Author : Maman Mama Category : Romantic Hausa Novels
a
rayuwar ta, ta saba taking responsibilities,
tun Baba Hadiza tana da rai sai da yawa
Safiya ce take cewa ayi kaza ko kar ayi kaza
and most of the times Baba Hadiza tana bin
maganar ta ta ne dan ita din ta saba da bin umarnin wasu a tata rayuwar, dan haka
yanzu Safiya bata da damuwar daukan
responsibility and risks a rayuwar ta as she
had nothing more to lose except her life,
and to her, her life doesn't have much value.
Sai da suka ci abinci a gidan suka yi wanka
suka chanja kaya sannan Hajiya Kyauta ta
zauna dasu ta fara yi musu bayanin aikin da
za'a kai su suyi, wadansu daga cikin yaran
already sun taba yin aikin a wani guri dan
haka sun saba, Safiya kuma da bata taba
aikatau na kudi ba itama ta saba da wahalar
rayuwa dan haka bata jin cewa aikin zai
gagare ta.
"Babban abu mai muhimmanci da zaku rike
a aikin nan shine tsafta, kunga mutanen nan
yan gayun nan suna son tsafta ba sa son
kazanta ko kadan, amma kuma basa son su
wahala, dan haka babban aikin ku a gidan
shine ku tabbatar da tsaftar gidan. Aikin da
za'a baku ya danganta da gidan da suka
dauke ku, wasu masu shara da wanke
wanke kawai suke nema, wasu mai kula da
yara, wasu mai wankin kayan yara da guga,
wasu, wasu kuma mai girki. Ya danganta da
hannun wadda kuka fada. In munje a
gabanku za'a yi cinikin kudin da za'a ke
baku, amma kuma ba ku za'a ke bawa ba, ni
za'a ke bawa ina kaiwa iyayen ku. Duk Duk
abinda ya faru a gida ni zan lira a sanar
muku, kuma Icuma dulk abindia ya faru da lau
ni za"a kira a gaya min. Duik wadida tayi sata
ko munafunci ko zalunci za'a kore ta ta
koa garin su babu ruwa na".
Ita dai Safiya tana jinta amma a ranta tasan
babu wani abu da zai mayar da ita garin su,
ba zata koma ba ko da kuwa zata ke kwana
ne akan titi
Bayan sun shirya suka fita gabaki dayan su.
Tun a gidan farko da suka je Safiya ta kara
tabbatar wa da cewa ta shigo birnin tarayya,
dan ita dai bata taba gain irin wannan
gidan ko kuma makamancinsa a garin su ba.
Suka shiga falon gidan suka zauna, sai da
suka yi jira na gurin awa daya sannan matar
gidan ta sauko daga sama, sai a lokacin ta
tashi daga bacci. Ta zauna tana ta bata
fuska da daga hanci sama kamar wadida aka
ajiye mata kashi a gabanta.
10
9
115 AM
"Hajiya Kyauta nace miki ki ringa saka yaran
nan suna yin wanka sosai in zaki zo dasu
gidan nan. Ni zuciya ta saurin tashi take yi
wallahi". Hajiya Kyauta tace "ai kam sunyi
wanka Hajiya, duk babu wadda bata yi
wanka ba, sai dai kawai ace rashin turare
kuma gashi mun shiga rana". Ta fara bin su da kallo daya bayan daya
kamar mai zaben atampa a kasuwa sai ta
nuna Safiya. "Waccan zaki bani. Tafi kvan
gani'"., Hajiya Kyauta ta kalli Safiya tace
"wannan banda ita, akwai yar'uwar ta a
garin nan ita ta aika ni kauyen su takanas na
dauko mata ita" Hajiyan ta bata rai "to ai
kinji, ni duk sauran basu yi min ba gaskiya.
Duk sunyi min kazanta da yawa" Hajiya
Kyauta tace "to ai da sun kwana biyu anan
zaki ga sun gyaru sun koma yadda kike so.
Yanzun rashin kulawa ne ya saka suke haka"
ta sake girgiza kai" gaskiya basu yi kin ba, in
kin koma kya samo min wadansu wadanda
suka fi wadannan kyan gani".
A haka suka tashi suka fita, sai safiya ta
samu kanta da tambayar kanta me vasa
matar ta zabe ta bayan duk sauran yaran
sun fita kyan gani?
Suna fita Hajiya Kyauta ta kuma samar musu
abin hawa tace "gidan Hajiya Maryama
zamu fara zuwa gaskiya, in ba haka ba
wahala zamuyi ta sha, in dai sun ganki cewa
zasuyi ke suke son dauka" Safiya ta
tambaye ta "me yasa?" Hajiya Kyauta tace
"saboda kina da kyau. Shi ido yana son abu
mai kyau, kuma shi abu mai kyau in yana
guri yana disashe kyawun abubuwan da
suke zagaye dashi", Sai Safiya ta samu kanta da mamakin haka,
ita bata taba tunanin kanta a matsayin mai
kyau ba, ita ba zata iya ma fasalta kan ta ba,
ita ba ma zata iya tuna last time da ta kalli
kanta a madubi ba. Ta san dai Baba Hadiza
da Sauda da Khadijah suna da kyau. Sune
mafiya kyawun halitta da ta sani a
rayuwarta.
Daga nan suka tafi gidan Hajiya Maryaman
da aka jima ana gaya wa Safiya. Tun daga
bakin gate din gidan Safiya ta fahimci gidan
ya banbanta da daya gidan da suka baro.
Shi wancan babu kowa sai mai gadi shi
kadai, shi kuma wannan maza ne sun kai su
hudu a bakin gate din suna hira. Daga can
gefe ga wasu samari nan suna buga ball, a
can karshen katanga kuma ta hango wata
mata tana shanya kayan wanki. Wannan ya
tabbatar mata da abinda Hajiya Kyauta ta
fada cewa gidan mutane ne.
Yanayin gidan katon gida ne a tsakiya, sai
kanana a gefe da gefe, inda daga baya
Safiya take fahimtar gurin yan aiki ne maza
da mata. Suka gaisa da mutanen gurin
sannan suka shige ciki. A cikin Safiya ta
tsaya tana kallon haduwa da tsarin gurin,
kujerun falon kadai abin kallo ne haka fentin,
ga kuma sanyin ac da kamshin da ya ratsa
su suna shiga,
Yammata ta gani guda uku a falon a zaune suna kallo a tv, biyu akan kujera daya a
zaune a gabansu, a shekaru ba zasu fi
sa'annin ta ba amma a jiki sun kusa ninka ta
saboda hutu da yanayin cimar su da ta
banbanta. Yammatan suka tsaya suna kallon
su kamar yadda suma suke kallon su, daya
daga cikin su tace "lafiya? Daga ina? Kawai
zaku shigo wa mutane gida ku tsaya musu
aka kuna kallon su?"
Hajiya Kyauta tayi murmushi tace "Hajiyan
tana kusa? Munyi magana da ita tace min
tana gida" dayar ta kan kujerar tace "tana
nan, amma dan Allah kuje waje ku jira ta, in
ta sauko sai ayi muku magana". Suka juya a
jere suka fita kamar yadda suka shigo a jere.
Suka je kuma suka jeru a baranda. Sun jima
a haka sannan Hajiya Kyauta tace '"bara dai
in kira ta a waya in gaya mata nazo, ba zamu
yi ta zaman jiran tsammani ba" Jamila, daya
daga cikin yaran da suke tare tace "to wai
Hajiya su wadannan da suka koro mu waje
yayan ta ne?" Hajiya Kyauta ta girgiza kai
"sai dai yayan yan'uwa ko kanne, Allah bai
taba bata haihuwa ba".
Tayi ta kiran Hajiya bata same ta ba, har duk
suka kosa, sai ga matar da suka gani tana
shanya nan ta zagayo inda suke, suka gaisa
da Hajiya Kyauta sai tayi mata bayanin cewa
Hajiya suke son gani, matar ta shiga ciki sai
gata sun fito tare da yarinyar da suka gani a
zaune a kasa a ciki, matar ta fara yi mata fada "kina kallon mutane sunzo suna son
ganin Hajiya sai ki bar su anan a zaune? Ba
zaki shiga ciki ki duba musu ba? Kin fiso ki
biyewa su Sa'adatu kuyi ta yiwa mutane
rashin kunya ko? To wallahi kin san
15
5
1:15 AM
halin Hajiya ko ki shiga hankalin ki ki kama
kanki ko kuma ta sallame ki zuwa gidan
iyayen ki".
Yarinyar ta zumburi baki tana kunkuni ta
koma ciki. Safiya ta fahimci yarinyar yar aiki
ce. Bata jima ba ta sake dawowa tace "tace
tana zuwa" matar ta ce "to ko ke fa? Yanzu
ba ya fi ba? Amma wulakanta mutum ai
babu dadi" sai kuma ta koma ta kawowa su
Safiya ruwa, suka karba suka yi godiya,
dama duk kishi suke ji.
Matar ta cigaba da zama tare da su tana
taya su hira, sai a lokacin Safiya ta san
sunan sauran yammatan da suka taho tare
dan babu wata maganar kirki da ta hada su
a hanya. Suna nan zaune har Hajiyan ta
sauko. Tun daga inda suke zaune a waje
suka fahimci ta sauko saboda maganar ta da
suka jiyo.
"Waye ya bar remote akan kujera? Sai am
zauna akan sa an balla shi"
"Aka ce nayi baki, Ina bakin nawa suke?" "Aka ce nayi baki, Ina bakin nawa suke?"
"Me suke yi a waje a cikin ranar nan?"
Sai ga yarinyar dazu ta fito da sauri tace su
shiga. Hajiya Kyauta ta dakatar da su Safiya
tace su jira ta fara shiga suyi magana
tukunna. Ta shiga suka gaisa sosai da Hajiya
Maryama, "Hajiya ya kasuwa? Ya kuma fama
da jama'a" Hajiya Maryama tace "lafiya lau.
Ya taki kasuwar da naki jama'ar? Ina fatan
dai kin kawo min yarinya mai hankali, kinga
wannan Lawisan?" Ta fada tana nuna
yarinyar da ta shigo da Hajiya Kyauta "rashin
samun wata ne ya saka har yanzu nake
zaune da ita, bata jin magana kuma bata
girmama mutane, babu abinda ta sani sai
kula maza, duk mazan can na waje samarin
ta ne" yammatan da suke zaune akan kujera
suka yi dariya, ta juya tana kallon su tace
"ku tashi ku bani guri, ina magana kuna bin
bakina da kallo kuna haddace abinda nake
cewa" suka tashi sum sum suka shige ciki,
ita ma yarinyar da aka kira da Lawisa ta tashi
ta bisu.
Bayan sun ta shiga ciki ne Hajiya Kyauta
tace "na kawo miki yarinya Hajiya,
musamman saboda ke na taho da ita Abuja"
Hajiya Maryama ta gyara zama tace
"alhamdulillah. Tana da hankali kenan sosa"
Hajiya Kyauta tace "tana da hankali da
nutsuwa, amma ba wannan ne dalilin da yasa na kawo miki ita ba, na kawo ta nan ne
saboda ita marainiya ce ke kuma na san ke
uwar marayu ce. Bata da uwa bata da uba,
bata da danuwa shakiki ko daya, ba kuma ta
da dangin uwa ko daya, sannan dangin
ubanta basa kaunarta" sai ta bata labarin
abinda ta sani a daga rayuwar Safiya.
Hajiya Maryama tayi shiru tana tunani sai
tace "kira ta in ganta inyi magana da ita
tukunna" Hajiya Kyauta ta leka ta kira Safiya.
Safiya ta shigo kanta a kasa tana kallon
yadda kafafuwanta suke nutsewa a cikin
carpet din falon da ta kasa tantance da me
aka yi shi. Kamar da katifa kamar kuma da
gashin rago.
Ta durkusa daga nesa da su ta gaishe da
Hajiya, Hajiya tace mata "ya sunan ki?" Tace
"Safiya" Hajiya ta kalli ciwon da yake kafar
Safiya tace "ya akayi kika ji ciwo haka
Safiya?" Safiya ta dago kanta tana kallon ta
tace "kusa na taka guda biyu, lokacin da
nake kokarin tono yaruwata da katangar
dakin mu ta fada mata".
Duk hajiyoyin biyu suka bude baki, thinking
about the trauma, dan itama Hajiya Kyauta
bata san yadda mutuwar Sauda ta kasance
ba, Hajiya Maryama tace "ina yar'uwar taki
take to yanzu? An fito da ita?" Safiya tace
"ta mutu. An fito da gawarta daga karkashin kasa, sal aka sake mayar da ita aka binne a
kasan wata kasar a makabarta" suka sake
yin shiru baki daya, sai kuma Hajiya ta sake
tambaya "mamanki fa? Me ya faru da ita?"
Safiya tace "Baba Hadiza, Mota ce ta kade
ta, sanda take gudu zata cecemu ni da
Sauda daga hannun Dauda" suka sake yin
shiru, safiya ta kara cewa "Dauda din yayan
mu ne" ba tare da sun tambaye ta ba,
Sai Hajiya Maryama taji tana son jin cikakken
labarin Safiya, ta tambaye ta, ita kuma ta
bata labari tiryan tiryan a yadda rayuwar ta
ta kasance tun daga kan abinda ta sani na
labarin auren iyayen ta har zuwa rasuwar
Alhaji Haladu da kuma tragedies din da suka
biyo baya.
16
1:15 AM
Bata san tana kuka a labarin nata ba sai da
ta gama taga audience din nata suna share
hawaye sannan ta share nata ita ma. Ta
cigaba da magana "so nake in samu hanyar
da san zamu jari in fara sana'"a, shine naje
grin Hajiya Kyauta ita kuma tace min zata
kawo ni nan in yi aikatau sai in tara kudin da
zan yi jari dasu, Hajiya dan Allah ki dauke ni
aiki, zanyi miki aiki sosai kuma zan ringa
girmama mutane yadda ba zaki kore ni ba, in
na tara kudi sai in gina wa Baba Hadiza
masallaci in roki Allah ya gina mata gida a
aljanna da ladan masallacin". Hajiya ta sauko daga kan kujerar da take ta
durkusa a gaban Safiya tace "zan dauke ki
aiki kinji? Kuma ba zan kore ki ba ko da kinyi
laifi, in kinyi laifi zanyi miki fada in baki
tarbiyya kamar yadda uwa ya kamata ta
bawa yar ta tarbiyya. Kin zama yata daga
yau kinji? Ina fatan nima Allah zai gina min
katon gida a aljanna da ladan rikon da zanvi
miki"
Hajiya Kyauta ta share nata hawayen tace
"Amen Hajiya. Dama nasan zaki karbe ta.
Banyi tunanin kowa ba sai ke. Allah ya dubi
niyyar ki ya baki ikon sauke wannan babban
nauyin da kika dauka" Hajiya tace "Ameen.
Ke ma Allah ya baki ladan taimakon da kika
yi mata da zuciya daya. Da baki dauko ta ba
da yadda zuciyar ta ta bushe din nan
gudawar zata yi ko da kuwa an daura mata
auren ne, kuma kinga da ba'a san hannun
wanda zata fada ba".
Ta juya gurin Safiya tace "zan dauke ki aiki,
zan ke baki albashi kamar yadda bake bawa
sauran yan aikin gidan nan, zanyi hakan ne
saboda ki samu ki cika burin ki na gina wa
mahaifiyarki masallaci da gumin ki, amma ba
zan rike ki a matsayin yar aiki ba, zan rike ki
a matsayin yata, Kuma ina so ki saki jikin ki,
duk wata magana da kika san zaki iyayi da
Baba Hadiza ki zo kivi da ni, in wata shawara
kike nema ki zo gurina, duk wani abinda ya
shige miki duhu ki tambaye ni, duk wani abu da kike bukata ki tambaye ni. Kinji?" Safiya
ta gyada kai tana share hawayen ta, rabon
da ayi mata magana with motherly concern
irin haka tun Baba Hadiza tana da rai, hakan
yasa ta tuna irin yadda take missing
mahaifiyar tata.
Daga nan sai Hajiya ta dauki wayarta ta yi
kira, "Sa'adatu zo ina neman ki". Jimawa
kadan sai ga daya daga cikin yaran da aka
kora dazu ta fito daga ciki ta zauna a kusa
da Hajiya tace "Hajiya ganj" Hajiya tace
"ga
yar'uwa kun samu ke da A'isha, ta zama
kanwar u daga yau" Sa'adatu ta kalli Safiya
ta a yatsina fuska tace
"Hajiya yar'uwar mu
kuma? Ji nake sabuwar yar aikin da aka
kawo miki ce?" Hajiya tace "shi dan aiki ba
mutum bane ba kenan? Ba zai zama dan
uwa ba? So nake kuje ku samar mata kayan
sawan da suka yi muku kadan a cikin kayan
ku, da duk sauran kayan da kuka san zata
bukata kafin in fita in siyo mata. A dakin ku
zata zauna tare da ku saboda ina son ku
kula min da ita, duk abinda tayi ba dai-dai
ba ku gyara mata har ta gane ta saba da irin
rayuwar nan. Kin gane?"
Sa'adatu ta ce "eh" amma daga ganin
fuskarta kasan bata ji dadin maganar ba,
Hajiya ta kara sa da cewa "saura kuma kije
kiyi tayi mata wannan fadan naki da baya
karewa". Ta juya kan Safiya tace "wannan kanwata ce
uban mu daya sunan ta Sa'adatu, daga
yanzu ta zama yayarki. Zata ke kula dake
kamar yadda yaya zata kula da kanwarta. Sai
dai tana da fada" ta karashe maganar cikin
tsokanar Sa'adatu da har lokacin take zaune
fuskar ta a bace. Hajiya tace "ku je ki nuna
mata dakin ku.
Ta juya gurin Hajiya Kyauta tace "to sai
kuma a bani yar aikin"
Sa'adatu ta mike Safiya ta bi bayanta
hannunta rike da ledar da hotan su yake ciki,
wannan ledar ita kadai ce abinda Safiya ta
shiga da shi gidan Hajiya.
Wani dan corridor suka bi sannan suka yi
kwana, sai suka tarar da kofofin dakuna
guda biyu da kuma toilet a tsakiya. Sa'adatu
ta bude kofa daya ta shiga sai Safiya ta bita
amma sai ta tsaya a bakin kofa kanta a kasa.
Babu abinda bata so a rayuwar ta irin a
wulakanta ta, ta kuma lura kamar yammatan
suna da wulakanci. Kallon dai suke cigaba
da yi a dakin a tvn dakin. Daya yarinyar tana
zaune a kan gado, Lawisa tana zaune a
kasa,
6
3
1:15 AM
Sa'adatu ta zauna akan kujerar dakin tace
"Fati ga bakuwa nan inji Hajiya, tace zata
zauna anan a wajen mu. Kuma zata zama kanwar mu" wadda aka kira da Fati ta kalli
Safiya sannan tace "yar'uwar ku ce?"
Sa'adatu tace "ni dai ban san ta ba, ban san
a ina ta samo ta ba, tace kuma mu bata
kayan sawa da abubuwan bukata" Lawisa da
take zaune a kasa tace "yar aiki ce fa, na
ganta tare da wannan matar da tazo"
Sa'adatu tace "ina ruwan ki? Bana hanaki
muna magana kina saka mana baki ba?
Tashi ki fita?"
Lawisa ta taso saura kadan ta bangaje
Safiya sai ta bata guri ta wuce. Tana nan dai
a tsaye Sa'adatu ta bude wardrobe din dakin
ta fara debo kaya tana ajiyewa akan dago,
sai data bata kaya sunfi set goma, har da
mayafai da hijabs, sannan ta bude drawer ta
bata sabulun wanka, tooth brush da paste,
da kuma man shafawa da roll on da turare.
Ta tsaya tana kallon ta sai ta kalli Fati tace
"kuma fa kyakkyawa ce. Gyara kawai take
bukata" Fati ta kalle ta ta tabe baki tace
"fatan dai ba nan dakin zaki ajiye ta ba. Sai
dai ki kata can dayan dakin" Sa'adatu bata
ce komai ba ta saka hannu ta kwashi kayan
tace "debo sauran mu tafi" Safiya ta debi
sauran kayan suka fita suka shiga dayan
dakin. Ta lura kamar dakin ba'a amfani da
shi kamar wancan, amma kuma shima
exactly kamar wancan din yake, Sa'adatu ta
ajiye kayan akan dago tace "ga kaya nan na
baki, ki zuba a cikin wardrobe din nan ki ki zuba a cikin wardrobe din nan ki
ringa sakawa, ga kuma kayan gyaran jiki
suma na baki, kin iya amfani da su?" Safiya
bata ce komai ba sai Sa'adatu ta nuna mata
yadda zata yi amfani da komai, sannan ta
nuna mata yadda zata kunna kayan
electronics din dakin, sai kuma suka fita ta
nuna mata yadda zata yi amfani da toilet,
daga nan ta mayar da ita falo.
Sanda ta koma falo already Hajiya sun gama
maganganun du da Hajiya Kyauta, Safiya ta
fahimci Hajiya ta dauki Jamila aiki itama a
gidan, amma instead of cikin gida da aka
shiga da ita sai aka hada Jamila da Dije,
matar da suka gani a waje, ta tafi da ita
bangaren yan aiki mata.
Hajjya ta tambayi Safiya in ta samu duk
abinda take bukata, Safiya tace "ta bani
kaya masu yawa, Nagode sosai Allah ya kara
arziki" Hajiya tace "Ameen. Tana da kirki ai
da kyauta, sai fada fal cikinta" Sa'adatu ta
tura baki tana kunkuni.
Daga nan suka yi sallama da Kyauta da
sauran yaran, Kyauta tayi mata alkawarin
duk sanda ta shigo Abuja zata je zuwa tana
ganin ta, Ta tsaya tana kallon su har suka
fita daga gate sannan ta juya ta koma ciki, A
lokacin Safiya tana da shekaru goma sha
hudu a duniya, dai dai da shekarun Baba
Hadiza sanda aka aura mata Alhaji Haladu. A hankali Safiya ta fara adjusting to rayuwar
gidan duk da dai ba xata ce babu challenges
ba amma tana jin dadin changes din sosai.
Ita kadai take kwana a dakin da Sa'adatu ta
kai ta, and all the nights she misses her
mother and siblings, wishing suma rayuwa
ta basu irin wanna damar ta kwanciya a irin
wannan gadon da kwana cikin ac a
lafiyayyen dakin da baya zuba ballantana ya
fada a kansu. Kullum ita take fara tashi a
gidan, kafin kuma mutan gidan su tashi ta
gyara duk inda take da access to, tun daga
dakin da take kwana har falo har kitchen da
duk wani daki da ya ke bude ko da kuwa
babu kowa a ciki. So take ta nuna wa Hajiya
irin gwanintar ta dan Hajiyar ta san bata yi
kuskuren daukan ta aiki ba. Satin ta daya a
gidan Hajiya ta