Author : Maman Mama Category : Romantic Hausa Novels
jin akwai namijin
da zan bude masa jikina kamar yadda na
bude wa Mukhtar yau, sannan mu shiga
daki daga ni sai shi, sannan ga igiyar aure
uku a tsakanin mu, kuma ace yayi
rejecting dina yayi tafiyarsa.
Wannan ya kara tabbatar min da abu uku,
na farko Mukhtar ne yayi raping dina, na
biyu kuma ya san ina zargin shi, na uku
and the most important thing shine the
scar is there,
A yadda na bashi labarin daren da akayi
raping dina in details ya tabbatar masa da
cewa ina cikin hayyacina sanda na ji masa
ciwo, and the way that I tried seducing
him tonight bayan halin ko in kula da nake
nuna masa kafin in tare ya tabbatar masa
da cewa shaida nake nema a kansa, kuma
wannan scar din ita ce shaida. Wannan
realization din kuma sai yay unblocking
another fear in me, he will now try to get
rid of the scar ta kowanne hali. Tunda a
ganin sa ita kadai ce shaidar da zata
tabbatar min da kuma duniya cewa shine.
Musamman tunda yana tunanin Junior ya
mutu. And that was where I had upper
hands in the matter, na kuma gode Allah
da yasa nayi wancan tunanin dan in da
yasan Junior yana raye kuma ya san ina
zargin sa zai iya kokarin ma kawar da ni
daga duniya to cover his crime.
Wannan daren shine ya kawo karshen
plan A dina. My plan A was to seduce him
to my bed, handcuff both his hands idan
na dauke masa hankali da jikina, and then
check his body for the scars. It was risky
but worth a trial considering bani da
tabbas din shine dan haka bana son cutar
da shi.
Yanzu kuma it is going to be an eye for an
eye. Dan yanzu zamu shiga plan B.
Sai dai kuma daga alama shima Mukhtar
ya chanja takunsa gabaki daya. Dan ganin
shi ma daga ranar gagara ta yayi. Da
asuba yake fita, sai cikin dare kuma yake
dawowa, wani lokacin ma in ya tashi
dawowa ta can daya kofar falonsa yake
shiga zuwa dakinsa sannan in zai fita ma
ya fita ta can. Mun koma kamar mage da
bera a cikin gidan auren mu. And that
frustrate me more than anything.
Kamar yadda nayi alkawari ba zan yi girki
a gidan Mukhtar ba, ban taba dafa ko da
noddles ba, order abinci nake yi kuma a
kawo min har gida. Shima kuma bai taba
tambaya ta abinci ba, ban san kuma inda
yake zuwa ya ci ba. And I didn't care. Bai
taba kawo abokansa gidan ba, nima kuma
ban gayyaci kawayena ba duk kuwa da
korafin da suka ringa yi min a waya cewa
anyi bikina amma ban gayyace su ba
kuma gidan nawa ma ban gayyace su ba, I
told them suyi hakuri abin ne yazo min
lokaci daya amma na yi musu alkawarin
shirya musu walima wata rana. Amma na
fada musu hakan ne dan su rabu da ni inyi
concentrating akan abinda yake gaba na.
Sati biyu da biki na aka yi na Abdul. Tun
kafin bikin na kira shi a waya nayi masa murna tare da lallaba shi da kyar ya turo min account details dinsa and I sent him heavy da sai da uncle Sufyan da kansa ya kira Daddy and Daddy said babu ruwansa
ni nayi niyya kuma tsakanin mu da Abdul
ne. Lokacin bikin Abdul Mommy tazo gari,
dama munyi waya da ita tace min in shirya
zata zo muje gidan bikin tare ni da ita da
Safina, and I wasn't looking forward to
that. Nayi ta neman hanyar da zan zame
in fasa zuwa na rasa kuma gashi ina son
zuwa din ko dan Aunty Hajjo, na san zata
ji dadi sosai idan naje. But I was in no
mood to neither meet nor talk to Safina.
Sai dai cikin ikon Allah ranar da Mommy ta
zo gari take gaya min Safina ba zata samu
damar zuwa ba, bata da lafiya,
"gashi shi kuma mijin nata har yanzu bai dawo ba,
ina tunanin da ita zan koma Kano gaskiya,
gwara in san a gabana take, ko kuma in je
gidan iyayen nasa inji me zasu ce, amma
wannan ai ba aure ba ne ba" ban ce
komai ba kuma banyi niyyar cewa komai
ba, sai kuma tace "ya kamata dai kije ki
duba ta" nace "insha Allah". Amma sai
naji dadin cewa ba zan hadu da Safina ba,
Ranar yini Mommy tazo ta dauke ni muka
je tare. I kept thinking ko zamu ga Junior?
Ko zata gane shi? Amma da yake a event
center akayi bikin I guess Aunty Hajjo
bata tafi da shi ba dan duk baza ido na
ban ganshi ba. Washegari da dare muka
sake zuwa dinner. Aunty Hajjo taji dadin
ganin mu sosai kuma ta karrama mu
sosai, naje har gurin ango da amarya na
taya su murna and they looked so happy
and so in love with each other. Abdul yayi
introducing dina a grin amaryarsa muka
gaisa sosai, yana tsokana ta wai ina ango
na. Sai ganin su naji ya fama min wani
ciwo a zuciya ta da nake ta ajjiye da shi,
and as I sat down looking at them I
thought about him, ko ina yake? Ko me
yake ciki? And I so much wanted to
unblock his phone number and call him,
maybe inyi pretending kamar babu abinda
ya faru and say '"tsokanar ka fa nake yi
Yaya Muhammad. It was all a prank. I miss
you so much", I remembered the sound of
his voice over the phone, the deepness of
it and how it has always reach deep into
my heart "hey Piya, you have no idea how
much I miss you" na sunkuyar da ido na
kasa ina jin hawaye yana taruwa a idona, a
hankali nace "I miss you too Yaya
Muhammad".
A lokacin ne naji Mommy tana taba ni
"Kinga mother in law din Safina, Ashe ta san su Sufyan" nayi sauri na dago kai and
I saw her tana tafiya zata zauna. Ban taba
ganin ta ba amma na tabbatar ko da kuwa
Mommy bata nuna min ita ba zan iya gane
ta idan na ganta. Kana ganin ta indai
kasan Muhammad to zaka san cewa ita ta
haife shi.
Mommy ta ja hannuna "zo muje ku gaisa
da ita" na zame hannu na tare da
langwabe kai "Mommy please" tace "ke
fa matsalar ki kenan ba kya son mutane,
ai sai kiyi ta zama" ta tafi ta barni. Nayi
ajiyar zuciya na cigaba da kallon Mama
da ga nesa, naki zuwa ne saboda ina jin
toro, ban sani ba ko ta taba ganin hotona
a wayar Muhammad ko something like
that, ina tsoron kar ta gane ni, duk da dai
na san karin maganar hausawa da suke
cewa idan kere na yawo zabo na yawo
watarana dole za'a hadu.
Wasa wasa dai sai naga Mommy ta samu
kujera a can ta zauna sun cigaba da hira.
Ni dai ina zaune a guri daya har aka gama
sannan Mommy ta zo muka tafi. Tun kafin
mu fita na san cewa I was in for hirar
Safina da mijinta har muje gida, ai kuwa
dai muna shiga mota ta fara "mutanen
nan suna da son kansu wallahi, kinji wai
basu san Safina babu lafiya ba, wai bata
gaya musu ba shima bai gaya musu ba,
Amma dai munyi magana tace zata je gidan ta dauke ta ta mayar da ita can
gabanta su zauna tare kafin mijin ya
dawo. Ai ce mata kawai nayi tafiya zanyi
da Safina Kano inyi jinyar ta a can" naji
kamar in toshe kunnena irin yadda nake
mata in bana son jin maganar da take yi
sai kuma na fasa, tunda na mayar da
zargina kan Mukhtar a fara sassautowa
akan Mommy. Sai kuma tayi ajjiyar zuciya
tace "ni tausayi take bani yarinyar nan,
Allah ya sassauta mata wanna lamarin.
Ko babu komai iyayensa masu kirki ne".
Ranar daurin aure ma muka sake komawa
gidan Aunty Hajjo, ranar ni na fara fita a
motata naje na dauki Mommy sannan
muka wuce, muna yin packing na dauko
envelope din dana taho da ita da kudi
masu kauri a ciki na mika wa mommy
nace "gashi Mommy ko zaki bawa Aunty
gudummawa" ai kam taji dadin haka sosai
"kai amma kin kyauta Safiyya, dama ina ta tunanin abinda zan bata na rasa" nayi
murmushi kawai na fita.
Ranar babu mutane sosai tunda daurin
aure ne, sai yan uwansu na jiki sai kuma
few close friends kamar mu. Muka zauna a falo Mommy ta samu wata yar uwar
Aunty Hajjo itama mai surutu suna ta
zance ni kuma na koma gefe ina ta rubuta
wani sabon plan da nake shiryawa akan
maganar reopening Oasis da nake son yi
as soon as I get rid of Mukhtar.
Muna nan sai ga wata yarinya ta shigo
falon da Junior a hannunta, tazo ta zauna
opposite din su mommy ta na bashi
madara shi kuma yana ta rigima yaki sha
sai dawo da ita yake yi. Na ajiye waya ta
akan cinyata ina kallon su. Kanwar Aunty
Hajjo ta juya gurin su itama tace "ke
Husna yaron nan fa ya koshi, daga alama
bacci yake ji ki goya shi mana" wadda aka
kira da Husna ta kwabe fuska kamar zata
yi kuka tace "na goya shin fa yaki yin
baccin wallahi. Wannan yaron rigimamme
ne" Mommy ta juya tana kallon su ita ma
sai tace "ki kaiwa maman sa shi mana to,
maybe goyon ne baki iya ba" yarinyar
tace "to ai maman tana gurin mutane, ita
tace in rike shi" Mommy ta mika mata
hannu "bani shi in gani, watakila diaper
za'a chanja masa ko kuma kaya ne suka yi
masa yawa" yarinyar ta zo ta mika mata
shi ta karbe shi and she laughed and said
"wow, ina karbar yaron nan sai naga
kamar twins sanda suna babies" ta sake
jujjuya shi a hannunta and she looked at
me, muna hada ido na sunkuyar da kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna, ta sake
kallon sa ta kalle ni a take na fahimci ta
gane shi.
Ta juya tana kallon yarinyar tace "dan
waye?" kanwar Aunty Hajjo da suke tare
tace "au wai kema baki san ta haihu ba?
Dan Hajjo ne fa. Matar nan babu wanda ta
gayawa tana da ciki kawai sai kiran mu
tayi tace ta haihu. Kin san in aka girman
nan in Allah ya kawo rabo sai kiga ana jin
kunyar fada ana gain kamar abin kunya
ne" Mommy ta mika wa matar shi tace
"haka ne. Allah ya raya shi", Matar tace
ameen sannan ta tashi ta jefa shi sama ta
chafe shi, naji kamar zuciyata zata fado
kasa, shi kuma ya takarkare ya chanyara
kuka, sai kuma ta rungume shi a kirjinta
tana dariya sai tace "yaron nan ajebo ne,
bai san cika masaki ba. Bara inje in yi
masa wanka in goya shi, bacci yake j"
tana tafiya Mommy ta juyo tana cigaba da
kallona, fuskarta na nuna alamun bacin
rai. Sai kuma ta mike tayi hanyar waje
tana cewa da sauran mutanen gurin "na
tafi. Allah ya bamu alkhairi, idan Hajjo ta
shigo kuce mata na tafi" na mike nima da
sauri na dauki jakata da waya ta nabi
bayanta.
A hanyar fita muka hadu da Aunty Hajjo
tana shigowa cikin gidan, ta yiwa Mommy
magana amma Mommy ko kallon ta bata
yi ba, muka kalli juna ni da ita and she
understood what happened sai ta bi mu a
baya "Sa'adatu naga sako na gode Allah
ya bar zumunci, Allah kuma ya huta
gajiya, sai munyi waya insha Allah" stil
bata ce mata komai ba ta shiga mota, na
russuna nace "Aunty mun tafi Allah ya
sanya alkhairi" sannan nima na zagaya
drivers seat na zauna na tayar da motar
muka fita fully knowing that mai raba
Mommy da ni ranar sai Allah. Amma sai
naji tayi shiru bata ce komai ba. Fuskarta
cike da bacin rai. Sai naji babu dadi, na
saba da in nayi mata laifi zata yi ta min
fada ne ba wai tayi fushi da ni ba.
Har muka je gida bata ce min komai ba,
nayi packing sannan na juyo ina kallonta
nace "Mommy am sorry" ta juyo tana
kallona tace "no, don't be. Ba laifinki bane
ba ai. Laifi na ne" sannan ta bude motar
ta fita. I thought about following her
inside in sake bata hakuri but sai na
chanja shawara na juya mota na fita, dan
bana cikin mood din bata hakuri ina
tsoron kar in sake kwafsawa again.
Washegari ta koma Kano gurin Daddy, A haka ranaku suka cigaba da wucewa,
satittuka suka shude, har aka yi six weeks
da bikin mu da Mukhtar amma ya ki bani
damar aiwatar da plan B dina a kansa.
And for my plan B ina bukatar getting
close to him. Akwai ranar da nayi niyyar
zuwa dakinsa ma cikin dare in ritsa shi
yana bacci amma sai na tarar ashe kofar
dakin ma rufe ta yake yi. Wato bashi da
niyyar taking any chance with me. Ya kan shigo gurina kusan kullum da assuba, ko da safe idan bai fita da assuba ba, amma a bakin kofar dakina yake
tsayawa "good morning sweetheart. Hope
babu abinda yake damun ki. Aiki ya matsa
min a office ki dan kara yi min hakuri,
soon everything will be over kinji? I will
soon plan us a vacation"
Ko da wasa baya shigo wa cikin dakin,
and da ga na taso zuwa gurinsa zai juya
ya fita. He never let me gets two meters
close to him. Abinda na fahimta bayan
rashin gaskiyar sa shine muguwar
sha'awa na damunsa, and he chose to
avoid me akan yay letting his guard
down. I knew he was trying to get rid of
the scar and duk ranar da ya samu yayi
hakan he will come for me. Wannan kuma shine abinda yake keeping me up wide awake at night.
A cikin six weeks din abubuwa da yawa
sun faru. Har lokacin Mommy fushi take yi
da ni, dan in ba ni na kira ta a waya ba ta
daina kira na. Daddy kuma ya matsa min
lallai in koma bakin aikina, na fahimci he
was worried about me and the way da
yake jin sound of my voice a cikin waya
yana ganin in na koma aikin it will keep my
spirit up, gani yake kamar zaman bana yin
komai ne ya jawo nake cikin damuwa. Na
ce masa ya dan kara hakuri kadan na kusa
komawa, but he didn't believe me sai
gashi ya turo uncle Ahmad har gida wai
yazo yayi min magana in cigaba da
abubuwan da na fara a office. Na gaya
masa shima soon zan dawo, akwai abinda
nake jira ne.
Sai da ya tashi tafiya sannan yace
"Safiyya wannan gidan naku yayi muku
kadan. Ya kamata ku samu babba ku siya
ku koma tunda in kika koma bakin aikin ki
ai mutane zasu ke zuwa gurinki, manyan
mutane, this house shouldn't be
presented as yours" nayi mamakin
maganar sa amma sai nace masa "okay
babu komai. Za'a sayi wani insha Allah" ya yi murmushi '"a fara duba muku?" Na
girgiza kaina "later.…. In lokacin siyan yayi i
will talk to you".
And then one fateful day, ina zaune akan
sallaya ta da daddare na gama shafa"I da
wutiri ina adduoina naji shigowar motar
Mukhtar, ban wani mai da hankali akan
hakan ba dan nasan ba lallai ne ma ya
shigo ta nan falon ba, amma ga mamaki
na kawai sai ji nayi an bude kofar dakin da
nake ciki, na dan tsorata kadan dan ban
saka ran shigowar sa ba, nayi sauri na
shafa adduar na juyo na ganshi a tsaye a
bakin kofa, ya rungume hannayensa a
kirjinsa with that smile that I now so much
understand a fuskarsa.
Naji kirjina ya buga da karfi, tsoro ya
kamani but I tried as much as I can to
keep my face neutral, nace "you scared
me, me kake yi anan kuma yau?" ya gyara
tsayuwarsa "hello sweetheart, sorry na
baki tsoro, laifi ne dan miji ya shigo dakin
matar sa da dare?" na fara dauke kayan
sallata nace "au dama ni matar ka ce, ai ni
har na manta ma. Thank you for
reminding me" yayi dariya tare da karaso
wa cikin dakin "kiyi hakuri, I know I
haven't been a good husband, but believe me things are going to change a gidan
nan from today" na jawo drawer,
pretending kamar sallaya nake sakawa a
ciki, na dauko abinda zan dauka a ciki na
boye a cikin hijab dina na juyo tare da
bata rai nace "ka riga kayi wasa da
damarka ai Mukhtar, I gave you a golden
opportunity ka debi kasa ka watsa min a
fuska, yanzu mun riga mun wuce wannan
stage din" na fada meaning every word of
what I said. Ya fara tahowa zuwa inda
nake "na san nayi ba dai dai ba, and
believe me it hurt me more than it did
you, why do you think na daina zama a
gida? It was because I couldn't get that
site out of my head, it drove me crazy, it
is still driving me crazy. Bana son in
hurting dinki, especially after what you
went through shi yasa na baki chance dan
ki warke sosai. But get ready" ya fada
smirking "because I am ready".
Na yi getting ready din kuwa exactly like
he said, but not in the way he meant, and
I watched him come closer har yazo
gabana ya tsaya idonsa yana bin jikina da
kallo duk kuwa da cewa still akwai hijab a
jikin nawa, ya tsaya so close har ina iya jin
saukar numfashinsa a fuskata yace "I have dreamt about this night Safiyya, fiye
da adadin da zan iya lissafawa, I have
planned for this night Fiyya more times
than I can remember, for years na yi
dakon soyayyar ki a raina mai tarin yawan da ban san adadin ta ba. And tonight, finally, burina zai cika, I
am finally going to make you mine, tawa
ni kadai, har abada".
Na mayar masa da murmushinsa, sannan
nace "I also have been planning for this
night Mukhtar, amma not for years but for
weeks"
And then just as I said that, allurar da
nake rike da ita a cikin hijab dina ta huda
hijab din nawa, ta huda kayansa, ta huda
tsokar cinyarsa sannan na juye masa
abinda yake cikin syringe din a jikin sa.
It happened in seconds, and it was done
before he realize what was happening.
The next second na matsa da sauri away
from him nayi hanyar bakin kofa na tsaya
ina kallonsa, ready to run dan jininsa yafi
karfin allurar,
Ya juyo yana kallona hannunsa rike da
cinyarsa, fuskarsa cike da mamaki " Safiyya!" ya ambata idanunsa suna juyewa,
"What have you done?" yayi taku
biyu zuwa inda nake yana miko hannunsa
gare ni, sannan yayi taku daya baya, na
dawo cikin dakin na karasa gaban shi na
tsaya daf dashi sannan nace "| am giving
you the taste of your own medicine" sai
kuma na saka hannayena biyu da karfi na
tura shi ya fada kan gadon da baya, and
he lost consciousness a lokacin.
My thought was drugging Mukhtar will be
the hardest part of plan B, amma sai
bayan da na same shi unconscious akan
gado na sannan na fahimci it was the
easiest. My plan was to use my handcuffs
in daure hannayensa a both sides of the
bed and then strip him naked in duba
abinda nake nema. Zan daure
hannayensa ne saboda ban san karfin
jinin sa ba ina tsoron kar ya tashi kafin in
gama abinda nake yi.
Amma sai lokacin na fahimci cewa karfi na
bai fi cikin cokali ba, ba karamar wahala
na sha ba kafin in jashi zuwa position din
da zai bani damar dare hannayensa duk
biyun. Kuma nayi hakan ne cike da tsoro
ina gain zai iya farkawa anytime. Bayan
na gama sai da na tabbatar handcuffs din
sunyi locking hannayensa completely
sannan na zauna na huta na sha ruwa sai na fara next task dina na checking his body for the scar, target dina dama shine bayan sa da cinyoyin sa, sai kuma a
lokacin na fahimci cewa ba zan iya cire
masa rigar ba saboda yadda hannayen sa
suke daure, so I