SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   83 / 113

246K to 249K   out of 336.6K words

feels like a background noise. Nayi ajiyar zuciya ina kallon wayar sannan na dora ta akan kirjina na dora pillow akan ta na rungume ina cigaba da murmushi, Nayi bitar maganganun mu da muka yi and I understand dalilin da yasa yake ganin zai iya convincing Mama cikin sauki, saboda bai san maganar Mukhtar da

amma yana motsa bakin sa da alama azkar yake yi. Na kama hannun sa na kai bakina nayi kissing sai ya bude ido ya kalle ni "good morning Daddy" a fada a hankali, ya gyada min kai kawai, nace "ya jikin?" Ya mayar da idonss ya rufe bai ce min komai ba sai na mayar masa da hannunsa kan cinyarsa a tashi ina tambayar nurse din ya yake ganin jikin daddyn. Yace "da sauki sosai Madam. But we will need a breathing machines on standby dan gudun kar a kuma samun irin
wancan attack din." na gyada kai da sauri '"dr Ma'aruf yayi min magana jiya a asibiti, har na bashi go ahead to order it, yace guda biyu za'a siya ko?" yace "yes, abinda ya kamata kenan, akwai bipap machine, shi kamar mask ne da za'a ke saka masa kullum danbya taimaka masa wajen jan enough air, sai kuma mechanical ventilator da za'a ajiye just in case of another attack" nace "za'a kawo su insha Allah" yace "okay. Sai kuma maganar abinci, baya iya hadiye abincin da zai wadace shi yanzu, dole a fara feeding dinsa through a feeding tube. But zainiya cigaba da gwada ci da kansa din amma kuma sai muke supplementing through a tube dan kar yake zama da yunwa" na gyada kai duk da hawayen da yake kawowa idona, a raina nace "a feeding tube it is, dan my father will not die hungry",

Na juya ina tafiya yana bina a baya yana cigaba da yi min bayanin yadda zasu ke Needing din nasa da kuma duk abinda suke bukata. Sai da muka kai parlour sannan na dakata har ya gama sai nace *kuyi magana da Dr Ma'aruf in ya shigo. Kace nace ayi duk abinda ya kamata" ya gyada kai "okay ma'am" gar na juya zan tafi kuma sai na dawo da baya ina kallon sa nace "will there be pain? Zai ji ciwo sosai?" Ya girgiza kai "no, Just discomfort kafin ya saba. The whole thing about ALS is that it is painless. Babu pain ko kadan" na gyada kai sannan nayi masa godiya na koma ciki,

A dakina bayan na koma na kwanta nake lissafa wanna shine kusan machine na goma da za'a siya wa Daddy to help him with the most basic things that healthy mutum yaje yi cikin sauki. Health is truly wealth, Bayan power wheelchair dinsa da take taimaka masa wajen tafiya automatically ba tare da an tura shi ba, tana kuma ina yin kwana sannan ta hau karamin tudu kamar na bakin kofa da sauran abubuwan da normal wheelchair bata yi, akwai machine din da yake taimaka masa wajen transferring dinsa from the wheel chair to the bed da daddare and back to the wheelchair da safe, akwai wanda ake daura masa a hannu wanda yake taimaka masa wajen aiki da hannun kamar cin abinci da operating wayarsa da sauran basic amfanin hannu, Da akwai wani a toilet da
yake taimaka masa wajen hawa toilet seat din da kuma sauka, da kuma tsaftace jikin sa in ya gama, da akwai na exercise, wanda ake dora shi kullum ya motsa dukkan jikin sa to avoid yankwanewa da nannadewar da jiki yake yi idan ba'a amfani da shi. Da akwai wani ma da muka yi order last week, wanda zai taimaka wajen amplifying voice dinsa yadda za'a ke jinsa sosai tunda yanzu maganar ta sa tayi kasa sosai, akwai wanda yake taimaka masa wajen yin tari ya kuma yi clearing airways dinsa tunda bashi da karfin yin hakan da kansa. Wadannan duk abubuwa ne da healthy mutane suke yin su kullum ba tare da sun biya ko kwandala ba. Ban iya komawa bacci ba, na jima akan gado ina saka da warwara, gabaki daya zuciya ta a dagule, daga baya sai na dauko wayata dan inga ko ina da meeting ko wani abu da zai dauke min hankali na and keep me sane, Sai naga sakon barka da tashi daga Muhammad "morning sweetling. Just want to put on a smile on your beautiful lips, with an assurance that today is going to be a good day insha Allah kinji? No matter what is going on in life I will always be by your side sharing the joy and the sorrow,
Forever and ever. With lots of love from your Baby". Nayi murmushi sannan nayi dariya ni kadai kamar tababbiya. Sai kuma nayi masa reply "hey Baby. Ya jikin? Thank you for the smile, really needed it. Sending
lots of love from a stupid heart crazily in love with you".

Daga nan sai naji na samu karfin fuskantar ranar. Na tashi a shiga wanka na dauki lokaci ina wanke jikina da
mayukan wanka na da suke karawa fata ta kyalli, laushi da santsi, Na fito daga shower na tsaya a gaban mirror din cikin toilet din ina goge jikina ina kuma kare wa kaina kallo, har yanzu ba zance na dawo yadda nake ada ba but na chanja sosai from yadda nake sanda na dawo daga Berlin, fata ta ta dawo color dinta na ainihi sai kyalli take tana daukan ido amma har yanzu ban mayar da kiba ta ba saboda har yanzun hakalina ba'a kwance yake ba, na tsaya ina kallon fuska ta da yadda tsarin komai yake a cikin ta, sai na sauke ajiyar zuciya ina godiya ga Ubangijin da ya halicce ta dan ko ni idan nibaka bawa ikon halittar kaina bana jin zan yi wa kaina kirar da tafi wadda nake da ita a yanzu. Na dan ja da baya ina kallon gurin da aka yanka a ciki na aka fito da Junior, na saka hannua hankali na taba gurin, ya danyi taurin da in ka taba zaka ji shi a hannunka amma a ido it is barely showing sai dai in kasan da shi dama and you are looking for it shine zaka gani, and it has been just 5 months, hakan ya sa na kara jinjinawa likitocin a bisa kwarewar aikinsu sannan kuma na kara tabbatar da abinda suka ce akan aikinsu baya barin scar. Cikina ma kuma bai nuna alamar cewa dan mutum ya zauna a ciki ba, ko dan bai karasa girma ba aka cire shi? Dan ko wata bakwai cikin Junior bai karasa ba sanda aka yi min aiki. Sai kawai naji ina jin tausayin sa, bai gama jin dumin cikin mahaifiyarsa ba bai kuma ji dumin ta a ranakun farkon rayuwar sa ba. Sai naji ina son ganin sa, just to hug him I little and assure him that I love him and that everything will be okay.

Amma kuma na san zuwa na Berlin a yanzu wani abu ne da zan iya cewa is close to impossible, babu yadda za'a yi in iya tafiya in bar Daddy kamar yadda babu yadda za'a yi in iya daukan Daddy a halin da yake ciki in tafi da shi. Na sake sauke ajiyar zuciya sannan a hankali nace "I am sorry Adam, You are going to be okay", A daki na zauna na shirya cikin doguwar riga marar nauyi bayan na shafe jikina da mayukan da suke kara gyara fata ta, sai kuma na jawo system dina na koma kan study table dina na bude na fara going through abubuwan da ya kamata inyi a yau. Na ga cewa ina da meetings har guda biyu daya da rana 12 daya kuma da yamma 4pm. Sai kuma na mayar da
hankali grin karanta wani breakdown da aka turo min na retailers dín kayan mu da yawan kayan da kowa yake siya a wata daga kamfani. Ina so ne zan yi musu kyauta ta bajinta dan in kara rike su gam a hannuna, Na gama dubawa sannan nayi deciding abinda zany musu a rubuta na tura wa marketing department, Ina cikin aikin Esther ta shigo ta gaishe ni tace "Madam breakfast fa yana kasa tun dazu, ko a kawo miki sama ne?" Na dan girgiza kai "kawo min coffee kawa'" ta bata rai "Madam, in ba kya cin abinci zaki fadi watarana" na daga ido ina kallon ta sai tace "so nake ki zama katuwa" na bata rai "I don't want to be katuwa" sal tayi dariyar yadda nake yatsuna fuska tace "to ki dal ci abinci please, Breakfast is the most important meal of the day. Ki samu ki ci protein sosai da breakfast, it will help you go through the day, ko da ace kin zama too busy to eat a complete meal to ba zaki rasa energy ba, Kuma breakfast baya saka kibar da ba kya so, tunda shi You will burn it down during the day ba karar dinner da ake ci a kwanta ba" na yi
murmushi "thank you for the lecture. Now, bring my coffee" ta dan bata rai ta juya tana magana kasa kasa, da alama mita take yi. Na bi bayanta da kallo ima murmushi sai kuma wani tunani ya zo min na mike na rufe system din tare da na da karamin mayafi a kaina na fita. A stairs na wuce ta da sauri ina hada
bibbiyu, ta biyo ni a baya tana haki, na juya nayi mata gwalo "idan da baki hada wannan kibar ba ba zaki yi haki for just coming down the stairs ba" ta bata rai tace "nima dai slimming din nan zan yi", A dining table na zauna tazo ta fara zuba min abinci tana cigaba da yi min lecture akan nutrition, "Idan kin ci da yawa ma you can always go to the gym and turn the fat into muscles" na bata rai "I don't want to have muscle" na fara cin abinci na ta zauna ita ma tana kallo na tana ta zabga murmushi. Ma juya ina kalion ta tare da yi mata alamar tambaya da hannuna sai ta girgiza kai "nothing
Madam. I am just happy that you are in a good mood today. Kwana biyu baya duk fuskarki babu smile" nayi murmushi "someone put a smile on my lips early this morning, and I am going to hold on to it har dare" ta danyi dariya tana tafa hannu "wonderful. I am so glad madam. Zanyi zaman daki. Please take me with you" na bude ido "I said someone, ya akayi kika san namiji ne?" Tace "I know love when I see it, and you madam are in love"., Nayi murmushi kawai bance komai ba.

A lokacin naji alamar wani ya shigo gurin, naga kuma Esther ta gyara fuskarta sannan ta tashi tsaye tana gaishe da wanda ya shigo din. Na juya na ga Mustapha sai na dawo da ido na kan abinci na na cigaba da ci. Ya karaso ya zauna Esther ta fara hidimar zuba masa abinci, ya kalle ni na dago kai nace "goodmorning" yace "how are you?" Ban amsa ba na cigaba da cin abinci na amma ina jin idonsa still a kaina sai yace "ci ba kiba dai inji hausawa sun ce asarar abinci ne" dariya ta kusa ta kwace min sai na mayar da ita, hakan ya sa na kusa kwarewa, Esther ta bar shi ya dawo gurina ya zuba min ruwa ta miko min, na karba na sha nagode mata nacigaba da cin abincin still ba tare da nace masa komai ba.

Yana cigaba da kallo na yace “why are you laughing?” Na danyi kokarin bata rai nace “dariya kuma? Waye yake dariya” yabata rai “wai da” nakara kokarin danne dariya ta na cigaba da cin abinci na. Esther tagama zuba masa ta juya ta fita ta barmu mu kadai. Yafara cin abincin sa yana kallo na har lokacin sai kuma yace “akwai maganar da nake so muyi dama fiyya. I have been thinking of a way to get you alone Amma na rasa, kin san yanda kike yanzu, kin zama hukuma sai lallashi” na gyara zama na tare da daukan cup din coffee na ina karasa shanye abinda yake ciki, na daga gira nace “wacce maganar ce knan ?” Yayi ajiyar zuciya “maganar ai guda daya ce. It is about us. I don’t know why you are still shying away from the truth, chasing a dream that will mever come true” na ajiye cup din ina jin raina yana baci nace “haryanzu dai ban gane maganar ba. Kace about us. Wacce magana ce about us” yayi shiru yana noticing changing yanayin fuska ta yace “kin sani ai” na mike tsaye nace “akwai maganganu da yawa da na sani about us Mustapha, maganar sanda kake cin zalina a bayan mutane sanda muna yara idan na kai kara kuma Safina tayi karya ta kare ka? Ko maganar sanda kayi ta trying to sexually assault me in then threatened me cewa idan na fada sai kayi da gaske?" Ya mike tsaye, jikinsa gabakidaya yana rawa idonsa kamar zai fado kasa dan tsoro yana kalion hanyar shigowa gurin "shishsh, me kike cewa Safiyya? Me ya kaio wanna maganar kuma?" Nace "ban gama ba ai, akwai wata maganar kuma, maganar sanda bayan mun girma kake shiga dakina a dukkan opportunity da ka samu and begging me to let you do
it ko da sau daya ne" ya tako da sauri zuwa gabana yay kokarin rufe min baki da hannunsa, fuskarsa cike da toro, na matsa baya da sauri na kuma cigaba da magana, "you told me babu wanda zai sani, you told me ko na fada babu wanda zai yarda, I had to find a way to protect myself from you Mustapha, Saboda kai
komawa nay kamar yar daba, duk dakin da na zauna ina ajjye da wuka a gefe saboda kai, har yau akwai wuka a dakina saboda in kare kaina daga sharrin ka. You traumatized my childhood, and you traumatized my nights at my teenage Na kasa gaya wa Daddy saboda maganar tayi min nauyi, na kasa gayawa Mommy dan mahalfiyar ka ce kuma ba lallai ta yarda ba kamar yadda kace. But maybe this is the right time to tell them, Maybe in na fada musu a yanzu
zasu fahimci dalilin da yasa na zarge ka akan abinda ya same ni. Kuma zasu fahimci dalilin da yasa nace bana son auren ka" ya sake kokarin rufe min baki, na juya da sauri na dauki wuka a cikin set din kanana wukaren da suke jere a cikin shelf din da take bangon dining room din "the next time you touch me will be the
last time you have a hand".

Ya yi taku biyu baya yana kara lekawa cikin parlour sannan ya juyo yana kallona. '"na riga na baki hakuri ai Safiyya. Me kike so in yi miki ne kuma? Kuskure ne da rudin kuruciya da kuma sharrin shaidan kuma babu wanda yake above mistake. Kuma ai banyi ba ko? To me yasa ba zaki yafe ki manta maganar ba? What do you want from me?" Nace "kaje ka gaya wa Mommy da Daddy cewa ka janye maganar aure na. In baka fada ba ni kuma zan gaya musu dalilin da yasa ba zan aure
ka ba" ya fara jujuya kansa "Safiyya. Wannan maganar ai ba ta kai wadda za'a fasa aure saboda ita ba. I promise you ban taba yi ba, a kanki ma kuskure ne da rudin shaidan, I mean you are very beautiful and we live together and I was young and hot blooded. But that doesn’t mean….” Na katse shi “I don’t care about shaidan and all his sharri stuff. Kai kayi min laifi kuma kai nake hukunta wa by not marrying you. I may forgive you but I can't marry you. Make them understand that or I will”.

Yayi shiru muka cigaba da tsayuwa muna Kallon juna. A lokacin ne muka ji shigowar Mommy, tun kafin ta shigo parlour muryarta ta karade gidan da Fada, Ya juyo yana kallona da sauri yace "I will do it, just don't talk about this again" ya fita da sauri ya taffi gurin ta. Nima fitowa nayi daga dinning din na tsaya akan steps din da ake takawa daga parlour kafin a shiga dinning din ina kalion kofar shigowa pariaur.

Mommy ta shigo mayafin ta a hannu tana zazzaga fada "ban taba ganin mahaukaciya, marar zuciya a duniya irin wanna yarinyar ba. Da ace bata kama da
ni tsaf zance chanja min ita akayi a asibiti. Ta yaya za'a yi ni yadda nake da wanna zuciyar amma ace ita tata kare ya dauke?" Mustapiha da yake kokarin
daidaita yanayin fuskarsa yace "Mommy lafiya? Ke da waye haka?" Hassan daya biyo ta a baya da jakarta yace a hankali “ita da yaya Safina”.

lta kuma Mommy tace "ni da wa kuma in banda waccan shashashar kanwar ta ka? Wai yarinyar nan ance za'a sallame ta yau na tashi da sassafe na tafi dan mu taho gida tare amma budar bakin ta wai ita
gidan mijinta zata koma, Ko a ina mijin yake? Dan wancan fitsararren yaron dai ba miji bane ba. Kuma wallahi ni da ita ne" ran Mustapha ya baci "kuma Mommy kika barta ta tafi baki babballata a asibitin ba?" Mommy tace "bar ni da ita. Bar mishi aikin
nayi. Jira nake yi yayi gunduwa gunduwa da ita ya watso ta waje kuma na gaya mata wallahi ba zan koma asibiti zaman jinyar ta ba sai dai ta tafi Katsina wadanda suka aura mata shi suyi jinyar ta a can.
Haka kawai yara suna nema su haukata ni. Wannan yaron ya zamar min annoba a cikin gidan nan wallahi. Ya mayar min duk yaran sun zama mahaukata. Daga safinan har Safiyya da nake ganin kamar tana da hankali".

Jin ta ambaci sunana sai nayi saurin yin baya zan koma inda na fito. Ban san ta ganni ba sai ji nayi tace "ina zaki je? Dawo nan" na juyo na dawo cikin falon na
gaisheta "good morning mommy" tace "wanne morning din? Wacce Mommy din? Yaushe rabon da ki gaishe ni a gidan

83 / 113