SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   44 / 113

129K to 132K   out of 336.6K words

suka
sakar mata kudi sosai. Ta kuma yi amfani
da damar wajan kyautatawa du wadanda
suka yi playing major roles a rayuwar ta,
kusan aikin tun daga farkon sa har
karshen sa da Alhaji Nasir da Hajiya
Maryama aka yi shi. Cikin shekara daya
aiki ya kammala, a gurin kananan
ma'aikata ta bawa mutanen ta dama sosai, a lokacin ta samu fada sosai a gurin
yan'uwan Adam dan ta dauke su sosai har
sai da Adam yayi mata magana yace sunyi
yawa, ta aika wa da Hajiya Kyauta slots ita
ma tace in tana da wadanda take so a
bawa aiki ta turo su ayi musu interview,
Hajiya Kyauta kuwa ta turo yayanta da
jikokin ta sosai kuma kowannen su aka
bashi inda ake ganin ya dace da
qualifications dinsa da kuma experience
din sa. She then send slots to makotansu,
wadanda suka taimakawa Baba Hadiza a
lokuta da dama sanda tana raye, bayan
rasuwar ta ma kuma they were kind to
them, suma suka aiko samari biyu a gidan
kuma Safiya ta basu aiki suma.

A lokacin ne ta sake yin baki.

Ranar tayi baccin safe ba ta tashi da wuri
ba, Adam kuma yana Kano suna shirye
shiryen bikin kaninsa Ahmad da aka kusa
yi. Ta tashi ta shirya tsaf da niyyar zuwa
gidan Hajiya gurin Sa'adatu, tana
saukowa daga stairs idanunta suka sauka
akan yaya Malam da Dauda a zaune a kan
kujerun ta na falo, Ta tsaya tana kallon su,
suma kuma motsinta ya saka suka juyo
suna kallon ta, sai suka mike a tare suna
washe mata baki, Dauda yace "ga antin
namu nan ta sauko, An sha bacci" yaya
Malam yace "ba dole tayi bacci ba,
wanna hidima haka". A dai-dai lokacin da daya daga cikin
ma'aikatan gidan ta shigo ta ajiye musu
drinks da fruit a cikin plate. Tana mikewa
Safiya ta kira sunan ta "Hassana, waye ya
shigo da wadannan cikin gidan nan?
Dawo kizo ki duke min lemo na ki mayar
da shi fridge ko kuma ki bawa almajirai a
waje" yadda tayi maganar cikin fada yasa
yarinyar ta rikice, dan basu saba jin
Hajiyar ta su ta daga murya ba. Ta dawo
hannu yana rawa zata dauka Dauda ya
mike "ke! Zan kwarfe ki anan gurin in kika
taba wallahi" ta ja da baya a tsorace tana
kallon Safiya.
Safiya ta nuna mata hanyar waje "kira min
mai gadi" har yarinyar tayi hanyar waje sai
kuma tace "barshi ma, zo kiyi tafiyarki", ta
tuna cewa ba wancan mai gadin bane ba,
su biyu ne masu gadin nasu kuma shifting
suke yi, so wanna bai san yaya Malam
ba, and the girl was greatful to go.

Ta tsaya at the foot of the stairs ta
rungume hannayen ta a kirjinta tana
kallon yadda suke rige rigen cin abinda
aka ajiye a gabansu, "Safiyan Baba
Hadiza kenan, Safiyan Baba, kai Allah dai
yaki kan Baba, Baba zai ji dadi idan da ace
zai ganki a yanzu, kinyi kyau abinki, Baba zai ji dadi idan da ace zai gan mu a yanzu
tare da ke, yayye sun kawo wa karamar
kanwarsu ziyara. Kai zumunci yayi",
Ta saka hannu a jakarta ta dauko wayarta
ta nemo number din dpo din police
station da take kusa da su. Wancan
zuwan da su yaya Malam sukayi a cikin
matakan da suka dauka ita da Adam
akwai reporting issues din to the police
station nearest to them cewa akwai
wadanda sue bibiyarta kuma suna tsoron
kar su cutar da ita, sai dpo din ya rubuta
case din kuma ya basu number din sa
akan cewa in suka sake zuwa ta kira shi
direct.
Ta danna kira ta saka a kunnen ta still
idonta yana kan su Dauda, yana dauka
tace "hello dpo" suka gaisa ta fara yi
masa bayanin ta yace ya gane ta ai. Sai
tace "the people I once lodge a complain
about are here again, they are threatening
my life and frightening my house staff.
Okay. Thank you. Ina jiran ku" and she
hing up and continued standing up and
staring at su yaya Malam.

Dauda yana kallon ta shima ya taba yaya
Malam yace "yaya me take cewa ne, kai
ka dan fini iya turancin" yaya Malam
shima yana kallon ta fuskarsa cike da takaici da mamaki yace "yan sanda ta kira
mana, tace su zo su kama mu wai munzo
zamu kashe ta" Dauda ace "kut...... To
ke idan kashe kin zamu yi ai da tuni kina
lahira wallahi. Shikenan ba zamu zo gidan
ki muyi zumunci da je ba sai ki ce zamu
kashe ki? Da tun kina jaririyar ku bamu
kashe ki ba sai yanzu?" Still bata ce komai
ba sai ma gyara tsayuwar ta da tayi ta
cigaba da kallon sa, yaya Malam yace "ko
magana fa bamu isa tavi mana ba. Bamu
isa tayi magana da mu ba. Lallai kudi
masu gidan rana. Ko ba zakiyi magana ba
na san ai kina jina tunda ke ba kurma ba
ce ba, mu yan uwanki ne uba daya ya
haife mu kuma munzo neman taimako
gurin ki. Safiya ko abincin da zamu ci
bamu da shi amma ke kina nan kina
rabawa mutanen gari wanda babu dangin
¡ya babu na baba manyan aiyuka, kina
zaune a wanna katon gidan, kalli irin
abincin da kike ci...'
" Ya fada yana nuna
[07/01, 10:42 pm] +234 906 816 1960: Dauda yana kallon ta shima ya taba yaya
Malam yace "yaya me take cewa ne, kai
ka dan fini iya turancin" yaya Malam
shima yana kallon ta fuskarsa cike da takaici da mamaki yace "yan sanda ta kira
mana, tace su zo su kama mu wai munzo
zamu kashe ta" Dauda ace "kut...... To
ke idan kashe kin zamu yi ai da tuni kina
lahira wallahi. Shikenan ba zamu zo gidan
ki muyi zumunci da je ba sai ki ce zamu
kashe ki? Da tun kina jaririyar ku bamu
kashe ki ba sai yanzu?" Still bata ce komai
ba sai ma gyara tsayuwar ta da tayi ta
cigaba da kallon sa, yaya Malam yace "ko
magana fa bamu isa tavi mana ba. Bamu
isa tayi magana da mu ba. Lallai kudi
masu gidan rana. Ko ba zakiyi magana ba
na san ai kina jina tunda ke ba kurma ba
ce ba, mu yan uwanki ne uba daya ya
haife mu kuma munzo neman taimako
gurin ki. Safiya ko abincin da zamu ci
bamu da shi amma ke kina nan kina
rabawa mutanen gari wanda babu dangin
¡ya babu na baba manyan aiyuka, kina
zaune a wanna katon gidan, kalli irin
abincin da kike ci...'
" Ya fada yana nuna
abinda aka kawo musu,
"amma mu hatsin
da zamu dama wa yaran mu kunu su sha
safiya gagararmu yake yi. Inna Gaje ta
rasu. Inna Sa'ade tana bukatar taimako
kuma kina da halin da zaki taimaka mata,
zaki iya kaita asibiti ayi mata kafar katako
ko ki siya mata keken guragu ko kuma ki
daukar mata mai kula da ita, duk zaki iya.
Mu kuma ki sama mana aikin yi Safiya. Ga
yayanki nan Dauda ko gidan da zai ajive iyalinsa ba shi da shi a yanzu sai gida
matar ta shi ta koma. Ki daure ki bashi ko
da aikin gadi ne. Ga su Haruna nan da
badamasi duk basu da wan takamaiman
aiki. Ga danki nan Salisu shima ya gagara
yin aure saboda rashin aikin yi. Ki taimaka
mana kamar yadda Allah ya taimake ki ya
mayar da ke yadda kike din nan".
Ko motsa bakinta bata yi ba ballantana
tace masa kala. Ya mike tsaye zuciya tana
cinsa yace "lallai yau kin tabbatar min da
abinda nake zargi a kanku, cewa ku shegu
ne ba yayan baban mu ba.
12
9
4
10:03 PM
Dan babu dan uwan da zai viwa dan
uwansa irin wannan wulakancin, jini ai ba
wasa bane ba" Dauda shima ya mike ya
doso ta "tunda tace kashe ta muka zo yi
gwara in kashe ta din ai shikenan kowa ya
huta" yaya Malam ya rike shi "kar ka taba
ta. Tarko ta dana mana so take mu taba
su taji dadin rufe mu. Kar ka jefa mu a
tarkon ta, Wanna yarinyar shaidaniya Ce"
Dauda ya kwace daga hannu sa ya karasa
gabanta suka tsaya suna kallon juna, ko
motsawa bata yi ba, sai kuma yayi
murmushi yace "an gaya mana ai, an fada
mana cewa ke juya ce ba kya haihuwa. Ki cigaba da tara mana dukiya kinji? Kina
mutuwa zamu zo mu kwashe tas. Allah ne
ya bamu", Ya juya ya saka kafa yayi ball da
drinks din da aka ajiye musu sannan ya
fita yaya Malam yana bin sa a baya.
Sai da suka fita sannan ta saki numfashin
da ta rike tun sanda Dauda ya kira ta da
juya, a take jikinta ya dauki kyarma har
saida ta kasa cigaba da tsaiwa ta zauna a
kasa tana ruke da kirjinta, zuciyar ta zafi
take yi mata. A haka police din da ta kira
suka karaso suka same ta, ba ta iya tayi
musu bayanin komai ba sai yarinyar ta
Hassana ce ta zo tana kwatanta musu
kamannin wadanda suka zo din da kuma
kayan jikin su, aka kira mai gadi shima
yayi bayani sai kuma ya kara da cewa
"sun gaya min su yanuwanta ne daga
garinsu suke shi yasa na barsu suka
shigo, kuma naga suna kama, kama irin ta
jini".

A ranar Adam yana jin labarin abinda ya
faru ya juyo daga Kano, yana zuws ya
zarce dakinta da sauri yaje ya rungume
ta, sai da taji dumin jikinsa sannan ta saka
kuka. Ya bar ta tayi kukan ta ta gama
sannan tace "sunce ni juya ce ba na
haihuwa, sun ce ina mutuwa zasu zo su
kwashe duk abinda na tara. And they will
do that idan na mutum" ya girgiza ta "and who told you zaki riga su mutuwa? Waye
ya san gawar fari? Kuma waye ya gaya
miki ba kya haihuwa?" Ta bude hannun ta
"to ina yayan suke? Gaya min suna ina?
Nuna min su" ya girgiza kai "'it has been
just four years. Babu wanda zai ce bama
haihuwa dan muni shekara hudu bamu
haihu ba. And if it will put your mind at
rest zamu iya zuwa orphanage muyi
adopting baby, baby sabuwar haihuwa
yadda babu wanda zai ce bamu muka
haife shi ba. Wannan zai dakatar da su
daga irin wadannan threats din". Ta sake
girgiza kai. "We can fool them. Amma
Allah yasan ba namu bane ba kuma ba shi
da gadon mu" yace "Okay then. We can
start fertility treatment in kina so, duk da
dai ni nasan lokaci ne bai vi ba. Ga Sufyan
nan da matarsa Hajjo sun riga mu aure
amma basu haihu ba suma har yanzu.
Akwai couples da na sani da suka yi
shekaru ashirin basu haihu ba daga baya
kuma suka haihu. We should just be
patient Safiya, muyi ta gayawa Allah zai
dube mu ya share mana hawayen mu".

Wannan maganar ta kara kusanci mai
karfi tsakanin Hajjo da Safiya, they
understood each other irin tunda suna
cikin the same situation, a hankali har
suka koma kawance, daga baya kuma
suka koma aminci yadda kowa ta san komai na kowa. They support each other
through ups and downs.

Exactly a year later matar Ahmad kanin
Adam ta haihu, wata goma bayan bikin su,
ta haifi dan ta namiji aka saka masa suna
Mukhtar. A shekarar ne kuma finally
Sa'adatu ta gama ruwan idonta ta zabi
miji, kamar yadda ta jima tana mafarki,
babban mutum ta zaba, wani dan majalisa
acan garin su Katsina amma anan Abuja
ya sama mata gida zata zauna a matsayin
ta na amarya, matar sa kuma ta farko tana
Katsina. Aka yi bikinta, Safiya tayi mata
zumunci sosai ta tare a gidan mijinta.
Daga nan suka cigaba da zumuncin su.

A shekarar ne kuma ta sake yin baki daga
Kura. Wannan karon ba maza bane ba
mata ne. Lami da Lantana. Ranar ta dawo
daga unguwa mai gadi ya gaya mata tayi
baki mata, bata yi tunanin komai ba
saboda akwai wadanda take expecting
kuma dama ta gaya wa security din gidan
cewa wasu mata zasu zo neman ta, wani
program ne take leading a lokacin na wani
ngo da zasuyi training mata a bangaren
catering,
19
3
10:03 PM
Sai dai tana shiga sai ta tarar ba matan da
take tunani bane ba. Lami ne da Lantana
da kuma mata duburwar yarinya da take Safiya ta gane ta saboda ta sha wahala a
gurin rainon ta sanda tana baby. Ta tsaya
kawai tana kallon su a zazzaune akan
kujerun ta. Lantana tana yiwa yarinyar
magana a hankali can kasa yadda ba dan
falon yayi shiru ba da Safiya ba zata iya ji
ba "kin dai gane duk abinda muka gaya
miki ko? Mu mun san abinda zamu ce
mata yanzu ta karbe ki, in dai har muka
samu ta yarda kika zauna a gidan
shikenan mun samu abinda muke bukata"
Sai kuma Lami tace "wai ni a ina kike
ganin yarinyar nan ta samu wannan uban
kudin ne?" Lantana tace "kin manta an
tabbatar mana da cewa Hajiya Kyauta ce
ta fitar da ita daga gari? Kin manta kuma
safarar yammata dama take yi? Ai kasar
waje take kai su suyi karuwanci su samu
kudi, an ce fa a wajen har karnuka ake
hada su da su sai kuma a basu miliyoyin
kudi"

Cikin bacin rai Safiya ta kwala kiran mai
gadi, ranar duk masu gadi biyun ne a
gidan, suka taho a guje cikin tashin
hankali, ta nuna su Lami "waye ya shigo
min da wadannan mutanen cikin gida
na?" Daya yace "Hajiya bakin ki ne da kika
ce zasu zo, su suka ce mana su bakin ki
ne" tace "wadannan fa sune bakin da na
ce kar a sake bari su zo min gida,
wadanda nace in sun dawo a harbe su"
mai gadin ya bude baki cikin mamaki "Hajiya wallahi bamu gane su ba. Gidan
nan mutane suna shiga suna fita kullum,
ba zamu iya gane kowa ba" ta dauko
wayarta daga cikin jaka ta juya gurin su
Lantana tace "ku dan kalle ni kadan" suka
juya suna kallon ta sai ta dauke su a hoto,
ta juya gurin masu gadin tace "ga hoton
su nan zan tura muku, kuyi ta kallon hoton
har ku gane kamannin su, ko su ko masu
kama da su bana son gani a jikin gidan
nan ballantana cikin gidan nan. Idan kuma
kuskure irin haka ya sake faruwa zaku
rasa aikin ku"

Ta juya da sauri ta doshi stairs Lami ta
mike da sauri ta rike hannunta "haba
kanwata, wai me muka yi miki haka mai
zafi ne. Ubangiji yana son zumunci kuma
yana son masu sada shi, sannan kuma
baya son masu yanke shi. Mu kadai kike
dasu kaf duniya. Bana son yadda kike
zaune a garin nan baki da kowa naki a
tare da ke. Shi yasa muka kawo miki yarki
ta zauna a gurin ki dan mu gyara
zumuncin da yake tsakanin mu. Allah yaji
kan mahaifin mu",

Wani mugun kallon da Safiya take binta
da shi ya saka ita da kanta ta saki hannun
ta fara ja da baya tana girgiza kanta. Lami
tace "duk kiyayyar da kike yi mana ba zaki
taba cire jinin mu da ga jikin ki ba, ba zaki
taba cewa mu ba vanuwanki bane ba" Safiya ta juya tana kallon security dinta
"'ku je ku kunto karnukan nan daga cikin
kejin su ku hada su dasu su fitar da su in
ku ba zaku yi ba" ta kalle su tace "maybe
in suka hadu da karnukan zasu fahimci
wahalar da ake sha kafin ayi kudi" a take
suka fara rige rigen fita daga falon har
suna yin tuntube da juna. Sai dai har sun
kai bakin kofa Lami ta juyo tana kallon ta
tace "lokacin da zamu dawo yana nan
zuwa, ko bama raye zamu bar wa yayan
mu wasiyyar su zo su karbi gadon ki in
kika mutu. Kuma dole zaki mutu, dole
kowa zai mutu".

Shekaru biyu bayan auren Sa'adatu ta
haihu ta haifi namiji aka saka masa
Mustapha, a lokacin kuma matar Ahmad
ita ma ta kuma haihuwar namiji aka saka
masa sunan Adam. Sanda suka je barka
ita da Adam sai Ahmad ya kawo masa dan
"yaya nayi maka takwara, idan an yaye shi
ni da mamansa muni alkawarin bar muku
shi tunda babu yara a gurin ku" yayi shiru
yana kallon su sai kuma ya kara da "kafin
ku samu naku" suka sake yin shiru sai ya
sake cewa "in kuma Mukhtar kuke so sai
mu baku shi tun yanzu, tunda yayi wayo
already" Safiya tayi ajjiyar zuciya tace
"mun gode sosai Ahmad, Yaran ai duk
namu. Allah ya raya du yayi musu
albarka" Shekara daya bayan nan Allah ya
albarkaci Sufyan da haihuwa shima ya
samu namiji, aka saka masa Abdul Hakim.
Haihuwar Abdul ta dan daga hope din su
Safiyya, sai kuma a lokacin ta yarda suka
fara fertility treatment.
15
8
10:03 PM
Ita duk tsahon lokacin nan tashin hankalin
ta shine kar taje asibiti ayi mata
confirming cewa ba zata taba haihuwa ba,
without knowing she was holding on to
hope cewa zata haihu watarana.

Shekaru suka cigaba da tafiya, har Safiya
da Adam suka shekara goma da aure,
babu ciki babu labarin sa, sai war dukiya
da take ta ninka kanta both a side din
adam dana Safiyya. Ita kanta kudin da
take dashi toro yake bata in ta zauna
tana lissafin sa, a anniversary dinsu na
shekara goma da aure ne suka bude their
first personally owned textile factory, two
years after that suka bude na takalma da
jakankuna and that was in addition to all
the other companies da suke da manyan
hannayen jari a ciki, one of the major one
of which is the gold company wanda har
yau Safiya ba ta taba taba share dinta ta
ciki ba, it just kept growing, Safiya tayi charity da yawa a tsahon
rayuwar ta, most of which tana yi ne da
sunan mahaifiyarta, wasu kuma tana yi da
niyyar neman haihuwa. And deeply in her
tana jin wani assurance na cewa adduoin
ta ba zasu tafi a banza ba, that she will
one day get a child.

Five years haihuwar Mustapha Sa'adatu
ta sake haihuwa ta haifi mace ta saka
mata Safina. Safiya ce ta kaita asibitin
haihuwar kuma a hannunta aka haifi
Safina. Sa'adatu tana labour tana yiwa
Safiya addu'ar samun haihuwa har Safiya
tana tsokanar ta cewa bata in ciwon
haihuwar shi yasa. Ranar suna aka saka
wa yarinyar Safina, Sa'adatu tace wa
Safiya "sunan ki fa na saka a wayan ce,
bana son saka mata Safiya Hajiya ta saka
ni a gaba tace dan kudin ki na saka mata
sunan ki, kin san Hajiya gani take kamar
nafi kowa son kudi a duniya" Safiya tayi
dariya tana kara rungume yarinyar "Safina
is my daughter, ko taci suna na ko bata ci
ba".

Sam yan'uwan Safiya basu barta ba, an
sha gaya mata cewa an ga Dauda ko wani
daga cikin su around unguwar su, sai da
suka kai pictures dinsu duk gurin yan
sandan da suke kusa da su sannan suka
kara security din gidan. Gidan ya koma
duk wamda zai shiga sai any waya cikin Sam yan'uwan Safiya basu barta ba, an
sha gaya mata cewa an ga Dauda ko wani
daga cikin su around unguwar su, sai da
suka kai pictures dinsu duk gurin yan
sandan da suke kusa da su sannan suka
kara security din gidan. Gidan ya koma
duk wamda zai shiga sai any waya cikin

And then two years later all of a sudden
Safiya became pregnant. Ranar da taje
asibiti suka yi confirming pregnancy dinta
wuni tayi tana kukan jin dadi, da daddare
kuma kasa rufe idonta tayi dan gani take
kamar tana rufe idon zata farka ta ga
cewa ashe mafarki take, sai ta raya daren
wajan godiya ga Allah a bisa wannan
kyautar bazata da yayi mata. Mutane sun
kasa gane tsakanin Adam da Safiya waye
yafi murna da cikin nan, waye kuma yafi
son cikin, su kan su basu sani ba.

In celebration of samun cikinta ta shirya
bikin bude sabon gidan gonar ta data
sanya wa suna "The Oasis",. Gidan gona
ne da yake da bangarori daban daban,
akwai bangaren kiwon kaji layers akwai na
broilers, akwai gurin kiwon raguna akwai
kuma na kifi, sannan ga side din exotic
animals wadanda aka saka su dan su
kawara gurin kuma su zama ababen debe
kewa. Sai kuma aka yi shuke shuke shuke na
different varieties of fruits.

44 / 113