan
su, yayan ta Balarabe wanda Inna Sa'ade
take ji da shi a cikin yayanta ya mutu, ita
kuma kasar da ta kashe Sauda ita ce ta
lalata nata ginin na zamani sannan babu
zato babu tsammani dakin ya fado mata
ita ma cikin dare, abinda yayi sanadiyyar
kafafuwanta biyu duk sai da aka yanke su.
15
8
4
6:52 AM
Ita dama bata da yaya mata, yaya mazan
suka fara jinyarta kamar gaske daga baya
duk kowa ya kama gabansa sai Dauda da
yayi aure yanzu yake zaune a asalin dakin Baba Hadiza. Su sauran yayan daudan
suke aikowa kudi wai ya kula da
mahaifiyar ta su, shi kuma sai ya cinve
kudin. Hatta fitsari da bahaya a lokuta da
dama sai dai tayi su a kwance.

Inna Gaje on the other hand tsufa yazo
mata da tabin kwakwalwa, kanta ya kwace
bata gane kowa bata gane komai. Lami da
lantana duk suna gida suna zawarci. Anan
Safiya ta gaya wa Hajiya Kyauta abinda
yake ran ta. "Hajiya Kyauta ina son siyan
gidan mu idan zan samu. Ina son ki samo
min wanda zai siya da sunana dan ba lallai
su siyar ba idan suka ji ni zan siya" Hajiya
Kyauta tace akwai dan ta zai iya. Safiya ta
cigaba "so nake ya bisu daya bayan daya
yayi musu tayin siyan gidan, tunda gidan
gado ne nasan da yawa zasu siyar, ina da
takardun bangaren mu har yanzu a
hannuna, idan da zan samu ko da rabin
cikin ne sai in hada da inda muke da shi
ina son gina wa Baba Hadiza masallaci a
wajen. In kuma sunki siyarwa sai a samu
wani filin daban a siya ayi ginin" Hajiya
Kyauta tace "zasu siyar ma, Gabaki dayan
su fa a kone suke talauci yayi musu
katutu, babu wanda za'a yi masa tayin
kudi yaki karba, Wadanda kawai suke
cikin gidan sune babu tabbas din zasu
siyar, amma kuma sauran sunfi su yawa".

Bayan sun ci abinci sunyi sallah anan
gidan sai suka dauki hanya suka koma
Abuja.

Zuwan su Kura ya taimaka wa Safiya sosai
gurin samun composure da ajiye past
dinta a gefe ta kuma fuskanci future. Cikin
dan kankanin lokaci cinikin gidan su ya
kammala, kuma kamar yadda Hajiya
Kyauta tayi predicting haka ne ya
kasance, kusan kowa a gidan ya siyar da
kason sa, hatta Dauda ya siyar da nasa da
kuma na Inna Sa'ade, yayan Inna Gaje ma
sun ce a siyar da nata a basu kudin, Lami
da Lantana ne kadai su ka bijire dan basu
da gurin zama, sai Safiya tace a kara
musu kudin yadda zai ishesu su sami
gurin zama, bata son shiga hakkin kowa
ba kuma ta son takurawa kowa.
Ganin cewa in sunki siyarwa ma kason
subbashi da yawan da zai ishe su su
zauna a ciki sai suka hakura suka siyar
suka nemi rent din wani gidan suka tafi da
mahaifiyar su. Safiya kuma a bisa
amincewar hakimin garin ta fara cika burin
ta na gina katon masallacin da sunan
mahaifiyarta a matsayin sadakatul jariya a
gare ta. Gini aka tsara mai kyau irin na
zamani, tun daga harabar masallacin har
cikin sa abin sha'awa ne, Sai kuma Adam
vavi furnishina masallacin va saka duk abinda ake bukata tun daga kan fankoki
da mic da Alqur'anai da sauran littattafan
addini har carpets, ya kuma yi borholes
guda uku a zagaye da masallacin duk da
sunan Baba Hadiza. Bayan an kammala
komai sai suka danka masallacin a hannun
Haruna dan Hajiya Kyauta saboda
maintenance, suka ce duk abinda ya
lalace ko kuma abinda ake bukata sabo a
ciki ya kira ya fada musu.
And then life goes on. Suka koma back to
their various kasuwanci. Shekara guda
bayan auren su Safiya ta bude awara joint
a Abuja, tace ba zata bar sana'ar awara
ba. A shekarar ne kuma suka yi handing
over na shago da Hajiya, shagon ya dawo
completely na Safiya ne. A karshen
shekarar ne kuma kamfanin gold din da
suka yi investing in ya gama kammala ya
fara functioning, har zuwa lokacin dai
bass samun komai daga gare shi amma
kuma hankalin su ya kwanta tunda sun
zama confirm share holders na kamfanin.
Da shekara ta sake zagayowa ne aka fara
basu profit, Safiya sai da ta girgiza da
adadin kudin da ta gani a rubuce kuma
wai nata ne ita kadai a matsayin riba kawai
bayan jarin ta da still yake ciki. Adam ma
yayi mamakin nasa, tun farko ya san cewa
akwai alkhairi a cikin abin amma bai dauka zai kai haka ba. A take Safiya ta sake
mayar da ribar ta cikin kamfanin ta kara
girman share dinta, while Adam used his
own profit ya siya musu gidan zama a
Abuja. Dama ya gaji da biyan rent.
23
9
6:52 AM
The house was huge and it was all Safiya
have imagined as aljannar duniya. The
first thing she did a gidan shine enlarging
picture din su ita da Baba Hadiza da su
Sauda ta kafe a babban falon gidan.
Together, they furnished the house to
their exotic taste. Babu ce kawai babu a
cikin gidan. Sai kuma yaya.
Tun bayan auren Safiya take saka ran
ganin ciki amma shiru, duk wata sai tayi ta
addu'a ta kuma yi ta sadaka amma a
karshen watan ta sai taga period. Tun
tana tura maganar to the back of her
mind har ta fara fito da ita tana furtawa.
And Adam kept saying lokaci ne bai yi ba
that their princes and princesses are on
their way, amma shiru basu karaso ba. Sai
dukiya ce take zuwa. Her story and
marketing strategies became a legend,
Kullum cikin signing business contract
take yi da different companies wasu
neman shawara suke yi daga gare ta wasu
aiki suka bata to market their products
wasu kuma ambassador suka bata na

brand dinsu. Wasa wasa duk kamfanin da
ta fara hulda da su sai suga cigaba sai
wasu kamfanin suma su fara neman ta.
A shekaru uku na farkon auren Safiya tayi
signing business contracts babu adadin,
at a point, she even had to have her own
lawyer da zai taimaka mata wajen tace
contracts din kar taje tayi signing akan
abinda yake illegal. A lokacin Safiya tafi
Hajiya da Alhaji gabakidayan su kudi.
Ranar nan ta dawo daga wani taro a
gajiye, babu tunanin abinda take yi sai na
zuwa gida ta samu tayi wanka ta kwanta
ta yi dogon bacci. Sai dai tana tsayawa a
bakin gate ta ga mutane a zaune a kasa
dirshan, Allah ne kadai ya san dadewar su
a gurin. Sai dai duk da gajiyar da take ciki
da kuma rashin kyawun yanayin su, ta
gane su. Yaya Malam ne da Lantana.
Taji kamar ta saka reverse ta fita da motar
a guje, amma kuma gidan ta ne wannan
ba nasu ba, ita zata kore su ba su zasu
kore ta ba. Sai dai babbar tambayar anan
ita ce "ya akayi suka san gidan? Me kuma
ya kawo su", Tayi kamar bata gansu ba ta
danna horn. Mai gadi ya taso da sauri ya
bude mata gate a lokacin da suma suka
taso da sauri suka taho wajanta, yaya
Malam kamar zai fadi. ta danna motar cikin gidan a guje, tana packing ta hango
su suna rigima da mai gadi, yana kora su
waje yana kokarin rufe gate su kuma suna
kara cuso kai. Bata ce komai ba har sai da
ya gama rufe gate din sannan ya taho
inda take "Hajiya sannu da zuwa.
Wadansu ne tun safe suka takurawa gidan
nan, na rasa yadda zanyi dasu, babu irin
zagi da tsoratarwar da bani musu ba
sunki tafiya" ta bude kofa ta fito tana jin
zuciyar ta tana zafi, mai gadin ya cigaba
da magana
"sunce su yayyen ki ne, wai
daga Kura suke" ta juyo da sauri tana
kallon sa tace "ka gaya musu na basu
minti goma, ko su bar kofar gidan nan ko
in saka a rufe min su, ka gaya musu nan
Abuja ce ba Kura ba, in na rufe su babu
mai fito da su har abada".
Daga haka ta shige ciki ta rufe kofa. Sai
dai baccin kasa yiyuwa yayi duk kuwa da
wankan da tayi ta kuma kwanta a
lallausan gadon ta. She have forgiven
them, amma ta kasa manta irin abubuwan
da suka yi musu da kiyayyar da suka nuna
musu, bata fatan wata mu'amala ko da ta
magana ne ta shiga tsakaninsu. Tana nan
a kwance Adam ya dawo daga tasa
hidimar, Ya tsaya a bakin kofar dakin ta
yana kallon ta, yace "baccin yamma babu
kyau" tayi juyi "yaki zuwa ma baccin, I am
extremely tired" yace "I know. How did the meeting goes?" Tace "just like we
expected, wai suna son in je musu taro ne
a Beijing, kuma inyi magana a matsayin
representative din su" yace "okay. Sai mu
shirya zuwa china kenan" ta tashi zaune "I
didn't say yes, nace sai nayi magana da
kai first" yace "to ni na ce miki yes. It is a
golden opportunity, zaki hadu da mutane
da yawa a can. Kawai kiyi amfani da
marketing strategies dink and win their
hearts, daga nan zaki samu connections
da zasu kaiki next level in life".
Bata ce komai ba har ya karaso ya zauna
a bakin gadon yana kallon ta. Sai yace
"akwai baki a falon kasa" ta tashi tsaye da
sauri, ta fahimci bakin da yake nufi "I will
not see them" ta fada matter of factly" ya
gyada kai "then I will see them.
24
6:52 AM
Ba zan iya barin su a waje ba knowing
jinin ki ne su, and they refuse to go, kuma
sun taho tun daga Zamfara sannan basu
san kowa a Abuja ba bai kamata mu ki
ganin su ba".
Ta sake maimaita wa "I will not see them.
will have nothing to do with them" shima
ya maimaita "then I will see them". Ya juya kuma ta mike ta fita daga dakin itama. A
kan barandar da ta zagaye babban falon
gidan, wadda kuma ita ce zata kai ka
dakunan sa da nata, anan ta tsaya tana
kallon bakin nasu a zaune a kasa suna ta
kalle kalle, tana kallon yaya Malam ta tuno
sanda mota ta kade Baba Hadiza yayi
tafiyarsa ya barsu rungume da gawar ta,
sai a lokacin ta lura har da bagkon kaya
suka taho. Ta ga Adam ya bude dakunan
da suke kasa sannan yazo guri su yace
"tace ba zata gan ku ba, ta kuma ce in
kuka sake dawowa zata dauki matakin
shari"a a akan ku, amma nayi mata
magana, ga dakuna nan ku shiga akwai
duk abinda kuke bukata a ciki, za a kawo
muku abinci, ku kwana anan, gobe zan
bawa maigadi kudin mota ya baku ku
koma inda kuka fito"

Yaya Malam ya mike daga zaunen da yake
a kasa ya koma kan kujera ya zauna yace
"'wai kai in tambaye ka, uban waye ya
daura muku aure da ita? Shin wai auren
ma kuke vi o kuma zaman dadiro kuke
yi? Saboda ni dai ban daura mata aure ba
kuma kaf dangin mu babu wanda ya
daura mata aure, Zan kai ku kotun shari'ar
musulunci in yaso sai inga wanda zai
daure wani tsakanin ni da ku".

Maman Maama
[07/01, 10:42 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹SAFIYYA❤️‍🩹
Episode Thirty Two: The Legacy

Not Edited
Safiya ta bar inda take ta sauko kasan da
sauri kamar wadda ake hankada ta, tazo
ta wuce su da sauri tana jin Adam yana
cewa tunda ba da mutunci suka zo ba ya
fasa basu dakin, ya juya yana rufe kofar
dakin da ya bude, Lantana ta fara kokarin
yiwa Safiya magana amma bata amsa
mata ba ta fita waje, tana fita sai gata sun
dawo tare da maigadi ta tsaya a tsakiyar
falon tana bin su da kallo tana lura da
yadda yaya Malam yake kokarin washe
mata baki "gata nan ta dawo ma ai,
kanwata ce, baban mu daya ni da ita" ta
juya tana kallon mai gadin tace "anan
kusa akwai irin matasan nan yan shaye
shaye wadanda basa jin tsoron uban
kowa?" Mai gadin ya fara fahimtar me
take nufi yace "babu anan layin Hajiya,
amma akwai anan layin bayan mu, neman
su kike yi?" Tace "ka zagaya dan Allah da
sauri ka samo min kamar guda biyar, ina
son su zo su fitar min da wadannan daga
cikin gidan nan ba ta hanyar mutunci ba,
kai kuma ka gane fuskokin su, in na fita
gobe zan sivo maka bindiga, duk wanda ya kuma dawowa a cikin su ka harbe shi a
kata ni na saka ka", Mai gadin ya gyada
kai da sauri "to shikenan Hajiya, bara in yi
sauri in kirayo su, harbi kuma sai dai in
ba'a bani bindiga ba, duk wanda aka kora
yaki tafiya kam ai barawo ne......
...." Ya fita
yana cigaba da maganganun sa
Safiya ta juya ta koma sama da sauri
kamar yadda ta sauko da sauri. Yaya
Malam ya kira sunan ta "Safiya..... Safiya
yanzu ni zaki ce a kira wo wa yan shaye
shaye suyi min korar kare daga gidan ki?
Ni zaki ce a harba idan na kuma zuwa
gidan ki? Uba daya ne fa ya haife mu ni da
ke. Wa kike dashi a duniya da ya wuce
mu. Mu kadai zaki gani ki kira da yan'uwa
kaf duniya" ta dakata a saman stairs din
ta juyo tana kallon su kamar zata yi
magana, duk suka tsaya suna jiran abinda
zata ce, sai kuma ta kuma juyawa ta hau
kan baranda suka daina gain ta.
Suka juya suka kalli juna
"ato magana
ma bamu isa tayi mana ba, wato bamu isa
ma tayi musayar yawu da mu ba, lallai
duniya mai abin mamaki, wai Safiya?
Safiya dai yarinyar da in nazo gida take
wankewa yaya na kashi take yi musu
wanka idan sunci abinci sun rage su bata
taci ita da kanwarta, wai ita ce yanzu take
yi mana korar kare da ga gidan ta". Yaya Malam ya koma ya zauna akan
kujera tare da yin tagumi da hannun sa
"duniya kenan. Ance fa kudin da take da
shi yafi dukkan tunanin mai tunani. Amma
ruwa yarinyar nan ba zata bamu musha ba
kenan take nufi?" Lantana taji an taba
gate ta zabuwa "yaya ka tashi mu tafi,
wanna yarinyar mai idanu a tsatstsaye
wallahi in bamu bar gidan nan ba ba
karamin wulakanci zata yi mana ba, ka ga
fa ta tura a dauko mata yan daba. Ka tashi
mu tafi" ta fada tana jan rigarsa" ya ture
hannunta "mu tafi ina wai? Kina da kudin
motar komawa gidan ne?" Tace "bani da
shi amma zan nema a waje, wallahi ba zan
zauna a nakasta ni a banza ba, wannan
katon gidan ko kashe mu ta saka akayi
tana da gurin da zata binne mu babu
wanda zai sani. Kazo mu je ko gidan
abokin na ka ne mu kwana a can"

Ya mike yana kallon been da Safiya ta
hau sannan yayi kwafa "zamu sake
haduwa ne" Lantana tace "kai dai kazo
mu tafi. Da mun sani mun lallaba mijin ta
naga kamar ya fita saukin kai shi zamu iva
samun wani abu a gurin sa, ko kuma ya
lallaba mana ita ta saurare mu, amma
yanzu kayi mana wasa da damar mu.........
Suka fita suna cigaba da maganganu kasa
kasa.

Safiya ta bisu da kallo har suka bar falon
sannan ta juya ta koma daki ta kwanta a
kan gado tare da jan bargo ta rufa. Ta san
babu wasu yan daba a unguwar, shima
mai gadin ya san babu, kuma yadda suke
din nan ko mai gadin shi kadai ta saka zai
iya daukan su aka ya fitar da su daga
gidan ballantana akwai sauran ma'aikatan
gidan, amma tana so ne ta nuna musu
how far she can go akan hana su shiga
rayuwar ta. Kuma yanzu from
maganganun su kadai ta san abin da ya
kawo su, ba komai bane ba sai kudi, kuma
ta rantse ta kuma rantsewa, kwandalar ta
ba zasu ci ba.
23
A
00
3
10:03 PM
Adam ya shigo dakin yana kallon ta, ya
san idonta biyu, yace "naso ace da
mutunci suka zo, da ko kudin mota sun
samu. Now they are stranded in Abuja
basu da ko kudin da zasu koma gida" ta
mike zaune tana kallon sa tace "da in
basu kudi na gwara na bude window na
watsa kudin waje, watakila almajirai su
dauka suyi amfani da shi. They are after
my money, my hard earned money, kuma
wallahi kwandala ta ba zan basu ba".

Adam ya zauna a bakin gadon ya rike
hannunta yace "wannan shine Zuwan su
na farko gidan nan, ina so ki fahimta kuma
ki saka a ranki cewa it won't be the last,

they will come back. Kudi suke so kuma
na yarda da ke idan kika basu they will
want more and more kuma tunda akwai
kiyayya a tsakani they will use every
means possible to get it" taji ajjiyar
zuciya"to yanzu ya zan yi? How can I get
rid of them? Ko gida zamu chanja ne?"
Yace "yadda suka gano wanna gidan
idan mun chanja ma haka zasu gano shi.
But we will take security measures for
protection"
Sun jima suna magana akai sai ya fita, ta
koma ta kwanta, sai ta tuno da maganar
Hajiya Maryama years back, ta sake tashi
ta zauna, yanzu idan ta mutu bata haihu
ba duk abinda ta tara a duniya su yaya
Malam ne zasu gada? Except for 1/8 da
za"a cirar wa Adam.

Three weeks after that maganar tafiyar su
Beijing ta tabbata. Wani taron karawa juna
sani ne na wani international organization
na yan kasuwa, anan ne aka bawa Safiya
dama tayi magana da yawn small scale
entrepreneurs na Nigeria da kuma irin
kalubalen da suke fuskanta. A cikin
bayanan nata ne ta bada labarin ta da
yadda ta rasa iyayen ta da yanuwanta da
kuma yadda ta fara kasuwancin ta hanyar
suyar awara a kofar gidan su har zuwa
matakin da take kai a yanzu,

Bayanan nata sun taba zuciyoyin mutane
da yawa a fadin duniya baki daya, aka
bata award suka yi pictures da mutane da
dama, mutanen da ada take gain sunyi
mata nisan da ko hanya ba zasu hada da
ita ba. And kamar yadda Adam ya gaya
mata, she got a lot of contracts and
connections, a ciki wanda tafi jin dadin sa
shine na wani textile industry da suka yi
mata alkawarin zasu zo su bude branch a
Nigeria and she will be their lead. Ita zasu
bawa contract din tun daga selection na
site din da zasu yi ginin industry din har
aikin ginin, siyo machineries da kuma
daukan ma'aikata. Bata dauka da gaske suke ba sai da suka
dawo Nigeria taga sun kira sun cigaba da
maganar. Nan da nan ta hau hidima tare
da taimakon Adam. She got an
opportunity and she used it wisely. Ta
tsaya tayi musu aiki akan gaskiya da
gaskiya and she got their trust har

43 / 113