SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   66 / 113

195K to 198K   out of 336.6K words

idan aikin ba'ayi nasara ba sai
mu kira gidan ku su dauki gawar ki, Ko ba
kwa so su yi miki sallah su binne ki?"' Nayi
shiru ina tunani sannan bayi deciding ina
so su binne ni.

Amma kuma sai na rasa number din wa
zan saka. Definitely not Daddy. Mommy kuma munafuka ce as far as I was concerned. Ni kuma bani da wani wa da zan ce a kira. Sai kawai na saka number
din Mukhtar.

Da kaina naje na kwanta akan gado
sannan na rufe idona lokacin da naga ta
dauko allura zata yi min. A raina ina
lissafin ko dai in farka a duniya ko a lahira.
Amma in a duniya din ne na san zan farka
ne ba tare da wanna mayataccen cikin
ba.

Sai dai ga mamaki na sanda na farka din,
ina duniyar, kuma cikin still yana tare da
ni, bayan shi kuma akwai iyaye na. Naji
wani rage ya kama ni, wannan likitan ta
yaudare ni. Naji muryar ta tana magana
"this girl is severely depressed. She is
suicidal. She is going to kill herself"
Mommy tace "ki daina fadar haka dan
Allah" likitan tace "but it is true. Idan ba
dan nayi mata wayo ba zata cigaba da
neman wanda zai cire mata ne har ta
samu, za kuma ta iya rasa ranta. Babu irin
tsoron da ban bata ba amma bace ita
bata damu ko ta mutu ko tayi rai ba. Dole
ku chanja approach din ku a kanta or else
you are going to lose her".

Na bude ido na, wanda na fara gani a
kusa da gado na shine Mukhtar. Sai
Daddy da Mommy da uncle Ahmad a can gefe tare da dr din. Naji wani irin bakin ciki, shikenan Mukhtar yasan abinda ya faru dani. Wannan wanne irin abin kunya ne.

Nayi sauri na mayar da ido na na rufe.
Bayan an ima kadan naii uncle Ahmad
yana fada "wannan yarinya ta jawo mana
abin kunya da bamu taba gani ba a dangi.
Yaya aure ya kamata ayi mata. Tana
haihuwa ayi mata aure. Ga Mukhtar nan,
dama ya jima yana son ta kai da ita ne
kuka ki amincewa. Tana haihuwa sai a
daura musu aure kawai"

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹


Episode Forty Five: Love



Na juya baya na na fara kuka feeling
totally betrayed. Ina jin Mukhtar yana yi
min magana amma ban ma fahimci me
yake cewa ba. I felt betrayed by everyone,
Mommy da ta boye kin cewa ciki na bai
zube ba, Dr Salma da ta yaudare ni tace
zata zubar min da cikin, Mukhtar da na
saka number dinsa kuma ya kira iyaye na.
Naji tamkar kowa da kowa na duniya ya
tsane ni nima kuma naji na tsani kowa,
Especially kaina.

Uncle Ahmad ya cigaba da fada, ta inda
yake shiga ba ta nan yake fita ba. Blaming
Daddy da Mommy wai su duka bata ni
bana jin maganar kowa babu wanda ya isa
ya juya ni yanzu ga abinda na zama.

Har sai da Daddy ya cire alkunya yayi
masa magana yace ya rabu dani,
musamman saboda abinda Dr tace dan
haka fada ba zai yi maganin komai ba sai
dai a lallaba ni. Sai uncle Ahmad yayi fushi
ya fice daga dakin, Ina jin Mukhtar yana
cigaba da yi min magana, making me promises na cewa babu abinda ya ragu a zuciyarsa na son da yake min kuma kamar yadda baban sa already ya fada shi ma ya yarda zai aure ni duk kuwa da abinda nayi.

Ganin bani da niyyar kula shi sai ya tashi
ya fita.

Daga baya Dr Salma ta dawo ta zauna
dani ta yi ta kokarin inyi mata magana
amma na ki kulata, haushin ta nake ji ba
kadan ba. Ashe wai she is a psychotherapist as well as a gynecologist dan haka Daddy ya bude min file a gurin ta wai zan ke zuwa duk sati ina ganin ta.
Daga nan aka sallame ni bayan uta ma ta
bani wasu magungunan. Muna komawa
gida na kwanta a falo na rufe idona
pretending kamar bacci nake yi sai naji
Daddy da Mommy suna rigima, Daddy
yana ta fada sosai muryar sa har makale wa ta ke

"How can you do this! Ta yaya kin san
cikin nan bai fita ba amma zaki ja bakin ki
kiyi shiru? Menene hujjar ki ta yin hakan?"
Tace "kana ganin da ta san da cikin da
zata barshi?" Yace "nima da nasan da shi
da ba zan barshi ba ballantana ita, Ke
yanzu da kika barshi me zai yi miki?" Tace
"I don't care about cikin, but I do care
about her. Ni na san halin da na tarar da ita a ciki a wancan karon da tayi kokarin
zubar da shi kuma in no way zan kuma
barinta ta saka kanta a wanna halin.
Likita ta gaya min cewa those pills are
effective kuma Safiyya overdose din su
tayi ma. Still kuma cikin bai fita ba. In dai
har ta sake sha zata iya rasa ranta
maimakon ta rasa cikin. In dai ta kashe
kanta ta mutu kafura fa kenan, ba gwara
ta haihu mu san yadda zamuyi da dan ba
sannan kuma sai a guji gaba, ayi mata
aure. Shi yasa na nuna mata cewa ya fita
dan ta hakura har zuwa sanda cikin zai
girma yadda dole ta hakura da zubar da
shi. Ba a kanta aka fara ba ai. Ni dai ta
bangare na nobody will know. Haka ta
bangaren yaya na. Amma yanzu da su
Ahmad suka shigo cikin maganar i am not
so sure akan rufuwar asirin"

Daddy yace "but you could have told me.
Tare dani da ke ya kamata mu zauna muyi
wannan shawarar. I should have had a say
in what goes on with my daughter's life.
Idan da kin gaya min abinda likitan tace a
lokacin I would have take her to duk kasar
da nasan suna da likitocin da zasu cure
mata cikin successfully, Ko a Nigerian nan
ma ba za'a rasa likitan da zai cire cikin
few weeks ba tare da complications ba.
Kuma kin san da haka. Amma kika bar
marainiyar Allah da ciki a jikinta har ya kai
lokacin da cire shi ya riga ya zama haramun. Wato kin bar mu da choice din ko dai mu aikata sabo wajen cire cikin ko kuma mu barta ta haifi shege and then we
will have no choice then to get her
married and cover up abinda ya faru,
shine target din ki ko?"

Mommy ta hau "how can you say that?
Kana ganin zan cutar da Safiyya dan ta
auri Mustapha? Abinda kake nufi kenan? I
made the decision for you dan nasan duk
abinda ya shafi Safiyya idonka rufe wa
yake yi ba ka ganin gaskiya, duk laifin da
tayi you will cover it up and find someone
to blame for it. Yanxu ma kuma abinda
kake yi kenan. Kana so ka juya laifi zuwa
kaina ba yan kasan laifin ka ne. Ka riga ka
bata yarinyar nan iyakacin bata wa. Yanzu
kuma da lokacin karbar sakamako yayi
you are looking for someone to blame". Daga lokacin rayuwa ta kara chanja min, duk da uzurin da Mommy ta bayar amma ban kuma jin cewa na yarda da ita ba,
abinda na saka a raina shine ta vi ne
saboda a matsa min lallai in auri
Mustapha, Wannan kuma sai ya kara min
zargin cewa Mustapha ne uban ciki na, za
kuma ta iya yiyuwa cewa Mommy ta san
da haka, sun hada baki ne dan su ci kudina.

Daddy a bangaren sa ya rage yi min
hayaniya sosai. Amma kuma ni kaina bana
jin dadin zama a gabansa dan wannan
bond din da yake tsakanin mu sam babu
shi, bana o son kallon idonsa dan
disappointment kawai nake gani a cikin
su. Yayi kokarin nuna min ba komai, har
sabuwar wayar da ake yayi a lokacin ya
siyo min wai inyi keeping in touch with my
friends tunda ba ma tare, amma ni na san
yayi hakan ne kawai dan yana gudun zan
sake kokarin halaka kai na.

Idan nace I was depressed a lokacin sai
inga kamar na rage wa abinda naji girma.
Babu anar da ba zanyi wa kaina addu'ar
mutuwa ba. Abu daya ne ya hanani
loosing hankali na completely shine sallah
da na rike na koma ga Allah. Kullum ina
dakina akan sallaya, anan nake kuka na
anan nake baccina anan nake wuni. Sai
dai Mommy ta shiga ta loda min uban
magunguna in shanye ta bani abinci in ci,
Safina ma tana shigowa, amma sau da
yawa in ta shiga gurina ko kallo bata ishe
ni ba ballantana har muyi magana dan
haushin mahaifiyarta da dan uwanta ya
shafe ta ita ma. Twins suna boarding suna
kokarin rubuta jarabawar kammala
secondary school dan haka bani da tabbas din sun san halin da nake ciki ko basu sani ba.

Ciki na kuma tun daga sanda na fahimci
yana nan shikenan sai ya cigaba da
girman sa kamar wanda ake hura shi
kullum, tun riga tana boye shi har ya fara
fitowa a cikin rigar ma sai dai in na saka
babba ko kuma na saka babban hijab.

A haka Daddy ya yanke wata shawara ya
kira ni ya gaya min "akwai asibitin da aka
yi min maganar sa a Berlin, likitocin su
sun kware akan kula da masu ALS, zan je
can, zan kuma tafi da ke ki zauna tare da
Sufyan da matarsa har sai kin haihu. She
is a good woman and a good friend of
your mother's. Na san ba zata tona
asirinki ba. Kafin nan kuma dole ki gaya
min uban dan saboda in kai masa
kayansa. And you, kina haihuwa zanyi miki
aure dan ba zaki kara min wani abun
kunyar ba. Besides, my time is running
out and I want to see you settled before I
go"

Na fara kuka amma bai chanja shawarar
sa ba sai ma yace in tashi in bashi guri, na
shiga daki na cigaba da kuka na and I
knew it was time to let Muhammad go....
Dole in hakura da shi. Tunda na san ba
zan aure shi ba. Na san Daddy zaiyi
kokarin aura min wanda in aka tashi auren ba za'a vi bincike ba ballantana a gano
abin kunyar da nayi. Sai dai kuma na rasa
yadda zan yi in rabu da shi din. Me zance
masa? Dole in gaya masa wani abu da zai
saka ya hakura da ni dan idan nayi
ghosting dinsa just like that ba zai hakura
ba zai cigaba da nema na ne har sai ya
same ni, kuma ina tsoron garin neman
nawa kar ya binciko abinda nayi.

Kafin tafiyar mu tafi sai na yanke shawara.
It wasn't the best shawara nima na sani
but I wasn't on my right senses sanda na
yanke ta. Ni da mahaukaciya banbancin
mu kadan ne. Amma kuma a raina ina son
in sake ganin sa, ko da sau daya ne.

A lokacin tafiyar mu ne naci sa'a jirgin mu
ta Abuja zai tashi, Daddy yaso sai ranar
tafiyar mu zamu je Abuja amma sai nace
"Daddy muje mu kwana mana, tunda ba
ka da lafiya ka samu ka dan huta ba wai
muna sauka kuma mu shiga jirgi mu tafi
ba" It has been long rabonda na saka baki
in ana magana, maybe shi yasa Daddy ya
bi shawarata to encourage me to talk
more, Ni kuma plan dina shine in samu
damar zuwa ganin Muhammad, Ina ganin
ya yarda na tura wa Muhammad sako
cewa na shigo Nigeria, mu hadu a office
din sa, akwai magana mai muhimmanci da
zamu y" Muna zuwa Abuja kuwa bayan
an shigar da kayan mu na shiga daki kamar zan kwanta in huta ne sai na dauki key din mota na faki ido na fice.

**. *. *. *. ***.

Present days…..

And now, all the possible tablets have
turned in all the impossible directions Mommy ta bude kofa ta shigo dakin. Ta
tsaya a bakin kofa tana kallo na, sai kuma
tayi ajjiyar zuciya "zaman cikin duhun dai
yana nan" sai ta kunna fitilar dakin sannan
ta karasa shigowa. Ta tsaya tana kallona
sai kuma ta zauna a kusa dani. "Safiyya?"
Ta tafa da karyayyiyar murya, sai na dora
kaina a kafadar ta tare da sakin kuka. Ta
juyo ta rungume ni sosai "Safiyya. Kiyi
hakuri. Ya isa kukan haka nan. You have
cried enough. Ya isa haka" ta fada cikin
sigar lallashi. Na daga kaina ina cigaba da
sheshshekar kuka. Ta kama hannuna "kiyi
hakuri Safiyya. Ni ban san da wanne bakin
ma zan baki hakuri ba, Daddyn ki ma
haka, Kiyi hakuri dan Allah ki yafe mana
rashin fahimtar ki da bamu yi ba, Wallahi
yanzu dukkan mu mun yarda, ba ma
bukatar ma da test din abinda muka ji da
kuma yanayin Mukhtar kadai ya gamsar
da mu. Mun yarda da ke. And it breaks my heart yanzu da na fahimci cewa you went through all that kuma you are innocent. Sannan kuma mu iyayen ki mun ki yarda
cewa you are innocent. Kiyi hakuri dan
Allah".

Na gyada kai na tare da share hawaye na
da hannu biyu. Sai kuma nace "ke ma kiyi
hakuri, I have been disrespectful to you a
lot of times" ta girgiza kai "babu komai. Ni
ban taba rike ki ba. Most of the times in
kinyi abu Daddyn ki nake hucewa a kan
sa" sai kuma tayi murmushi "yanzu kam
shima duk jikinsa yayi sanyi. Na san
kunyar hada ido zaiyi da ke. In kinje gurin
sa you should use kind words to ease
guilt feelings din sa" nace "to Mommy
sai kuma tace "su Ahmad sun tafi. Sunce
zasu bincike shi sosai. But sum jikin su
yayi sanyi. Uwarsa ko magana ba ta sake
yi ba har suka fita. Da kyar ma ta iya
mikewa da ga inda take zaune. I guess he
will confess sooner or later" muka vi shiru
gabakidaya sai kuma tace "kai! Allah ya
isa wallahi. Raina zafi yake yi. Ji nake
kamar in bisu in je gidan in zazzaga musu
masifa, Wannan wanne irin zalunci ne?"

Na dan yi murmushi nace "you don't need
to go to them, zasu dawo ne da
kafafuwan su suna begging for
forgiveness and then you can talk to them in all manners da kike bukata".

Sai washegari sannan a koma gurin
Daddy da safe na gaishe shi kamar yadda
nake gaishe shi duk safiya. Ya amsa
sannan yayi shiru, nima nayi shiru kaina a
kasa sai da muka jima a haka sannan na
mike da niyyar bashi guri tunda naga
kamar baya son muyi maganar sai kuma
ya kira sunana, na dawo na zauna sai
yace "me yasa?" Na dago kai da mamaki
"Daddy me yasa me?" Yace "me yasa kika
zabi auren Mukhtar bayan kuma kina
zarginsa da wannan mugun abun? Me
yasa tunda kika fara zargin sa baki zo kin
same ni kin gaya min ba? Ko dan kina
ganin I dismissed you sanda kika ce min
kina zargin Mustapha? Haka ne? Idan da
Mukhtar kika ce I would have given it
more thoughts than Mustapha. Me yasa
baki fada min ba?"

Na sake sunkuyar da kaina nace "Daddy
nima ban fara zargin shine ba sai bayan
da muka dawo Nigeria, bayan da aka riga
aka daura auren, Tun lokacin ya fara nuna
min ya damu da abinda na haifa and I
found that suspicious, Daga baya kuma
saw some kind of resemblance tsakanin
sada…...da.... Junior, Shine nace masa ya
mutu, and he acted kamar uban da aka ce
masa dan sa ya mutu" Daddy ya sake girgiza kai "but still you should have come to me ai. Da sai in dakatar da bikin in kashe auren in kuma bincike shi. Bai
kamata ki saka kanki in danger ta hanyar
tarewa a gidan sa alhalin kina zargin sa da
wannan maganar ba. Zai iya yi miki komai
dan ya rufa asirin kansa, zai iya daukar
ranki ma. Akwai rapist da yawa da suke
kashe victims din su dan gudun kar su
tona musu asiri. Da kin gaya min sai mu
tuhume shi in yaso in yaki sai mu dauko
Junior ayi dna din, shikenan".

Nayi shiru ina wasa da yatsun hannu na,
ina jin kunyar Daddy sosai akan duk wata
magana da ta shafi Junior, amma wannan
magana ce da ya kamata muyi. Nace
"Daddy I did all that for Junior. I was
trying to avoid doing the DNA. Ina tsoron
dna test din will blow off Junior's cover,
Mukhtar zai san shi sauran yan'uwa zasu
san shi, mutane zasu gane cewa ba dan
Aunty Hajjo ba ne ba. I was trying to
protect him from people and from the
reality of his life. Na san zai sani watarana. Amma nati son in zai sani din ma sai ya zama strong
enough to accept it, yadda ko ma me
mutane zasu fada din ba zai affecting
ginin rayuwarsa ba".

Daddy yace "so you were trying to
protect him by putting your own life in
danger? By risking your life?" Na gyara
zamana ina kallon sa nace "Ammie
jumped to her death to protect me. She
went through a lot of things dan taga na
samu rayuwa mai kyau. Wannan shine
version na motherhood da na sani.
Wannan shine irin uwar da nake so in
zama".

And I saw him smile. It has been 20 years
amma babu yadda za'a yi a ambaci sunan
ta ba tare da zuciyar sa ta russuna ba.
Babu yadda za'a yi ayi labarin ta ba tare
da yayi murmushi ba.

He said "shikenan. Allah ya bada sa'a yayi
jagora. Allah kuma yayi miki albarka.
Ahmad ya roka cewa a basu lokaci da
Mukhtar, zamu jira shi muji abinda zai ce
da kuma abinda zaiyi. Idan kuma bai yi
abinda ya dace ba, mu zamu yi abinda ya
dace".

And then the waiting began ………. Muka fara
zaman jiran hukuncin da Uncle Ahmad zai
yanke,

Kwana na uku a gida ranar nan muna
zaune a falo da Mommy muna ta hirar twins and how they are coping with aikin su sai ga Safina ta shigo. Naji gabaki daya mood dina ya chanja. Har da gudun ta taje ta fada jikin Mommy tana murna.
Mommy ta ture ta tana dariya. "ke dalla
saukar min a jiki kar ki balla ni" Safina ta
fara shagwaba "haba Mommy, na rame
fa" Mommy ta kalle ta "kin rame tabbas
amma yanxu ai naga kin fara dawo da jikin
ki, kin murmure ba laifi. I guess your
inlaws are treating you right ko?" Safina
ya gyara zamanta sosai tana kallo na tace
"suna da kirki sosai. Mama is the best
mother in law in the whole world" Mommy
tace "uhumm. Sai shine bashi da kirki
kenan. Bai yi gadon halin kirki ba gaskiya"
Safina ta bata rai "kai Mommy, baya... "Baya gari ne fa
. " Mommy ta karasa tana kwaikwayon muryar ta. "Zancen kenan kullum baya gari. Ni ba zan ki fadar
gaskiya ba fa. Mijin ki bashi da kirki. Ko a
gaban sane ko a gaban iyayensa zan fada
ballantana a gaban ki. Bashi da kirki ko
kadan. Yanzu ji nake bikin Safiyya aka yi
ko waya baiyi mana yace Allah ya sanya
alkhairi ba ballantana ya kawo mana
gudummawa. A haka kuma kullum kice
wai aiki yayi masa yawa shi yasa baya
zama a kasar, To ya dauke ki ya tafi da ke
inda yake zuwa mana in da gaskiya ne……”

Ta cigaba da wanke Muhammad ni dai na
mayar da hankali na kan waya ta bance
musu komai ba.

Sai daga baya Safina ta mike ta ajiye
mayafin ta tare da cewa "Mommy me
kuke da shi abinci a gidan nan? Ina Esther
take? Ta zo ta jefa min danwake, shi nake
son ci da manja"

Mommy tace "ke zauna tukuna ba
maganar dan wake ake yi ba. Wai baki ga
Safiyya ba? Ko bata baki labarin abinda
yake faruwa ba? Ki zauna ki jajanta mata
mana" Safina ta koma ta zauna tana
kallona sannan tace "me ya faru?"
Mommy ta fara bata labari "zancen cikin
ta, ashe dai da na Mukhtar ne...." Ina jin
su ta bata labari tiryan tiryan tun daga
farko har

66 / 113