Author : Maman Mama Category : Romantic Hausa Novels
ni da shi. Sunan da ya kara stirring abubuwa da yawa a cikin zuciya ta. Amma kuma ido na babu abinda yake gani sai shi da Safina,
making a baby. Na wuce shi ba tare da na
kalle shi ba, Safina ta mike tsaye da sauri
a lokacin da shima ya biyo baya na da
sauri "Piya" ya sake kira na amma ban
waigo ba sai ma saurin dana kara nayi
hanyar gate.
A cikin falon muna fita Safina ta juya gurin
Mommy tace "congratulations. You just
ruined my life. Me yasa ba zaki yi shiru
ba?" Sai ta juya da sauri tayi akin ta.
Mommy ta bi hanyar da muka fita ni da
Muhammad da kallo sannan ta bi hanyar
da Safina ta bi ita ma da kallo sai kuma ta
bude hannun ta alamar tambaya "me ya
faru wai? me nace?" Ya juya tana kallon
Mustapha ta sake cewa "me nace?"
Mustapha ya daga kafada alamar shima
bai sani ba.
Maman Maama✍🏻
Longest episode ever ko?😁
I just want to finish this novel but I am
loving it
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Forty Nine : Broken
*Contact Bojuwa HERBAL'S for all your*
*kayan mata for*
*Amarya*
*Uwargida*
*Bazawara*
*Mai jego*
*Saiwowin sanyi gangariya da na dahuwar
kazar sababi har da na tattabaru da
ciccibi all from Chad.*
*Kayan gyara masu kyau da inganci kala
daban daban, special maganin sanyi for
women of class*.
*Contact Surayya HALIN YAU on*
*08032773332*
*. . .
Ina zuwa gate na kama kokawa da kofar
na ma rasa inda zan murda in bude, il
nake yi kamar wuta ce take ci a cikin
zuciyata, Mai gadin su ya taso da sauri ya bude min amma kafin in fita Muhammad ya karaso. Kusan tare muka fita nayi kokarin kara sauri amma sai ya rike jaka
ta, na juyo a fusace na nuna shi. "Sakar
min jaka" naga yanay in sa gabaki daya ya
chanja fuskar sa tana nuna alamomin
tambaya da yawa "Safiyya? Me ya bata
miki rai haka?" Na sakar mass jakar nayi
gaba, dan rainin hankali, wato ni zai raina
wa hankali har yayi min wata tambaya
marar ma'ana.
Ya sha gabana da sauri yana kokarin hada
ido dani, saura kadan muyi karo saboda
saurin da nake yi. "Piya dan Allah ki tsaya
muyi magana" na zagaye shi naci gaba da
tafiya, bana son ganin shi sam, bana
kuma son jin muryarshi dan ji nake yi
kamar in shaki wuyansa, munafiki.
Ya sake rike mayafi na, "Piya Please now.
Me nayi ne wai ni?" Na juyo da sauri ina
kallon sa cike da masifa sai na nuna masa
gidan sa nace "she is pregnant" nan take
naga yanayin fuskar sa ya juye zuwa guilt,
pure guilt. Ya saki mayafin nawa a hankali,
bana bukatar wani dogon bayani kuma na
san ba karya take yi ba, gaskiya ta tada
this time around. Naji abinda ya tokare
min a kirji ya fadje6, wata kila ma tare da
zuciyar tawa suka fashe. Kawai sai wani kuka yazo min, ai kuwa na fashe da kuka. Yayi sauri ya kara matsowa kusa da ni "Piya!" Kuma sai ya kasa cewa komai, yayi attempting magana ya kai sau biyar amma
ya kasa furtawa.
Na juya na barshi anan a tsaye na cigaba
da tafiya ta ina kuma cigaba da kuka na.
Idan ka ganni zaka dauka sakon mutuwa
aka aiko min ko kuma patient ce ni a
psychiatry. Ya cigaba da bina, "Please
Safiyya people are looking, ki daina
wannan kukan, let me get my car and take
you home. We will talk on the way" ba
tare da ma juyo ba nace "I don't care
about people, I don't care about anything,
I don't care about you or your wife or your
baby. Ka juya ka koma gurinta and don't
ever talk to me again. Karma ka kara
nuna ka san ni. I wish ban sanka ba a
rayuwata"
Ya sake zagayowa gaba na, ya tare min
hanya, kokari kawai yake sai na kalle
idonsa ni kuma naki daga kai in kalle "look
at me Safiyya, Let me get the car. We will
talk" na karbi jakata daga hannun sa
sannan na dake shi da ita a kirjinsa, "Get
out of my way, get out of my site, Get out
of my life, Me zaka ce min? Zaka ce min
ba naka bane ba?" Yayi shiru bai ce komai
ba amma tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskar sa. Na nuna shi da yatsa na "babu ni babu kai har abada" na sake zagaye shi zan cigaba da tafiya sai va
sake rike jaka. "Piya....... Dan Allah..... Ki
tsaya muyi magana" na sake sakar masa
jakar sai kuma kawai na durkusa a inda
nake dan ji nayi ba zan iya cigaba da
tafiya ba. Na kife kaina akan guiwowina na
cigaba da russ kuka kamar wadda aka ce
Daddy ya mutu.
Ina jin wasu mutane suka zo wucewa suka
yi masa magana ya basu amsa amma
banji abinda suka ce ba sai suka wuce.
Sai naji motsinsa shima ya zauna a kasa a
kusa da ni, ina iya jin kamshin sabulun da
yayi wanka dashi. Ji nake yi a raina tamkar
komai na rayuwata ya tarwatse. Tamkar
zuciya ta ta tarwatse, tamkar duk
achievements dina are nothing because
of this. Kamar ni din kaina is nothing
tunda har Muhammad ya manta da ni
already yayi settling da Safina. Dama haka
kishi yake? Lallai na jinjinawa mata masu
kishiya musamman idan suna son mijin
sosai, Sai da nayi kuka na sosai sannan na dago
kai ina kallon sa, fuskarsa tayi ja kamar shi
yake yin kukan, muna hada ido ya miko
min hankyn daya dauko daga cikin jaka ta da take hannun sa "ya isa haka kar kiyi
ciwo kuma. I promise you it is nothing. It
doesn't mean anything. I don't know how
to explain to you but I promise you zaki
fahimta" na karbi hanky din na goge fuska
ta sannan na mike tsaye ina jin kirjina yayi
min nauyi, ya mike shima sai nace masa in
a much calmer voice "you don't have to
explain anything. Na riga na fahimta. Ni
kadai nake haukana da ma. I ......" Ya
katse ni "Piya haukan da nake yi akan
sonki na tabbatar yafi naki yawa. Yarinyar
can makira ce. She did something. Kuma
dama this is exactly what she wanted.
This is exactly why she did what she did"
na girgiza kaina "I don't want to know
what she did or what you did. It is over
between us again. I am breaking up with
you for the second time" na fada tare da
fara kokarin tare taxi, mai taxin yana
tsayawa Muhammad yace masa "get out
of here, go" mutumin ya bi mu da kallo
sannan ya ja motar yayi gaba.
Muhammad ya juyo kaina "you are not
breaking up with me Safiyya. Never again,
I will never let it happen" ya fada with so
much confidence, Na juya na cigaba da
tafiya tare da cewa "watch me" na cigaba
da kokarin samun abun hawa.
A lokacin mota ta tsaya a gabana, motar
Mustapha, yana zaune a seat din driver
fuskar sa cike da alamomin tambaya ya
kalle ni ya kalli Muhammad da yake tsaye
a kusa da ni hannunsa rike da jaka ta, ya
ambaci sunansa "Muhammad?"
Muhammad yayi kamar bai ji shi ba, sai ya
sake kallo na yace "Mommy tace in biyo ki
in kai ki gida, are you coming or not?"
Kamar ransa a bace yake amma bani da
option dan babu abinda nake so a lokacin
irin inyi nisa da Muhammad.
Na warce jaka ta daga hannun sa da karfi,
karfin da nayi amfani da shi ya sa nayi
baya kamar zan fadi, ya saka hannu daya
ya tare ni sannan ya mikar da ni tsaye
sosai. Ina jin na tsaya nature hannun sa
tare da nuna shi "you hurt my heart, you
hurt my heart really bad. I don't want to
see your face again, ever" sai kuma na
zagaya na bude motar na shiga na zauna.
Mustapha ya ja muka tafi.
Na kwantar da kaina a jikin kujera ina
kokarin hana kaina cigaba da kuka, wata
irin tafasa zuciya ta take yi. Na rufe ido na
ina ta jan numfashi da karfi trying to calm
myself amma sai naji Mustapha ya fara
magana cikin daga murya "what just
happened? What was that? Are you in a
relationship with mijin Safina?".
Na bude ido na juyo ina kallon sa raina
yana kara baci, sai ya cigaba da magana
"wancan munafikin yaron. He have been
giving Safina trouble all along and now
this? Yarinyar nan tana can tana kuka
Mommy ta saka ta a gaba ta kasa gane
kanta ashe uta ta san abinda yake faruwa,
ashe kukan da take yi kenan. What do you
think Mommy and Daddy will think idan
suka ji wannan labarin?"
A hankali nace masa "Mustapha, ko kayi
shiru ka daina min hayaniya a kai ko kuma
ka yi packing in fita. I don't owe you an
explanation. I don't care what you think.
am not going to explain anything to you"
bai yi shiru din ba ya sake cewa "but you
owe our parents explanation na how you
are in a relationship with min sister din
kj" "step sister" na gyara masa tare da
jawo ear piece na saka a kunnuwa na
sannan na kwanta a kujerar na rufe ido
na,
Ban sani ba ko ya cigaba da maganar ko
kuma ya hakura, Sai da naji mun tsaya
sannan na bude ido na na dauki jaka ta na
fito. Shima ya fito yana kallona yace
"yanzu ni what do you want me to do with
this information" nace "whatever you
want. Ko ka wuce ka gaya wa Daddy ko ka
koma ka gaya wa Mommy ko kuma ka shiga gidan radiyo ka fada, ko kuma ka rike a zuciyar ka. I don't care",
Na juya da sauri na shiga gida, kuma har
zuciyar ta wa ban damu ba din. In dai
Muhammad ne Safina ta je na bar mata. In
dai Safina ce Muhammad yaje na bar
masa. Nayi saving Daddy da Mommy
stress din solving wannan issue din. Na shiga cikin gidan da sauri, ina jin Esther tana yi min magana ko kallon ta banyi ba na hau sama na tafi dakina na
shiga na kulle kofa. Kokari nake vi lallai sai
na hana kwakwalwa ta tunanin
Muhammad da matarsa, irin abinda na
kanyi tun da aka yi auren su, amma kuma
yau zuciya ta tayi over powering
kwakwalwar ta karbe ragamar controlling
emotions dina. Dan haka na zauna a kasa
a gaban gado na cigaba da rusar kuka na.
My heart was so broken beyond repairs.
But my brain was trying to tell me the
truth, sai dai zuciyar ta wa taki bata
damar yin magana.
Sai da na gama sannan na tashi na cire
kayan da nayi masa kwalliya da su nayi jita
da su a tsakar dakin sannan na saka kafa
na tattake su. What was I even thinking?
That we will be back together bayan yana auren Safina? Ni kaina na san babu yadda
za'a yi Daddy da Mommy su yarda da
hakan but I love him so much, yanzu
kuma na tsane shi, I hate him so much
amma kuma ina son sa, how is that even
possible?
Him👳🏻♀️
Tun da ya dawo baya zama a gida, kamar
yadda Abba ya fada aiki ne dankar a
office yana jiran sa, ga shi kuma yana so
ya fara implementing knowledge din da ya
samu a gurin tarukan da yaje, dan haka
abu ya taru ya cakude masa. Sai da weekend ya zagayo sannan ya samu hutu ya zauna a gida. But he was being careful yanzu a gida yana kiyaye
abinda zai ci ko zai sha ko kuma ma duk
abinda zaiyi amfani da shi. Shi gani yake
yi asiri Safina tayi masa da ya saka shi
acting that way a daren can. Wannan ya
sa kofar part din sa yanzu kullum a rufe
take, yana shiga zai rufe ta ciki, in ya fita
ma kuma ya rufe ya tafi da key din. Yanzu
ko abincin da take ajiye wa kullum ba ta
da damar ajiyewar.
A ranar Saturday din ne ya samu ya
kwanta yayi bacci mai nauyi sosai da
rana. Sai da zuhr ya tashi, ya shiga toilet yana wanka yana gab da fitowa yaji wayarsa tana kara, ya gama ya fito ya duba sai yaga Mama ce ta kira shi. Ya na
kokarin kiran ta kenan sai ga wani kiran ya
shigo, ya dauka ta tambaye shi a ina yake
sai ya gaya mata yana gida, nan take ta
hau shi da fadan wai ana ta nemansa a
gidan ya rufe kofarsa, he tried to explain
to her bacci yake yi amma taki sauraren
sa tace maza ya je ya gaishe da Mommyn
Safina tazo tana neman sa.
Da sauri ya zura riga ko gama drying
jikinsa bai yi ba ya fita dan da gaske ya ji
Mama ta dau zafi. Sai dai yana shiga falon
Safina ya ganta, ba Safina ba Safiyya. She
looked different, more matured but more
beautiful. Amma kuma hankalin ta a tashe
yake, ranta a bace yake, and he was more
concerned about abinda ya bata mata rai
ya tayar mata da hankali haka then fadan
da yaji Mommy ta fara yi masa. Bai ma ji
me take cewa sosai ba, kamar dai she
was showing dissatisfaction akan yanayin
zaman su da Safina har tana magana in
baya son ta su suna sonta, But then he
heard something. "Ga Safiyya nan da
auren ta ya mutu babu abinda ya same
ta" and it caught his attention, a take
kuma ya gane me hakan yake nufi. Auren
Safiyya ya mutu.
As he was trying to assess the situation
sai ya ga Safiyya ta bar inda take tsaye
tayi hanyar waje da sauri, and bai tsaya
cigaba da jin fadan da ake yi masa ba ya
mike shima da sauri ya bi bayan ta yana
kiran sunan ta.
Har waje ya bita taki kula shi, daga baya
kuma sai ta gaya masa abinda ya bata
mata ran, his worst nightmare, maganar
cikin Safina. Tabbas maganar ta bata
mata rai sosai and she cried like a baby.
She sat down on the floor a bakin titi and
cried. Wannan kukan nata ba karamin
kona zuciyar sa yayi ba. Ya rasa mai ze ce
mata. Yasan zai iya yi mata bayani amma
kuma ba zai iya ba. To me zai ce? Ya rasa
menene ya fi daga masa hankali yanzu,
the fact that matar da baya so is pregnant
for him or the fact that matar da yake so
is crying because of him.
Yayi kokarin yi mata magana ya kasa, yayi
kokarin lallashin ta amma bai san kalaman
da zaiyi amfani da su ba. So he just sat
with her and wished he can cry with her.
A karshe dai ta gaya masa maganganun
da suke nuna zurfin bacin ranta sannan
tace masa "I am breaking up with you
again". Amma duk ba wannan ne damuwar sa ba,
damuwar sa shine Mustapha da yazo ya
dauke ta a mota suka tafi.
Ya tsaya yana bin motar da kallo, and the
first thing that came to his mind was ranar
da suka yi haduwa ta biyu a duniya, ranar
da Mukhtar ya zo ya dauke ta a mota suka
tafi, she later married Mukhtar. Ya girgiza
kansa a hankali yace "no…..no. not this
time. Not again" ya juya da sauri ya koma
cikin gidan sa sannan ya shiga part din sa
da sauri totally forgetting about the
problem with Safina and Mommy. Shi
kawai abinda yake ransa shine Mustapha
da Safiyya a mota. She is broken. She
may even open up to Mustapha and give
him a chance to lallashe ta. Ya sake
girgiza kansa da sauri "uhm uhm" wannan
rarrashin shi zai yi shi tunda shine yayi
wannan laifin. Frantically yake neman key din motar sa, totally forgetting cewa yana kan abinda
aka tanada musamman dan ajiye car keys
a palon sa, sai daga baya kuma ya tuna
sannan ya tafi da sauri ya dauka, Unlike
before yanzu ai ya san gidan su, ya san
har falon Daddy.
Wayar sa ce tayi kara a cikin aljihunsa. Ya
saka hannu ya dauko ta and he saw sunan
Mama. Yaji gabansa ya fadi, sai a lokacin
ya tuna da inlaw dinsa da ta kira shi tana
yi masa fada. Yaji kamar kar ya dauki
wayar. Allah ka dai yasan abinda suka kira
suka gayawa Mama. Wannan wanne irin
kaddararran aure ne?
Amma kuma ba zai iya barin Mama tana
kiran sa bai dauka ba. Tafi karfin haka a
gurin sa. Yayi sliding wayar ya dauki kiran
ya saka a kunnen sa "hello Mama" ya
saurara yaji ta fara yi masa fada amma sai
yaji tace "kaje ka gaishe ta?" Yace "eh
naje, har na fito ma" tace "kana ina
yanzu?" yace "ina daki na" tace "okay ka
2o ka same ni a gidan Mommy" daga nan
ta katse kiran.
Ya rike wayar a hannunsa yana jujjuya ta.
Shi kukan Safiyya kawai yake tunawa. So
yake yaje yace mata "I am sorry" but
sorry for what? Ya kawar da maganar
daga zuciyar sa sannan ya fara kokarin
chanja kayansa, Shi dai ya san indai har
maganar gaskiya za'a bi bai aikata laifin
komai ba ballantana ya bada hakuri,
amma ba maganar gaskiya ake yi ba,
maganar Safiyya ake yi. And as far as magana ce a tsakanin sa da Safiyya then she is always right. Kuma zai bada hakurin ko da kuwa cikin charbi ne.
Ya gama chanja kayan ya dauki key din
mota ya fita, sai da ya kunna motar
sannan ya yi tunanin dolen sa a yanzu
gidan Mommy zai je gurin Mama, sai dai
yana fatan gain maman ba zai dauki
lokaci ba. Ya na tuki yana tunanin
maganganun Safiyya, she said she is
going to break up with him, amma shi dai
ya san dama they broke up already, bai
kuma san sanda suka dawo ba ballantana
har su sake wani breaking up din.
Kukan ta tabbas ya tayar masa da
hankalin amma kuma a wani bangaren ya
kwantar masa da hankali ne saboda ya
tabbatar masa da matsayin sa a gurin ta
and yayi boosting confidence din sa. Ya
tuna kalmomin ta "ashe ni kadai nake
haukana" and he smiled tare da sauke
ajjiyar zuciya. Whether she have been
with Mukhtar or not, shi dai abinda ya
fahimta shine yana cikin zuciyarta kamar
yadda take cikin ta shi. And that is all that
matters.
Sai da ya tsaya yayi sallah a masallacin
kofar gidan sannan ya shiga cikin gidan,
ya ga motar Mammy ya san tana ciki ita ma, dama al'adar su ce sukan je gidan
Mommy duk Saturday su yini tare da ita. A
falo ya tarar da Mammy ita kadai tana
kallon tv, tayi murmushi tana kallon sa
"ubana maganin kuka na" ya yi mata
murmushin shima sannan ya karasa ya
gaishe ta. "Kai yanzu tunda kayi aure
kuma shikenan an daina gain ka, matar
kata boye ka a gida" yayi saurin kare
kansa "Mammy wallahi aiki ne ya sako ni a
gaba. Abba sam baya daga min kafa. Shi
yasa dama tun farko na gudu daga gurin
sa na tafi MD" tace "haka ne. We are all
proud of what you have achieved so far.
Allahu yayi jagora" yace "Ameen" sai ta
nuna masa dakin da yake kusa da gurin
tace "mamanka tana ciki tana Sallah.
Maybe ta idar" ya mike ya shiga dakin da
ta nuna masa. A ciki ya samu Mama ta idar da sallah
tana addu'a. Ya zauna yana jiran ta sai da
ta shafa sannan ta juyo tana kallon sa, ya
gaishe ta "Mama barka da rana" bata
amsa ba sai ta cigaba da kallon sa, ya san
irin wannan kallon and it made him
nervous, sai a karshe tayi magana and
she asked exactly abinda ya san zata
tambaya "me yake damunka?" Ya danyi
dariya nervously "Mama babu abinda
yake damuna fa, stress din aiki ne" ta cigaba da kallon sa "kun yi fada da Safina ne? I don't like the tune of her mother sanda ta kira ni dazu" ya girgiza