SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 113

51K to 54K   out of 336.6K words

ya sa gashi dai shekarun girma sun zo min amma bana kukan rashin yaya, yaran da na rike sun zama gata na. Yayan yanuwana da na mijina duk dauka nake yi in rike su kamar ni na haife su, sannan kuma in debo marayu in rike su suma in basu duk kulawar da ya dace iyaye su bawa yaya, ko yan aiki aka kawo min na lura basu da cikakken gata a gidajen su sai in mayar da su yayana in rike su har in aurar da su. Ba zan iya lissafa yan aikin da na rike ba, tun daga kan Safiya har zuwa wannan yarinyar ta gaba na Lubabatu. Allah sarki Safiya Allah ya kai rahama kabarin ta. Duk da bata raye amma har yanzu ina morar gatan da na yi mata".

Su Gidado suka ce "Ameen" ta cigaba "ina gaya maka wannan ne dan ka saki jikin ka, nan gidan mutane ne, kowa kuma namu ne ballantana kai da aure zai hada mu. Ka fahimta ai ko?" Gidado yayi gyaran murya yace "na gane. Na gode kuma sosai. Allah ya kara lafiya" tace "Ameen ya Rabbi. Ai an gaya min cewa kai jika ne a gurin marigayi ambassador Muhammad Dikko. Mutumin kirki. Allah ya kai rahama kabarin sa. Na san shi ai lokacin da yana da rai, na kuma san matarsa Hajiya Fatima, ban sani ba ko zata gane ni amma in kaje kace mata Hajiya Maryama matar Alhaji Nasiru Atafi tana gaishe ta" Gidado yace "insha Allah za'a gaya mata".

A lokacin wata mata ta sauko daga sama, kallo daya Gidado yayi mata ya fahimci cewa ita ta haifi Safina, kamar su daya sai dai safina zata fi ta farar fata sannan da kuma bambancin shekaru. Ta zauna akan kujera a gefen su Gidado, suka juya suka gaishe ta ta amsa musu babu yabo babu fallasa sannan tace "sai yau ka samu damar zuwa gaishe mu kenan".

Hajiya tace "menene haka Sa'adatu? Tunda yazo ba shikenan ba?" Tace "ni kinsan bana barin magana a ciki na. Amma muna gari daya ace sai few days to auren Safina sannan zamu ga mijin da zata aura? A hakan ma kuma sai da nayi waya nayi wa mahaifiyar sa korafi sannan yazo, da bai yi niyyar zuwa ba ai. Da sai dai ranar bikin muma mubi cikin mutane muna tambayar ina angon yake"

Hajiya tace "tunda dai ita amaryar ta san shi ba shikenan ba?" Sai kuma ta juya gurin Gidado tace "rabu da ita, ita in dai idonta ya ga abu sai bakin ta yayi magana, haka halinta yake, zaka saba da ita a hankali. Tana da kirki sosai sai dai zaka sha faɗa" Mommy tana daga gefe ta kuma cewa "an anyi abu ba dai dai bane ba ai nake yin fadan" Hajiya ta chanza maganar ta hanyar yi musu korafin ba su ci komai da aka kawo musu ba, su kuma suka bada uzurin cewa sunci abinci a gida kafin su fito. Amma duk da haka sai ta saka aka kwashe komai da aka kawo musu aka kai musu mota. Da haka suka yi musu sallama suka tafi.

Suna shiga mota tun kafin su bar gidan Haidar yace "I don't like wannan surikar taka" Gidado yace "that makes the two of us" bayan sun dauki hanya kuma sai Haidar ya fara dariya yace "ka san tunanin da nayi, ina ma ace tare da Aunty Hafsat muka je gidan nan matar nan tayi mana wannan mulkin" Gidado yayi murmushi yace "da anyi yaki kuwa. She will humble her. Zan so inga yadda zasu kare da bikin nan".

*Her* 🧕🏻

Kwanaki suna ta tafiya har ya rage saura sati biyu lokacin da likita ya saka za'a yi min aiki yayi, amma sai naji sam bana jin tsoron aikin da za'a yi min ban damu da cewa wai cikina za'a yanka a fito da ɗan mutum ba, ni dai kawai burina shine in rabu da mayataccen cikin nan ko na samu in shaki iska mai daɗi, ko na samu in dai na ganin disappointment a fuskar Daddy a duk lokacin da ya kalle ni, ko na samu in manta da abinda ya same ni.

Sai dai ni kaina na san cewa rabuwa da cikin ba zata taba goge abinda ya faru daga zuciya ta ba, babu abinda zai fari da zai saka in manta da abinda aka yi min. Zalincin da aka yi min. Babu kuma abinda zai saka in yafe wa wanda yayi min. Har abada.

A lissafin Daddy naji yace aiki na zai kama washegarin daurin auren Safina. Ni kam ban ma rike date din da aka saka na auren Safina ba. Dan ni ba ma na gane ranaku a yanzu. Akwai kawayen mu da yawa da suke ta yi min magana a chats akan bikin Safina, ni kuma na kan basu amsa da cewa nayi tafiya jinyar Daddy dan haka bana nan za'a yi. Safina kam sai shirye shiryen ta take yi. Ta kan turo min pictures na kaya tace in taya ta zaba, har kayan da zata saka na kowanne event da zasu yi sai da ta turo min, sometimes na kan yi ignoring dinta dan ni abinda yake gaba na yafi karfin zaban kayan sawa, sometimes kuma sai in bata amsa dan kar ta ga kamar dan nasan kudin indirectly daga gurina zasu fito shi yasa na ke wulakanta ta.

Kamar yadda nayi tunani, su yan uwan nata da ta tafi Katsina gurin su dan suyi mata aure babu abinda suka yi mata na kayan daki, haka a dole Mommy ta sauko daga fushin da tayi da Daddy ta dame shi da waya akan ya bada kuɗin da za'a yi wa Safina kayan daki, direct yace mata bashi da kuɗi, besides, ai tace masa Safina ba yar sa bace ba. Sai ta koma gurin Uncle Ahmad shi kuma yace mata ta tambaye ni amma sai ta kasa tambayar tawa ta cigaba da bin Daddy, har sai da Daddy ya tabbatar tayi laushi sannan yace da Uncle Ahmad ya bata. Haka suka yiwa uncle Ahmad bill tun daga kan kayan daki har zuwa kayan da zasu saka na fitar biki, shi kuma ya raba biyu ya basu rabi yace ba zai bayar ga baki daya ba. A lokacin ne Safina ta yi min dogon message akan maganar, wai uncle Ahmad zai saka suji kunya, wai tun yanzu ya fara nuna musu cewa su ba yanuwan mu bane ba, dan Allah inyi masa magana.

Banyi masa magana ba sai na yiwa Daddy magana, tunda na fahimci shi sulhu yake so yayi a tsakanin mu shi kuma uncle Ahmad so yake a raba gari kowa ya kama gabansa. A ƙarshe dai Daddy ya saka Uncle Ahmad ya cika musu kuɗin suka yi duk siyayyar su suka gama.

A ranar da yake saura sati daya aikina, na tashi da safe kamar yadda na saba na shiga kitchen na haɗa smoothie na sha sannan na shiryawa Daddy breakfast. Na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana kwance idonsa a rufe amma daga gani na gane ba bacci yake yi ba. Na jawo table gabansa na dora abincin na zauna a gefe nace "Daddy ga breakfast. Ka tashi ka ci". Ya tashi zaune da kyar, na lura da effort din da ya saka yanzu gurin tashin yafi yadda yake yi da, ciwonsa yana kara cigaba a kwanakin nan fiye da yadda yake da.

Ya zauna ya debi oats din dana dama masa a hankali ya kai bakin sa, na kara lura da yadda hannunsa yake rawa sannan da kuma yadda ya hadiye abincin da kyar. Ya lura da kallon da nake yi masa yayi gyaran murya yace cikin muryar da ta kara zama weak "doctor yace nan da wata uku, that's idan na kai nan da wata uku, I will be needing a feeding tube, ba zan iya cigaba da hadiye abinci da kai na ba. Kin gane?" na gyada kai na da sauri tare da sunkuyar da kaina ina kallon ciki na da yanzu baya boyuwa a cikin riga ta. Ya kira sunana "Safiyya" na dago kai na kalle shi yace min "don't cry" na sake sunkuyar da kaina ina jin hawaye na suna zuba kan cinyata. Nayi saurin goge su. Sai ya sake kiran sunana "Safiyya" na dago kai, yace "munyi magana da Ahmad, za'a daura auren ki da Mukhtar washegarin da akayi na Safina, in anyi miki aiki da safe, da yamma za'a daura miki aure. Saboda baƙin da zasu zo na Safina ba sai sun koma ba sai a daura naki. Do you understand?"

Na sake gyada kaina ina rike hawayena. Sai na mike na yi hanyar fita, har na kai kofa ya sake kiran sunana "Safiyya " na juyo yace "kin fahimci dalilin yin auren nan ko?" Na sake gyada kaina ban ce komai ba na fita da sauri.

Daki na na wuce da sauri na rufe kofa sannan na zube a kan carpet din gaban gadon dakin na fara rera kuka. Kukan abubuwa da yawa. Kukan da ban san ranar da zan daina shi ba
[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: Daki na na wuce da sauri na rufe kofa sannan na zube a kan carpet din gaban gadon dakin na fara rera kuka. Kukan abubuwa da yawa. Kukan da ban san ranar da zan daina shi ba

alamar an bude kofar dakin an shigo, ban
dago kai na ba amma a raina na san waye
saboda mu biyu ne kadai a cikin gidan,
besides, motsin wheelchair dinsa daban
yake da motsin tafiyar sauran mutane. Ban
juya na kalle shi ba amma nayi kokarin
sassauta kuka na tare kuma da kokarin goge
goge hawaye na. Ya jima anan a zaune yana
kallo na sannan yace "I knew it. Dana na san
kina nan kina kuka. But what I do not know
is kukan menene kike yi? Uhmm, fada min,
kukan me kike yi".
Na cigaba da goge fuskata da bayan hannun
rigata, ina jin yadda already fatar idon ta
kumbura. Ya sake tambaya,
"ina jin ki?
Kukan menene kike yi?" Nace "I want you to
get better. I need you to get better" yayi
shiru na wani lokaci sannan yace
"you know
it is not going to happen. Sai kuma menene
again?" Na girgiza kaina "shikenan dama.
Shine kadai abinda nake yi wa kukan" yace
"liar. You are also crying saboda maganar
auren ki. Haka ne?" nayi shiru banyi magana
ba. Ya sake tambaya ta "ba kya son auren
Mukhtar? Kina so a fasa yi da shi?" Nayi
shiru still ban ce komai ba. Ya zagayo
kujerar sa gaba na yace "Safiyya. Ina so inyi
miki aure kafin in tafi in barki. Idan na mutu
na barki babu miji this people will tear you
apart. Kuma dole in aura miki wanda ba za'a
yi bincike ba ballantana a tono abinda ya
faru da ke. Wannan ya bar ni da very limited da ke. Wannan ya bar ni da very limited
options. I gave you the options. And you
chose. Wanda kika zaba ba shi zuciya ta
take so ba, hi zuciya ta tafi yarda da ki auri
Mustapha. But you adamantly chose
Mukhtar. And now you are crying. Tell me
why".
Na dago ido na ina kalion sa "Daddy, me
yasa kake son Mustapha?" Yace "saboda a
hannuna ya tashi, ni na bashi tarbiyya.
Saboda mahaifiyarsa ce ta raine ki, ita ta
baki tarbiyya. And sometimes family means
more than blood. Sa'adatu will never harm
you. But I am not so sure about Ahmad" Na
dauke kaina gefe nace "you know what they
want" yace "and what makes you think
cewa su Ahmad ba the same thing suke so
ba?" Nayi shiru ban ba shi amsa ba sai ya
sake cewa "a rayuwa Safiyya, most of the
relationships if not all da zaki shiga, ko ta
auratayya ko business ko zamantakewa to
trade by batter ake yi, to get something you
have to give something. The best logic is ki
san abinda mutum yake so daga gare ki, and
then use that to get kema abinda kike so"
Nace "Amma Daddy Mustapha fa..." Yace
"he didn't do it. Ban san how many times
zan gaya miki ba. He didn't do it" nayi shiru
ban ce komai ba, bana son gaya wa Daddy
abinda Mustapha yayi, bana son inyi using
the only card din da nake amfani da shi
grin taming Mustapha.
Jin nayi shiru bance komai ba sai yace
"are Jin nayi shiru bance komai ba sai yace "are
you changing your mind or not?" Na goge
hawaye na tare da girgiza kaina "no. Am not.
Ina neman alfarma dai guda daya. Dan Allah
Daddy bana son komawa Nigeria. I want to
live here. Or somewhere else. Anywhere
that is not Nigeria",. Ya juyo yana kallona, sai
kuma ya juya kujerar sa yayi hanyar fita ba
tare da yace min komai ba. Har ya kai bakin
kofa sannan ya juyo yace min "about
Mukhtar, ko da ana gobe daurin aure ne in
kika chanja shawara let me know ni kuma
zan tsayar da maganar".
Ban amsa ba nima har ya fita, ban kuma bar
space a zuciya ta da zan yi tunani akan
maganar ba. Na riga na yanke shawara and I
am not going back on it, duk kuwa da zafin
da zuciya ta take yi min akan hakan. Yana
fita waya ta ta kama kida, na san waye tun
kafin ma in kalle ta dan mostly ya kan kira ni
by this time. Sai dai sam bana son daukan
wayar ta sa. Zuciya ta bata so. Sai nayi
murmushi ina mamakin rayuwa ta, yanzu na
gama ja in ja da Daddy a kan sa, akan nace
shi zan aura, amma kuma still zuciyar ba son
sa take yi ba.
4
8:00 PM
Har ta katse ban dauka ba sai da ya sake
kira sannan na dauka. Na saka wayar a
kunne na banyi magana ba yace "ko baccin
ne dai? Na ga alamar ke ba kya gajiya da
bacci" nace "na tashi, kawai dai yau na tashi
bana jin dadi ne" yace "ni kuma yau cikin jin bana jin dadi ne" yace "ni kuma yau cikin jin
dadi na tashi. Have you heard the good
news? In the next eight days you are going
to be my bride. Duk da dai su Daddy suna ta
insisting babu taron biki, but I want us to
have ko da yar walima ne haka in kin dawo
nija...
.." Nace "yaya Mukhtar, I am sorry, but I
don't want any walima dan Allah. And I also
don't think zan dawo Nigeria." Yace "why
not? Fiyya komai da ya faru ai ya wuce
kuma. Daga anyi daurin auren nan shi kenan
we will put everything behind us muyi facing
sabuwar rayuwar mu and the ways to build a
new family k0? Gashi ma Allah cikin ikonsa
we will soon have a child to start the family
with. Abeg, ki shafa min kansa ko kanta and
tell them they are already loved at home".
Abinda ya fada was supposed to made me
feel better amma sai naji raina ya baci dan a
lokacin bayan uban dan cikina babu abinda
na tsana sama da dan cikin nawa. Amma sai
na daure zuciya ta nace "kayi hakuri yaya
Mukhtar. I can't. Abun zai wuce physically,
but the trauma will always haunt me, and
the best thing to do idan mutum yana son
moving on from a traumatic experience is to
change environment. Idan na dawo Nigeria
ba zan iya bawa family na kulawar da suke
bukata daga gare ni ba" yace "kina ganin
zaki ke tunawa da shine?" Nace "not just
him, Zan ke tunawa da komai" amma a raina
na san babban abinda nake gudu a komawa
Nigeria shine Muhammad. A yanzu da na
dan saka distance a tsakanin mu gani nake
kamar na samu wata kariya daga ciwon son kamar na samu wata kariya daga ciwon son
sa, amma ina komawa Nigeria na san zanji
tamkar an rushe katangar kariyar ne, and
there is a chance na cewa zamu iya haduwa
da shi, and that would be a disaster.
A haka dai ya hakura ya bar ni amma bai ce
ya amince ba kamar yadda Daddy ma bai ce
ya amince ba, ya dai ce min zaiyi tunani a
kai.
Daga ranar sai na kara cigaba da lissafi na.
Ina lissafa ranar aiki na kuma ina lissafa
ranar daurin aure na. Safina kept calling me
har sai da na daina daukan wayarta wai taji
labarin daurin aure na and tana son mu
shirya wani abu special ni da ita tunda muna
da friends daya musamman yan secondary
school din mu. Sai da taga na nuna mata
bacin raina sosai sannan ta rabu da ni.
Mustapha ma ya kira ni ban dauka ba, sai
gashi ya turo min dogon message a
Whatsapp wai yana yi min fatan alkhairi and
he wants us to put everything behind us a
cigaba da zumunci, and whenever I need a
big brother he will be there for me. A karshe
ya kara da cewa duk sanda nake bukatar a
dan sassama min Mukhtar I should just give
him a call.
Ya rage kwana biyar daurin auren Safina ni
kuma nawa shida sai ga Mommy ta kira ni.
Na dauka na gaishe and she lost the words
to say to me, sai kuma ta kama fada "yanzu
wato da ban kira ki ba ke ba zaki taba
daukan waya ki kira ni ba ko?" Nace "kivi daukan waya ki kira ni ba ko?" Nace "kiyi
hakuri Mommy" ta cigaba "na dauka a ranar
da muka taho yarinyar nan a ranar zaki fara
nema na amma ke ko ajikin ki ma sai kika
cigaba da sabgar gabanki ko?" Nayi shiru
bance komai ba, ta cigaba "ance min nan da
six days za'a yi miki aiki. Kina shan
magungunan ki dai ko?" Na ce "eh ina sha"
amma a zahirin gaskiya rabon da insha
magani tunda ta bar kasar. Tace "good. Ki
kula da kanki. Ki kuma kwantar da hankalin
ki, kin san a haihuwa babu abinda ake gudu
irin hawan jini" na yi shiru ban ce komai ba
sai ta sake cewa
"ko ba ki auri Mustapha ba
still ke ya ta ce" nace "Nagode Mommy".
*Him*
Kwanakin sauri suke tayi a gurin Gidado, so
yake su tsaya, dan ya samu at least ya shaki
numfashi amma sun ki tsayawa and every
day there is something to do. Gidan su
already har ya fara cika da mutane
musamman saboda bikin biyu za'a hada,
gashi kuma bikin farko ne da za'a yi a gidan
na su. Wannan ya saka a dole ya rufe dakin
sa ya tattara ya koma gidan sa, gidan da aka
fara siya masa yanzu kuma da ya takura aka
sake masa wani.
8:00 PM
Babu shiri Haidar shima ya tattara nasa
kayan ya bishi, duk da hakan bai yiwa
Gidado dadi ba dan yaso ya samu these
days to himself dan in suka kare kuma shi
kenan zai shiga cikin sabuwar rayuwar da kenan zai shiga cikin sabuwar rayuwar da
bai ma san ta inda zai bullo mata ba. Yana
sane yaje ya kamawa

18 / 113