SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   67 / 113

198K to 201K   out of 336.6K words

karshe. Na lura da yadda
yanayin fuskar safinan yake nuna tsananin
tashin hankali,

A karshe Mommy tace "to yanzu dai
maganar da nake miki zaman jiran
hukuncin da iyayenku maza zasu dauka
muke yi. Bamu san dai abinda zasu ce ba
amma abinda na tabbatar shine auren
Safiyya da Mukhtar ya kare" Safina ta yi sauri ta kalle ni and I smiled brightly at her. Ta dafe kirji cikin tsananin tashin hankali "innalillahi wa inna ilaihir
rajiun. Hasbinallahu wa niimal wakel"
Mommy tace "dole kiyi salati yar nan..
wannan abin tashin hankali ai ya kai inda
ya kai. Sai dai kawai muyi mata addu'a
Allah ya musanya mata da wanda ya fishi
alkhairi" Safina ba ta yi magana ba sai ni
nace "Amen Mommy. Nagode"

Mommy ta mike, bara inje in gano ko
baban ku ya tashi daga bacci in taimaka
masa...." Ta cigaba da magana tana tafiya,
tana fita na sake yiwa Safina murmushi
"Hi dear sister.... Kinga ikon Allah ko? Har
na kusa gamawa da dayan saura ke, ina
gamawa da shi zan dawo kan ki kamar
yadda nayi miki alkawari. I will not wait for
karma to catch you. I will come for your
head as soon as na gama da wancan
munafikin. Kuma ba zan yi miki da sauki ba Safina, ke
da kanki zaki ciro kan naki kiyi min serving
din sa on a tray, You will regret sanda kika
dora don ki a kan Muhammad".

Tayi shiru tana kallo na, fuskar ta da
idonta sunyi ja, ta bude baki amma ta
kasa magana, daga dukkan alamu duk
karerayin ta da mugayen maganganu ta sun kare, a karshe sai tace "he is my husband. And Daddy will never let you marry my husband and iyayen sa will
never let him marry kanwar matar sa.
Ballantana kuma someone with your
reputation".

Na mike tsaye ina kallon ta nace "har
yanzu ko shekara ba'a yi ba da fara
wannan dramar, and abubuwa da yawa
sun faru most of which a shekarun baya
nake kalla as impossible. Misali ke a
matsayin matar Muhammad. Hakan yana
nufin cewa God can change impossible to
become possible through the most
impossible way. Just wait and see, zaki
sha mamaki. Ban san yadda abubuwa
zasu kasance ba but na san cewa the
moment da mijin ki yaji labarin aure na ya
mutu he will run back to me as fast as his
legs can carry him. And the rest will be
history".

Da niyyar kwana Safina tazo gidan amma
bata iya kwanan ba, haka ta dauki mayafin
ta ta dauki motar Mommy ta tafi da ita.
Yanayin ta gabaki daya ya koma tamkar
wadda aka cewa Mommy ta mutu, ita
Mommy duk ta dauka labarin abinda ya
fari da nine yayi affecting dinta hakan
bata san ita Safina abinda ya faru da ni ko
a jikinta ba dan ko jajanta min bata yi ba, ita tsoron ta kawai shine zan kwace mata mijinta.

Ni kuma a lokacin ba zan ce Muhammad
baya gaba na ba, dan in nace bana son sa
nayi karya, amma na fadawa Safina
wadancan maganganun ne dan in bata
mata rai. Amma ni kaina na san akwai
obstacles da yawa a tsakanin mu.

Daga nan na cigaba da zaman jiran
hukuncin da za'a yanke, ko dan ance aski
in yazo gaban goshi yafi zafi? Sai naji
yanzu nafi damuwa akan duk dadewar da
nayi ina jiran bayyanar gaskiya. Mukhtar
da yake kunya bata ishe shi ba haka yayi
ta zabga min kira da messages a waya
akan wai yana son muyi magana, naki kula
shi sam, nayi blocking kiran sa na bar
messages din duk wanda ya turo sai inyi
screenshotting in ajiye ko zasu zamar min
evidence.

A haka har na kwana biyar a gida. Ranar
ne ina zaune a dakina ina aiki akan system
kawai naji an bude dakin an shigo sannan
an mayar da kofar an rufe, na san mutum
daya ne yake yi min hakan amma kuma
ranar na san bashi ba ne ba, na juyo da
sauri sai naga Mukhtar a tsaye ya jingina
da jikin kofar yana kallo na. Kallo daya
zakayi masa kasan cewa rayuwar sa
gabaki daya a upside down take.

Nayi sauri na saka hannu na a kasan gado
inda nayi ajjiyar sabuwar wuka ta
musamman saboda Mustapha, na juyo na
nuna shi da ita nace "fita, ko a fitar da
gawar ka" maimakon ya fita sai ya zame
ya zauna a wajen yace "kill me, idan
hakan shine abinda kike bukata" na
karaso na tsaya a gabansa fuskata cike da
tsanarsa hannu na rike da wukar nace
"zan kashe ka wallahi, in kashe banza a
banza kuma babu abinda za'a yi min".

Yace "zaki iya yin hakan. Ko kuma zaki iya
tsayawa ki saurare ni. Wata kila mu samar
da mafita a cikin maganar da zamuyi"
nace "bana bukatar wata mafita wadda ta
shafe ka. I already know what I want kuma
shine abinda zan samu. I want to see you
locked up in prison for as long as
possible" ya dago ido yana kallo na,
fuskarsa kamar ba ta Mukhtar din da na
sani ba. Yace "I don't care about going to
prison Safiyya. I care about more
important things than my freedom" nayi
shiru ban ce komai ba, trying to control
my heart da take zugani a kan in soka
masa wukar hannu na,

Ya cigaba "Umma ta fadi, tana asibiti
kwanan ta biyu bata san waye a kanta ba.
Abba yace babu shi babu ni har abada,
And you" Cikin tsawa nace "don't
talk about me. Kar inji sunana a cikin
bakin ka. I don't care me iyayen ka suke
ciki ko me suka yi maka. Ni ka damu da
halin da nawa iyayen suka shiga a sanadin
abinda kayi min? a damu da halin da na
shiga a saboda abinda kayi min? Ka cuce
ni Mukhtar! Ka cuce ni! Kayi min cuta ta
har abada. Allah ya isa! Allah ya isa! Allah
ya isa tsakani na da kai". Na fada ina kukan da har sai da wukar ya fadi daga hannu na. Ya kife fuskarsa akan
guiwar sa yana kuka shima, jikinsa har
rawa yake yi. Na zauna a kasa nima na
jingina da jikin gado ina jin wani tarin
tsanarsa tana kara yawa a zuciya ta. Gani
nake yi da ace Mustapha ne yayi min
wannan abun da ba zan tsane shi kamar
yadda na tsani Mukhtar a yanzu ba.

Ya dago fuskar sa yana kallo na yace "
want to confess a gaban iyayen mu su
yanke min hukuncin da zasu yanke min,
but before then I want to tell you why I did
it" nace "I don't want to know, I don't
care"

Yace "I know. But I want to tell you
anyway. I did it because I love you. Ban
taba son wani abu ba a duniya kamar
Manna nake con ki Safivva Tin kina taba son wani abu ba a duniya kamar
yadda nake son ki Safiyya. Tun kina
karama nake sonki. I tried duk yadda
zanyi inga kin so ni amma kika ki, babu
yadda banyi ba, ke ma kin san babu
yadda banyi ba. I even tried involving
iyayen mu amma Daddy ya goyi bayan ki.
Meanwhile you got some guy and you
kept rubbing him on my face. I wanted to
have you. I wanted you so bad...." Ya fada
miko hannunsa zuwa gare ni, na janye
jikina out of his reach nace "in ka sake ta
bani sai na cire hannun ka. You are
insane" ya ajiye hannun sa a gefe yace "I
thought in na same ki ta wannan hanyar
zan daina jin zafin soyayyar ki da take ci
na. I thought in nayi miki haka maybe zaki
rabu da wancan saurayin and might
consider me. I thought maybe in iyayen
mu suka fahimci abinda ya faru they
might consider aura min ke. I never
thought you will get pregnant. I never
thought anyone will notice. But believe
me Safiyya wallahi I regretted it tun a
lokacin, sharrin shaidan ne da sharrin
zuciya ta da na kasa controlling a akan ki.
Na kai ki gida and I watched you har kika
shiga gidan, thinking za'a yi miki fada ne
kawai for staying out late and shikenan",

Yayi shiru, maybe jira yake inyi magana,
jin bani da niyyar yi sai ya cigaba "I was
wrong. Maimakon abinda nayi ya rage min son ki da bukatar ki sai kara min ma da
yayi. I waited inji kin rabu da wancan
saurayin kinyi kokarin shiryawa da ni but
you didn't. I thought kin manta ma da
abinda ya faru and you have moved on,
sai kuma ga kira daga asibiti that you
went kina so zaki zubar da ciki, tun a
lokacin na san cewa nawa ne. And I
thought I hit the jackpot, nasan dole ki
rabu da wancan saurayin naki and
chances dina na auren ki ya karu. when
you chose to marry me kuma sai naji
kamar nafi kowa sa'a a duniya, I thought
chance ne Allah ya bani na rectifying
mistakes dina by taking care of you and
abinda zaki haifa. Allah kuma sai ya saka
min son sa shima a zuciya ta kamar yadda
ya saka min ya kuma kara min naki. Ban
san cewa tarkon kamani ne Allah ya dana
min ba".

Ya goge hawayen fuskarsa "I know all this
doesn't matter. It doesn't change
anything. Amma ina so ne kawai in gaya
miki cewa I love you and I never meant to
hurt you" idona yana rufe nace "and yet
you did" yace "yes, amma nayi nadama
tun a lokacin, you have no idea how it
haunted me" na bude ido ina kallon sa
nace "da kayi nadama da tun a lokacin
you will turn yourself in, zaka kawo kanka
gurin iyayen mu ko gurin hukuma ka nemi ayi maka hukunci. But you stood by and
watched me suffer, hoping to have me
again. No Mukhtar, ba ka yi nadama ba,
not yet. I trusted you but You are just a
selfish and entitled bastard with no single
atom of imani a cikin zuciyarka. Your
reason, duk a wadannan maganganun
naka is just cewa kana so na, and who
told you dan kace kana sona sai nima
lallai na so ka? And let me tell you, ka cire
kalmar so daga bakin ka. Kai baka sona,
baka sona ko kadan. Ni na san menene so
and it neither look nor sound like what
you just described"

Na gyara zamana nace "ina da wanda
nake so kuma yake so na. And what I did
sanda wanna musibar ta same ni shine
na rabu da shi duk kuwa da son da nake
yi masa, saboda na san cigaba da
kasancewa tare da shi zai shafa masa
bakin fentin da maybe har abada ba zai
¡ya goguwa ba. Babu abinda Daddy bai yi
min ba, amma naki ko da kuwa ambatar
sunan sa, duk kuwa da nasan maybe da
na ambaci sunan na sa da yanzu ina gidan
sa a matsayin matar sa.

But I couldn't hurt him that way, I can
never hurt him in any way because I love
him. Wannan shine love"

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya😥❤️‍🩹

Episode Forty Six: Decision Making


Na tashi na koma inda nake zaune kafin
ya shigo na zauna sannan nace "idan ka
gama maganar da zaka yi ka kuma gama
kukan zaka ¡ya fita" nayi kamar na cigaba
da aikin da nake yi a system.

Ya jima a gurin a zaune sai kuma ya mike
yace "I know you have recorded all that I
said, kamar yadda na san kinyi
screenshot na messages dina, but you
won't need them. Kamar yadda na gaya
miki I am going to confess, ba kya bukatar
wadansu shaidu tunda zan amsa laifina
da bakina. Amma abu daya ne ba zanyi ba Safiyya, abu daya ne ba zan iya yi ba. Ba
zan iya rabuwa da ke ba. You and my son
are mine".

Naji kamar ya soki zuciya ta na mike "your
what? Did you just say your son?" Ya
daga kafada "Allah ne kadai yasan dalilin
da ya sa yaron ya zo duniya but I am
greatful for him, maybe a saboda shi you
will learn to love me, maybe he is meant
to bring us back together"

Na nuna shi da hannu nace "don't you
ever call him your son again. Ba dan ka
bane ba, ba shi da hadi in whatever way
da kai. And I will never like you ballantana
love, da da nake maka kallon mutumin
kirki ma ban so ka ba Mukhtar ballantana
yanzu da na san the kind of monster that
you are? Get out of my room tun kafin in
tara maka mutanen gidan nan".

Ya bude kofa sannan ya sake juyo wa
yana kallo na. Na fahimci maganar yake
so ya cigaba sai na juya na shige toilet na
rufe kofa. Na zauna dirshan a cikin toilet
din na jingina da jikin bango, zuciya ta
tana yi min zafin ambatar Junior as son
da Mukhtar yayi. In da ace zan samu
yadda nake so Mukhtar will never lay his
eyes on Junior har karshen rayuwarsa.

Sai da na tabbatar ya tafi sannan na fito,
na sauka kasa muka ci abinci tare da
Mommy, na lura ba ta san Mukhtar yazo
ba dan da ta sani zata yi min maganar,
Mustapha yazo shima ya zuba abincin
yana ci suna magana da Mommy akan
wadansu abokan babansa an siyasa da
ya kaiwa takardun sa zasu sama masa
aiki. Sai da suka gama maganar su ta
tashi sannan yace min "can I kill him
now?" Na girgiza kaina "not yet. Saura
kadan" yayi ajiyar zuciya "I don't even
know why I am listening to you, you of all
people, after wulakancin da kika yi min a
gidan nan" na juya ina kallon sa nace 'I
thought you said you wanted to make it
up to me?" Ya mike tsaye ya saka hannu a
aljihu yace "yes, I want to do something
for you dan in gyara tsakanin mu and dan
in yi making up for my mistakes, but case
din that bastard is my case dan haka
babu ke a ciki. Kawai na baki time da shi
ne out of the goodness of my heart,
amma sai ya raina kansa wallahi, he tried
to frame me Allah ne ya kare ni. I will
return the favor to him, ni kuma in na haka
masa nawa ramin muguntar ba zan jira shi
ya fada ba ni zan je in hankada shi da
kaina".

Nayi murmushi bance komai ba sai ya
juya zai fita. Na mike tsaye na kira sunan
sa ya tsaya yana kallona, na je gabansa na
tsaya nace "in har da gaske kana son
gyara tsakanin mu then accept the job I
offered you. Let's work together and take
care of our parents" yace "so that ki
samu damar yi min gori with every
opportunity da kika samu?" Nace "in kace
haka ba kayi min adalci ba, when na taba
yi maka or anyone a gidan nan gori?" Ya
danyi shiru sannan yace "I will think about
it" nayi masa murmushi "that will be
good"

Mommy ta fito daga hanyar kitchen sai
kuma ta tsaya tana kallon mu, Mustapha
ya juya da sauri ya fita ni kuma na dawo
cikin falo, na lura da yadda farin ciki ya
cika fuskarta and I hoped 'she is not
thinking what I think she is thinking'

Sai da nayi sati daya a gida sannan uncle
Ahmad ya dawo. Ranar da yazo ina
kitchen naje zan dauko ruwa in sha naji
muryarsa ya shigo gidan, sai nayi zama na
a kitchen din naki fitowa har sai da Esther
ta shigo tace Mommy tazo tana nemana
wai in je inji Daddy, Na koma sama na
dauko hijab na saka sannan na tafi falon
Daddy, Ina shiga na gansu gabaki daya
kamar ranar nan, Umma ce kadai babu.
Na je in da na zauna ranar nan na sake zama nayi shiru, yau ma ban gaishe da kowa ba. Uncle Ahmad ya danyi gyaran murya sannan ya fara magana a hankali, na lura yayi loosing duk zafin kansa da takamar
sa. Yace "ban san abinda zan fara fada a
wannan zaman ba, kawai dai na san ni ne
ya kamata in fara magana a matsayi na na
baban ku gabaki daya. Musamman tunda
yaya bashi da lafiya. Amma abinda na sani
shine nayi nadama babba a rayuwata,
nadamar da nayi kuwa ita ce ta haihuwar
ka Mukhtar " ya fada yana nuna Mukhtar
"da nasan wanna ranar zata zo min da
ma shake ka tun kana jariri ka bar duniya
dan ubanka"

Ya karasa maganar cikin daga murya, na
kalli Mukhtar na ga yadda ya takure a
waje daya fuskarsa tana kallon kasa, and I
wondered me yasa yazo gurin. Mommy
tace "babu zancen yin dna test din
kenan? Har na fara binciken asibitin da
suka kware a wanna bangaren" Uncle
Ahmad ya juyo yana kallon ta yace "na
san farin ciki kike yi da wannan maganar,
wannan kuma ya kara tabbatar min da
who you really are. Wannan maganar ba
abin murna ba ce ba. Abinda ya kamata
mu zauna gabaki daya mu jajanta sannan
mu nemi mafita akai ce" Mommy tace "wancan satin da aka zauna ai baka jajanta ba. Kin yarda ma kayi. Ka fara kokarin kare dan ka. Kuma ni ba murna
nake yi ba amma bana jajantawa, na riga
na jajanta na kuma zubar da hawayena
tun a lokacin da aka zalunci yarinya,
yanzu kuma da lokacin karbar mata
hakkin ta yayi in banyi murna ba ma ai ba
zan jajanta ba" Yace "babu wanda yafi karfin kaddara ta saukar masa..... Mommy tace "Allah ya raba mu da
mummunar kaddara...””


Daddy yayi gyaran murya yace "yanzu
menene abinda kazo zaka ce Ahmad?
Kace a baka lokaci da yaro zaka tuhume
shi kaji gaskiyar magana da ga bakin sa.
Mun baka lokaci. Ka dawo. Fada mana
abinda ka jiyo daga bakin nasa" uncle
Ahmad yace "ni dai godiya daya da zan yi
wa Allah a cikin wanna maganar ita ce da
ya azurtani da wadansu yayan bayan
Mukhtar, ina kuma saka ran insha Allah
Allah ba zai hada min lalatattun yara irin
sa ba" ya juya yana kallon Daddy yace
"yaya, Mukhtar ya fada min da bakin sa
cewa ya aikata laifin da yarinyar nan ta ce
yayi. Mukhtar ne yay'" ya fadi maganar
kamar zai yi kuka,

Sai kuma yayi shiru yana kokarin daidaita
muryar sa sannan yace "farko na ce masa babu ni babu shi har abada, sannan kuma kunyar ka da kuma kunyar yarinyar nan ta hana ni zuwa in gaya muku abinda ya ce min din. Amma kuma yanzu sai naga
rashin zuwan nawa kamar kara wa laifina
girma zaiyi a gurin ka. Kai yaya na ne, duk
duniya bani da kamar ka".

Ya sake juyawa wajen Daddy "yaya, dan
Allah, kayi hakuri ya yafe min" Daddy bai
ce komai ba yana dai kallon sa amma
yanayin fuskar sa yana nuna tashin
hankali da rudanin da zuciyar sa take ciki.
Uncle Ahmad ya cigaba "yaya ka yafe min
dan Allah. Ba wai Mukhtar nake nema wa
yafiya a gurin ka ba dan nasan abinda yayi
abu ne da zai yi wahalar a yafe masa
lokaci daya, ni nake nema wa kaina yafiya
a gurin ka saboda na gaza gurin tarbiyyar
yaron nan. Amma Allah shine shaidata
kuma kuma zaku iya zamar min shaida ko
a lahira ne. Nayi iyakacin kokari na gurin
tarbiyyar yaron nan" yayi shiru yana
mayar da numfashi sannan ya cigaba "da
nace babu ni babu shi har abada, amma
kuma sai na ga hakan ba zai cire jini na
daga jikin sa ba, Idan har zai iya aikawa
wanna mummunan abun alhalin yana
tare da mu me zai hana shi aikata abin da
yafi wannan muni idan baya tare da mu?" "Gashi nan yaya na kawo maka shi. Kayi masa duk hukuncin da kake gain ya dace da shi".

Falon yayi shiru, sai zuwa can Mommy
tayi magana "chafi. Lallai duniya ta zama
abin toro. Wai dan uwanka shi zai vi
maka wannan cin mutuncin". Aka sake yin
shiru zuwa can sannan Daddy yace
"Mukhtar"' Mukhtar yayi shiru bai amsa
ba. Kamar wanda yake kokarin shigewa
cikin kujerar da yake zaune a gabanta.
Daddy ya sake cewa "Mukhtar kai ne

67 / 113