SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   54 / 113

159K to 162K   out of 336.6K words

lallaba Daddy ya ga Muhammad
ko yaga iyayen sa just to prove to him
cewa ba yaudarar sa nake yi ba, in yaso
sai in cigaba da karatu na kamar yadda
Daddy yake so.
33
11
12:01 AM
Amma sai Daddy ya kira ni yace "I will go
to your school and withdraw you tunda ba
karatun kike ba, sai in sama miki
makaranta a waje ki tafi can kiyi karatun,
dama ke kika nace wannan kike so" da
kyar na samu na lallaba shi ya hakura ya
bar ni in cigaba da karatun a nan bayan
nayi masa alkawarin babu ni babu kula
wan saurayi har sai nayi graduating. And then two years into my studies, muna
exams din gama level two zamu shiga
three, I decided to take a bold step in kawo Muhammad gidan mu duk da babu
amincewar Daddy sai in ga yadda drama
din zata yi unfolding.
anar birthday din Muhammad ne, he was
turning 27 years. Ranar ne kuma Daddy
zai shigo Abuja shi da Mustapha. Ya kira
ni ya gaya min cewa ni zanje airport in
dauko su idan sun sauka. Saukar dare
zasu yi. And I planned on spending time
with Muhammad har zuwa lokacin saukar
ta su sannan sai in tafi da shi airport din
mu dauko su Daddyn tare. I was scared of
what will happen amma kuma I was
determined.
So I took Muhammad to the restaurant
and celebrated his birthday, a gurin kuma
nayi masa alkawarin a ranar zai ga
mahaifina. He was so happy...
I was so happy…….

And then as muna tsaka da cin abincin
mu, his phone rang, ya dauka
"hello, who
is this?" Sai ya ajiye "bana ji.....
.." Nace
"hope it is not important" ya kalli wayar
"new number, ban san waye ba", Muka
cigaba da magana, and he was already
planning on yadda zai siye Daddy na da
dadin baki, "He is a difficult person, I am
not sure idan zai yarda da dadin baki" ya
daga kafada "I am use to difficult people,
Don't worry, he will like me ko da baya so, But I suggest you go alone to the airport
ni kuma sai kiban address din gidan da
zaki kai shi sai inje in jira ku a can. He may
not like seeing us together a titi"
Na gyada kai, agreeing with him. Wayar
sa ta sake kara yayi ignoring nace "ka
dauka, maybe it is important" ya dauka
wayar "bana ji ai, kamar network din is
bad hear" ya saka a kunnen sa "hello?"
Sai kuma ya mike tsaye yayi min
murmushi tare da yi min alamar zai je
waje da hannun sa, I nodded and smiled
back at him and watch as he goes out.
Yana fita na dauki fork dina na cigaba da
cin abincin gaba na ina lissafin yadda
haduwar shi da Daddy zata kasance da
challenges din da zan fuskanta. Na saka
abincin a bakina kenan kira ya shigo tawa
wayar, na kalli screen din and I saw an
unknown number, without thinking about
anything na dauka na saka a kunne na
"hello?" And I heard a voice that sounded
so much like Mustapha's

"Fiyya! Kina ina? Mustapha ne. Jikin
Daddy ya tashi mun tafi dashi asibiti.
Hurry up"

Na mike da sauri gabaki dayan jikina yana
daukan karkarwa "hello, yaya Mustapha?
Mustapha?" But watakara kawai nake ji on
the other side ban kuma jin magana ba. I
cut the call and called again aka kuma
dauka but still bana ji "Mustapha? Kun
shigo gari? Kuna ina?" Still static, and
then another sound "hurry up" na saka
hannu na dauki handbag dina cikin sauri
nayi waje a hankali ina magana da kaina
cikin tashin hankali "Daddy.
.....
• Wayyo
Daddy na...... Wayyo Allah na…....
" Nayi
waje a rikice hawaye yana bin fuskata.

Ina fita na cigaba da kokarin trying
number din da aka kira ni da ita amma
kiran baya tafiya, zuwa lokacin sam na
manta ma da cewa tare muke da Gidado
ballantana in neme shi gabakidaya hankali
na yayi kan mahaifina da yake fama da
rashin lafiyar da already likitoci suka fara
lissafa masa lokacin da ya rage masa. Da sauri na doshi mota ta babu kowa a
gurin motar sai securities da suke daga
can bakin gate, na san asibitin da Daddy
yake ganin likita in yana gari, sai da naje
gaban motar na fara kokarin bude ta
sannan na lura da fork din da nake cin
abinci da shi a hannu na, ban san ma na
fito da shi a hannu na ba, Ina zaro key din
motar naji saukar hannu a fuskata ya
toshe hanci da bakina a lokaci daya, toshe hanci da bakina a lokaci daya,
tunanin da ya fara zuwa kaina shine
kidnappers ne, wani matsanancin toro ya
shige ni, zuciya ta ta buga da karfi making
my whole body weak, duk da haka sai da
nayi kokarin fighting amma sai aka hada ni
da jikin motar aka matse sannan aka kara
matse min hanci da baki aka hana ni
25
6
3
12:01 AM
numfashi, weakening my body more. I
started to paint, and I felt tsining allura
yana huda fata da tsokar kafada ta, and
then I lost consciousness.

Tsananin azabar zafi ne ya farkar da ni.
Zafin daga kasa na yake farawa sannan
yay vibrating through dukkan gabobin
jikina, blocking every line of thought,
destroying everything that made me who
I was and stealing every dream I ever had.
The strokes did not only took my virginity,
they took away my life.

An dare min idanuwana very tightly,
babu abinda nake gani sai duhu. At first
pain din da duhun ba su barni na gane
abinda yake faruwa ba, I later realized
what was happening and I was
devastated, I started fighting, trying to hit
the man above my with the little bit of
energy that I had, at the same time kuma ina kokarin bude idona but allurar da aka
yi min har lokacin ba ta bar jikina ba, and
also karfi na was no match for karfin
namijin da yake tare da ni.

A cikin kokawar da nake yi ne hannu na ya
sauka akan something metallic a gefe na,
ina dauka na fahimci fork ne from it's
shape, fork din da yake hannuna lokacin
da na fito daga restaurant din. In seconds
na dauka sannan da dukkan karfina na
soka wa wanda yake tare da ni.

I didn't think zai huda jikinsa but it did,
yayi sauri ya matsa daga jikina and I felt
his blood on my hand. Nayi sauri na fara
kokarin kunce daurin da aka yi wa idona
duk kuwa da zafin da nake cigaba da ji a
kasana. But an saka karfi sosai gurin yin
daurin and my hands and my whole body
was shaking violently, amma kuma a
lokacin babu abinda nake son gani sai
fuskar wannan azzalumin, fuskar wanda
ya dauki rayuwata,

Amma kafin in samu damar kunce ko da
dauri daya ne he came back and held
both my hands in one of his hands and I
felt another allura pierced the flesh of my
arm,

" will kill you!" Na fada "I will kill you" na
maimaita and then I lost consciousness
again.

Sanda na sake farkawa I was alone, lying
at the back seat of my car completely
dressed. Jaka ta, wayata, and mayafi na
all together akan seat a kusa da ni. Motar
a kunne, with the AC on. Nayi kokarin
mikewa zaune amma gabakidaya jikina
ciwo yake yi, kafafuwana har karkarwa
suke yi. Har lokacin ina jin alamar allurar a
jiki na, dusu dusu nake gani, hatta
kunnuwa na jin su nake yi kamar ruwa ya
shiga ciki ya toshe su.

Sannan ga bakin cikin da ya toshe
makogwaro na ya hanani numfashi. Na
kama kujerar gaba for support sannan na
mike zaune da kyar jikina gabaki daya
yana karmarwa, kokari kawai nake yi in
samu in leka waje ko zan ganshi, ko zan
ga wanda ya dauki rayuwata.

Duhu na gani a wajen, na kalli agogon
cikin motar naga 12:30 na dare. Wajen
yayi duhu sosai except for the street light,
da street light din kuma na gane inda
nake, layin gidan mu ne, just two houses
away from gidan mu, Na dauki waya ta na
duba and I saw several missed calls daga
Muhammad da Daddy da kuma
Mustapha, Mustapha,

I was 70% sure it was Mustapha because
of the encounters I had with him before
that, because of his name and his voice
that was used, and because of how him
and his mother reacted ranar da Daddy
yayi revealing my wealth. And also
because of how they treated me before
su san kudin da nake da shi and after sun
san kudin da nake da shi.

Na bude kofar motar na fito zuciya ta tana
tafasa, duk da ban ga fuskarsa ba but I
was sure Mustapha ne. Babu abinda nake
so a lokacin irin in nemi nearest makami in
Illata dan iska,

Sai dai ina fitowa dana cikin motar na
yanke jiki na fadi a gurin. Na sake mikewa
nayi taku uku zuwa hanyar gidan mu na
sake faduwa ina jin kaina yana juyawa
ganina yana gushewa. Sai da na huta
sannan na kuma mikewa still not giving
off, a haka na ja kafa har kofar gidan mu
sannan na sake faduwa a gurin ina jin
kaina kamar zai tsage.

Na ga an haske ni da fitila, na saka
hannuna na kare, naji muryar mai gadin
gidan mu "Safiyya?" Sai ya koma da sauri
ina jin sa yana magana "yallabai! Ga
Safiyyan da naji ana nema" sai kuma gasu fara kokarin dagani "Fiyya? Are you okay?
Lafiyar ki kuwa?" Na fara ture shi "karrrrr
ka tabbba ni.
14
9
2
12:01 AM
Dan isssska. Allah yaaaaa isaa na" and I
realized cewa irin maganar yan shaye
shaye nake yi.

Sai naga ya sake ni ya tsaya yana kare
min kallo, and he said the words "are you
drunk?" A lokacin Daddy ya fito da sauri
kamar zai fadi "Safiyya? Daga ina kike
haka?" Nayi kokarin tafiya gurinsa cikin
tangadi "daddddy" and I fall down again a
kusa da kafafuwan sa. "She is drunk"
Mustapha yayi concluding,

Avi hakuri da wannan.

*. *. *. *. *

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹

Episode Thirty Nine : A Trap



Kunga ji da neman indazaku samu kayan
tsabtace muhallinku da kamsa sawa duk
awuri daya to this is ur bustop El Wada's
sun tanadar maku da komi d kuke bukata
cikin Amin ci.
Munda turarukan wuta irin su
Sandaliya Arab
Exclusive hawii
White House Kajiji
Special flasks
Habeel florals
Brown humra
Classic
VIP white humra
Soulmate da sauransu
Toilet cleaner
Mopping mist
Air fresheners
Ceramic/ tile cleaner and more
https://chat.whatsapp.com/
IHHSMB9AyPcEDUMpYkJh4a

Muna marabada masu siyen daya ko sari.

Not Edited

A gigice Daddy ya fara kokarin daga ni.
Na kama shi na mike amma saboda ba shi
da karfi shima sai muka tafi kamar zamu
fadi, Mustapha ya taho da niyyar taimaka
mana sai na tura shi baya da hannuna.
"kar ka taba ni na gaya maka" na fada
cikin murya irin ta yan maye. Daddy ya
ture shi shima yace "kar ka taba ta tunda
bata so" Mustapha ya matsa gefe yana
kallon mu sai na zagaye hannayena a
wuyan Daddy na cusa fuskata a wuyansa
na fara kuka, feeling safe at last.

A haka ya tafi da ni ciki, muna ta tangadi
tare kamar zamu fadi amma ya hana
Mustapha kama ni saboda nace bana so,
har muka shiga ciki sannan ya kwantar da
ni akan kujera yana kallona fuskarsa cike
da tashin hankali. Ya juya gurin Mustapha
yace "call the doctor, da sauri" sannan ya
juyo gurina "Safiyya?" Yace yana kallon
cikin ido na "what happened to you?"
Kafin inyi magana Mustapha da yake
tsaye a gefe yace "wallahi Daddy wannan
yarinyar a buge take, kalli idonta ka gani"
Daddy ya mike a fusace "zaka je kayi
abinda na aike ka kayi ne ko zaka cigaba
da tsayawa a kaina kana gaya min
maganar banza?" Mustapha ya juya da
sauri ya fita,

Daddy ya sake juyowa inda nake ya tsaya
yana kallona, a hankali yace "inna lillahi
wa inna ilaihir rajiun" na daga kai nima ina
kallon sa sai naga kamar jujjuyawa yake yi
ba'a tsaye yake a guri daya ba. Hatta
bangon falon da kujerun gani nayi suna
motsawa kamar wadanda suke yawo a
cikin ruwa. Mustapha ya sake dawowa ya
ajiye kayana na cikin mota a gabana
"Daddy na ga motar ta a waje, kofar a
bude, ga jakarta da wayarta nan ta bari a
cikin motar, na shigo da motar ciki.....
Daddy ya sake rufe shi da fada "I don't
care about the car. Ka kira Dr din ko baka
kira shi ba? And call the police as well"
Mustapha yace "police kuma Daddy?"
Daddy yace "yes, police" Na mayar da ido
nana rufe, a take bacci ya sake daukata.

Cikin baccin naji Daddy yana ta magana
da karfi "I need the lab result now!" Na
bude ido na kadan na ganshi a tsaye tare
da doctor din da yake duba mu a Abuja,
doctor din yace "kayi hakuri Alhaji ka
zauna, ka ga ba lafiya ce da kai ba. Na
dauki jininta ai gobe da safe zany duk
tests din da suka dace a kai" Daddy ya
girgiza kai "ba gobe da safe ba. Yanzu
nake so kay running analysis din, in ba
zaka yi ba in kira wani yayi" yace "za'a yi
Alhaji. Zanje in bude lab din yanzu inyi, In zargin mu na cewa a buge take gaskiya
ne zamu gani a jinin ta and then sai
musan matakin da zamu dauka"

Bayan ya fita Daddy ya lura da cewa na
farka sai ya sake dawowa inda nake
"Safiyya, wake up! Tashi ki gaya min
abinda ya faru da ke? Daga ina kike? Me
ya same ki? Tashi ki gaya min" nayi
kokarin tashi amma naji na kasa, ko'ina na
jiki na ciwo yake yi min amma kuma ciwon
da yake cikin zuciyata yafi da jiki na
damuna.

Maimakon inyi magana sai na kama kuka,
I should have told Daddy there and then
what happened to me amma sai naji
maganar tayi min nauyi da yawa inyi da
mahaifina, and I missed my mother a
ranar fiye da kowacce rana. Akwai
maganganu da yawa da ya mace ba zata
¡ya yi da babanta ba sai dai da mahaifiyar
ta, ni kuma bani da mahaifiyar, and the
woman that is suppose to be my mother
figure is the mother of the person da nake
zargi da laifin rusa rayuwata,
WhatsApp.com
EL WADA'S GLOBAL VENTURES
EM
WhatsApp Group Invite
13
9
4
7:19

I had to switched off my phone saboda
kiran da Muhammad yake ta yi min, and
my heart broke for him dan nasan yana
can cikin damuwa akan tafiya da nayi na
barshi, yana kuma tunanin cewa ta
tabbata yaudarar sa nake yi kuma karya
nake yi masa da nace zan kawo shi gurin
baba na.

A falon muka kwana daga ni har Daddy,
but I doubt shi yayi bacci ma throughout
the night. Sanda na tashi da assuba naji
allurar ya dan sake ni dan ina iya gani
sosai sai dai ciwo da kaina yake yi sosai,
sannan kuma jiki na gabaki daya yayi
tsami. Na tashi da kyar na shiga dakina na
hada ruwa nayi wanka and I cried kamar
idanuna zasu fito lokacin da nake yin
wankan, I felt like a used and discarded
rag. I have heard about rape and read
about some cases of rape online amma
ban taba tunanin cewa haka feeling din
yake ba, bakin cikin is undescribable in ba
wanda ya shiga cikin matsalar ba, which
bana yi wa kowa fatan ya shiga din, babu
wa da zai fahimci abinda ake ji a cikin
zuciya,

Har lokacin kaina a toshe yake, dan haka
ban samu nayi zurfin tunani akan komai
ba ballantana in yanke wani hukunci mai
ma'ana. Ina fitowa na saka riga a jikina
kenan naji knocking a kofar dakina and muryar Mustapha, "Ki zo inji Daddy", Naji
wani bacin rai ya tokare min kirjina, tsanar
sa tana kara ninkuwa a cikin zuciyata.
Ina saukowa naga Daddy a zaune. Na
cigaba da tafiya a hankali ina dafa bango
da kujera dan har lokacin kafafuwana
karkarwa suke yi. Daddy ya bini da kallo,
shi a tunanin sa har lokacin a cikin maye
nake shi yasa nake irin wannan tafiyar. Na
zauna a kasa ina kallon sa amma na kasa
cewa komai. Ya sake tambaya ta "daga
ina kike jiya da daddare? Me yasa muka yi
ta kiran wayar ki ba kya dauka?" Na
sunkuyar da kaina hawaye suna sake
cigaba da bin fuskata. Na bude baki na
wajen sau uku amma kalmomin sun kasa
fitowa. Shin cewa zanyi Daddy I was
raped yesterday ko kuma me zan ce? Na
san dole zan fadi abinda ya faru ko dan a
bi mini hakkina amma ba xan iya gayawa
Daddy ba.

Muna haka doctor din jiya ya shigo tare
da Mustapha, ya zo ya gaishe da Daddy
yana kallona sannan ya mikawa Daddy
wata farar takarda, Daddy bai karba ba
yace "tell me, Gaya min kawai" likitan ya
dan yi gyaran murya yace "akwai
percentage mai yawa na hard drug a cikin
jinin ta" Daddy ya dafe fuskarsa da
hannayensa biyu "innalillahi wa inna ilaihir
rajiun" na dago kai na kalle shi, na jima
banga tashin hankali a fuskar Daddy irin wannan ba.

"Shaye shaye kike yi Safiyya?" Ya
tambaye ni muryar sa cike da
disappointment. Na kara karfin kuka na
"Daddy wallahi ban sha komai ba, ka bari
zanyi maka bayani" ya mike tsaye yayo
kaina "yi min bayanib mana to inji, idan ba
ki sha komai ba menene ya kawo hard
drug cikin jinin ki?" Nayi shiru tare da rufe
idona, maganar tana yin kuna a cikin
zuciyata amma bakina ya kasa furtata.

A lokacin ne naji abinda ban taba ji ba a
rayuwata, saukar kyakkyawan mari akan
kuncina, na bude idona a tsorace ina
kallon Daddy, kafin in ankara wani marin
ya kuma sauka wanda ya fi wancan karfi a
daya kuncin. Karfin marin ya saka mayafin
kaina ya kunce, sai ya kama gashina da
hannunsa ya finciko ni fadi a tsakiyar falon
"ba zaki gaya min gaskiya ba?", Doctor
din da Mustapha suka taso da sauri suka
rike shi, shima kansa neman faduwa yake
yi. Na kwanta a inda ya jefar da ni ina kuka
matsananci, Daddy bai taba duka na ba
tunda aka haife ni duk kuwa da tarin
laifuffuka na, amma yau gashi ya dake ni
akan laifin da ban aikata ba,

A lokacin naji sallamar wasu sun shigo
gurin, na cigaba da kuka na ban tashi ba har suka zauna suna gaishe da Daddy
amma bai amsa ba dan kamar magana ta
dauke a bakin sa, a lokacin na fahimci
police ne and I remembered Daddy
mentioning police jiya cikin dare.
Sai da Daddy ya gama mayar da
numfashin sa sannan yace musu "ina so
ku bincika min inda yarinyar nan take a
jiya da dare. Ta dawo min gida a buge and
something is telling me that there is
something or someone behind that. Da
akwai abinda ya faru wanda taki fada min"
sai ya dauki passport size picture dina a
aljihunsa ya mika musu "a M.D University
take zaune a hostel. Ku fara binciken ku ta
can.

See if you can get their cctv ku ga sanda
ta bar makarantar and if possible, with
who"
Nayi kokarin mikewa zaune ina jin wani
sabon tsoron yana kamani. Muhammad
ne yaje makaranta ya ajiye motarsa a can
sannan muka fita tare a tawa. Kamar
Daddy yaji abinda nake tunani sai yace da
Mustapha "show them her car, su dauki
hoton ta da details dinta",
Sai da duk suka fita sannan ya dawo
gurina yace min "in na tarar kina boye min
wani mugun abu ko Safiyya, sai na babballaki".
E3
Police din basu jima ba suka dawo suka yi
reporting findings dinsu back to Daddy.
Sunje MD din sunyi magana da security
kuma sun basu access to cctv din gate
din su, sannan kuma sunga fita ta daga
makarantar "ba ita kadai ta fita ba, tare da
wani suka fita a motar ta, but we couldn't
get his face from the camera. Amma
zamu cigaba da bincike, duk abinda muka
samo zamu gaya maka". And Daddy
almost lost his mind after that information
"ku koma makarantar, press the security
su baku more information, su gaya muku
waye yake zuwa makaranta yana fitar min
da yarinyar da na basu amana" sai kuma
ya juyo kaina "waye shi? Waye a cikin
motar ki jiya? Shi ya baki kwaya kika sha?
Ina kuka je? Menene hadin ki

54 / 113