SAFIYYA BOOK COMPLETE MAMAN MAMA.txt

Author :  Maman Mama Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 113

54K to 57K   out of 336.6K words

abokansa da suka zo
gari musamman dan bikin hotel rooms duk
kuwa da cewa akwai wanna spare gidan
amma shi so yake ya zauna shi kadai. Haidar
din ma sai ya bude masa part din da ya
kamata ace shine nashi, shi kuma ya shiga
wanda ya shirya saboda Safiyya.
Ya san cewa hakan da yayi ba karamin
emotional damage zai jawo wa kansa ba
amma ya zabi hakan.
Babu komai na furnitures a gidan dan haka
sai katifu suka je dasu suka shimfida suke
kwana akai, sai kuma boxes din kayan sawan
da zasu yi amfani da su da sauran
abubuwan da zasu bukata. Kullum da safe
yake fita gurin hidimomin sa and they kept
his emotions on check har sai ya dawo gida
tukunna, shi farko ya dauka in ya gaji bacci
zaiyi saurin daukansa kamar yadda Ya
Amen ya gaya masa, amma kuma sai ya ga
shi ba hakan bane ba a gare shi. Ko ya gajin,
in ya kwanta sai dai yayi ta juyi, amma bacci
baya zuwa idanun sai gari ya kusa wayewa.
Kullum a ransa babu abinda yake yin bita sai
rayuwar sa da Safiyya, babu abinda yake so
irin ya fahimci abinda yayi missing, ya
fahimci inda hint din cewa tana da aure yake
wanda yayi missing a baya amma ya kasa
gani,
Except kin kai shi gidan su da tayi. She kept
on delaying and delaying giving all sorts of on delaying and delaying giving all sorts of
excuses. Farko excuses din nata akan cewa
tana gidan uncle dinta ne kuma uncle din zai
yi mata fada in ya ganta da saurayi because
yana tunanin cewa bata isa yin saurayin ba,
daga baya da ya fara nuna mata shi fa da
gaske aure yake son yi, aurenta yake son yi,
sai ta koma yi masa maganar rashin lafiyar
babanta and the fact that baya zama a kasar
sosai, and ranar nan da ya takura mata she
said bata son ta kaishi gurin uncle dinta sai
dai babanta, saboda uncle din yana son
hada ta aure da dan sa Mukhtar.
Ya san Mukhtar. Tun the second haduwar su
da Safiyya ya san Mukhtar, kuma tun a
lokacin jikinsa ya bashi cewa something was
going on at least a zuciyar shi Mukhtar din,
tun sanda ya ganshi din kuma yaji cewa
baya son sa. Amma kuma a zuciyarsa ya san
cewa kishi ne yake yi.
Ya san cewa kishi yana daga cikin
weaknesses din sa akan Safiyya, yana da
mugun kishin da har toro yake bawa kansa
sometimes, ya kuma san kishin nasa a
yanzu yana daga cikin abinda yake cin
zuciyarsa. The memory of her dauke da
cikin wani, knowing fully well abinda ya faru
kafin a samu cikin shine babban abinda yake
hana mishi bacci a yanzu.
A yau ma bai dawo da wuri ba sai late,
hopping to fall asleep as soon as possible,
yana shigowa ma da yay packing bai shiga
cikin gidan ba sai ya cire dogayen kayan. cikin gidan ba sai ya cire dogayen kayan
jikinsa ya bar singlet ya zagaya bayan gidan
yana jogging da niyyar karawa kansa gajiya.
A bayan ne kuma yaga wani guri da Safiyya
ta saka musamman ya ware mata bai yi
paving ba
"spices zan shuka a gurin, akwai spices din
da ba a samu sosai a kasuwa ko kuma ba
za'a samu fresh one ba, to gwara in samu
seeds din su in shuka da kaina in ringa
using".
Ya tsaya a gaban clearing din yana hakin
jogging din da yake yi. "damn you. Damn
you Safiyya" ya fada a fili, sannan ya wuce
da sauri ya cigaba da jogging din sa. Yana
cikin haka yani alamar an bude gate, ya san
Haidar ne ya dawo amma kuma baya son
kowa yayi masa magana a yanzu, dan haka
yayi sauri yayi kwana ya shige gidan ta kofar
baya ya shige dakin da yake kwana. Direct
toilet ya wuce ya kunna wa kansa shower ya
rufe idonsa yana jin dadin sanyin ruwan.
"'Komai zafi bana iya wanka da ruwan sanyi,
mura yake saka ni"
Yaji muryar ta kamar a yanzu take gaya
masa, Ya tuna da amsar da ya bata a
lokacin, "Kar ki damu, zan koya miki ne. Ita
kan ta murar sai ta hakura ta bar mu".
Ya fita daga shower din ya goge jikinsa,
yana kallon fuskarsa a mirror din toilet din, yana kallon fuskarsa a mirror din toilet din,
"Da wata farar fuskar ka anan" yayi
murmushi. "Burge ki tayi"
4
8:00 PM
Ya fito daga toilet din ya saka pajamas
sannan ya karo karfin AC ya kashe fitila yayi
addu'a ya kwanta, hoping to center his mind
on something important, anything apart
from Safiyya, amma babu abinda ya gani a
idonsa sai Safiyya da ciki a office din sa.
Babu kuma abinda yake son sani a lokacin
sai abinda Safiyya take yi a wannan lokacin,
babu abinda mind dinsa take saka masa sai
different scenarios a abinda Safiyya take yi
din. Ya mike tsaye ya kara wa kansa fanka
sannan ya koma ya kwantatare da zagaye
kansa da pillows, few minutes after that
kuma ya sake mikewa zaune ya jawo
wayarsa ya nemo number din Safina ya kira
without realizing cewa karfe sha biyu ne na
dare har da rabi.
Sai da ta dauka sannan yayi realizing
mistake din sa. "Hello Habibi. Ba ka yi bacci
ba?" Ya matsar da watar daga fuskarsa yace
"shit!" a hankali cikin jin haushin kansa.
Sannan yace "hello? Uhmm, I think I made a
mistake ba wannan number din zan kira ba"
ta danyi shiru sannan tace "wa za ka kira to?
By this time?" ya fara tunanin karyar da
zaiyi, another of his weakness shine karya,
bai iya karya ba kwata kwata. Yace "my
friend, akwai wani friend dina Sahabi shi zan kira yanzu" ta sake cewa "by this time?"
Yace "eh, baya bacci da wuri, nima haka"
tace "ko dai ita zaka kira?" Ya dan bata rai
"wa kenan?" Tace "your ex da ka fada min.
Ko ita zaka kira Allah ya sa ka kira ni" ya
danyi shiru sannan yace "I wish I can call
her, there is nothing da ba zan iya bayarwa
ba a yanzu to be able to call her. But she
blocked my number. And beg me not to find
another way to contact her. So to answer
your question, ki kwantar da hankalin ki, ba
ita zan kira ba".
Tace "okay. Because I don't want to ruin the
memory of the first time you call me da
dare. Ba na son sunan wata ya shiga cikin
memory din. It has always been a dream of
mine. In ga ina waya da kai irin yadda
yammata da samari suke y" yace "I told you
abokina...." Tace "right. At least let me
pretend ni ka kira. And since you called ya
kamata mu danyi magana ai ko? At least tell
me something about you da kake ganin ya
kamata in sani, maybe about your friends or
family ko aikin ka, anything, just talk to me "
yace "okay. Let me start with the things I
like, I like honesty, na tsani karya. I like tsafta
a lot. Bana son hayaniya, bana son mita,
bana son tsegumi ma'ana telling me
something that do not concern me. And
most importantly, I love my family, a lot"
tace "yauwa, about the family, ban san su
ba sam in banda Mufida, ita ma kuma a
waya ne kadai ko hoton ta ban taba gani ba,
ya kamata in san su ko?" Yace "zaki san su
ai. A hankali, But the immediate family basu. al. A hankali. But the immediate family basu
da yawa, daga Mama sai Abba sai Haidar
and then Mufida. I am the eldest. Akwai
cousins da yawa, I can't list them all. You will
get to know them watarana" tace "haka ne.
And your friends, aside Sahabi" yace "waye
Sahabi?" Tace "Sahabi dai da zaka kira
yanzu" yace "ohh that Sahabi, Sahabi my
friend. Yes, akwai Sahabi and the rest. Zaki
san su suma later. Now, let me call Sahabi
kafin yayi bacci".
Tayi ajjiyar zuciya "okay, shikenan. At least
we are one step ahead. Good night Habibi".
Sai dai daya ajiye wayar, maimakon ya koma
ya sake gwada baccin sai ya tashi ya zauna
ya dauko takarda da biro a cikin takardun da
Abba ya bashi zai yi cike cike na sabon aikin
da zai fara, ya juya bayan takardar kawai ya
kama zane a jiki, zanen fuskar Safiyya. Sai
da ya gama zana ta tas kamar zaka kira
sunan ta ta amsa, sai kuma ya dukunkune
takardar yayi jifa da ita ya koma ya kwanta.
Da safe bai tashi da wuri ba dan baiyi bacci
mai nauyi ba sai bayan sallar asuba, ya
manta cewa a ranar zasu fita da Abba
maganar chanjin aikin sa. He is going to take
over some parts of managerial work na
Company din Abba bayan bikin sa. Sai dai
bai tashi ba har sai da Abban yazo gidan da
kansa daukan sa kamar yadda suka shirya,
ya kuma shigo har cikin gidan har dakin da
yake kwance ya same shi yana bacci,
takardar da ya gani a kasa ya sunkuya ya. takardar da ya gani a kasa ya sunkuya ya
dauka ya warware. Sai ya samu guri a gefen
katifar da Gidado yake kai ya zauna yana
kallon zanen yarinyar da yake hannunsa.
8:00 PM
Gidado yayi juyi sannan ya bude jajayen
idonsa ya dora su akan Abba, sai kuma ya
karasa bude don da sauri tare da mikewa
zaune yana shafa fuskar sa a kokarin kore
saurin baccin da yake kansa "Abba ka
shigo? Ina kwana" Abba ya bishi da kallo
sannan ya sake kallon takardar hannun sa.
Sai lokacin Gidado ya lura da takardar, ya
kara gyara zamansa yana shafa kai tare da
kallon takardar da gefen ido.
Abba ya nuna masa zanen tare da tambayar
sa "Safiyya?" Gidado ya gyada kai bai ce
komai ba. Abba ya nannade takardar ya ajiye
a tsakanin su yace "ba ka son waccan
yarinyar, zaka aure ta ne kawai saboda ni da
mahaifiyar ka muna son kayi aure" babu
alamar tambaya a cikin maganar dan haka
Gidado bai bada amsa ba. Abba ya cigaba
da cewa "abu na farko da na san ka riga ka
sani shine we only want what's best for you.
And right now, mantawa da wannan yarinyar
shine the best thing for you" ya fada yana
nuna zanen Safiyya with bitterness in his
voice, abinda yake nun irin haushin Safiyya
da yake ji a ransa. Ya cigaba da magana,
"mun yanke shawarar aure shine babban
abinda zai taimaka maka wajen mantawa da
ita maka kayi moving forward. Sai dai daga
ni har mahaifivar ka are not perfect, kuma. ni har mahaifiyar ka are not perfect, kuma
bama ganin gaibu, zata iya yiwuwa abinda
muka zaba maka ba shine alkhairi a gare ka
ba, amma ni na san wanda yake perfect
wanda kuma ya san gaibu, Allah. Ina son zan
baka wani assignment, idan kayi shi dai dai
zaka samu reward mai girma. Ina so kuma
inyi maka wani alkawari. A cikin kwanakin
nan da suka rage kafin daurin auren ka, ina
so kayi istikhara, idan har kafin daurin auren
ka cigaba da jin a ranka cewa still ba ka son
aure to ka gaya min, ko da kwana daya ya
rage zan dakatar da abin domin ya tabbata
ba alkhairi bane ba. Amma idan kaji a ranka
cewa ka amince kana son auren yarinyar, to
sai mu cigaba da shirye shiryen mu har mu
tabbatar da faruwar abin".
Ya mike tsaye yana kallon sa yace "ka tashi
ka shirya, your new job awaits you ", Gidado ya karbi shawarar Abba sosai, dan
tun da suka yi maganar ya dukufa da yin
adduoin neman zabin Allah. Babu dare babu
rana. Ya kuma cigaba da shirye shiryen duk
da suka kamata na bikin. Yan'uwansa sunzo
na kusa da na nesa, maza da kuma mata. Da
yake Abba da Mama first cousins ne sai ya
zamana yan uwan duk daya ne babu
banbanci, duk kuma treatment daya ake
basu.
Yan'uwansa samari da suka zo gari suka
kuma fahimci a gidan da yaje ya boye kansa
duk sai suka tattaro suka dawo gidan,
sa'annin Gidado suna bangaren da yake
while sa'annin Haidar suma suka tare a
bangaren da yake. Gidado bai ji dadin haka
ba saboda an takura masa an hana shi zama
yayi hira shida zuciyarsa, shi da safiyyan shi.
Sai dai kuma a wani bangaren yaji dadin
hakan dan cikin kwanaki biyu kacal sai gashi
yana hira da dariya sosai a cikin su. Wani
lokacin idan suka nutse a cikin hira har
mantawa yake yi da cewa wai aurensa ake
yi, kuma wai baya son yarinyar da zai aura.
Sai dai kuma yana iyakacin kokarin sa gurin
danne wa dan baya son yanuwansa su
fahimta har suyi ta yayata maganar a cikin
dangi. Sai dai kuma yanuwan are making it
extra difficult for him. Casually someone
would ask him "ina yarinyar nan kuma da ka
susuce akan ta kwanan baya?" His answer
to that question was always "Allah yayi mata
rasuwa" daga haka ba sa sake tambayar sa.
In wani ma ya dauko tambayar sai a samu In wani ma ya dauko tambayar sai a samu
wani ya hana shi dan kar su taba wa angon
feelings din sa. Sometimes kuma su kan
tambaya "wannan gidan na ka ai yafi
wancan girma Gidado, me ya sa ka chanja?"
And shi kuma ya kan amsa musu da cewa
"amaryar ce tafi son wancan". Alhalin ita
amarya ko gain gidan ba ta taba vi ba sai
da masu yi mata jere suka je suka yi suka
dauko mata pictures da videos.
Gidan da za'a kai amaryar mai kyau ne, dan
sosai iyayensa suka nuna masa gata a siyan
gidan kamar yadda suke nuna masa gata a
komai. Part dinsa daban na matar daban
sannan a waje kuma akwai bangaren baki
maza sannan da part din ma'aikatan gida
(boy's quaters). A bangaren sa akwai
bedrooms biyu da parlor, a nata bangaren
akwai bedrooms uku da parlor. Part din
bakin kuma parlor ne karami da dakuna
biyu.
Kamar yadda iyayen ango suka yi kokari
wajen kure adakar su akan gidan Gidado
haka bangaren amarya su ma suka yi nasu
kokarin, dan duk dakunan da suke part dinta
babu inda ba'a cika shi da kaya ba, kaya
kuma na gani na fada wa da suka yi dai dai
kuma suka dace da tsaruwar gidan. Abin har
sai da ya bawa dangin angon mamaki, dan a
binciken da suka yi wa iyayen amarya basu
samu labarin cewa suna da irin wannan
kudin ba,
A bangaren amarya tun a week to bikin A bangaren amarya tun a week to bikin
Mommy ta tafi can Katsina suka cigaba da
kammala shire shiryen su, duk wani shiri da
za"a yi wa amarya na gyaran jiki anyi wa
Safina shi, ita kanta ta san tana da kyau, ta
kuma shirya siye zuciyar angon na ta da
wannan kyan nata da kuma duk kan wata
kissa da kisisina da Allah ya halicci mata da
ita. Ta san cewa akwai challenge a gabanta
amma kuma ta shirya karbar sa hannu
bibbiyu dai har zata samu muradin
zuciyarta. Ta yarda da kalmar hausawa da
suke cewa mahakurci mawadaci.
Mommy tayi mata shirin duk da akeyi na
gyaran amare dan taimaka musu wajen
sauke hakkin aure da zai hau kansu, amma
Mommyn ba ta san cewa ita ma da kanta
Safinar ta gama siyan duk wadannan kayan
har ma da wadanda suka fi na Mommyn. A
shirye take tsaf da yin amfani da dukkan
baiwar da Allah yayi mata wajen ganin ta
mallaki Habibin na ta.
5
+ 1 4:15 PM
anar Lahadi ta tafi garin Abuja. A ranar ne
kuma bayan kiran wayar angon sau ba adadi
kamar yadda ta saba kullum ba tare da kiran
ya shiga ba sai ta tura masa message. "Na
shigo Abuja, Dan Allah ka zo in ganka, Ina
gidan Hajiya" Sakon ya shigo masa ya
karanta ya rufe ya ajiye,
A ranar da ya rage saura five days daurin
aure ne gidan da angon ya ke ciki ya kara. aure ne gidan da angon ya ke ciki ya kara
cika fiye da kullum, yan uwan sa da suka 20
gari suma sun gayyato abokan su da suke
gari, wasu abokan kuma sun gayyato nasu
abokan. Gidan ya zama kamar wani dan
karamin biki ake yi amma na maza zalla.
Mama kuma ta daure musu gindi ta hanyar
aiko musu da kulolin abinci kala kala. Daga
nan sai hira ta balle, aka fara zancen aure da
rayuwar cikinsa da challenges din sa, masu
auren ciki suna baje fasahar experience din
su, yayin da samari suka baje kunnuwa suna
daukan darasi. Wannan ya sa angon ya
zame ba tare da sun sani ba ya fice ya bar
musu gidan. Sai da ya shiga motar sa kuma
sannan ya fahimci bashi da gurin zuwa, dan
duk friends din sa da zai iya zuwa gurin su
suna cikin gidan sa, a lokacin ne sakon
Safina ya sake shigowa. "Na gama abinda
zanyi a Abuja. Gobe aka ce in koma. Dan
Allah ka shigo".
Ya rufe idonsa yana tunani for some
seconds sai kuma ya bude ya kira number
din ta. Tana dauka yace "gani nan zuwa" bai
jira amsa ba ya katse kiran. Mintuna kadan
suka kaishi kofar gidan, mai gadi ya taho da
sauri da fara'a a fuskar sa amma sai Gidado
ya bata rai tare da daga masa hannu alamar
baya bukatar zuwan sa, sai da mai gadin ya
juya sannan kuma sai yaji babu dadi a ransa
tunda mutumin bai yi masa komai ba. Ya
dauko wayarsa ya sake kiranta "ina waje"
yace tare da sake ajiye wayar.
Few minutes sai gata ta fito. Jikinta sanye Few minutes sai gata ta fito. Jikinta sanye
da hijab fuskarta babu kwalliya. Ta bude
kofar gaban motar ta shiga ta zauna, sai ya
dauke kansa yana jin haushin ta zauna a
seat din Safiyya. Amma kuma ai shi ya kira
ta. And only God knows me Safiyya take yi
with her husband, why won't him enjoy
himself too?
Ta fara mishi magana "har na fitar da rai na
dauka ba zaka zo ba. But now I am glad
tunda kazo" ya juyo yana kallon ta fuskarsa
a matukar daure yace "me yasa kike
nemana?" Tana kallon sa tace "what's with
that face? Ko nayi wani laifin ne kuma ban
sani ba, I just wanted to see you kuma
banga abin laifi dan ina son ganin ka ba".
Yace "what's wrong with my face? I thought
ita kika gani kika ce kina so" ta sunkuyar da
kanta kasa fuskarta tana nuna damuwa tace
"na san nina ce ina son ka ba sai ka goranta
min ba. Kawai naga ranka a bace ne. Ni face
din da nayi falling in love with is always
happy always smiling" yace "you better get
use to the unsmiling face. Because you are
going to see a lot of it" suka yi shiru gabaki
daya, sai da aka jima sannan da dago kai
tace masa "dama nazo gari ne zanyi kunshi
da saloon, and da akayi min kunshin sai na
ga yayi kyau sosai, and I thought ya kamata
kai zaka fara gani, I never thought hakan zai
zama laifi".
Yace "are you telling me kin taho tun daga
Katsina zuwa Abuja kawai dan kiyi kunshi?
Duk masu kunshin da suke Katsina ba zasu. Duk masu kunshin da suke Katsina ba zasu
yi miki ba?" Ta dago kai tana kallon sa tace
"actually, na fadi haka ne kawai a gida dan
su barni in taho, Mommy like classy things
and ta san a Abuja zan fi samun taste din ta,
but in reality I just wanted to get away from
her" yayi mamakin jin haka yace "why?"
Tace "fada. Tun da taje Katsina take yi min
fada. She is not happy with this marriage
saboda bata san ka ba, she kept
complaining cewa bata san sanda muka
hadu ba ballantana sanda muka saba har
zamu yi aure. Farko bata kasar, da tazo
cewa tayi sai an daga. Da kyar ta yarda za'a
yi din" tayi shiru tana jujuya hannunta
sannan tace "she said you don't love me.
Tace ko waya bata ga muna yi ba. There is
no love vibes at all".
Ya juya fusakarsa

19 / 113