SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   75 / 113

222K to 225K   out of 336.6K words

kai "babu
abinda ya faru Mama. Su suna da
kananan maganganu ne kawai. Dan Allah
kar kike biye mata in ta gaya miki abu har
ki bata ranki" ta dauke idon ta daga kansa
tace "in ba fada kuka yi ba to wani abun
ya faru da ban. Me ya faru?" Ya gyara
zamansa, she will not let the issue go.

Yace "Mama, even if I tell you yanzu ba
zaki gane ba, zaki damu ne kawai. I will
tell you sanda na zama confidence cewa
zaki fahimce ni kuma ranki ba zai baci ba"
ta juyo tana kallon sa tace "okay kai ka
fahimta amma ni ba zan fahimta ba?" Ya
girgiza kansa "ba haka nake nufi ba. Ni
kaina ban san stand dina akan maganar
ba, I just don't want to worry you for
nothing. Nima ban fahimta ba ballantana
in fahimtar da ke" ta dan vi shiru sannan
tace "shikenan. Allah ya jishe mu alkhair'"
yace "Ameen" suka dan yi hirar gida
kadan sannan tace mass yaje ya gaishe
da Mommy (his grandma).

Ya shiga dakin ta ya tarar ita ma ta idar da
Sallah tana kokarin fitowa, sai ta koma ta
zauna tana yi masa murmushi "mai gidan
katako" yace "na karfen dai, Ya Amen ne
na katakon ai" tace "duk daya, Da kai da shi duk babu wanda yake yi min cefane dan haka duk na katako ne a waje na. Na karfe na yana aljanna" ya durkusa a
gaban ta "barka da yamma" ta shafa
kansa tare da amsawa cikin sakin fuska
"ina amaryar ka? Tun da tazo ranar nan ba
ta kuma dawowa ba. Ko ba ka koya mata
zumunci ne?" Yayi murmushi bai ce komai
ba sai ya fara kokarin mikewa, shi duk
hankalin sa yana kan Safiyya, ko ta daina
kukan?

Har ya mike sai Mommy tace "mamanka
ta gaya min ashe Safina jikar Hajiya
Maryama ce, matar Alhaji Nasiru" ya juyo
yana kallon ta yace "ba jikar ta bace ba,
yar kanwar ta ce, but kanwar a hannun ta
ta tashi shi yasa ake dauka jikar ta ce" ya
gyada kai cikin fahimta, har ya sake
juyawa sai tace "har na dauka yar Safiya
ce" yaji gabansa ya fadi, ya juyo yana
kallon ta yace "Safiya?" Tace "eh safiya,
akwai yar Maryama sunan ta Safiya, very
beautiful girl, sun taba zuwa gidan nan
shekaru da yawa da suka wuce tare,
lokacin duk iyayen ka suna makaranta, har
nake cewa ta bani ita in samo mata miji a
Nijar sai tace min an saka ranar ta a
lokacin, da wani mai suna Adam".
Ya juyo da baya kamar wanda ake ja da
igiya ya dawo gabanta "Safiya kika ce Mommy are you sure? Kuma Adam zata aura?" Ta bata rai "me kake nufi ne wai? Na gaya maka sunan yarinyar Safiya kuma zata auri Adam sanda suka zo and you are
still asking me?" yace "I mean shekarun
da yawa, are you sure about the names?
Saboda Hajiya Maryama bata taba
haihuwa ba" ta harare shi "shekaru da
yawa? Ni fa nonon rakumi na sha while
growing up ba processed milk irin wacce
kuke sha yanzu ba. My memory is very
good. Safiya sunan ta. Kuma Maryama
tace min yar ta ce, wanna shine abinda
na sani"

Sanda ya shiga mota ya fara driving sai
yaji ya kasa tantance wanne tunanin ya
kamata yayi yanxu. Safiya matar Adam
will definitely mean mahaifiyar Safiyya. In
dai kuma ba wani babban coincidence ba.
In haka ne akwai dangantaka ta jini kenan
tsakanin Safiyya da Safina? Ya tuna
maigadin gidan su Safiyya ya taba gaya
masa cewa tun mahaifiyar Safiyya na da
rai Mommyn Safina take zuwa gidan gurin
ta amma bai san dangantakar su ba. Are
they related?

Direct gidan su Safiyya ya tafi. Shi yanxu
yasan yana da license din shiga gidan a
matsayin sa na mijin Safina, Sai dai kuma
bai san abinda zai ce ya samu ganin Safiyya ba musamman tunda fushi take yi da shi sosai kuma ba lallai ne ta bashi hadin kai ba. Kuma yana tsoron kar ace Mommy ta dawo gida dan kar ta sake yi
masa hayaniya a tsakiyar ka. And that guy Mustapha ya gansu tare kuma bai san kallon da yayi wa abin ba.
Dan haka dole ya zama careful kar ya
bata goma daya bata gyaru ba.

Mai gadi yana ganin sa ya tafi da niyyar
bude masa kofa amma sai yayi masa
alama da yazo, ya fasa bude kofar ya taho
gurinsa sai ya tambaye shi "Safiyya tana
gida?" Baba Ya'u yace "a'a sun fita da su
Hajiya da farko, sai kuma suka dawo tare
da Mustapha, daga nan kuma sai na ga ta
fita ita kadai, ban san inda taje ba".
Muhammad yaji babu dadi. Ya sake
tambaya ko ita Mommy ta dawo sai mai
gadin ya ce masa bata dawo ba,
Mustapha ma kuma ya sake fita. "Kamar
gidan ka naji ance sun tafi ai",
Daga nan dai sai ya shiga gidan yaje ya
gaishe da Daddy, bai ji dadin gain jikin sa
ba but yaji dadin gaishe shin da yayi da
kuma yar maganar da suka yi, sai dai a
cikin sauri yayi ya gama dan baya son
Mommy ta dawo gidan ta same shi ba tare da ya samu Safiyya sunyi magana ba dan bai san zuwa yanzu abubuwan da Safina ta gaya wa Mommy din ba. Bai
kuma san me zai ce da Daddy ba a yanzu
ba tare da ya yi magana da Safiyya ba.

A haka dai ya hakura ya fita daga gidan
thinking of a way da zai samu ganin
Safiyya ko kuma at least yayi waya da ita.
Yanzu ko number din ta bashi da ita a
wayarsa and even if he is to get the
number ya san tayi blocking dinsa months
ago dan haka ko ya kira ba lallai ta shiga
ba. So he got another sim card just in
case.

Bai koma gida ba sai very late, ya san dai
dole Mommy ta bar gidan a lokacin. Ya
shiga part dinsa ya rufe kofa kamar
kullum sannan ya hada tea ya sha yayi
wanka yayi shirin kwanciya bacci. Ya
kwanta akan gado rigingine yana kallon
ceiling, idanunsa babu bacci ko kadan a
cikin su, babu abinda yake gani a cikin su
din sai fuskar Safiyya tana kuka, babu
kuma abinda yake ji a kunnen sa sai
muryarta tana kuka. Ya jima a haka sai ya
mike tsaye ya dauki wayarsa ya fita da
sauri ya shiga part din Safina. Dakin da
yasan tana kwana a ciki ya dosa kai tsaye,
ya je ya tura kofar ya shiga, har ta kwanta dan dakin da duhu babu fitila.

Ya kunna fitilar dakin. Tana kwance akan
dago ta rufa da bargo, ta juyo da sauri
tana kallon sa, daga alama ta kwanta ne
kawai amma ba bacci take yi ba. Ta mike
zaune da sauri tana kallon sa idanunta
cike da mixed emotions, akwai toro a
cikin su dan har lokacin bata manta da
ranar nan ba, akwai kuma anticipation and
hope din cewa ya dawo ne for more.
Kirjinta yana bayyana cika da kuma
firmness irin na masu ciki. He looked so
manly in his armless rigar bacci mai hade
da gajeren wando iyakacin guiwa.

Ya karasa bakin gadon da take kwance
akai ya dora kafarsa daya akai yana kallon
ta cikin ido yace "bani wayarki" she
looked confused "me zaka yi da waya ta?
Na rantse babu komai a cikin ta. Me aka
ce maka navi kuma?" Ya mika mata
hannun sa '"bani wayarki nace" ta jawo
wayar a gefen pillow din6ta ta mika masa
"wallahi babu komai a ciki. Kuma ka duba
ka gani" ya karba ya jujjuya ta sannan ya
mayar mata da ita yace "bude ta" ta bude
ta sake mika masa with confidence dan
tasan ita dai bata da wani abun boyewa a
cikin wayar. Ya dan jima yana daddanna
wa sai kuma ta ga ya dauko tasa wayar ya
daddanna ita ma, and she realized abinda yayi, and her heart breaks to thousand pieces.

Yana gama wa ya jefa mata wayar kusa da
ita ya juya zai fita, cikin karyayyiyar murya
tace "me kayi? Me ka dauka a cikin wayar
ta wa?" Ya juyo yana kallon ta yace
"number din Safiyya" sannan ya juya ya
fita, ya bar mata kofa a bude fitila a
kunne.

Direct ya koma dakin sa ya dauko sim din
da ya siyo dazu ya saka a cikin wayarsa,
yayi recharging sannan ya koma ya
kwanta yana kallon ceiling kafafuwan sa a
kasa yayi dialing, not even considering
how late it is. Ta shiga, har ta katse bata
dauka ba and he called again, tana cikin
ringing ta dauka kuma daga muryarta ya
san ba bacci take yi ba "hello? Who is
this?" Ya lumshe ido yana jin yadda
zuciyar sa tayi contracting, he so much
misses jin muryarta over the phone and
the memories of all those late night
phone calls just came flooding back to
him,

Ta sake yin magana "hello? Waye wai?"
Yayi magana a can kasan makogwaronsa
"sunana Muhammad Gidado, Please don't
hang up"

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹

Episode Fifty: Breaking News


Yaji tayi shiru daga can barin, amma kuma
ya san ta ji shi sannan ta gane cewa
shine. Yace "kiyi hakuri na kira ki cikin
dare, but na kasa bacci ne, ba zan iya
bacci ba without at least talking to you. I
tried seeing you ban samu ba. Dan Allah
ki bani dama muyi magana".

Tace cikin dacin murya "babu wata
magana a tsakanin mu Muhammad, kai
mijin yayata Safina ne, kuma ban yayan
ta, wannan shine kawai alakar da take
tsakanin mu. Bayan wannan ban san wata
da har zata hanaka bacci ba" yace "naji.
And ina so ki sani na shirya jin duk abinda
zaki fada min as long as zaki saurare ni
nima. Yanzu dai tambaya daya nake
©️2 neman alfarmar ki amsa min, just one
question, koma menene zai biyo daga
baya" bata ce komai ba amma kuma bata
katse kiran ba, sai yace "dazu naji
Mommy tayi wata magana, tace auren ki
ya mutu, I want to know idan da gaske ne,
I want to make sure dai dai kunne na yaji min ba wai ya gaya min son raina ba ne ba" tayi shiru bata amsa masa ba. Ya sake cewa "Piya, please ba dan hali na ba l want to confirm from you, this is very
important, bana son in dawo da tunanin ki
cikin zuciyata, bana so bakina ya furta
kalaman da suke cikin zuciyata akan ki
alhalin kina matar wani, bana so in yiwa
Allah laifi, dan Allah ki bani amsa".

Ta sake yin shiru, sai da ya kara roka "Piya
Please!" Sannan tace "aure na ya kare da
Mukhtar, but that does not mean
anything. Now this is a warning, kar ka
sake kira na" daga haka ta katse kiran.

Ya dora wayar akan kirjinsa lips dinsa
suna curving into a wide smile,
"alhamdulillah" ya ambata, shi yasan
second chance ne Allah ya bashi at
happiness kuma ba zai taba yin wasa da
wannan chance din ba, zai yi fighting for
his happiness with everything da yake da
shi a duniya, Ya san dai abin ba mai sauki
bane ba, musamman considering
dangantakar matarsa da Safiyya, both
iyayensu ba zasu yarda ba, Safina also
will do everything in her power ta hana
abin kasancewa but ba ita ce damuwar sa
ba. Damuwar sa a yanzu shine yadda zai
yi convincing iyayensa da kuma Daddyn Safiyya.

Yayi ta bitar abubuwan da suka faru a
ranar a cikin kansa, musamman
maganganun Safiyya na dazu da kuma na
yanzu, yasan cewa ranta a bace yake
sosai kuma bai yi blaming dinta ba for
that, amma kuma sam kalamanta basu
bata masa rai ba sai ma sanyaya masa
zuciya da suka yi, saboda dukkan
kalaman nata were screaming "I love you"
shi kuma wannan wan security ne a
wajen sa ya san space dinsa yana nan a
cikin zuciyarta. Abinda ya rage masa
shine ya samu ta huce daga fushin da tayi
and then the battle will begin.

Ya jima a haka yaji karar shigowar
message wayarsa, zuciyarsa ta harba da
sauri, ko bakar magana zata turo masa
indai har ta turo din to wani step ne for
him. Amma yana daga wayar sai yaga
Safina, yayi dan karamin tsaki sai kuma ya
karanta sakon nata.

"Just for the records, ban taba yin
nadamar wani abu ba a rayuwata kamar
yadda nake nadamar auren ka a yanzu.
Ban taba ganin azzalumin mutum, mugu,
wanda bai damu da kowa ba sai kansa ba
a rayuwata irin ka. I have been saying na
yafe mata dukkan abubuwan da kake yi
min da saboda wadannan tsakani na da kai ne, amma wanna ban yafe ba tunda saboda wata ne, ban yafe ba kuma sai Allah ya saka min"

Har ya ajiye wayar ya fara shirin yin bacci
sai kuma ya dauka ya tura mata reply.

"You are mistaken, it has always been
because of her, da ace baki ci amanar ta
ba, da ace baki yi min karya a kanta ba, I
might have been the best thing that
happened to you"

Tun daga lokacin Muhammad ya daura
damarar dawo da matsayin sa a gurin
Safiyya amma abin yana neman ya gagare
shi. Tun ranar da suka yi waya da ya tashi
da safe ya kira ta sai yaji ta rufe sabon
layin nasa shima. Bai hakura ba haka ya
cigaba da siyan layuka tana kuma rufe su
da zarar ta fahimci shine, daga baya kuma
sai ta daina daukan kiran ma kwata kwata,
maybe tayi deciding ta daina daukan new
numbers saboda shi. Messages kuwa babu ta hanyar da bai tura mata su ba har ta e-mail din ta amma
babu reply, bai ma sani ba ko tana gani ko
kuma bata gani amma haka ya cigaba da
tura mata su kullum safe da rana da
daddare kamar shan magani.

Yayi zirga zirga zuwa gidan su yafi adadin
da zai kirga amma baya samun gain ta,
lokuta da dama tun daga gate mai gadi
yake gaya masa bata nan, wani lokacin
kuma ya samu ya shiga sai ya kare da
gaishe da Daddy amma ba zai ga Safiyya
ba. Daga baya ma da yaje sai mai gadin,
wanda zuwa yanzu ya fara yi masa wani
irin kallo saboda yawan tambayar Safiyya
da yake yi, ya gaya masa cewa Safiyya ta
tafi Umrah.

Babu abinda kuma ya rage masa yayi illa
ya jira ta ta dawo, while jiran kuma ya
cigaba da tura mata messages telling her
every detail about his days da kuma halin
da zuciyar sa take ciki akan soyayyar ta.
Duk da bashi da tabbacin tana karantawa
or not. Har da bata sakon tsarabar da
zata taho masa da ita daga Saudiyya,
wani turare da ta taba kawo masa wani
zuwa da tayi lokacin suna tare.

Ya lura cewa Safina ta zama bitter a cikin
yan kwanakin nan, har tsayawa ta kanyi a
waje ta jira shi ya dawo da daddare ta
tambaye shi daga ina yake. Ko kuma in
taga yana waya ta tambaye shi da wa
yake waya, shi har dariya ta kan bashi
idan tayi masa irin wannan tambayar, baya
kuma bata lokacin sa gurin bata amsa. A cikin lokacin ne Humaira matar Al'ameen ta haihu, ta haifi baby boy. Tun a asibitin da ta haihu da shi aka yi komai har aka
sallame ta ta dawo gida sai kuma Mama
ta matsa masa tace ya dauki Safina ya
sayi kayan babies ya bata suje tare ta
kaiwa Humaira.

He did that, duk da cewa zuciyar sa bata
so amma baya tsallake maganar Mama
dan haka yaje ya hado kayan babies masu
kyau ya zo ya dauki Safina a mota suka
tafi gidan Al'ameen. Ya dauka zata yi
masa surutu yauma irin wanda take yi
masa a duk chance din da ta samu amma
sai ya ga ko kallon sa bata yi, wayarta
kawai take danna wa, wannan ya bashi
damar driving din sa hankali kwance har
suka je gidan.

A bakin gate yayi packing, sannan yace
mata "ga kayan barka nan a baya, ki
dauka ki shiga ki kai musu" ta juyo da
sauri tana kallon sa '"ba tare zamu shiga
ba? Mama tace min zaka kaini inyi barka"
ya daga kafada "kuma na kawo ki ba, Ga
gidan nan. Suna ciki. I guess akwai
mutane sosai ma a ciki duk sun sanki har
ita mai jegon in ke baki san su ba. Just
go……. In na gama abinda nake zan zo in
dauke ki".

Ta bude kofar ta fita reluctantly sannan ta
bude baya ta dauki ledojin da ya ajiye a
ciki, yayi murmushi mugunta, ya san tana
avoiding shiga family dinsa tun ranar da
ya kaita gidan kakannin sa and yanzun ma
yasan gidan Al'ameen din a cike yake da
yan barka. Bai dawo daukan ta ba sai
dare, and sanda ya zo daukan ta tana
shiga motar ta fara kuka, ya mika mata
tissue box and she cried har suka je gida.

Her🧕🏻

Ranar da muka je gidan Safina

Bayan na gama kuka na a daki sai kuma
wani tunani ya zo min, na san yadda naga
Muhammad dazu akwai yiyuwar zai iya
biyo ni gida and zai iya yin dabara irin ta
ranar nan yaje wajen Daddy ya saka
Daddy ya kira ni, pretending zai bani sako
or something. Ni kuma idan akwai abinda
bana son yi a yanzu to shine ganin sa.
Wannan ya sa na tashi na share hawaye
na na sake fita na tafi inda a can ne yanzu
na ke samun solace, the oasis, ina fita da
mota naga guards dina sun biyo ni and I
felt safer with them, ko ya biyo ni zasu
hana shi karaso wa inda nake,

A Oasis na wuni ni kadai, har sai da naji an
fara kiran magrib sannan na sake dauko
mota na taho gida, na san Daddy ba zai neme ni ba tunda ya na tunanin muna tare da Mommy a gidan Safina, amma kuma tunani na shine abinda ya faru a gidan Safina din bayan ni da Muhammad mun
fita, me Safina tace wa Mommy? Na dai ji
Mustapha a cikin maganganun sa ya
ambaci cewa Safina tana gida tana kuka,
na kuma san yadda Mommy take son
yayanta zata saka ta a gaba ne da
tambayar abinda ya saka ta kuka, and I
definitely know Safiya will lie and make
my the villain. Ina dawowa gida na tarar har lokacin su
Mommy basu dawo ba, na shiga gida na
wuce dakina nayi alwala na fito kenan zan
tayar da naji shigowar su Mommy, na
tayar da sallah ta, sanda na idar sai na
zauna akan sallaya ta for the first time na
rasa addu'ar da zanyi, gani nake na rasa
Muhammad, and with him na rasa komai
da nake aiming for a rayuwa ta. Duk wani
hope for a brighter future da naji sanda na
rabu da Mukhtar naji ya tarwatse a zuciya
ta.

Ina nan zaune akan sallaya ina aikawa da
annabin tsira salati sai naji an bude kofar
dakina an shigo, na daga kai na ga
Mommy ce da alama ko cire mayafin ta da
ta je gidan Safina da shi bata yi ba. Ta shigo ta zauna akan kujera tana kallona har na shafa addu'a ta sannan nayi mata sannu da zuwa. Tace
"ya ciwon kan naki?" Nace da sauki. Sai ta sake cewa "dazu kuma da kika ji kan ya dame ki maimakon
ki sha magani ki kwanta a can sai kika fito
ke kadai zaki taho gida? Kamar wadda
taje bakon guri? Gidan yar uwarki ne fa,
gidan Safina ne fa" na tashi daga kan
sallayar na fara ninke hijab dina nace
"Mommy nafi relaxing ne a gida, shi yasa"
ta danyi shiru tana kallona sannan tace
"sanda kika fita kun hadu da
Muhammad?" Na dauke kai ina nade
sallaya nace "wanne Muhammad?" Tace
"'kin san muhammad din da nake nufi ai,
mijin Safina" naji ciwon kalmar mijin
Safinan amma na danne nace "a'a, neman
shi ake yi?" Tace "sai naga kamar ke ya bi
sanda kika fita yana kiran sunan ki. Na
dauka zai dawo dake ne yace ki sha
magani ki kwanta kuma naji ku shiru,
shine na tura Mustapha yabi bayan ku in
kin

75 / 113