SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 113

45K to 48K   out of 336.6K words

yana makarantar, sai na kudiri aniyar zan san yadda zanyi ya ganni kuma ya fara yi min magana.

Daga nan na fara monitoring dinsa, na lura da sanda yake shigowa makarantar da kuma sanda yake fita. Sai na shirya plan dina. Sai da na daidaici lokacin da yake fita sannan na kwashi littattafai da takardu na tafi kan stairs din offices din nasu na baje wai ni lallai karatu nake yi. Ina zaune da uban takardu a gaba amma hankali na yana kan duk motsin da za'a yi a sama. A haka har na ji taku, na dan duba ta gefen ido na ga shine sai na dauke kai na cigaba da bude littafin gaba na amma ina jin zuciya ta tana ta bugawa da karfi. Ban ankara ba sai gani nayi yazo ya wuce ni ba tare da ko kallon inda nake yayi ba, yaje ya shiga motar sa ya tayar ya fice daga makarantar. Naji takaici ya kama ni. Amma na gaya wa zuciya ta cewa bai gane ni ba musamman saboda bayana zai gani sanda yaje saukowa.

Sai na chanja shawara.

Washegari takanas na samo kujeru guda biyu da dan karamin table na dasa a direct opposite stairs din su. Na baza takardu sannan na sawa kofar office ɗin sa ido, a haka har naga ya fito ya rufe kofa sannan ya fara saukowa, sai da naga ya kusa gama saukowa sannan nayi dabara na zubar da takardun gaba na, kamar irin iska ce ta zubar da su ɗin nan, ko bai ganni ba na san hasken takardun zai dauki hankalin sa.

Naji takunsa ya doso inda nake, ina jin kamar a cikin zuciya ta yake taka kafafunsa, sai kuma ya tsaya a dai dai sai ti na. A lokacin na tabbatar cewa ya ganni kuma ya gane ni amma ban kalle shi ba sai na cigaba da bude pages din littafin da yake gaba na. Naji Muryar sa "oh my God" still ban daga kai ba. Ya kara matsowa "oh my goodness. Piya? It is really you" na dago kai ina bata fuska, sannan na bishi da kallo tun daga kan takalmin kafarsa zuwa fuskarsa da take reflecting wani irin annuri da farin cikin da zuciyar sa take ciki.

Na bayyana mamaki a tawa fuskar "wow. Malam Muhammadu dan fillo. What are you doing here?" Ya ja kujerar da dama dan shi na ajiye ya zauna "ke zan tambaya Piya, what are you doing here? How comes? Taya kika zo nan? Shin ko mafarki nake yi ne?" Nayi murmushi ina nuna masa takardun gaba na "karatu nake yi. Anan makarantar nake. Kai fa?" Yace "I work here. Ga office dina can. I can't believe this. You have no idea yadda na sha wahalar neman ki a garin Abuja" a raina nace "taka wahalar ka sani ba ka san tawa ba".

Yace "ranar nan was the best and the worst day of my life. I can't believe I let you go ba tare da na karbi number ɗin ki ba. I went back to your car na zauna jiran mechanic dinki yazo daukan mota in karbi number ɗin ki a hannunsa, amma that good for nothing mechanic bai zo ba, anan nayi sallar la'asar da magrib" na rufe bakina ina dariya, shima yayi dariyar "stop laughing at me. Nasha wahala fa. Har dare bai zo. Da sassafe kuma dana koma gurin already har ya dauke motar".

Nace "to ai Allah ya yi yanzu, gashi mun sake haduwa" bai ce komai ba sai ya dauko wayar sa ya ajiye min a gaba na "i won't repeat the same mistake. Dauki ki saka min number ɗin ki" na dauka na saka, na mika masa amma sai yaki karba yace "save it" nace "okay, me zan saka maka yadda zaka gane. Safiyya Adam Muhammad kamar yayi tsaho, ko in saka maka Fiyya?" Ya girgiza kai "Piya. You will always be Piya to me" nayi murmushi ina jin zuciya ta fari kal. Nayi saving da Piya💝 na mika masa still sai yaki karba yace in kira, sai dana kira ya tabbatar ta shiga sannan ya karbi wayarsa. Na dauko tawa wayar a jaka nayi saving tasa number ɗin, farko na saka Muhammad, sai kuma na goge na saka "Pyar💝"

Forgive the typos

Say Hi to this number so that your number can be saved.

We are almost done with free pages insha Allah.

0704 203 0419

Yan kasuwa kofa har yanzu a bude take. Advert your markets with Safiyya and Gidado.[07/01, 10:41 pm] +234 906 816 1960: *❤‍🩹 Safiyya ❤‍🩹*



*By*



*Maman Maama*



*Episode Twelve: Twisted*



Free Episode

Masu bude telegram musamman saboda su karanta Safiyya, you guys have a special place in my heart. I really appreciate the love and support. Dan ku na kasa daina rubutu 😍💕


Gidado yayi taku biyu baya yana kallon hannun da mutumin ya miko masa, sai kuma ya kalli fuskarsa kamar mai kokarin gane wani abu "Mustapha? Mustapha kace" mutumin ya sauke hannun sa ganin gidadon bai yi shaking ba, Al'ameen yace "eh Mustapha yace, ka san shi ne?" Wani murmushi Gidado yayi, a zuciyarsa yana jin kamar an dauke masa wani babban dutse, yace "no. Ban san shi ba. At least not yet" mutumin ya mayar masa da murmushin sa yace "Yes. I believe we will soon know each other a matsayin in laws".

Yayi gaba su Gidado suka bishi a baya zuwa mota, sai a lokacin suka lura da cewa su biyu ne suka zo. Suka gaisa da dayan shima sannan suka shiga bayan motar su kuma suka shiga gaba, wanda ya kira kansa da suna Mustapha yana driving. Gidado ya juya kansa yana kallon waje yana jin daɗin iskar da take dukan fuskar ta sa, iskar yanci. Yanzu tabbas yana da tudun dafawa. Safiyya tana yawan ambaton Mustapha a maganganun ta kamar yadda take ambaton Safina. Ya kuma san cewa shi Mustapha ɗin yayan Safina ne uwa daya uba daya. It cannot be a coincidence ace wannan yarinyar sunan ta Safina sannan kuma tana da yaya Mustapha.

Ya san idan ya tabbatar wa da Mama cewa Safina yar uwar Safiyya ce to tabbas zasu yarda a fasa auren, ko ba dan komai ba ya san yanzu babu halittar da suka tsana irin Safiyya. Ya juyo da kansa, fuskarsa still dauke da murmushi, Al'ameen da yake ta kallon sa ya yi masa alamar tambaya "what?" Dan ya san ba da irin wannan fuskar suka taho ba. Amma Gidado bai kula shi ba so yake yi suje gidan ayi maganar a gaban Safina a gaban kuma Al'ameen yadda Al'ameen din zai zamo masa shaida a gurin iyayensa. Dan yanzu duk wani abun da ya shafi Safiyya ba yarda suke yi da maganar sa ba.

Basu yi nisa sosai ba suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi sannan suka shiga wani gida. Gidado ya bude ya fito yana kallon gidan, gida ne na masu rufin asiri, not luxuriously rich but middle class rich. Daga gani kuma gida ne mai mutane da yawa a cikin sa. Wadanda suka kawo su suka yi musu jagora zuwa bayan gidan, sannan suka shigar da su wani ƙaramin parlor. Suna fita Al'ameen ya tambayi Gidado "what? Menene kake ta fara'a haka? Don't tell me daga ganin yayanta har ka matsu da ka ganta" ya karasa cikin tsokana "Gidado ya zauna ya dora kafa daya akan dayar yana jujjuya ta yace "yes, in a way zaka iya kiran abinda nake ji a raina haka. Kai dai ka jira. You will be surprised with the outcome of this visit" Al'ameen ya zauna, trying as much as he can to be comfortable akan kujerar yace "to Allah ya sa muji alkhairi".

Basu dade da zama ba wasu samari suka shigo su biyu suka fara jera musu kayan ciye ciye bayan sun gaishe su. Gidado ya yi tilting kansa yana kallon yaran kokari yake lallai sai yaga kamannin Safiyya a tare da su, sai da suka gama sannan yace "are you guys twins?" Suka juyo suna kallon sa sannan suka kalli junan su suka yi dariya. "no" daya yace dayan kuma yace "a'a. Abokina ne wannan. Dan makotan mu ne". Gidado ya koma ya jingina kansa a jikin kujera tare da rufe idonsa, yana jin al'ameen ya bawa yaran wani abu suka yi masa godiya suka fita. Sai da suka fita Al'ameen yace "kannen ta ne twins din da kake nema?" Bai bude idon ba yace "kannen Safiyya ne" Al'ameen yayi ajiyar zuciya yace "Gidado, gidan su Safina muka zo nan ba Safiyya ba. What is wrong with you" gidado ya gyara zama yace "na sani, akwai abinda nake tunani. You will understand idan ta fito.

Ba'a jima ba kuwa ta fito ɗin. Kamshin turaren ta ne ya fara iso musu kafin ta karaso. Kyakkyawace son kowa kin wanda ya rasa. Fara tas mai cikar jiki da shape mai kyau wanda ta tabbatar ya fito a cikin doguwar rigar lace ɗin da ta saka, ba irin fitowar da za'a kira da tsiraici ba amma irin fitowar da zai dauki hankalin duk wanda ya kalle ta. Fuskarta da kwalliya dai dai gwardado. Tayi daurin dankwalin da ya zauna ɗas a kanta ya kuma bayyanar da yalwataccen gashin kanta ta baya. Ta yafa mayafi a side daya ya rufe rabin kirjinta.

Ta tsaya a bakin kofa tayi sallama. Suka amsa mata a tare sannan ta shigo kanta a kasa ta zauna a kujera ta gaishe su "sannun ku da zuwa. Da fatan hanya bata gajiyar da ku sosai ba" duk suka yi shiru babu wanda ya amsa. Kowa yana saka ran dayan zai amsa. Sai kuma suka kalli juna a tare suka amsa "lafiya lau" "yauwa".

Suka sake yin shiru gabaki daya. Ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta, Gidado kuma ya tsare ta da ido a ransa yana son ya ga ko zai iya tuno kamannin Safinar Safiyya, maybe ko ya taba ganin ta a hoto amma ya manta, yayin da shi kuma Al'ameen yake kallon Gidado da mamakin kallon da yaga yana yiwa Safina. Al'ameen ne ya katse shirun ta hanyar yin gyaran murya tare da cewa "malama Safina ya shirye shirye?" Ya fada already feeling awkward, dan shi ba gwanin magana bane ba musamman ga wadanda bai sani ba. Ta dago ido suka hada ido da Gidado, tayi murmushi tare da sake mayar da idonta kasa sannan tace "alhamdulillah. Ya naku?" Kafin ya amsa mata Gidado yace "ina twins?" Ta sake dago ido tana kallon shi, shi kuma yayi kokarin studying fuskarta yana neman yanayin mamaki amma sai yaga confusion. "Twins kuma? Wadanne twins?" Yace "naga Mustapha shi ya dauko mu dazu, na dauka tare da twins suka zo" ta sake bata fuska tare da girgiza kai "still ban gane abinda kake nufi ba. Mustapha daga ina yazo? Ai dama yana nan. But ka san shine wai?" Yace "shi Mustaphan ba yayan ki bane ba?" Ta gyada kai still cikin nuna rashin fahimta tace "eh yaya na ne, dan kanin baban mu ne. Ka san shi ne?"

Gidado ya mayar da kansa baya tare da rufe idonsa, yana jin dutsen da ya daga daga kan zuciyarsa dazu yana komawa yana cigaba da danne ta. Al'ameen yayi saurin cewa "kamar naga kin kawo mana snacks, ɗan zuba min" ta mike da sauri ta dauki dan karamin plate ta na zuba masa samosa amma hankalin ta yana kan Gidado, ta durkusa ta mika wa Al'ameen still tana kallon Gidado tace "is he okay? Ko baya jin dadi?" Al'ameen yace "fine, he is fine, akwai serviette ne?" Ta dudduba gefe sai ta mike tace "bara in kawo".

Tana fita Al'ameen ya ajiye plate din da ta bashi ya taba kafadar Gidado yace "kai lafiyar ka kuwa? What are you doing. What is with wani Mustapha and twins" Gidado ya bude idonsa, duk annurin da ya sauka a fuskarsa dazu ya kauce yanzu, yace "Piya tana da step sister mai suna Safina, and a step brother mai suna Mustapha. When I saw that guy yace min shi yayan wannan Safinar ne kuma sunan sa Mustapha, I thought......" Al'ameen yace "Muhammad! Must you relate everything to her? Komai na rayuwa sai ka jingina da ita sannan zai baka ma'ana. Are You telling me kazo gurin yarinyar da zaka aura and the first thing da kake kokarin tambayar ta shine ko ta san dangin tsohuwar budurwar ka? Does that even makes sense to you?"

Gidado ya dauki robar ruwa ya bude ya daga ya shanye gabaki daya sannan ya ajiye robar. Yayi murmushin takaici yace "maybe I am loosing my mind. But yes. To me everything relates to her. Nothing makes sense to me in dai ba'a haɗa da ita a ciki ba" Al'ameen yace "then I don't think you are fit to marry " Gidado yace "ha! Finally someone ya fahimta. Go and tell that to Abba and Mama watakila su ma su fahimta"

A dai dai nan Safina ta dawo hannunta rike da sabuwar serviette. Ta ajiye a gaban Al'ameen amma shi kuma sai ya mike. Tace "ba ka ci samosar ba" ya kalli samosar, shi ya manta ma ta ajiye masa, yace "thank you, zan dan je waje ne inyi waya" yana fita ta zauna akan kujerar da ya tashi daga kai tana kallon Gidado cike da damuwa tace "Habibi, kamar ba ka jin dadi ko? Ko tafiyar ce ta gajiyar da kai?" Ya dan juyo ya kalle ta "am fine. Kar ki damu. Yanzu zamu ga su baban? Gwara mu gama mu zo mu tafi"

Ta dan bata rai "tafiya fa ka ambata, yanzu fa kuka zo and ko gaisawa bamu yi ba sosai musamman tunda yau muka fara haduwa. Ya kamata mu danyi hira ai ko?" Ta karasa tana langwabe kai gefe. Ya gyara zamasa yana kallon ta yace "hira? Okay what do you want us to talk about?" Tace "at least ka fada min ya ka ganni? Tunda yau ka fara ganina. Gwara in san cewa nayi maka ko ban yi maka ba. And maybe tell me abinda yake damunka, watakila ina da maganin sa" yace "does that really matter? Kina ganin ra'ayi na akan ki yana da muhimmanci?" Ta mike ta ta bi ta gabansa zuwa inda kayan abincin suke ta zubo masa juice ta hado da snacks a plate ta dawo inda yake ta durkusa a gabansa ta mika masa juice din sannan ta koma ta zauna ta dora snacks din akan cinyarta tace "ra'ayin ka a yanzu shine yafi komai muhimmanci, musamman ni a gurina. Abinda kake so shine abinda zan saka a gaba na, abinda ba ka so shine abinda zan fi ki fiye da komai" yace "tell that to my parents" ya kurbi juice din ya ajiye yace "send me your account details, zan turo miki kuɗin da zaki yi hidima, am sure kina shirya wani abu da kike so kiyi. And if you need anything, message me".

Ranta ya baci har fuskarta ta nuna, tace "yanzu dai ba zanji cewa nayi maka ko banyi maka din ba? Duk wannan kwalliyar da nayi?" Ya mike tsaye "ban boye miki komai ba Safina. And you agree to take your chance with me. Wannan shine dai dai lokacin da zaki fara hakurin da kika yi alkawarin zaki yi" ta mike ita ma "kayi hakuri. Kar ka bata rai dan Allah. Kawai dai kasan mu mata muna da son yabawa, and when I walked in I noticed kana ta kallona, I thought na samu wani bangare na zuciyar ka" ya juya yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa sannan ya juyo yace mata "I was looking at you because I thought you were someone else, it turned out ba ita ce". Sai ya juya ya fita.

A waje ya hango Al'ameen yana waya, ya tafi gurinsa ya tsaya har ya gama, ya fahimci cewa da matarsa Humaira (read *Aisha Humaira*) yake magana saboda yadda yake ta zabga murmushi shi kadai, love is truly the most beautiful feeling ever. Sai da ya gama sannan ya juyo yana kallon Gidado yace "wai fitowa kayi ka bar ta ita kadai?" Yace "kai ma ba fitowa kayi ka bar ni ni kadai da ita ba?" Al'ameen ya danyi dariya "guri fa na baku ku gaisa sosai" Gidado yayo dan karamin tsaki "I can't stay inside with her. It is suffocating".

Haka suka cigaba da tsaiwa a waje duk su biyun, har sai da Mustaphan da ya dauko su dazu yazo yayi musu magana sannan suka koma ciki tare, basu tarar da ita ba. Ya zauna ya saka su a gaba sai da suka dan ci abinci kadan sannan ya nuna musu toilet suma yi alwala suka zo suka yi sallah, daga nan kuma ya fita sai gashi sun dawo tare da manya su biyu, wadanda duk suka baiyana wa su Gidado kansu a matsayin wan baban Safina da kuma kanin sa, suka tabbatar musu da cewa suna goyon bayan auren suka kuma bawa Gidado assurance ɗin cewa ba zai samu matsala da Safina ba.

"Tun tana jaririya mahaifinta ya rasu. Ni na rike ta tamkar ni na haife ta, ko bayan aure gurin na zaka zo akan duk wata bukata, kar ka yarda wani daga baya ya fito yazo yace maka shine yake da iko a kanta. Mune dangin ubanta mune komai nata" Babban cikin su ya faɗa. Da zasu tashi Al'ameen ya ajiye musu kudi masu kauri yace su sayi turare

Sai da zasu tafi sannan Gidado ya tuna da sakon ta da Mama ta bashi ya kawo mata, ya mika wa Mustaphan da yake tare da su yace ya kai mata, yayi dariya "kai dai kawai kace inje in kira maka ita kuyi sallama" ya kira wata yarinya "je ki cewa Safina tazo angonta yaƙi tafiya yace sai ya ganta".

Ba'a jima ba ta fito, ta yafa mayafi sosai wannan karon ta rufe jikinta. Gidado ya mika mata ledar hannunsa "inji Mama" ta karba tana murmushi "Nagode sosai. Zan kira ta inyi mata godiya" yace "good. Mu zamu tafi. Ki turo min sakon da nayi miki magana a kansa" ta girgiza

16 / 113