Author : Maman Mama Category : Romantic Hausa Novels
ka
aikata wanna mummunan aikin? Kai ka
cutar da kanwar ka Safiyya irin wannan
cutarwar mai girma?" Mukhtar ya sake yin
shiru bai yi magana ba. Daddy yayi kamar
zai tashi daga kan kujerar sa cikin tsawa
yace "answer me!" Mukhtar ya dago kai
sannan ya fara jan guiwarsa zuwa gaban
Daddy "Daddy dan Allah kayi hakuri..
Wallahi ina son ta ne....…. Wallah sharrin shaidan ne..........Ina sonta ne bana son in rasa ta, Dan Allah Daddy kayi hakuri ka yafe min".
Daddy ya koma ya zauna yana kallon sa
yace "kana son ta kake ce min Mukhtar.....
Kayi mata wannan wulakancin sannan
kace kana son ta? A haka ake soyayyar?
An taba yin soyayya dole ne?" Mommy
tace "zancen soyayya ma bata taso ba. Baka son ta Mukhtar ko kadan ba ka son yarinyar nan. Dan ko makiyin ka sai wanda kiyayyar tayi zurfi sannan zai iya aikata maka wanna mummunan abu. Karya
kake yi wallahi Mukhtar" ya juyo gurinta
"Wallahi Mommy da gaske nake.... Wallahi
ina son ta. Tun tana karama nake son ta
ita kuma tace bata so na" Mommy tace
"tun tana karama? Kace Allah ne ya kiyaye
mu da tun tana karama zaka aikata mata
wannan aikin kenan tunda kai irin version
of soyayyar ka kenan. To wannan ba
soyayya bace ba bari kaji in gaya maka.
Wannan sha'awa ce. Mummunar sha'awa
ma kuwa irin mai cutarwar nan. Inda auren
ya dore ma akwai yiyuwar zaka cigaba ne
da cutar da ita kana kuma cigaba da gaya
mata kalmar so, wannan shi ake kira da
toxic love. Yanzu kuwa tunda Allah ya toni
asirin ka mun gane halin ka to sai dai ka ci
kanka ka sha bakin ruwa. Wannan
yarinyar kai da ita sai hange daga nesa.
Kai daga nesan ma ba zaka ganta ba".
Mukhtar ya cigaba da kneeling a gaban
Daddy, "Daddy dan Allah kayi magana,
Wallahi nayi nadama" ya fada tare da
fashewa da kuka, Still Daddy bai ce komai
ba, Mommy tace "nadama tukunna
Mukhtar. Baka yi nadama ba zaka yi dai",
Uncle Ahmad yace "na yarda da ke a wannan karon. Nadama ai ba yanzu zaka yi ta ba tukunna. Kuma wannan kukan munafunci kake yi bana gaskiya ba. Kar
kuma ka dora wa shaidan, sharrin zuciyar
ka ne kawai da ka saka mata tunane
tunane marasa kyau a cikin ta. Kuma shi
da kake bawa hakuri ai ba shine wanda
kayi wa laifin direct ba. Ga wacce kayi wa
laifi can kaje ka durkusa ka bata hakuri".
Mukhtar ya tashi daga gaban Daddy ya
dawo gabana ya durkusa "Safiyya, na san
na cutar da ke cuta mai girma. Na san
nayi miki laifin da babu abinda zai taba
goge miki shi daga cikin zuciyar ki. Amma
wallahi nayi nadama. Dama kawai nake so
a bani in gyara kurakurai na. Safiyya dan
girman Allah da soyayyar da kike yiwa
annabin rahama kiyi hakuri ki yafe min"
Mommy tace "Sallallahu alaihi Wasallama".
Ban dago kai na kalle shi ba ballantana
inyi magana. Uncle Ahmad yace "to
alhamdulillah. Sai ka godewa Allah tunda
ya baka ikon neman yafiyar ta tun kuna da
rai duk ku biyun. Dan Allah baya taba yafe
laifin da akayi wa wani har sai in shi wanin
ya yafe da kansa" sai kuma ya juya gurin
Daddy yace "yanzu dai yaya da Mukhtar
nan da Safiyya, dukkan su yayan ka ne.
Ka yanke hukuncin duk da kake ganin ya dace da abinda ya faru a tsakanin su". Daddy ya danyi shiru yana bin mu da kallo sannan yace "yanzu Ahmad misali ace na bar maka wannan hukuncin. Nace ka
yanke duk abinda kake gain shine dai dai. Me zaka yanke a kai?"
Uncle Ahmad ya juyo yana kallon mu daya
bayan daya sannan ace "to yaya.
Wannan dai wani lamari ne mai sarkakiya.
Lamari ne da ya shafi mutuncin ba su
kansu yaran ba har da mu har da sauran
yanuwansu da kuma yayan da zadu haifa
nan gaba. Mutunci dai Mukhtar ya riga ya
zubar mana da shi, abinda ya rage mana
shine mu tattara wanda ya rage mana mu
cigaba da kare shi. Irin wannan idan ya
faru ko da ba'a cikin dangi daya bane ba
kokari ake yi a rufe dan kare martabar
dukkan bangarori biyun. Abunda akanyi
idan an samu yaro takadiri irin Mukhtar ya
haikewa yarinya irin haka to sai a matsa
masa akan ya aure ta dan a kare martabar
ta, shi kuma a bashi damar gyara
kuskuren sa. Ballantana kuma yanzu da
ya kasance har da rabo a tsakanin su,
dole in mun tashi yanke hukunci mu duba
har shi yaron da aka haifa. Muyi kokarin
kare mutuncin sa da kuma rufe wa
mutane hanyar da aka bi aka same shi ta
hanyar tabbatar da aure a tsakanin iyayen
sa. To alhamdulillah a wannan case din already ma akwai aure a tsakanin su. Already ubangiji ya riga ya rufa asirin abin. Duk hukuncin da za'a yiwa Mukhtar ayi masa amma a shawarce Yaya abar auren
da yake a tsakanin su dan kare martabar
yarinyar da dan da ta haifa da kuma bawa
Mukhtar shima damar gyara kuskuren da
ya aikata. Wannan shine nawa hangen.
Amma abinda kace duk shi za'a yi".
Tunda ya fara magana zuciya ta take zafi,
ikon Allah ne kawai ya saka banyi magana
ba har yaje karshe. Sai nayi shiru ina jiran
inji abinda Daddy zai ce, zuciya tana
bugawa tana bugawa da kaifi ina tsoron
kar Daddy ya goyi bayan maganganun
uncle Ahmad dan it will break my heart to
say no to him
Sai naji yace "na gane maganar ka
Ahmad. Kuma na fahimci manufar ka.
Sannan na yarda kana da gaskiya, dan
kusan abinda ake yi kenan a cikin
mutanen mu idan aka samu issue irin
wannan, kokari ake yi a binne dan a kare
martabar iyalin. Sai dai kuma matsalar
guda daya ita ce, Safiyya is not like all the
other girls da ake yin hakan akan su".
"Tun Safiyya tana yarinya, tun bayan
rasuwar mahaifiyar ta, loka6da na fara
bata tarbiyya. Kai da Sa'adatu da sauran
mutane da yawa kun sha gaya min cewa
tarbiyyar da na ke bata ba irin wadda aka
saba yi a kasar hausa ba ce ba, kuna
ganin kamar ina lalata tarbiyyar ta ne ta
hanyar bata freedom, musamman
freedom of speech. Kunce sai abinda take
so nake yi mata bana tursasa ta akan
abinda ni nake son tayi. To yau zan gaya
muku dalili. Za kuma ku fahimci result din
tarbiyyar tawa. Ina bawa Safiyya zabi ne
akan duk abinda ya shafe ta komai
kankantar sa saboda ina so ta koyi
making decisions a rayuwar ta dan nasan
zata fuskanci kalubale da yawa, duk da
ban hango mata wanna masifar ba
amma na san zata fuskanci kalubale da
yawa kuma dole zata bukaci courage din
saying yes or no as a final decision. Na
san kuma ba zan zauna tare da ita ba har
abada. A yanzu kuwa ku kan ku shaida ne
cewa Safiyya doesn't need anybody to
make her decisions for her. Namu shine
mu bata shawara a matsayin mu na
wadanda muka fita hangen nesa, But the
final say is hers" ya juyo yana kallo na
yace "Safiyya, Talk to us, Ga abinda
Mukhtar yace ga kuma shawarar da uncle
dinki ya bayar. Me kika ce"
Na dago kaina for the first time sannan na
gyara zamana ina kallon su daya bayan
daya, na sauke ido na akan Mukhtar nace
"Mukhtar. Naji ka bani hakuri. Amma
kuma ban karba ba. Ba zan iya hakura ba.
Mukhtar ba zan iya yafe maka ba har
abada. Ko da nace na yafe maka to ka
tabbatar karya nake yi maka". Ya fara
matsowa zuwa gaba na "Safiyya
please.….. dan Allah" na cigaba "Abu
daya zaka yi min in yafe maka" da sauri
yace "menene? Anything you want" nace
"ka je ka kai kanka kotun musulunci a
yanke maka hukuncin da addini ya
tanadar wa duk wanda ya aikata irin laifin
ka. Idan kayi haka zan yafe maka.
Ubangijin ma zai yafe maka tsallake
iyakarsa da kayi" nan take naga yanayin
fuskarsa ya chanja, ya juya ya kalli
mahaifinsa sannan ya sake juyowa ya
kalle ni. Nayi murmushi "na san ba zaka je
ba. Saboda kamar yadda Mommy ta fada
nadamar karya ce kake yi. You just want
to emotionally blackmail us and blame
shaidan for your actions, you want to eat
your cake and still have it. You want to
just say sorry to me and shade fake tears
and you expect everything to just
disappear, Sai a dauke ni a mayar da ni
dakin ka kamar wata unwanted akuya".
Na juya gurin Uncle Ahmad nace "uncle I
am not sorry for saying this, ba zan koma gidan Mukhtar ba. Ba zan cigaba da
zaman aure da Mukhtar ba ko da kuwa shi
kadai ne ya rage a matsayin namiji a
duniya. Tabbas abinda ka fada shine
abinda ake yi wa mata da yawa a kasar
hausa. Namiji yay raping mace sannan ayi
forcing dinta to leave with him a matsayin
mij for the rest of her life. Wannan zalunci
ne ba karami ba. I was raped. Ni nasan irin
tsanar da nake ji a zuciya ta ta wanda yayi
raping dina, dan haka na san yadda
wadannan matan suke ji a zuciyar su a
game da mazan da ake matsa musu suyi
zaman aure da su. Amma suna yin shiru
su zauna dan basu da bakin magana
kamar yadda Daddy yace. They are just
yes girls. They just do what they are told and live a
miserable life cikin kunci zuciya, hatred
toward their husbands da kuma cigaban
cin zali daga mazajen na su. Dan duk
namijin da zai iya raping yarinya to tabbas
cikakken azzalumi ne, kuma chances are
he will continue to rape her day after day
a cikin rayuwar auren nasu, Chances are
high that she will never know what true
marriage really feels like. Ga raping, ga
auren dole sannan ayi sentencing dinta to
life time of torture. And all for the crime
that she didn't commit. Amma shi wanda yayi laifin sai reward ma da aka bashi na auren ta, babu wani hukuncin da za'a yanke masa saboda a rufe maganar kar aji kunya".
Na girgiza kaina "no. Not me. That will
never happen to me. Not in thousand
years...…." Na juya kan Mukhtar nace "na
baka shawara naga baka yarda ba. Okay
in ba zaka yi hakan ba kana da wani
option din again. You will go to jail. You
will go to jail for as long as its legally
possible for someone with your crimes.
You will never go free, ba yan'uwan ta ka
ba ko uwa daya uba daya muke da kai. I
will make an example of you Mukhtar,
maybe sauran mutane zasu yi following,
maybe sauran mata zasu fara breaking
this chain of torture suna reporting
mazaje masu irin halin ka".
Ya fara girgiza kai "Safiyya dan Allah. Na
baki hakuri fa Safiyya nine fa Mukhtar.
Wallahi ban san maganar zata yi karfin
haka ba" ya juya gurin su Daddy "Daddy
dan Allah ka bata hakuri. Abba dan Allah
ka saka baki, Wallahi nayi nadama,
Wallahi ban san zata samu ciki har ta sha
wannan wahalar ba" Mommy tace "Allah ne ai ya kama ka shi yasa ta samu cikin. Da babu cikin da
maybe har abada babu wanda zai san
abinda ya faru sai dai tayi ta rije bakin ciki
a cikin zuciyar ta har mutuwar ta" na juyo
ina kallon ta nace "yes Mommy. Na
tabbatar akwai mata da yawa da aka taba
raping amma har su mutu babu wanda zai
san anyi, sai dai abun yayi ta cin su a
zuciyoyin su saboda fadar ma ya zama
abun kunya. In mace ta fada ita za'a vi wa
tambarin while culprit din will be free, ko
kuma ma ace sharri tayi masa"
Na mike tsaye ina kallon Mukhtar da yake
ta hada uban gumi nace "I will see you in
court" na juya zan fita sai uncle Ahmad ya
mike ya kira suna na "Safiyya!" Na juyo
ina kallon sa idanu na a bushe "what
about you? Idan kin kai maganar nan
court dole sunan ki yana ciki, ke yanzu
babbar mace ce a cikin al'umma dan haka
sunan ki zai yi tambari. Yes, za'a yanke
masa hukunci a rufe shi ke kuma sunan ki
zai baci. Shin ba zaki yi considering
wannan ba?" Na juyo na dawo tsakiyar
dakin nace "suna? Wanne irin suna ne ya
rage min uncle? Wanne bacin suna zanyi
wanda yafi wanda nake ciki yanzu? Maybe
maidan maganar ta fita cewa I was raped
in samu sympathy na sensible mutane.
mean cikin shege fa nayi uncle, I already
have a bastard child uncle, wanne mutunci ne kuma ya rage min?"
Na fada with raising anger. Mommy ta mike "still Safiyya…... Nima yanzu na fara
goyon bayan uncle din ki. You still have
your reputation to protect Fiyya. A yanzu
babu wanda ya sani sai gidajen nan guda
biyu. In kika fitar da magana kuwa duniya
gaba-daya zata sani" nace "for how long
Mommy? For how long maganar zata
tsaya a tsakanin mu? Safina will say it the
first chance she gets. And someday aure
zai iya taso min a garin bincike wani da ya
ga wani abu zai iya gaya wa wani shima ya
gaya wa wanj and then everyone will
know, abinda kuma zasu sani sannan
zasu fada shine Safiyya Adam
Muhammad tayi cikin shege. No body will
mention sunan Mukhtar a ciki. All fingers
will point at me. The innocent me"
Na ga duk still sun cigaba da kallona,
daga alama babu wanda yake goyon
bayana a cikin su sai na juya daga hanyar
zuwa cikin gida nayi hanyar waje., Mommy
ta rike hijab dina, "ina zaki je kuma
Safiyya? Kar ki fita a wannan yanayin" na
juyo ina kallon ta nace "zanje gidan radio
da television da duk wata media channel
that I can get to, zan je in bada labarin
how my cousin raped me, and how my
family are trying to cover it up dan su
"kare martaba' ta, martabar da already aka riga aka zubar min. And I am also going to write an article inyi
publishing on the Internet, in saka sunana
da nasa, in bada labarin abinda ya faru
sannan inyi tagging all the humanitarian
organization da zasu kwato min hakkin da
kuke kokarin hana ni karba"
A falon babu wanda yake zaune sai
Daddy, daga dukkan alamu duk na hada
musu zafi. Uncle Ahmad ya rike hannuna
shima "Safiyya. Yata ki nutsu ki dawo ki
zauna. We will talk about this. Zamu sake
magana. We will find a way out kinji?".
Mommy kuma tana cewa "ba dai jail kike
so ya tafi ba? Zai je jail but don't go and
publish your name a duniya.…...." Suna ta
maganganun su naji Daddy ya kira sunana
"Safiyya!" Ya juya ina kallon sa yace "ki
koma gida, Zamu yi magana in an jima" na
karbe hannaye na daga gurin su nayi
hanyar cikin gida, sai kuma Daddy ya juya
yana kallon su yana murmushi yace "na
tabbatar yanzu kun fahimci abinda nake
nufi, She can stand up for herself, Ba ta
tsoron uban kowa. Yanzu bani da
damuwa, Ko yau na mutu na san she will
take care of herself".
A ranar na zauna da daddare na rubuta
labari na da duk abinda ya far da ni.
Including names and places da komai.
Banyi publishing ba amma sai a barshi
sai naji abinda Daddy zai ce. Amma har
cikin zuciya ta bana jin damuwa wai dan
nayi publishing sunana a matsayin rape
victim.
Washegari da safe naje gaishe da Daddy
sai yace in zauna zamuyi magana. Ina
zaune har Mustapha ya gama taimaka
masa yaci abinci sannan ya fita ya bamu
guri
Daddy yace "naji maganganun ki jiya"
nayi shiru ina sauraron sa sai na ji shima
yayi shiru. Nace "Daddy to me zaka ce
akai?" Yace "I don't know Safiyya. Ni na
san zafin da nake ji a zuciya ta a
matsayina na mahaifin ki ballantana kuma
ke da abin ya faru da ke. Kuma zan so ace
Mukhtar ya samu hukunci wanda yafi
kowanne hukunci tsanani akan abinda
yayi miki. Zan ji dadi sosai idan hakan ta
faru ko dan ya zama izna ga yan baya"
nace "good, Then kana goyon bayan in
shigar da kara court kenan?" Yace "yes,
zan so hakan, Amma kamar yadda Ahmad
yace what about you?" Na girgiza kaina "I
don't care about me Daddy. I have no
honor left. Bani da wani sauran mutuncin
da zan kare " yace "kina da shi Safiyya. Kina da shi sosai. Idan kuma kamar yadda
kika ce you don't care about yourself
what about Junior? What about other
children da muke saka ran zaki yi aure
nan gaba ki haifa? What about their
reputation?" Nayi shiru ina kallon sa ina jin
raina yana baci sai ya cigaba "ke uwa ce
Safiyya. Just last week kika zauna anan
kike gaya min yadda kika saka rayuwar ki
a danger to protect martabar Junior. In
kika ce zaki watsa labarin nan a duniya kin
zubar da waccan maganar kenan
gabakidayan ta, duk abinda kika yi kinyi in
vain. And not only him, yayan duk da zaki
haifa nan gaba will also be tagged with
that. Zaki haifi dan halak nan gaba amma
mutane will also call him shege saboda
basu san wanne ne shegen ba. They will
tag all your children as bastard. Duk inda
kika je kika boye Junior sai anje an binciko
shi. Ba karamin aikin mutanen mu bane ba
ki ga pictures din sa suna yawo a social
media together with your story ko kuma
ma a kara wata karyar akai".
Naji hawaye yana bin fuska ta "to yanzu
shikenan Daddy? Shikenan ba za'a
hukunta Mukhtar ba" yace "za'a iya
hukunta shi Safiyya. But bata hanyar da
kika dauko ba" na share hawaye na nace
"ta wacce hanyar to, Daddy me zan yi? Ya
zanyi?" Ya daga kafada "I don't know, But I know something. Your mother is the
smartest person I know when it comes to
decision making. And you are smarter
than her. You are her modern version. Na
tabbatar you will make the smartest
decision"
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Forty Seven : The Decision
*Free baking master class*
I'll be sharing delightfully delicious
recipes including how to make soft and
fluffy doughnut for *free* it's completely
free A-Z
Click the link below to join
Females only
https://chat.whatsapp.com/
DN5w2VPGPhE0gf3700F9k0
0704248974
Zan koyarda snacks kala 8 kyauta
acikinsu akwai yadda zakiyi doughnut me
laushi da dadi classes dinnam kyauta ne
daga farko har karshe
Danna wannam link kiyi joining
Mata kawai
Or contact
07042486974
To be added
https://chat.whatsapp.com/
DN5w2VPGPhE0gf3700F9ko
Safiyya.....
Ranar kwana nayi banyi bacci ba ina saka
da warwara, a fahimci abinda Daddy
yake nufi, amma sai dai kuma fahimtar ta
sa ta toshe min hanyar da na biyo kuma
na kasa ganin wata hanyar da zata bulle
da ni xuwa destination dina. Na tashi nayi
sallah na gaya wa Allah bukata ta na roje
shi ya bani mafita tunda dai ni bani da ita.
Sai wajen asuba na kwanta akan sallayar
nayi bacci, bayan anyi sallah na tashi nayi
sallah sannan na koma kan gado na
kwanta bacci mai nauyi ya dauke ni.
Ban farka ba sai da rana tayi sosai. Na
tashi nayi wanka na shirya ina jin kaina
yana yi min ciwo duk kuwa da cewa nayi
bacci mai nauyi amma na san damuwa ce
ta saka min ciwon kan. Na dauko waya ta
ina dubawa sai na ga sako daga Abdul
yana yi min mitar bana neman su sai in
sun neme ni "munyi fushi" ya turo tare da
hoton Junior ya bata rai ya turo baki, Sai
na samu kaina da yin dariya, He looks so
cute and innocent and doesn't deserve all
this, Na shafa fuskar sa ta cikin wayar sai
nace a hankali "hey you, It is going to be
okay. You are going to be okay, I promise"
Nayi replying Abdul tare da tsokanar sa
ina tambayar sa labarin amarya. Sai kuma na tashi na tafi part din Daddy dan gaishe
shi. Ina shiga na tarar da shi a falon sa
tare da Mustapha suna gwada wani
machine da aka siyo masa da zai taimaka
masa wajen zama da tashi ba tare da an
rike shi ba. Na zauna a gefe ina kallon su.
Mustapha might be a bad