SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   86 / 113

255K to 258K   out of 336.6K words

hakan dan ka bani kariya kuma dan kayi forcing iyayen mu su bar mu tare".

Yace "then why didn't you let me do that? Yes, that's exactly what I would have done. Da kin barni nayi hakan da duk bamu zo wannan matsayin ba. Da magana ta wuce tuntuni" nace "da kuma iyayen ka har yanzu suna kallon ka da abin. Zasu yarda muyi auren but they will be very disappointed in you maybe har karshen rayuwar su akan abinda baka aikata ba. Yan'uwan ka, abokan ka, abokan aikin ka duk wanda ya sani ba zai kuma yi maka kallon mutumin kirki ba. Sunan ka zai baci akan abinda baka yi ba. And that's
something da ba zan taba yi maka ba a rayuwa"

Ya rufe idonsa tare da kwantar da kansa baya ya jingina shi a jikin kujerar da take bayan sa. Sannan a hankali yace "so you chose to lie to me. You chose to tell me that kina da aure. "I am married and I love my husband very much" ya karashe maganar cikin dacin rai, sai kuma ya juyo da kansa yana kallona yace "do you have any idea how much that hurt me?" Na girgiza kaina "it wasn't the best decision I know, But I wasn't thinking clearly. Tun daga samun cikin nan har zuwa haihuwar sa bana cikin hayyacina, Babu wani decision da nayi making a cikin lokacin da yake mai kyau ne except not telling you the truth, I mean, I tried to give up the innocent child for a close adoption a kasar da bama ta musulmai ba" na sunkuyar da kai na sannan na dago nace "I tried killing myself, twice" ya bude ido
sosai sannan ya gyara zaman sa yace "you told me kinyi kokarin cire cikin ko da a bakin ranki ne. Wannan ne second time din?" Na daga kafada nace "sanda kaje gidan mu ka gan ni tare da Mukhtar a mota, ya fita da motar, yana gudu a motar sosai and he said some bad words akan ka and I opened the door zan fita daga cikin motar".

Ya zaro ido sosai tare da rufe bakin sa da hannayensa, Fuskarsa cike da tashin hankali. Nace "na gaya maka wannan ne kawai dan ka fahimta kuma ka yafe min
maganganun da na gaya maka to break your heart dan ka rabu da ni" ya rike hannuna da sauri "ba maganar in yafe miki ake yi ba yanzu Safiyya. Promise me that you will never do something like that again" na gyada kai na "insha Allah", Sai kuma muka yi shiru for sometimes, kamar ya danyi calming down a little kuma ya dan fahimta duk da nasan sai yaje ya zauna ya tattauna da zuciyar sa sannan zai fahimta sosai ya kuma gane what he is getting himself into. Daga nan
kuma zai gane abinda ya kamata ya gaya wa iyayen sa, daga nan kuma zai san idan iyayen na sa zasu yarda da auren na mu or not, tunda shi ya sansu ya san abinda zasu dauka da wanda ba zasu dauka ba.

Mun jima a haka sannan ya ambaci sunana cikin sanyin murya "Safiyya" na dago kai na kalle shi sai na mayar da kaina kasa dan ba zan iya cigaba da kallon
jajayen idonsa ba. "I am sorry all this happened to you. Duk da har yanzu ban yarda cewa rashin gayamin was the best decision ba amma na fahimci girman soyayyar ki gare ni and na fahimci kin yi making that decision ne with my wellbeing in your mind, and I really appreciate that. And I will never take your love, understanding and care for granted. Kinji? Amma ina so kiyi min alkawari
saboda nan gaba, promise me you will never hide anything again from me. Through thick and thin, through joy and sorrow, for better or for worst, promise me we will always be together and look out for each other, Kiyi min wannan alkawarin kinji?"

Naji wata soyayyar sa tana karuwa a cikin zuciyata, shi a gurin sa wannan abin da na gaya masa bai ma kai abinda zai saka yayi considering rabuwa da ni ba. Shi kara jaddada min soyayyar sa yake yi a gare ni. Dama kuma na riga na san haka. But I want someone else to know. Dan haka na sake tambayar sa cikin karyayyiyar murya "Muhammad kamar kana manta wani abu. Ina da da. Dan da na haifa ba tare da aure ba. Wannan dan will always be attached to me and to yayan da zan iya haifa nan gaba. In kace zaka aure ni hakan yana
nufin abin zai shafe ka kai da yayan da zamu haifa nan gaba. Are you sure you want to........." Ya katse ni "I am more sure now than I have ever been. Babu abinda ya faru wanda yake laifin ki ko laifin shi yaron, kaddarar ku ce haka. Nima kuma soyayyar ki ita ce tawa kaddarar, kaddarar ki kuma ba ta rage ko kadan daga cikin tawa kaddarar ba sai ma karuwa da tayi. All I want to do now is to take care of you in tabbatar cewa ba ki sake zubar da hawaye ba sai na farin ciki" ,.

Na goge hawayen da suke bin fuskata, wadanda already na farin cikin ne ma. Ya sake matsowa kusa da ni. Yace "I want to marry you Safiyya. Will you marry me?" Na daga kai muka hada ido, murmushi yaso ya kubce min amma sai nayi sauri na rufe fuskata da hannuna na gyara mood dina sannan na bude fuskata a hankali nace "no".

Yayi shiru yana kallona fuskar sa cike da alamomin tambaya iri iri sai nace "I am sorry Muhammad. I am very sorry. This is the last part of maganar da zamu yi yau. And your answer is no. I love you so much, fiye da yadda kalmomin bakina zasu iya furtawa. Ba ni kuma da shakka akan son da kake yi min musamman yau
da ka sake tabbatar min. But I cannot marry you"

Ya koma da baya har sai da ya jingina da jikin kujera sannan ya zauna. Emotions dinsa mixed up. "Why?" Ya tambaya at last. Na fara kuka "saboda Daddy yace in
rabu da kai. Yace ba zai aura min kai ba. Ya kuma ce ko bayan ransa bai yarda in aure ka ba. Ba zan iya bujirewa maganar sa ba. He went through a lot a kaina, Ina so nima in faranta masa rai in yi masa
biyayya ko da kuwa hakan yana nufin zan rasa abu mafi soyuwa a gare ni. Dan Allah Muhammad kayi hakuri...…”.

Sai ya dafa kujera ya mike bai ce min komai ba, sai kuma jiri ya debe shi ya tafi zai fada kan kujura, na tafi gurinsa da sauri kamar zan rike shi sai ya daga mun hannu amma sai ya zauna akan kujerar, Na cigaba da kokarin yi masa magana Gidado, Iyayen mu sun fi koma muhimmanci a gare mu. Mama da Abba ba sa so. Daddy baya so. Both our families ba sa so. Soyayyar da muke yiwa junan mu is not enough especially in zata bata musu rai dan farin cilkin su yafi namu muhimmanci. Dan Allah ka fahimta." Ya dago kansa ya dafe da hannun sa yace "are you telling me inje in cigaba da zama da Safina kenan? Makaryaciya, mayaudariya munafuka? Ita kike so in zauna da ita ta haifa min yaya? And you? Who are you going to marry? Ko akwai wani ne dama da ban sani ba?

Na girgiza kaina tare da kneeling down a gabansa. “Babu kowa Muhammadu. Babu kowa a zuciya ta sai kai. Nima ban san wanda zan aura ba. Na yanke hukuncin zan bawa Daddy zabi ne kawai, duk wanda yaga ya dace sai ya aura min in dai hakan zai saka shi farin ciki. Dan Allah kai ma kayi haka. Ka bawa su Abba zabi”.

Ya mike tare da daukan key din sa sai na mike na kwace "dan Allah kar kayi fushi da ni Muhammad, It hurts me a lot to make this decision amma dole ne. Kai ne farin ciki na, amma farin cikin Daddy yafi nawa muhimmanci a gare ni. Dan Allah Muhammad kayi hakurj" ya miko min hannu, still expression dinsa unreadable '"bani key dina" na matsa baya ina girgiza
kai "ba zan barka kayi driving a wannan yanayin ba" cikin fada yace "you don't care. Don't pretend that you do" nace "but I do, more than you know" ya tako ya dawo gaba na ya tsaya yace "do you truly love me?" Na gyada kai na da sauri "fiye da yadda kake tunani" sai yace "then I will not give up. Ke kiyi abinda kike tunanin shine dai dai, nima zanyi abinda nake tunanin shine dai dai. Kamar yadda nace, soyayyar ki kaddara ta ce, then there is no turning back".

Ya juya ya sake yin hanyar fita nace "key din ka yana hannuna, I will not let you drive" yace "ki rike. Zan shiga ta haya".

Daga haka ya fita. Na koma na zauna akan kujera tare da dafe kaina ita share sauran hawayen fuska ta sai kuma na mike da sauri na bi bayansa, Sanda na hango shi har ya kusa kai wa bakin gate,. Tun daga tafiyar sa ma zaka gane cewa hankalin sa ba'a tare da shi yake ba, na ga Malam Ya'u ya bude masa kofa yana bin sa da kallo har ya fita ya rufe kofar sannan ya juyo muka hada ido, ya jima yana kallona nima sai kuma ya
koma gurin zamansa ya zauna.

Na sauke ajjiyar zuciya sannan na juya zuwa cikin gida cikin sauri mai hade da sassarfa. Na san next stop din Malam Ya'u shine gurin Daddy, a matsayin sa na loyal maaikacin Daddy da ya dauki shekara da shekaru suna tare, yana taya shi looking out for his family ne a lokacin da shi Daddyn yake kwance babu lafiya. Ni kuma haka nake so dama. Ina sane na bar shi ya ga komai. Babu kowa a parlour saboda an fara kiraye kirayen sallar magrib dan haka na wuce sama zuwa dakina na shiga na rufe kofa. A bakin gado na zauna tare da dafe kaina ina kokarin bitar maganganun mu da Muhammad amma na kasa saboda kaina gabaki daya ya toshe ya cunkushe. Hankali na gabakidaya yana kansa, Fatan kawai da nake yi shine ya fahimci
message din da na tura masa, ya fahimci ba da gaske nake ba cewar da nayi ba zan aure shi ba,

Na je window na bude labule amma bana iya hango shi. Ko ya samu abin hawa? Na hango Baba Ya'u a bakin gate yana alwala, na danyi murmushi kadan, na san yana yin sallah zai tafi gurin Daddy ya kai rahoton zuwan Muhammad kuma ya gaya masa inda muka zauna ni da shi. Ina sane nake barinsa yana ganin mu, ina sane kuma na zabi inda zamu hadu da Muhammad din dan ina so Baba Ya'u ya ga shigar mu. Dan ina so ya gaya wa Daddy exactly inda muka zauna.

Na fahimci cewa it took Daddy long to see maganganun mu da Mustapha saboda cameras din suna da yawa shi kuma bashi da isasshen lokaci, kuma bai san wacce Camerar zai duba ya samu wani abun kirki ba. Yanzu kuwa Baba Ya'u zai gaya masa exact camera din da zai duba da kuma exact time din da muka zauna. And he will see and hear everything.

And then he will know gaskiya akan komai da komai. Ni kuma nawa yanxu shine inyi folding arms dina in jira matakin da zai dauka. Na koma bakin gado ina shafa idanuna da suka kumbura saboda kukan da na sha yau, na dauki wayata na gwada number din Muhammad amma har ta gama ringing dinta bai dauka ba. Na sake jin hankali na ya tashi a kansa, na kara kira

still shiru sai na tura mass text

"Baby please call me as soon as you see
this. I need to explain things"

Na dan jira kadan sai kuma na tashi na shiga toilet nayi alwala ina gaya wa kaina maybe shima ya tsaya sallah ne ko kuma har yanzu yana hanya. Sai da na idar da sallah na gama adduoi na sannan na sake daukan wayar na duba amma babu call dinsa kuma bai yi replying message dina ba. A lokacin iya kololuwar tashin hankali na shige ta, na zauna akan gado na dafe kaina "ya Rabbi" na ambata a hankali.
Kamar daga sama naji ana buga kofar dakina, na tashi na bude na ga Hassan a tsaye yana kallona yace "Yaya ki zo inji Daddy" sai da naji kamar dan karamin
fitsari zai fito, na dafe kofa ina kallon Hassan da shima yake kallona da alamar tambaya yace "are you okay" na gyada masa kai da sauri sannan na koma cikin
dakin tare da rufe kofar na jingina da jikinta. Hankali na duk ya rabu gida biyu, ban yi tsammanin samun kira daga Daddy yanzu ba, sannan kuma ina tunanin halin
da Muhammad yake ciki.

Sai da na shiga toilet na dan watsa wa fuska ta ruwa duk kuwa da cewa babu abinda tayi sannan na fita da waya ta a hannu still expecting a call from Muhammad, Ina zuwa zan shiga part din Daddy muka hadu da Baba Ya'u yana fitowa, Ya bani hanya na wuce sannan ya bini da kallo. Sai na sauke ajjiyar zuciya tare da bismillah sannan nayi sallama na shiga,

Yana zaune akan kujerar sa. Kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin damuwa mai yawa. Na zauna a kasa ina addu'ar wannan damuwar da zan saka shi a ciki ta
zama ta karshe, nace "Daddy ganj" ya kalle ni ya dauke kai, kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "waye yazo gurin ki da zu?" Nayi shiru bance komai
ba. Ya sake cewa cikin karyewar murya "ba kya jin magana Safiyya. Me yasa ba kya jin magana ne wai? Yanzu idan Sa'adatu ta ga mijin Safina yazo gurin ki zance kina ganin zata ji dadi?" Nace "Daddy kayi hakuri, na kira shi ne na gaya masa abinda kace. Na gaya masa ba zan aure shi ba. Ba zan kara bata maka rai ba insha Allah Daddy. Duk abinda ka ce shi zany" yayi shiru yana studying dina sannan ya sake cewa "me motarsa take yi a gidan?" Nace "he couldn't drive after I told him that. Shine ya bar ta anan. Zai aiko a dauka" Daddy yay dan murmushi ace "lies........ He wants you to believe that. He wants you to think he care" nayi shiru ban ce komai ba sai ya ce "ki dauko key din motar Ki bayar a kai Bana son yayi amfani da wani uzuri ya sake dawowa gurin kj" na gyada kai sannan na mike zan fita yace "Safiyya" na juyo yace "you did good. Allah yayi miki albarka" a hankali nace "'Ameen ya Rabbi".

Sama na koma na dauko key din, ban sauko ba sai da na sake kiran number din Muhammad, amma yanzu bata ma shiga, na sauka da key din na bawa one of my
guards na bashi address din da zai kai. Duk zirga-zirgar da nake yi Mommy tana parlour tana kallona bata ce min komai ba kuma bata tambaye ni komai ba. Dama yanzu ta ja baya sosai da yi min magana tun akan issue din Mustapha, a fahimta ta kamar tana zargin ina da hannu akan korar Mustapha da Daddy yayi dan a rushe maganar auren mu.

Ban zauna a parlourn ba sai na koma dakina. Na zauna akan kujera ina jujjuya wayata hankali na a tashe. Nayi ajjiyar zuciya tare da lumshe ido na ina bitar maganganun mu da Muhammad. Tabbas maganar da ya fada min akan Safina ta taba zuciya ta sosai, fiye da yadda nayi tunanin zata taba ni din. All my life ba zan iya tuna wani abu da nayi mata da nayi deserving abinda tayi min ba. At least ta gaya masa gaskiya mana? Ko da gaskiyar ta gaya masa ba ta kyauta min ba ballantana wanna irin karya haka. Wato
ita duk halin da na shiga da abin da ya same ni bata ji tausayi na ba ma sam, maybe ma murna tayi da faruwar komai, Nayi tunanin labarin da ya bani na yadda taje social media tana cigiyar sa. Yace Mufida tace kusan shekaru biyu da suka wuce ne. Lokacin ma muna tare da Muhammad, lokacin muna tsakiya da kafa soyayyar mu, wato tun a lokacin tayi niyyar raba mu, kamar yadda Muhammad ya fada zata iya yiwuwa tun a lokacin ta dauki number dinsa a waya ta ta kira shi tayi masa tayin soyayyar ta yayi rejecting shi kuma, Shi yasa ta cigaba da yi min bincike with any opportunity da ta samu, looking for something that will link her to him.

Na sake kiran number din Muhammad, still a kashe, ji nake yi a kamar in zauna inyi ta kuka. Sosai nake so inji muryarsa. So nake inyi masa bayanin plan dina da
kumaoutcome din da nake saka rai. So nake in kwantar masa da hankali in kuma jaddada masa soyayyar sa da take cike a zuciya ta.[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: Na sake kiran number din Muhammad, still a kashe, ji nake yi a kamar in zauna inyi ta kuka. Sosai nake so inji muryarsa. So nake inyi masa bayanin plan dina da
kumaoutcome din da nake saka rai. So nake in kwantar masa da hankali in kuma jaddada masa soyayyar sa da take cike a zuciya ta.

Him👳🏻‍♀️

The last few weeks have been a rollercoaster of emotions for him. Daga wancan sai wancan sai wancan., And abubuwan ba Wai suna zuwa ne one after the other ba, suna zuwa ne wani issue din a cikin wani kuma har yanzu babu wanda ya samu yayi solving, dan duk issues din are linked to one thing, to one person, Safiyya.

Bai gama warkewa daga shock din karairayin da Safina ta gaya masa ba, wadanda ya san cewa Karya ce amma kuma still akwai something in them da yake son jin gaskiyar sa daga bakin Safiyya, Sai dai sanda ya samu Safiyya kuma har tayi alkawarth fada masa gaskiyar

86 / 113